Subscribe for N1000/month for downloading access and an ad-free site. Contact WhatsApp +2348140419490 if you can't pay / subscribe. SUBSCRIBE

24 yin

ZUMA A BAKI Complete Hausa Novel Document by ZUMA A BAKI


ZUMA A BAKI

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 58237



ZUMA A BAKI

Reading Time: 4 Hours

Added On: 07, Jul 2024

Author: Autar Manya ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : HOME OF QAULITIES WRT ASS

Author Phone : 08142105218

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 319.26 kb

File Type: txt

Views: 848+

Download: 1145+

Last download: less than 1 second ago

Description/Story: *ZUMA A BAKI...!*🌹
    {  Painful love Story  }
           

         NA
*AUTAR MANYA*

_HOME OF QAULITIES WRT ASS..._

_Bisimillahir Rahamanir Rahim dukkan yabo da godiya sun tabbata ga sarki buwayi gagara misali Allah mai saman bakwai Allah mai ƙasan bakwai Allah mai rufin asirin bayinshi, Tsira da amincin Allah su ƙara tabbata ga shugaba jagaba annabi muhammad s.a.w Amin, Alhamdulillahi ya Allah daka kuma dawo dani acikin wannan sabon littafin bayan na kammala AUREN BARE lafiya Allah yadda na soma lafiya kasa na gama lafiya kai riƙo da hannayena Allahumma Amin_

_My fans yauma gani tafe da sabon littafi mai cike da sabon salo, ina roƙon ubangiji daya baku iko tare da ƙarfin biyoni acikin wannan labarin Amin summa Amin_

_Gargaɗi wannan littafi mai suna a sama labarin ƙirƙirarre ne daga gareni ban yarda a juyamin shi ta kowace sigaba wanda yaga yayi dai dai da tasa rayuwar yayi haƙuri akasi aka samu amman labarin tsararre ne daga wajena_

                        *001*

GARIN KANO
_Ɗorayi Unguwar Bello_

Cikin lokaci ƙalilan na kammala shirina cikin shuɗiyar atamfa mai ratsin ja' ajikinta senai amfani da jan mayafi mai adon stone mai yawa ajikinsa, jakata na ɗauka mai kalar ja itama senai amfani da jan takalmi kasancewar kalar fatar jikina baƙa ce shiyasa wannan jar kalar dana ratsa cikin shigata taimin masifar kyau.

Kallon agogon dake cikin ɗakinmu nayi da sauri na waro idanuna waje har ina ɗan jan numfashi tare da saurin ɗaukar lesson plan ɗina nai gaba har ina haɗawa da ɗan gudu-gudu kaɗan sabida ganin lokaci yana ja kada nai latting zuwa makarantar danake koyarwa.

Abakin ƙofa na tarar da anisa ƙanwata ta uku tana faman waya wadda daga gani da saurayinta takeyi, dan naga se faman kashe idanunta take tana faman ƙasa da murya, tana ganina ta miƙe da sauri har tana ƙoƙarin yarda wayar hannun nata, tana cewa, "YAYA HUMAIRAH' har kin fito kenan?"  ina tafe ina ɗaura agogo a hannuna na ce mata "eh! anisa sena dawo ina Anty take?"   "tana can cikin ɓangaren Baffa ƙarami wajan ganin lefen sadiya, "tom idan ta dawo kice mata na tafi school amma ta duba saman madubinta zan aje mata kuɗin cefane"   "tom anty ALLAH ya kiyaye hanya" aƙasan leɓena na amsa mata da amin sannan na saka kaina nai gaba abina.

Da ƙyar na sami abin hawa zuwa cikin unguwar ciranci domin anan makarantar danake koyarwar take kasancewar tsakanin mu da ɗan tazara kaɗan, gashi makarantar private school ce sam basa yarda da yin latti ko kaɗan dan yanzu kace zaka makara se anemi korarka shiyasa iya yina nike domin  ganin na kare mutuncin kaina wajan mai makarantar dan kada ta cimun mutunci kamar yadda naga tanai wa sauran staff ɗinsu danni kam bata taɓa min ba dan ba makararar nikeyiba.

Duk da haka ban samu shiga da wuriba se wajan ƙarfe taran safiya na ƙarasa, da sauri na zaro naira hamsin cikin jakata na baiwa mai ɗan sahun tare da nufar cikin gate ɗin cike da kuzarin jiki.

Abakin office ɗin da muke singh na tsaya tare da zaro biro daga cikin jakata na nufi cikin office ɗin, da sauri najawo singh book din dake kan teburin na fara yin singhning ɗin sunana, ina kammalawa na ɗago idanuna haɗa idanu mukai da malamar english cikin far,a tace  "a,a yau malama Humairah nake gani da ranar nan haka hala ko lafiya dai?" murmushi na ƙago akan fuskata tare da cewa "wallahi makara nai bara na ƙarasa aji" na faɗa yayin danake mayar da birona na nufi cikin makarantar ɓangaren ajin danake koyar dasu darasin social studies,

Cikin ladabi ɗalibaina ke gaisar dani har na aje jakata akan tebur nan nafara binsu ina duba aikin dana basu na ɗauki kamar minti goma ina faman yin abu guda kafin na kammala na koma wajan zamana tunda tsarin school ɗin na teacher par class ne, cikin haka naga masinger dake aiki a office ɗin shugabar makarantar yazo aguje cikin rawar jiki yake sallama cikin ajin danake.

Ƙarasawa nai gabansa cikin mutuntaka muka gaisa dashi sannan na dubesa tare dace masa "masinja lafiya dai?"   "eh! lafiya daman ranki shi daɗe ce keson ganinki"   "ni kuma?" nafaɗa ina mai nuna kaina da yatsana guda tare da waro idanuna waje asual, "eh kefa malamar primary one koba malama Humairah Yusuf bace?" yafaɗa yana mai kallona, "eh nice jekace ina zuwa" da sauri ya juya nima komawa nai cikin ajin na dauki wayata batare dana dauki jakata ba na nufi cikin office ɗin mai makarantar.

Cikin ladabi muka gaisa da matar wadda waɗansu malaman ke mata kallon marar mutunci amman nikam bandani tunda bata taɓamin ba ko sau ɗaya,  da far,arta da komi ta karɓeni harda cemin ga waje na zauna bayan na zauna ne ta dubeni sannnan tace "malama Humairah ya akai yau kika makara keda bamu saba ganin hakan daga garekiba?"  cikin jin kunya na dubeta tare da cewa "dan ALLAH kiyi haƙuri insha ALLAH hakan baze kuma faruwa ba wallahi yau ɗinma akasi aka samu" murmushi ta ƙago kafin tace shikenan  babu komi tashi kije ALLAH yay maki albarka.

Sannan dan ALLAH idan babu damuwa kizo ranar juma,a ki karɓi addiress ɗin gidana ina son ganinki ranar asabar tunda babu school sabida da akwai maganar danike son yi dake.

"Babu damuwa nagode ALLAH ya nuna mana lokacin"   na faɗa ina mai tashi tsam na fita daga office ɗin.

Harna koma class ina tunanin wannan wani magana ce da shugabar makaranta bazata gayamin ba harse na je gidanta, nifa bana son irin wannan shige-shigen sam duk da kasancewarta matar ƙanin umma matar baffa ƙarami ƙanin mahaifina amman sam har yanzu ban ko taɓa zuwa gidan taba duk da irin faɗan da umma takemin na rashin ziyarar dangi.

Ƙarfe ɗayan rana na mike tare da nufar masallaci salla nai tare dayin addu,a akan lamarina ubangiji ya isar min yay min maganin matsalata wadda take addabar zuciyata.

Ina idarwa na koma class na dauki jakata ganin lokacin tashin yaran yayi sallama nai masu tare da nufar gate  batare dana sha wata wahalaba na samu mai ɗan sahu nai masa kwatancen anguwarmu tare da shiga cikin adai daitan na zauna gaba ɗaya wata mahaukaciyar yunwa nikeji acikina sabida ban ko karya ba na fita duk yadda anty da umma ke min faɗan yunwa amman sam bana ji shiyasa in ulcer ɗina ta motsa min sena dangana da asibiti.

Cikin mintuna goma mai napep ɗin ya kaini ɗorayi kasancewar layinmu da ɗan tazara da titi yasa na soma takawa da ƙafafuna duk jikina agajiye haka nan hannuna ya ƙage sabida nauyin jakar dake hannun nawa.

Tun daga farkon layinmu naga dan dazon matasan layin dama sauran da bana layin ba sunyi zaman jarabar kamar yadda na saka musu sabida yawancin su rashin aikin yine kan sakasu wannan zama domin inda suna da aikin yi da bazasu zauna zaman jarabar saka idanu ba, domin babu abinda ake a wannan majalissar face tsageranci da rashin daraja wasun suma kan ɗan taɓa shaye-shaye a wurin domin nakanji warin hayaƙi na tashi inna zo wucewa.

Sosai na haɗe raina tamau na kame jikina waje ɗaya kaina sunkuye haka nazo gab da su zan gifta araina nake ayyana da ranar Allah amman bazasu huta ba.

Sautin dariya naji daga bayana kafin naji fitar sautin ɗaya daga cikin samarin wajan.

"Waini kam B.smoll wannan ba tagidan su ƙwaro bace?"
Ina jin wanda aka kirawo da b.smool ɗin yace.
"Sosai ma ai yayar ƙwaro ce ƴar gidan yayan babansa ce shegiya mai baƙar fuska se uban girman kai kullum haka zaka ganta kamar ta faɗi, ita bata yarda ba ƴar boko, se tsabar baƙin jini duk ƙannenta sunata ɗagawa amman ita har yau babu wanda ya taya"
Banji abinda ɗayan ke cewa ba na ƙarasa gaban gidanmu.

Dab da zan shiga xauren mu naji hayaniyar su na tashi.
"Se OGA CIKA DAJI"
Haka naji majalissar tasu ta kaure da faɗi wanda sautin muryarsu tayi dai dai da sautin bugun zuciyata...............



SANNU SANNU..................✊

*ZUMA A BAKI...!*🌹
{ Painful love Story }


NA
*AUTAR MANYA*

_HOME OF QAULITIES WRT ASS..._

*002*


Da gudu na ƙarasa shiga zauren gidan namu sabida yadda numfashina yake ƙoƙarin ɗaukewa.
Cikin sauri na faɗa tsakar gida kamar wadda aka jefa ina shiga nai ɗakinmu tare da banko ƙofar na zauna turus a bakin gado ina mayar da numfashina dake barazanar ɗaukewa hawayen da suka sami zarafin zubo min a yanzu sunake saka hannu ina gogewa.
Cikin dakakkiyar muryarshi mai cike da amo!
Yake doko sallama tsakar gidan namu kafin naji sautin
Domin cigaba da karantawa sai ku downloading.
Yadda ake downloading na littafin: ku tabbata kunyi register da shafinmu sanna kunyi login, idan bakuyi register a kasa zakuga maballai guda biyu daya an rubuta LOGIN dayan kuma an rubuta REGISTER sai ku taba su kuyi register, daga nan sai ku yi subscription koda na naira 1000 ne, domin sai kunyi subs dinann ne kadai zaku iya dauko littatafanmu.

Ya ya akeyin Subscription namu : Bayan kun yi Login ko register daga kasa zaku ga wani jan maballi (button) an rubuta SUBSCRIBE sai ku taba shi zai kaiku inda zaku zabi package wato tsarin subs na ku da mu. akwai na wata guda, watanni biyar da shekara guda. da zarar kun zaba zai kaiku inda zaku biya kudin, wanda daga nan sai ku cigaba da downloading kawai abunku

ABUN LURA : duk wani littafi da kuka gani a shafinnan kyauta ne, wannan tsari mun zo da shine don mu samu hanyar da zamu iya rike shafin muna managing na shi, izan ku kayi subs na mu tamkar DONATION ne ku ka yi mana, ku ka bamu kwarin guiwa don mu ciagaba da kawo muku sabbin littatafai, amma duk wanda ya ga bazai iya ba toh zai iya karanta littafin kyauta a cikin shafinnan namu batare da ya downloading ba, kawai ya yi kasa zai ga Koren maballi (button an rubuta) START READING sai ya taba zai kaishi inda zai karanta littafin.

Sannan duk wanda yaga kamn wannan process din zai bashi wahala kai tsaye zai iya min magana ta whatssApp +2348140419490, ya tura min kudin ni kuma zan dora mai subs din akan account na shi

NB: iya ta haka ne zaku iya karanta wannan littafi a shafinmu babu wata hanyar. DAN ALLAH KU DAINA MANA MAGANA AKAN MU TURA MUKU LITTAFI TA WHATSAPP, BAMA TURAWA HANYA GUDA MUKE TURA LITTATAFANMU SHINE WEBSITE NA MU https://taskarnovels.com.ng DUK MAI BUKATAR LITTAFINMU YA JE CAN YA KYAUTA NE, AMMA DOWNLOADING KUWA BA KYAUTA BANE SAI YAYI SUBSCRIPTION NA WEBSITE NAM
This is not the real Download Button


Read / Download ZUMA A BAKI

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

This is not the real Download Button
Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album