Join Our WhatsApp Group

RANA DAYA Complete Hausa Novel Document by RANA DAYA


RANA DAYA

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

DOWNLOAD

Uploaded by @Taskar

Total Words: 269745



RANA DAYA

Reading Time: 22 Hours

Added On: 08, May 2023

Author: Miemiebee ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 1.44 mb

File Type: txt

Views: 2632+

Download: 3084+

Last download: 2 days ago

DOWNLOAD
Description/Story: [12/08, 22:25] ‪+234 907 483 8352‬: 🎀🎀🎀 🎀🎀🎀
🎀❣🎀
❣❣

💦💦 🍃🍃🍃
*RANA D'AYA!*
💦💦 🍃🍃🍃

_Written by Miemiebee👄_


_Assalamu Alaikum beautiful people, it's been a while, yes I know but here I am again with a different storyline. I would first of all like to thank and appreciate our mom, sister and a friend AUNTY SIS for everything she's been through for me all these time, know that am ever grateful._
_Then to my sister, SADNAS who's been a true ally, thank you for supporting me dearly and helping me come up with this story name, I love you_
_Lastly, to all my fans around the globe, my whatsapp group members in particular thank you for supporting me always I love y'all fisabilillah, happy reading!_


*PAGE 0⃣1⃣*


_Prime Lodge And Apartment hotels and suits - 1 Abba Kyari Abba Kolo Street Off Circular Road GRA Maiduguri, Borno state._

1:24pm

Samari ne guda biyu masu jini a jik'a wanda baza su wuce k'imanin shekaru ashirin da hud'u zuwa shida (24-26) ba, (kyawawa masu ginannen jiki.) Zaune suke bisa d'aya daga cikin teburan dake cikin restaurant na cikin Prime Lodge And Appartment hotels and suits suna fuskantar juna a yayinda kowanne ke da plate na fried rice had'e da co slow da kaza a gabanshi se kuma Schweps a gefe. Abincin nasu suke ci hankali kwance babu wata damuwa tattare da su. Kallo d'aya mutum ze musu yasan cewa ma'aikatan banki ne saboda corporate dressing da suke sanye da ita. Wanda ya kasance me haske sosai, mafi kyawu da kuma k'iran jiki yana sanye ne da sky blue long sleeves shirt with a red tie a yayinda d'ayan kuma ke sanye da white long sleeves shirt da black bow tie, duka da black pantsuit a yayinda suka mak'ala suit jacket nasu a jikin kujerun da suke zaune akai.

D'aya daga cikin wayoyin da suke kan table d'in ne ya shiga ringing, kyakkyawan ne yayi yunk'urin motsawa nuna alamun cewa wayarsa ne kenan. Drink nasa da yake zuk'a ya ajiye gefe guda sannan ya lek'a screen d'in ringing phone d'in wanda ya kasance iphone 7 plus jet black don ganin wake kira dum! Yaji zuciyansa ya buga. 

"F*ck!" Ya fad'a a cike da tashin hankali a murya chan k'asa-k'asa.

"Triple A lafiya?" Abokin nasa ya tambaya immediately, yana mey maida hankalinshi sosai wajen abokin nashi da tashin hankali ya bayyana karara a fuskansa yana me goge hannunsa jikin wani brown multicolored hanky yayin da yake da aniyar daukar wayar. "Old man ne wallahi ya kirani d'azu da muke meeting gashi na manta shaf in kirashi bayan da muka gama" ya amsa sa da sauri gudun kar wayar ta tsinke. Swiping yayi ya d'aga tare da maqalashi a kunnenshi.

"Uhm uhm" yayi gyaran murya tare da fad'in "Halo Abba?" cikin sweet husky like voice nasa wanda there's no doubt duk macen data kasance tana saurara dole ne ta tsinci kanta acikin wani yanayi. Murya ne da ke kwantar da hankalin me sauraronsa a yayinda yake sa ka mance duk wani damuwan da ke tattare da kai. Murya ne da ze iya sa bugun zuciyan mutum ya har6a, duk ba don komai ba se don coolness da calmness da take d'auke dashi.

"Prince?" Cewar Abba daga d'ayan 6angaren.

"Na'am Abba am sorry wallahi kai na ne yayi zafi kuma na manta in kiraka lokacin dana fito, I was in a meeting da ka kira d'azu" yayi mai bayani cike da biyayya.

"Oh haka ne? Nace kana ina ne?"

"Yanzu ina Prime Lodge ne ina cin abinci" ya amsa a takaice yana me duban rolex agogon da ke d'aure a tsintsiyar hannunsa.

"Alright ina buk'atan ganinka please as a matter of urgency" ya sanar dashi yana mey jaddada masa mahimmancin kiran.

"Sure Abba gani nan tahowa right away."

"Toh seka zo, Allah ya kare" daga haka yayi hanging tare da miyar da wayan kan table din "Huh!" Ya sauke nauyayyar ajiyar zuciya da ta ja hankalin abokin nashi.

"Guy how far? You seem tensed?" Tambayar abokin.

"It's Abba" ya amsa sa a kasalance yana me nazari.

"Mai ya faru da shi?" Abokin ya kuma tambaya determinately yana kai cizo wa cinyan kazan da yake riqe dashi.

"Nima ban sani ba kawai de something smells not right don daga yadda yake magana mutum zesan da akwai wani abu a k'asa and I've got to find out" ya k'arasa tare da miqewa wanda hakan ya bawa mai rubutu daman k'arewa tsawonsa kallo, ba shakkka tsayayyen na miji ne don kuwa ko ba a auna ba ido ya nuna he'll be nothing less than 6ft height. Damn!

"Abincin naka fah? Bazaka k'arisa ba?" Yayi saurin tambaya.

"Kiran mahaifi fa Sultan? Kuma baka san me ake nufi da urgently bane? Urgently fa yace yake nema na I have to go, here" ya tsaya tare da zaro black wallet nasa na gucci dake cikin pantsuit nasa "Pay for those" ya sanar dashi tare da ajiye N4,000 akan table d'in ta gefen Sultan.

"Toh se yaushe kuma?"

"Kai dai ka k'ware a wajen tambayar silly questions" ya amsa shi yana juya ido "Of course gobe mana ko ka manta yau Wednesday ne gobe akwai office kuma ina da meeting?"

   "Whatever!" Sultan ya amsa tare da jan k'aramar tsuka. Afzal be sake yi ta kansa ba ya shiga tattara assets da gadgets nasa then lastly suit nasa dake rataye jikin kujeran, ya6awa a hannunsa yayi sannan kaman yadda ya saba tafiya a hankali cike da k'asaita ya shiga takawa har ya fice daga building d'in ya shiga nufan inda yayi parking motarsa k'irar Genesis G80 dake jet black in color wacce tasha wanki k'al.

    Bud'e k'ofan gaba yayi ya jefa suit d'in a baya tare da miqa sauran abubuwan da yake riqe dasu a passenger's seat sannan ya tadda motar. Reverse yayi ya fita daga cikin harabar hotel d'in. Beyi nisa ba wayar sa dake jikin hanger ya shiga ringing ganin Abba ke kira again yaji gaban sa ya kuma bugawa wai me ke faruwa ne? Ya tambayi kansa. Ba tare da 6ata lokaci ba ya shiga neman car blutooth nasa wanda ke taimaka masa gun amsa waya ta hanyan sauqi ba tare da hankalinsa ya rabu ba a duk lokacin da yake tuk'i. A chan k'asar motan ya samu, be hankara ba yana d'aga kansa kawai yaga ya ma bar kan kwalta gabad'aya ya na nufan kan wata yarinyan da bazata wuce kuma baza ta gaza shekaru sha takwas (18 years) ba dake tsaye some meters away from him ta bud'e baki wide open in shock kawai tana jiran aikin gama ya gama; tsabagen yadda ta tsure ko motsawa takasa yi don ku6utar da kanta daga aukuwan wannan mumunar had'ari. Sanye take da baby pink color hijab me silky feel wanda ya mugun tafiya da golden skin color nata dake nan kaman irin na sudanese girls d'innan. Tana rik'e ne da manya-manyan ledoji da alama daga kasuwa take tayo siyayya da cefane. Ba shiri ya shiga neman inda brake nasa yake da niyyan takawa don hana aukuwan wannan had'ari dake neman afkuwa sede shima don yadda ya tsure ya ma rasa a ina brake d'in yake, ya juya sterring ma duk dabarar bata zo mai ba.
Kafin ya samu kan brake d'in ya taka ina aikin gama ya gama har ya buge 'yar yarinyan da tuni ta zube a k'asa sede Alhamdulillah a nan Allah ya tsaida abun, Allah beso ya hau kanta ya tattake ta ba. Bonnet d'in ne ya bugeta ta gun k'afarta wanda hakan yayi sanadiyyar sum6ulewar ledojin dake hannunta na fashewa suka fashe na zubewa suma suka zube sukayi d'ai -d'ai a k'asa.

Wani wawan ihu ta k'urma kasancewan wannan ne karo na farko da mota ya ta6a bugeta a tarihin rayuwarta. Wallahi duk bakin Mami ne (mahaifiyarta,) abinda ta soma cewa a ranta kenan. Saida Mami tace mata tabari se yamma yayi taje aiken amman ta dage ita inba yanzu ba bazata je ba, toh ai ga irinta nan, abinda babba ya hango yaro koda ya hau kan tudu ba lalle ne ya gani ba.

Ba shiri mutanen da suke kusa duk suka yo kanta. Salati kawai Afzal yakeyi acikin motar har izuwa lokacin da ya fito yayi kan yarinyan dake ta shar6an ihu har yanzu wane wacce ake zare ma rai.

"Wayyoo ya karya min k'afa ya kasheni Mami! Kizo ki taimakeni" se ihu take tana salati. Kanta Afzal yayi da sauri tare da tsugunawa gabanta, k'afan nata data rik'e take ta ihu a yayinda yake mata zok'i ya aza hannunsa akai don duban ko taji mummunan rauni. Hannunsa na kaiwa akan jikinta baiwar Allah tayi tsit mutum na iya rantsewa liqe mata baki akayi. Tunda take a rayuwarta, a duk tarihin rayuwarta d'a na miji banda Papi (kakanta) be ta6a ta6a wani sashi a jikinta ba inba yau ba, idan an ta6ata toh a hannu ne wanda hakan ke faruwa a garin miqa ma wani abu ko makamancin hakan. Ko a secondary school saida akayi mata shedan hakan, har ya kaiga classmates nata suna kiranta da ustaziya suna mocking nata da sunan 'yar mallam.
Shikenan yau nata ya k'are zatayi ciki, dama tunda ta fara menstral flow nata Maami tace mata duk sanda ta bari wani d'a na miji ya ta6ata toh zatayi ciki ranan, yau tana cikin wani yanayi. Wani irin d'an banzan ihu fiye da wad'anda take tayi tun d'azu ta saki, Afzal besan lokacin da ya sake ta ba ya shiga toshe kunnensa. Wannan wane irin mugun ihu ne! Yayi tunanin haka a cikin zuciyarshi.

    A rayuwa idan akwai abinda ya tsana shine hayaniya kasancewar be saba da shi ba, shi kad'ai ne d'a a gun iyayensa. Baida yaya bale k'anin da ze tak'ura wa rayuwarsa, gidansu kullum tsit daga shi se Abban shi se Umminsa da kuma masu aiki.

Kunnensa ya shiga murzawa a tunaninsa ma ya kurmance ne. Sleepy like eyes nasa that are surrounded by long thick eyelashes ya d'ago yana kallonta cike da mamaki shin how is it possible ma ace mutum nada irin wannan murya me uban k'ara haka? To his ultimate dismay kawai yaga itama kallon nasa take ko kyaftawa babu.

Ta fannin ta kuwa tana iya rantsewa tunda tasan kanta inba a TV ba bata ta6a ganin kyakkyawan na miji kaman wannan dake tsugune a gabanta ba it became impossible to even blink. Shima kallon nata ya tsaya yi badan komi ba kuwa se domin tayi mai kama da wani wanda ya sani sede ya kasa tuna a ina. Sun d'au tsawon lokaci suna kallon juna, kowa da abinda yake sakawa a cikin zuciyarshi, daga bisani yarinyar ta kawar da kanta tare da kuma k'urma wani ihun da ya tsoratar dashi har yana neman tuntu6ewa.

     "My goodness!" Yayi exclaiming a firgice anya kuwa ba aljana ya buge ba? Ya soma tunanin hakan a ransa.
"Wayyo bawan Allah ya karya min k'afa! Jama'a ku taimakeni!" Tasa kuka tana ta matse 'yar k'wallan da ya ciko mata a ido.

"I'm sorry" ya fad'a a kid'ime don ko gabad'aya ta rud'ar dashi saidai wane k'ara yace mata. "For heaven's sake kiyi hak'uri haka kibar kukan nan!" Ya sanar da ita a tsawace. Shi kansa besan lokacin da ya fusata ba. Saboda ta fara bashi haushi matuka, gashi de ya duba k'afan nata da take ta kururuwa mai bega wani ciwon arzikin da taji ba banda 'yar k'urzine guiwanta da tayi maybe sed'an internal pain wanda baza a rasa ba. Then mesa take mai ihu tana cika mai kunne haka? Bata san cewa ya tsani hayaniya bane musamman na shirme mai k'ara da ihu irin wannan nata?

Shiru tayi tana kallon sa cike da mamaki na matuk'a lallai kuwa ya cika d'an halas. Ma tukuna bai da kunya tayi tunanin hakan. Na farko ya bugeta ya karya mata k'afa ya sanya mata asara kuma ya tsaya yana mata masifa? Na biyu kuwa mamakin ya za'ayi muryan na miji ya kasance da irin wannan dad'i da sanyi take. Bata ta6a jin murya irin nasa ba, tana iya rantsewa muryansa yafi na duk wani mahaluk'in data sani dad'i. Masifa yake amman yadda kalamun nasa suke slipping daga pink full inviting and perfect carved lips nasa yasa tama manta inda take da kuma inda ke mata ciwo. Ganin kallon da take mai bana k'arewa bane ya sashi feeling guilty, baida right na mata masifa, does he?

  "Look am sorry but dan Allah ki dena mun wannan ihu haka and kibar kukan, yi hak'uri zan kai ki clinic su duba ki" kafin tayi magana wani mutum ya riga ta.

   "Mallam kayi sauri mana kayi wani abu ko se lokaci ya k'ure tukuna zakayi abinda ya kamata?" Ya tambaya yana tsaye a kansu.

    "I can handle this please duk kuna iya tafiya, ni na bugeta nasan abinda ya dace inyi, bana buk'atar wani ya gaya mun abinda zanyi so kuna iya tafiya" ya fad'a more like a command. D'aya bayan d'aya suka shiga watsewa ya rage daga Afzal se wannan drama queen dake ta faman kukan shagwa6a tun d'azu.

   "Ke bakiya jin hak'uri ne kam?" Ya tambaya girarsa a murtuk'e yana me dawo da kallonsa a gareta like ta fara bashi haushi.

"Ban sani ba" ta murgud'a mai baki cike da rashin kunya "Wallahi ni gida gun Mami na zaka kaini...


Read / Download RANA DAYA

DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

DOWNLOAD
Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album