Subscribe for N1000/month for downloading access and an ad-free site. Contact WhatsApp +2348140419490 if you can't pay / subscribe. SUBSCRIBE

24 yin

USTAZIYA KO YAR DUNIYA Complete Hausa Novel Document by USTAZIYA KO YAR DUNIYA


USTAZIYA KO YAR DUNIYA

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 57925



USTAZIYA KO YAR DUNIYA

Reading Time: 4 Hours

Added On: 15, May 2024

Author: Aunty Mamie ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 329.7 kb

File Type: txt

Views: 1340+

Download: 2682+

Last download: 3 hours ago

Description/Story: Compiled By Umar Dalha Funtua.



🧕🏼🧕🏼🧕🏼
*Ustaziya ko yar'duniya?*🤷🏻‍♀🤷🏻‍♀🤷🏻‍♀


*Dukkan yabo da godiya ya tabbata GA Allah S.W.A daya Kara dawo dani a lokacin da banyi tsammanin Kara dawowa ba kasancewar banida isashen lokacin kaina tun rubuta littafi na na karshe N@g@ TA K@IN@ Wanda akalla yanzu kusan shekara daya koma fiyeda haka, Gani na Kara dawo muku da Takaitaccen labarin da baida yawa Wanda cikin 70% yafaru da gske ina fatan zai amsu a makaranta kamar yanda kuke amsar littafina shima a karbe shi hannu biyu biyu*


*Written by Anty Mamie*

*Dedicated to sister Husnah Amaryar gobe😍*


1


Damko gashin kanta yayi yayinda ya Kara gwara shida bangon bayin a karo na biyu cikin wahalalliyar murya take ihu hawaye masu zafi nabin fuskarta, kazamar banza yar'iska ragowan Gayu Dan ubanki maina gaya miki kafun inbar gidan nan? Juyo da fuskarta yayi yayinda ya daga habarta matse bakinta yayi cikin masifa ya hankado ta wajen bayin saida ta buga kanta da kujerar dressing mirror take kan nata ya shiga zubda jini, kasa jurewa tayi jin azaban take har cikin kwakwalwarta hakan yasa ta Saki ihu tareda tsugunnawa tana murza hannayanta biyu Alamar hakuri, 'Dan girman Allah AK kayi hakuri na tuba nabi Allah nakuma bika mijina ka yafe mun, takowa yayi har inda take yayinda take matsawa baya saboda gudun azabar dazai Kara manna mata, damko gashin kanta yakara yi tareda janta a kasa har bakin gadon dake dakin ya zauna yana ware kafafuwan shi duka biyu, fuskarta datayi jaga jaga da jini da majina yakara dagowa hadeda kai fuskar shi saitin bakinta cikin magana kamar rada "fadi Laifin ki da bakinki ina jinki, hannu yasa yana dangwalo jinin dake bakinta, " yinwa nakeji, 'tafadi dukda sanin yasan da hakan saboda kulle kitchen dinda yakeyi idan ya shirya mata babban azaba.
shiyasa gakuma zazzabin Dana kwana dashi tun shekarun jiya rabona da Abinci....'shiiiiii ya katse ta yana lumshe ido tareda jefa mata banzan kallo cikin kyama, shiyasa kika samu damar kwanciya harda bcci bayan baki gama wanke mun motocina Dana Saki ba?? Shegiya mayya duk uban abincin Danake kawowa gidan nan bakida aikin yi saici kamar jaka, ooh jakar cema na tuna, yafadi yana jijjiga kanshi, jakar titi, jakar maza, u fat for front u fat for back Bakida wani amfani rashin Asali baiyi ba wlh saidai kici kiyi katon kashi kita cika mun Masai da wari koh? Dama abunda yasa kika Aure ni kenan, nikuma baiwa na Auro banga mata anan ba, ya nuna ta da yatsa harda dungure kanta Toh dole ki rage shegiyar kibar nan bazan Gina ma wani kato jikin kiba Danni kozaki kwana kina yawo tsirara baki burgeni so dole kifara rage tsoka Hahahaa yayi dariyar da bata wuce kalma Uku ba, "kinyi karya wlh tunda kika hanani farincikin rayuwata a haka zamuyita Rayuwa a gidan nan babu Wanda zai samu abunda yakeso nida ke sai karyan ustazanci Allah a baki fir'auna a zuciya, yafadi tareda tureta kasa, mayya mai nacin maza mai fuskoki dayawa ugly pig kawai, barin dakin yayi tanajin fitar motarsa daga gidan hakan yasa ta zube a kasan tels din dakin hawaye masu dumi nabin kumatun ta, 'Ashe laifi ne a duniyar mu yin biyyar Aure? Laifi ne tsarkake zuciya tareda Soyyah mai tsafta? Yazama laifi tona asirin zuciyarta?
Cike da nadamar rayuwar Tata ta Mike tana Jan kafarta dayayi mata tsami bayi ta shiga ta sakarma kanta ruwan zafi hadede gasa jikin nata kodata fito man zafi ta nema ta malka ma jikinta bata daddara ba takara bin lafiyar gado a karona biyu dukda tasan kotayi aikin daya sata ko batayi ba saiya samu dalilinda zai Kara jibgarta anjima garata kwanta saiya jibgeta da tushe.

Azabar yinwa neya tashe ta misalin biyar da Rabi na yamma gashi ko sallar la'asar batayi ba dakyar ta rarrafa tayi salla cikin zullumi tareda Addu'ar Allah yasa ya bude mata kitchen din jinta takeyi kamar zata mutu saboda azabar yinwa jiri na dibanta ta dakyar take iya bude idonta daya kumbura fuskar nan tayi suntum tareda dafa bango ta karasa kitchen tunkafun ta karasa ta ganshi a bude wani dadine ya ziyarce ta lokaci daya ta tattaro ragowar karfin jikinta kai tsaye fridge ta nufa tasan bazata rasa abunda zata faraci ba




Ur comment is needed saboda samun kuzarin typing.


Mr's Sadik Rumah💅🏻
🧕🏼🧕🏼🧕🏼
*Ustaziya ko yar'duniya?🤷🏻‍♀🤷🏻‍♀🤷🏻‍♀*

*Written by Anty Mamie*

*Dedicated to sister Husnah, my sister yar'amana Amaryar gobe😍ina yinki kanwata irin totally dinnan😎*

2


Tana budewa tayi ido biyu da ragowar biredi bata damuda sanyin shiba ta barka ledan lodawa takeyi hannu baka hannu kwarya hartana shakewa wurin fanfo ta nufa dukda akwai ruwa burjik a cikin fridge din budewa tayi tareda kafa kanta kamar mahaukaciya ta dinga kwankwadar ruwan Rabi nabin jikinta tana kara tura buredin dukta jika jikinta, saida tafara dawowa natsuwar ta sannan ta dauko Karamar tukunya ta dora ruwan shayi saboda tana bukatar Abu mai dumi a cikin nata, kamar ance ta kalli gefen dirowan kitchen din tayi ido biyu da manya manyan ledoji har guda Uku da farar takarda a kansu, sauri sauri ta karasa wurin
*sakwara da miyar Egusi, ferfesun kaji Dana kan Sa, dankali a soya da kwai, fresh coconut juice da Fruth salad kunun gyada na shinkafa is needed at 8pm.* wani murdawa cikinta yayi kafun kace kwabo ta yarda takardan bayi ta nufa tadunga kwarara amai saida ta amayo duk abunda ta loda tasan dadewa datayi ba abinci shiya jawo mata aman gashi kuma batayi cin hankali ba, cikin hanzari tagama ta gyara wurin kitchen ta nufa tana salati da kwallar tausayin kanta Dora hannuwanta duka tayi akai tareda tarin danasanin komawa bccin datayi, dabata komaba da yanzu taci karfin aikin tunda karfe biyu yabar gidan, da gudu tafito da kansa Wanda yayi kankara dauraye shi tayi dayake ta wanke tsaf sanda aka kawo prejar pot ta dauko nanda nan ta markada kayan miyan dazatai amfani dashi harda na kajin hada komai tayi tana neman agaji wurin Allah tasan yau kashe tane kawai AK bazaiyi ba, sauke ruwan shayin data Dora tayi batashi take ba yanzu yayinda ta Dora kansa din akan gas jawo ledojin daya kawo tayi ta fito da kaji guda biyu GA dukkan Alama Abokan shi zasuzo cin abincin gidan tasan idan Dan tashi ne bayacin girkin ta sai wani ikon Allah, gyara kajin tayi ta hada komai da komai ta Dora, kallan lokaci tayi taga shida harta gota nan takara rikicewa tunowa datayi har sakwara zatayi ga firan dankali🙆🏻‍♀😭 Ga kunun gyada dukda sunada soyyar markadadden gyada a fridge tana tanada saboda irin hakan, but aikin yamata yawa koda yake dama jakar shi ce kamar yanda yake cewa, haka taita aikin sauri sauri har tana konewa damai a hannu wurin soya dankali saboda rawan jiki bata damuda azabar dazata Shaba akan tijarar dazai mata a gaban Abokan aikin nashi, dukda ba bakon Abu bane suma a wurinsu duk Wanda mijinta ke kawowa gidan yana sane da cewa batada bambanci da banza, daza'a iya shiga kwakwalwar kanshi a shiga tunanin shi sauron🐝 dake yawo a gidan yafita muhimmanci Kota banza zai hanashi bcci da kuka, kallon lokaci tayi taga takwas saura kwata ko magrib batayi ba salati ta saka Dan sai a lokacin zata daka sakwara dukda tagama komai miyar neya rage ta karasa da coconut juice din, tana cikin dakawa taji dawowar shi gidan tareda hayaniyar mutane Alamar bashi kadai bane kamar yanda tayi zargi.
Cikin mintunan da basu wuce biyar ba taji taku Alamar za'a shigo kitchen din yayinda take kulla sakwaran a Leda dukta hada zufan gajiya, 'kallon kitchen din yakeyi a wulakance yayinda zuciyar shi ke Kara suya ji yakeyi kamar ya fusge tabaryar dake gefenta ya sata a turmin yaita kirbata Kila zai huce takaicin data sakashi
Naa...naaaa kusan gamaawa bari infara jera abincin a Dinning, tafadi cikin rawan jiki baiko ji karshen maganar Tata ba banda ta raina shi tun yaushe yabar gidannan? Lallai rainin nata gaba gaba yakeyi shikenan bai isa da gidan shiba? Mai Aisha take nufi Dashi? Laifin shine data fara ganin gadon bccin shi shekara Uku da Auren su amma har'yau bata bin umarnin shi? Komawa yayi tafkeken parlon nasu inda yabar bakin nasa su shida, Abincin data gama tafara jerawa akan dining table dinsu yayinda takoma kitchen domin jiran miyar Egusin yakarasa.
Domin cigaba da karantawa sai ku downloading.
Yadda ake downloading na littafin: ku tabbata kunyi register da shafinmu sanna kunyi login, idan bakuyi register a kasa zakuga maballai guda biyu daya an rubuta LOGIN dayan kuma an rubuta REGISTER sai ku taba su kuyi register, daga nan sai ku yi subscription koda na naira 1000 ne, domin sai kunyi subs dinann ne kadai zaku iya dauko littatafanmu.

Ya ya akeyin Subscription namu : Bayan kun yi Login ko register daga kasa zaku ga wani jan maballi (button) an rubuta SUBSCRIBE sai ku taba shi zai kaiku inda zaku zabi package wato tsarin subs na ku da mu. akwai na wata guda, watanni biyar da shekara guda. da zarar kun zaba zai kaiku inda zaku biya kudin, wanda daga nan sai ku cigaba da downloading kawai abunku

ABUN LURA : duk wani littafi da kuka gani a shafinnan kyauta ne, wannan tsari mun zo da shine don mu samu hanyar da zamu iya rike shafin muna managing na shi, izan ku kayi subs na mu tamkar DONATION ne ku ka yi mana, ku ka bamu kwarin guiwa don mu ciagaba da kawo muku sabbin littatafai, amma duk wanda ya ga bazai iya ba toh zai iya karanta littafin kyauta a cikin shafinnan namu batare da ya downloading ba, kawai ya yi kasa zai ga Koren maballi (button an rubuta) START READING sai ya taba zai kaishi inda zai karanta littafin.

Sannan duk wanda yaga kamn wannan process din zai bashi wahala kai tsaye zai iya min magana ta whatssApp +2348140419490, ya tura min kudin ni kuma zan dora mai subs din akan account na shi

NB: iya ta haka ne zaku iya karanta wannan littafi a shafinmu babu wata hanyar. DAN ALLAH KU DAINA MANA MAGANA AKAN MU TURA MUKU LITTAFI TA WHATSAPP, BAMA TURAWA HANYA GUDA MUKE TURA LITTATAFANMU SHINE WEBSITE NA MU https://taskarnovels.com.ng DUK MAI BUKATAR LITTAFINMU YA JE CAN YA KYAUTA NE, AMMA DOWNLOADING KUWA BA KYAUTA BANE SAI YAYI SUBSCRIPTION NA WEBSITE NAM
This is not the real Download Button


Read / Download USTAZIYA KO YAR DUNIYA

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

This is not the real Download Button
Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album