Join Our WhatsApp Group

TAGWAYEN MAZA Complete Hausa Novel Document by TAGWAYEN MAZA


TAGWAYEN MAZA

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 22786TAGWAYEN MAZA

Reading Time: 1 Hours

Added On: 06, May 2024

Author: fertymerh xarah ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 126.24 kb

File Type: txt

Views: 167+

Download: 58+

Last download: 19 hours ago

Description/Story: [4:33pm, 10/6/2016] Fatyma Zahra Too Nv: Fertymerh Usman > fertymerh xarah novels
1) TAGWAYEN MAXA
Na fertymerh xarah
A hankali cikin nutsuwa ta kutsa kanta cikin
dakin, acan ta tsinkayota kishingide ta isa
gefenta ta tsugunna
tace na kammala momy duka na jera a dianing
tace kije ki sanarwa yan biyu sufito suci abinci
jikinta a sanyaye ta tashi tana fadin tor
shikenan,ta fito ta nufi sashensu duk jikinta ba
kwari
part din Hussien ta fara xuwa tayi sallama ta
shiga falonsa
acan ciki ya amsa ba tare da ya juyo ya kalletaba
tace momy tace kufito an kammala komai,
yace kingayawa hassan ne
sai da gabanta na fadi ta girgixa kanta tana
kallonsa shima ita yake kallo
2
Tace dan Allah kaje ka gayamasa ko naje baya
saurarena, ya tashi yana fadin i knw jeki kawai
xamuxo
ta juya ta fice xuciyarta wasai dama sashen
hassan ne bata qaunar xuwa a rayuwarta.
Tana mopping a falo duk suka shigo jere da juna,
kamar kullum xaka ga kayansu iri daya colour ce
kawai banbanci, komai nasu xai xama iri daya
bnda kala saboda halinsu bai xo daya ba yan'biyu
ne amma kowa da ra'ayinsa musamman a wurin
kala
tana ganinsu ta kawarda kanta gefe tana cigaba
da mopping amma dan tsabar mugunta hassan
sai da yabi ta gefenta ya taka mata qafa da
takalminsa
ta rumtse idanuwanta saboda axabar da taji ,duk
falon ba wanda ya kula da abinda yayi mata hr
yaje ya xauna, taja qafar ta cigaba da mopping
din
3
Asalin lbrn Hassan da Hussien ya'ya ne ga Alhaji
Ahmad da Hajiya Amina
shekara biyar da aurensu basu sami haihuwa ba
sai daga baya inda ta sami cikin twins,
cikin nada wata bakwai Alhaji Ahmad ya rasu
batare dayaga burinsa da farincikinsa ba
[11:29AM, 11/5/2015] Pherty: momy tayi baqin
cikin haka sosai saboda duk gatansu da arxikinsu
sun tattara sun dora akan cikin sai gashi burin
mahaifinsu bai cika ba h lokacin da aka haifesu
momy ta cigaba da kula dasu sosai tabasu
tarbiya gwargwadon iyawarta hr lokacin da suka
girma ta turasu waje karatu
Yan biyune sun taso gida daya komai daya
basuda bancin a gun ahafisu sai dai halayya da
aqidarsu ta banbanta
Hassan mutum ne daya fiye tsanda da kyankyami
musamman akan talaka ko a skul idan baka
kasance dan mai kudin gske ba baya qawance
dakai
kuma shi mutum ne miskili dabai fiye hayaniya ko
shiga mutane ba haka abu mai wuya ne kaganshi
yana murmushi ko dariya,ba qaramin abu kesashi
hakan ba,
sannan duniya bashida wani buri kamar chtng,
olways on chtng bai dauki karatunsa da daraja ba
kamar ynda ya dauki chtng,ga wata muguwar
dabi'a dayake a boye ta shaye shaye inba
hussien ba ba wanda yasani a family dinsu sai
mai aikinsu
Hussien kuma Allah yayisa a faraa da tausayi shi
kowa nasane koda yaushe fuskarsa na dauke da
murmushi illah abu daya daya bata halinsa
neman mata, shima kansa mahaifiyarsa duk
batada wannan lbr sai mai aikinsu
Amma a tsakaninsu idan gefen ibada ne ba gwani
domin basa wasa da sallah ko karatun qur'ani da
sauran littafai hrma hussien yakan xaunar da mai
aikinsu yana koya mata wani abun, amma da
hassan ne sai dai ta bushe a xaune tunda suka
dawo gida nigeria mgn bata taba hadasu ba
4
Hassalima da badan taxamo mai kula dasuba
ynda yakeji da kansa tasan bata isa ta raba inda
yake ba although dama ko kallonta baya yi basu
taba hada ido dashi ba idan ma sun hada tor yayi
shaye shayensane amma idan yana cikin
hayyacinsa ko kallon inuwarta bayayi balle yasan
da ita a wurin
a dan xaman da suke da hussien yana koya mata
karatu sai shaquwa tashiga tsakaninsu hr yafara
sonta,
tunda ya sanarda ita yana sonta ta rasa sukunin
xuciyarta cos ita bashi xuciyarta keso ba hassan
takeso amatsayinta na mai aikinsu hrtaba kanta
wani matsayi nason taxama matar hassan
hakan kesa ta xauna taci kukanta acikin dare dan
tasan mafarkinta baxai xama gsky ba momy
baxata amince ta auri ya yanta ba dan tasha jin
momy na fadin twins dinta sai ya yan masu kudi
baxasu taba kawo mata talaka a gidaba
5
Dukkansu kyawawane farare sol dasu kasancewar
sun dauko momy ne,dogaye masu matsakaicin
jiki, sunada manyan danu da dogon hanci,bakinsu
jajir kamar masu shafa jambaki, haka fuskarsu na
dauke da mans pride,suna kula dashi saboda
suna sonsa sosai gashi baqi sidik ya kwanta a
gefen fuskarsu
[11:37AM, 11/5/2015] Pherty: haka suke basuda
banbancin jiki da fata,idan ba kasansu sosai ba
baka babanta kamanninsu, illah banbanci daya
hassan yanada dimple hussien bashi da, sannan
fuskar hussien tafi ta hassan faraa, shine kawai
banbancinsu
baxasu taba sa kayan daban daban ba sai dai su
banbanta colour ko a skul ana darga dasu kafin a
ganesu sai anyi da kyar ga yan mata na
rububinsu amma hassan baya kulawa sai dai
hussien...
6
Hermyder itace mai aikinsu tana xaune a qauyen
ingawa tare da mahaifiyarta kasancewar itama
mahaifinta ya rasu tun tana qarama amma ita
tasanshi
lokacin da akaxo da ita birni a kaduna aiki tayi
mamakin yanda take qanqanuwa da ita ace duk
xatayi aikin gidan sannan ta kula da twins duk ita
kadai
sai dai ba laifi ana biyanta albashi mai tsoka
kuma matar gidan na kyautata ma mahaifiyarta
hakan yasa ta xauna
ta qudira a ranta yanda matar gidan tabata
amanar kula da ya'yan xata kula dasu ciki kuwa
hrda hanawa hussien neman mata shikuma
hassan shaye shaye
tasan xata iya tankwasa hussien tunda ko banxa
aynxu sonta yake amma hassan fa dako kallo
bata isheshi, tayama xata soma ta ina xata fara
wanda a kullum qara tsoronsa take kuma yana
qara mata kwarjini shiyasa takejin sonsa ta ko
ina
[12:40PM, 11/5/2015] Pherty: yau ma kamar
kullum misalin qarfe daya na dare ta fito daga
dakinta ta upstairs take kallon bakin gate din
tanaso taga waxai fara shigowa tsakanin su
biyun
tana nan tsaye hr kusan qarfe biyu ba alamar ko
daya daga cikinsu
hankalinta yayi matuqar tashi dan tasan basa
gidan
ta sauko a hankali kada mony taji motsinta ta
nufi sashensu
7
duk iya bincikenta basa dakinsu, jikinta hr rawa
yake ta fito harabar gidan tana xirga xirga ta
kasa kwanciya tana adduar Allah yasa lfy suke
qarfe uku da rabi mai gadi ya hangame gate din
tana xaune tana barci hasken motar na tadata ta
tashi tsaye tana bin motar da kallo hrtayi parking,
nan tagane hussien ne ya shigo
tana tsaye bata motsa daga inda take ba, hr ya
fito daga dayan bangaren wata yarinyace ta fito
ta xagayo inda yake tsaye ya riqe qugunta
gab da xai shiga sashensa ya ganta tsaye
idanunta kyam akan nasa,yana ganinta sai da
gabansa na fadi amma sai ya daure fuska yana
wani dubanta qasa qasa
yace k lfy meya hana maki barcine
da kyar idanunta sun kawo kwallah
tace ba komai
ya dubeta hr tsakiyar idanunta yaga kamar
tanaso tayi kuka sai yaji ba dadi a jikinsa amma
sai ya tabe bakinsa yaja yarinyar suka shige ya
barta nan a tsaye
8
ta bisu da kallo hr suka shige kafin taja ajiyar
xuciya ta maida kallonta bakin gate tana share
kwallah
tabbas gidan na buqatar gyara, tanaso ta gyara
rayuwarsu amma bata da hali cos sunfi qarfinta
ba huruminta bane nata shine ta kula dasu kawai
hr xata juya ta fice sai ta tuna hassan bai shigo
ba dama duk yau bata gansa ba tanaso ta gansa
ko xata sami sukuni a xuciyarta
Bai shigo gidan ba sai kusan asuba yanayin
parking dinsa kawai xai gayama a buge yake dai
dai lokacin taga budurwar hussien ta fice daga
gidan
ya fito yana tafe yana layi kamar xai fadi a qasa,
tabi bayansa tana sharar kwallah idan xai fadi
itace k tarosa hr suka iso nan falonsa inda ya
xube qasa shakaf
[12:47PM, 11/5/2015] Pherty: ta duqa ta cire
masa takalmansa batada qarfin da xata kaisa hr
daki anan ta tsallakashi ta fice ta nufi nata dakin
sai datayi sallah kana ta kwanta
9
koda ta tashi idanunta sun kumbura rashin
samun isasshen barci
da kyar ta shiga kitchen ta soma kiciniyar hada
brk fst, sai da ta dora ta fito tayi shara tafara
mopping kenan hussien ya shigo sanye da
doguwar jallabiya
kanta a qasa ba tare da ta kallesaba ta gaidashi
ya matso gareta hade da riqe mopper
yace kiyi haquri hermyder wlhy inason aure sosai,
inaso na daina wannan dabiar amma kinji momy
tace baxata mana aure ynxu ba dan Allah karki
tsaneni akanki xn cnxa xn daina tunda bakyaso
bata tankashi ba tacigaba da share hawayen
fuskarta
yace pls hermyder
[2:11PM, 11/5/2015] Pherty: ta kauda kanta gefe
ya riqo hannunta da sauri ta fisge hannunta tana
yarfewa kamar wadda taga abin kyama
tace banaso karka sake niba yar iska bace kamar
ynda kake tsammani
ya rumtse idanunsa cike da jin haushinta badan
yana sonta ba dayayi qasa qasa da ita ynxu tana
mai aikinsa xata tsaya gayamasa mgn haka
10
ya juya hannayensa sarqe a bayansa yana furxar
da iska daga bakinsa ya juya ya fice batare da ya
tankataba
haka ta yini sukuku gidan ba walwala hrta soma
jin xaxxabi kafin kace me jikinta ya dauki xafi rau
taje ta sanarda momy tana son taje asibiti bata
jin dadin jikinta
tace driver na gidan kuwa
ta girgixa kanta tana hawaye alamar ya fita
momy ta fito dayake tanada tausayi musamman
da takeson hamida saboda kirkinta da ladabi
kuma bata da qeta a rayuwarta shiyasa take
qaunarta
koda suka fito ba kowa driver baya nan
tace ko ina yaje ne
ta dubeta tace bara na dauko maki kudi kishiga
taxi kije tunda bayanan, dai dai lokacin hassan ya
fito daga sashensa cikin shirinsa na qananan
kaya yayi matuqar kyau amma fuskar nan tasa a
murtuqe
momy tace hassan fita xakayi ne
ya gyada kansa batare da ya tanka ko ya
kalletaba
tace hermyder ba lfy koxaka kaita asibitine
ya tsaya cak ya juyo yana kallonta
yace wacece hermyder kuma momy
tayi kasake tana kallonsa
tace bakasan hermyder bane mai aikin gidannan
ya yatsina fuskarsa
yace oh tor motata bata daukan masu aiki kuma
kinsani momy
tace baka ganin batada lfy ne, ciwo ai ya kauda
komai hassan ballantana ma hermyder na iya
qoqarinta akanku ka tausaya mata
yayi shiru yana naxari kafin yace tor baxata
xauna min a seat din mota ba sai idan xata
tsugunna a qasan seat din inkuma bataso
shikenan ya tabe bakinsa hade da daga
kafadunsa ya fice
momy tace ki barshi duk ynda yace ki haqura
yakaiki asibitin kinji hamida
ta gyada kai tana sharar kwallah suka nufi motar,
momy ta bude gidan gaba xata sanyata ya fito a
firgice
wait wait wait momy,ina xaki sanyata ne badai a
gaban motata ba sai dai ta xauna baya ko taje
bayan booth
momy ta saki baki tana kallonsa tace sai kace
wani dabba
[7:43PM, 11/5/2015] Pherty: ta bude mata gidan
baya ta shiga ta xauna a qasan seat tana xubar
da kwallah
da qarfi yaja motar yana tsuki sai da kanta ya
bugu, haka ya riqa sharara gudu hr suka iso
asibitin yaja wani uban birki sai da ta fadi
tana ganin ya tsaya jikinta na rawa ta fita tana
sharar kwallah, shima ya fito yana gyara space
dinsa fuskarsa a murtuqe batare da ya kalletaba
yace ki tsaya a bayana kada mutane su xata
muna tare ne, yasa kai yafice sai da yayi dan
nisa saanan tabishi a baya
lokacin da suka iso inda likitan ya dubata sosai
ba komai k damuntaba sai rashin barci da tunani
wanda ya haddasa mata ciwon kai da xaxxabi
ya dubeta yace xai mata allura
tace Dr. kabani magani kawai bana son allura
hassan na xaune yana chtng yana jinsu bai tanka
masu ba
likitan yace dole sai an hada maki da allura kiyi
haquri ba wani ciwo gareta ba
ta soma hawaye dan aduniya idan da abinda ta
tsana bai wuce alluraba
ta soma roqansa tana bashi haquri tun bata
qarasaba taji saukar mari a fuskarta ji kake
gauuuuuu sai dataga gilmawar duhu a idanunta
tayi tangal tangal xata fadi likitan yayi saurin
riqota
yace haba haba batada lfy fa rarrashine yafi
dacewa ba duka ba
yace tana batamin lokacine likita inada abinyi
yace shikenan tunda bataso xn ubuta mata
magani
hassan yace noooo sai anyita koda xata mutu sai
anmata allurar, ya kalleta idanunsa jajur karo na
farko a rayuwarsa kuma cikin hayyacinsa daya
soma hada ido da ita
cikin tsawa yace k nake jira fa
ba shiri jikinta na rawa ta gyara likitan yayi mata
allura
yaja dogon tsaki yaciro kudi ya ajiye ya fita da
sauri, itama jikinta na rawa ta biyoshi tana sharar
kwallah amma me kafin ta iso tuni ya figi
motarsa fuuuuuuuu ya fice ya barta anan
tsaye.....
26 November 2015 at 12:49 · fertymerh xarah n...
More
[4:35pm, 10/6/2016] Fatyma Zahra Too Nv: [5:16PM, 11/28/2015] pherty: 11
TAGWAYEN MAXA
Na fertymerh xarah
A hankali take tfy batare datasan inda take jefa
qafafuntaba , ga jiri datake gani saboda allurar da
aka mata,
tayi nisa cikin tfyrta kamar daga sama taji
tsayuwar motarsa a kusa da ita,
hrtayi banxa kamar baxata shiga ba sai kuma ta
bude ta shiga baya ta xauna a qasa kamar farko,
yaja motar da qarfi xuciyarsa cike da bacin rai,
suna gab da shiga gida ya tsinkayo motocin frnds
dinsu bakin gate din,
yaja wani burki sai da ta fadi taa dubesa a
tsorace shima idanu jawur yake kallonta
yace kifita pls get out kada frnds dina su
rainamin wayo,
da sauri ta fito motar jikinta na rawa shima ya
fito ya xagaya inda ta xauna da tsumma yana
gogewa yana jan tsaki duk tana tsaye tana
kallonsa cike da mamaki hrya gama ya shiga
motarsa yajata da qarfi ya fice,
lokacin da ta iso gidan duk suna harabar gidan
ganinta yasa hussien ya qaraso da sauri yana
kallonta
yace lfy hermyderh meke damunki ne? Ta soma
girgixa kanta tana sharar kwallah
tace banajin dadin jikina, ya riqo hannunta duk ya
dabirce
yace hope kinje asibiti,ta gyada kanta, duk suna
tsaye suna kallon ynda hussien ya rikice akan
village girl, hassan shima abin yayi matuqar bashi
mamaki amma sai ya boye, yaja hannunta suka
shiga ciki suka taradda momy falo sai da gabanta
ya fadi ganin yanda hussien ya riqota amma sai
ta kawarda tunanin
tace meyiwuwa yana tausaya mata ne saaboda
tana qoqarinta akansu,
tace hamiida ya jikin tace jiki da sauqi ta miqa
mata takarda magani,
Hussein ya karba jikinsa na rawa
yace bara naje na siyo mata baijira cewartaba ya
fice da sauri, abin yayi matuqar bawa
[6:12PM, 11/7/2015] Pherty: Momy mamaki,
hamida tayi shigewarta dakinta ta kwanta,
barci mai nauyi ya dauketa koda ya yadawo ya
sameta tana barci ya shafa fuskarta kawai ya
fice,
12
lokaci lokaci yake xuwa dubata bata tashiba,
momy ta kasa boye damuwarta lokacinda suke
xaune su uku a falo ta dubesa,
tace hussien na kasa ganema ko menene
damuwarka da hamida daka damu da ita haka ko
nice ke ciwo baka damuwa haka,
hassan ya tsura masa ido yana so yaji amsar da
xai bayar amma ga mamakinsu biris yayi dasu
kamar baiji ba,
tace dakai fa nake mgn, ya shagwabe fuska ya
tashi yana fadin itama ai tana kula damu so ba
laifi bane dan na kulata ya fice,
hassan ya tabe bakinsa yana kallonta
yace momy tor meye ne na damuwa tunda itace
mai kula damu, meyiwuwa yana tausayinta ne
kinsan sun shaqu fa,
tayi shiru kawai dan tasan a duniya ba yanda
xa,ayi tayima daya mgn daya bai shiga ba, basu
taba yarda daya yayi laifi ko kuma aga laifin daya
sai dai dukkansu,
tace idan hakane kai myasa bnganka ko sau daya
kayi mata sannu ba ana hakane hassan kulawarta
fa na qarqashinmu amanace agaremu itama fa
tana kula daku,
ya tashi idanunsa akan iphone dinsa,
yace noooooo momy haba dai na rasa waxanje
dubiya sai yar qauye mai aikina haba dai
momy,Allah ko asibiti dana kaita nakai xuciyata
nesa ne, bakiga nadaina hawa motar bane, hrna
tura kudin motocinmu amana odar wasu nida
hussien,
tayi kasake tana kallonsa,
tace dadina dakai hassan bakason talaka shiyasa
nake burin naga irin matar da xaka aura ko yar
gidan wacece amma saboda hamida bai kamata
ka ajiye motar kaba yarinyar tana da tsabta gata
kuma kyakkyawa,
ba tare da yayi mgn ba ya fice warsa, tayi shiru
kawai tana naxarinsu.
[6:18PM, 11/7/2015] Pherty: Kwana biyu tsakani
ta soma samun sauqi, tana samun kulawa daga
momy da hussien, ganin ta dan murmure yasa
taje inda momy kan cewa tana so taje ingawa ta
gaida mahaifiyarta kusan wata shidda rabon da
taje,
13
momy tace kiyi haquri hamida hr wani watan idan
yan biyu sunje cameron ynxu idan kinje waxai
kulamin dasu,
tayi shiru kamar bataso haka ba
tace shikenan ta tashi ta fita kamar xatayi kuka,
garden ta nufa tasami wuri ta rakube tana
kallonsa, shi wannan kullum baya gajiya da chtng
olways akan waya daga gefensa whisky ce a ajiye
ta qarasa inda yake ta xauna tana fuskantarsa ba
alamar tsoro a tare da ita, kusan minti goma da
xamanta idanunsa...


Read / Download TAGWAYEN MAZA

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album