Subscribe for N1000/month for downloading access and an ad-free site. Contact WhatsApp +2348140419490 if you can't pay / subscribe. SUBSCRIBE

24 yin

MURADINA Book 1 Complete Hausa Novel Document by MURADINA Book 1


MURADINA Book 1

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 27067



MURADINA Book 1

Reading Time: 2 Hours

Added On: 20, Aug 2024

Author: Fateey Zaarah ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : 07077791941 /09047574404

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 167.33 kb

File Type: txt

Views: 535+

Download: 260+

Last download: 4 days ago

Description/Story: ๏ปฟ๐Ÿ’ซ ๐— ๐—จ๐—ฅ๐—”๐——๐—œ ๐—ก๐—” ๐—–๐—˜ ๐Ÿ’ซ




An Imaginary Love Storyโค๏ธ




๐š‚๐šƒ๐™พ๐š๐šˆ ๐™ฐ๐™ฝ๐™ณ ๐š†๐š๐™ธ๐šƒ๐šƒ๐™ด๐™ฝ



๐™ฑ๐šˆ ๐™ต๐™ฐ๐šƒ๐™ด๐šˆ๐š‰๐™ฐ๐™ฐ๐™ท๐š๐™ฐ๐™ท




Alhamdulillah! Godiya ta tabbata ga Allah SWT da ya bani Ikon ฦ˜ara kawo muku wannan Littafin Allah yasa yadda na fara Rubuta shi lafiya in ga ma lafiya.

โ— ฦ˜irฦ™iraren labari ne idan wani Abu yayi kamanceceniya da Rayuwar Wani/Wata to Arashi ne.

โ— Yana ษ—auke da abubuwa daban-daban kada ku bari ayi tafiyar babu ku ๐Ÿซฐ๐Ÿซฐ๐Ÿซฐ


Na Chanja masa suna daga MURADIN ZUCIYATA zuwa MURADI NA CE



๐— ๐—œ๐—ž๐—œ๐—ฌ๐—” ๐—ช๐—ฅ๐—œ๐—ง๐—˜๐—ฅ'๐—ฆ ๐—”๐—ฆ๐—ฆ๐—ข๐—–๐—œ๐—”๐—ง๐—œ๐—ข๐—ก




Follow My WhatsApp Channel




https://whatsapp.com/channel/0029VaOeCGv42DcbctBrce2I





ุจุณู… ุงู„ู„ู‡ ุงู„ุฑุญู…ู† ุงู„ุฑุญูŠู…





๐™ต๐™ฐ๐šƒ๐™ด๐šˆ๐š‰๐™ฐ๐™ฐ๐™ท๐š๐™ฐ๐™ทโœ๏ธ




๐‘ƒ๐‘Ž๐‘”๐‘’ 1๐Ÿฆ‹






๐‘ณ๐’Š๐’Ž๐’‚๐’˜๐’‚ ๐‘บ๐’•๐’“๐’†๐’†๐’•, ๐‘ซ๐’–๐’•๐’”๐’†, ๐‘ฑ๐’Š๐’ˆ๐’‚๐’˜๐’‚ ๐‘บ๐’•๐’‚๐’•๐’†.






Tuฦ™i yake a hankali kamar baya son yi a bakin wani tangamemen Gida ya tsaya Horn yayi gate man ne ya leฦ™o ganin motar yasa ya koma ciki ya buษ—e gate ษ—in shiga ciki yayi tare da yin parking zaman sa yayi a cikin motar bai fito ba ya ษ—auki gurin minti talatin a ciki sannan ya fito tsayawa yayi kana ganin shi kaga ฦ™arfaffan mutum da motsa jiki ya ratsa shi {Giant} ฦ™are wa compound ษ—in gidan kallo ฦ™aton gida ne dan daga ciki yafi girma Part-Part ne gurin guda Shabiyar daga can gefe garden ne mai kyau cigaba yayi da tsaiwa a gurin jikin motar sa. Babban Mutum ne ya shigo gidan kai tsaye gurin sa ya nufo Bata fuska yayi sannan yace masa


"Daga ina kake Fawzan?" Da Sauri ya juya yana kallon sa baiyi tsammanin zai haษ—u da kowa yanzu ba Ko takwas bata yi ba ya dawo Shiru yayi masa yana ษ—auke Kansa daga kallon sa, cigaba da yi masa magana yayi


"Yau ma baka kwana a gidan ba kenan?" ฦŠauke shi da mari yayi "a ina ka kwana nace maka" nan ma shiru ya ฦ™ara yi masa yana cin magani da ฦ™unkuni ฦ™asa-ฦ™asa sai kuma ya ce masa


"Malam ka dame ni da surutun tsiya kai ba haifa ta kayi ba amma kana mari na, ษ—aga maka ฦ™afa kawai nake amma wallahi da sai na rama"


"Rashin Kunyar taka har ta kai kace zaka mare ni Dan na maka faษ—a, to zoka rama marin mara tarbiyya kawai"


"Na rasa inda ka samo wannan banzan halin mu dai duk zuri'ar mu babu ษ—an iska sai kai maybe a Gurin Uwarka ka kwaso wannan mummunan halin"


"Kaga rashin tarbiyya a ฦดaฦดan ka tsohon banza kawai, kuma ba Mahaifiya ta ka zaga ba Tsohuwar ciki ka zaga kaji, mtwssssss" ya faษ—a yana shige wa Part ษ—in da yake kallon sa. Masifa ya cigaba da yi a gurin ba jima wa sai ga Tsohuwa ta fito itama daga Part ษ—in ta "Kabiru kai da wane haka da sanyin safiyar nan?, Yawanci duk ba'a tashi ba kar hayaniyar ka taja hankali"


"Hajiya kema kin san wanene zai saka mutane magana iyanzu ai"


"Sai yanzu ya ga damar dawowa gidan Kenan, na rasa me yake damun Fawzan baya son kwana a gidan nan yanzu, Kabiru kira min shi yanzu ku same ni a palour na da Iyayen sa"


"Allah ya Kyauta dai Insha Allah yanzu zaki ganmu"






๐Ÿ”ฅ๐Ÿ’ฅ๐Ÿ’ฆ






๐‘ซ๐’‚๐’Ž๐’‚๐’•๐’–๐’“๐’–, ๐’€๐’๐’ƒ๐’†, ๐‘บ๐’•๐’‚๐’•๐’†.






Palour ne kato an yalwata shi da kujeru masu kyau kirar Italy set Uku daga ษ—ayan side ษ—in kuwa katon Dinning ne ba kowa a cikin palour ฦ™ofofine gurin guda shida sai Stairs daga tsakiyar Palour'n daga gurin Dinning ษ—in ฦ˜ofa ce a buษ—e da alamu kitchen ne.





Wata kyakkyawar budurwa ce tsaye take a bakin sink Doguwa ce dirarriya daga fuskar ta fara ce kal ฦ™aramin lips ne da ita tana da dara-daran idanu masu kyau ruwa take tara da alamu ta faษ—a Duniyar tunani Wata Babbar Mace kana ganin ta kaga wadda Naira ta zauna a jikin ta cikin kitchen ษ—in ta shigo a baฦ™in kofa ta tsaya tana kiran"Jaanan!, Jaanan!, Jaanan" jin shiru ne ya sata ฦ™ara so wa kusa da ita


"Jaanan! Jaanan" ta ฦ™ara faษ—a shiru bata answer ba ษ—aka mata duka tayi a firgice ta ษ—ago "Yaushe kika ฦ™ara so ne Ummu?" Ta tambaye ta


"Ban sani ba, bacin kina jina amma baki amsa ba sai da nazo dai-dai inda kike ke ga ishashiya" ta faษ—a kamar ta rufe ta da duka


"A'a Ummu banji kina magana ba ne"


"Ai dama ba zaki ji ba, kin raina kowa a gidan nan musamman Ni"


"Kiyi haฦ™uri dan Allah" ta faษ—a tana yin ฦ™asa da kanta kafin ta ฦ™ara wani laifin. wata mace ce ta fito daga ษ—aki daga ita sai sleeping dress alamun ta sun nuna yanzu ta tashi daga bacci tsayawa tayi tana kallon su tabe baki tayi Sannan ta ฦ™ara so kitchen kusa da Ummu ta tsaya tana watsa wa Jaanan Mugun Kallo ฦ™asa tayi da kanta magana ta fara yi musu


"ummu ya Naji kina ta faษ—a tun dazu?, Hayaniyar kice ta tashe ni daga bacci"


"Ba Dole kiji ina ta faษ—a ba, Yarinyar nan nake ta kir amma tayi banza dani bata amsa ba, nasan har maฦ™ota suna jiyo mu yanzu"


"Uhmmmmm, Indai Jaanan ce ai ta saba tana jin ka kana mata magana amma tayi maka banza, wallahi na tsani Yarinyar nan ji nake kamar na kashe ta, an auro mana wahala mtwsssss"
"Ban san me Yaya ya gani a jikin Yarinyar nan ba ya nace mata sai Wulakanta shi take amma ya nace mata" ta faษ—a tana galla mata harara


"Bari yazo shima zai ci Ubansa, Sakin ta zai yi nan bada daษ—ewa ba na gaji da halin ta"


"Ummu dan Allah Kiyi haฦ™uri, me za'a yi miki yanzu?"


"In kinyi laifi kin san kice ayi haฦ™uri, wai Uban me kike ta zaman yi baki fara wanke-wanke nan ba, Da gani ko breakfast Baki haษ—a mana ba kuma kin san ษ—aki na yana jiran ki zan fita aiki Kizo yanzu ki gyara" cewar budurwar


"Na kusa gama breakfast ษ—in, Bari in ฦ™ara sa wanke-wanken Sai inzo"


"Auuuuuu Har sai na ma jira kin ฦ™ara sa?, ai tashi zaki yi Kizo ki gama da shi kafin na fita, in kin gama kya dawo kiyi wanke-wanken" ta faษ—a tana fice wa daga kitchen ษ—in zuwa ษ—akin ta.









Tashi tayi daga wanke-wanken ta bita zuwa ษ—akin kafin ta ฦ™ara yin wani laifin cikin ษ—akin itama ta shiga katon ษ—aki ne an cika shi da kayan alatu kala-kala, kaca-kaca yake kamar ba mace ce a ciki ba. Ko kallon wacce take cikin ษ—akin bata yi ba ta wuce Toilet shima ba kyan gani haka ta fara gyara shi tassss ta gyara shi Sannan ta fito. Harara ta watsa mata sai kuma tace "sai nace ki fara aikin nan ษ—in sannan zaki yi ne?"


"A'a ba sai Kince ba, amma ai sai kin tashi daga kan gadon sai in fara"


"Ki fara gyara kasan sai in tashi daga nan" Tom tace mata tana fara gyara wa tashi tayi ta koma kan kujera tana danna wayar ta bata daษ—e ba ta tashi tana mata wani kallon banza tare da cewa


"saura in fito daga wanka in tarar Baki gama ba" tana shigewa Toilet ษ—in. Da sauri sauri ta cigaba da yin aikin tana kuka hawayen daya zubo mata ta share____________________________โœ๏ธ






# ๐™ต๐™ฐ๐šƒ๐™ด๐šˆ๐š‰๐™ฐ๐™ฐ๐™ท๐š๐™ฐ๐™ท๐Ÿ‘ฏ



Rashin Comments na iya maida shi Paid Book.



09047574404
WhatsApp Only


Comments & Share Fisabillah๐Ÿฅฐ๐Ÿ‘



๐”ฝ๐”ธ๐•‹๐”ผ๐•โ„ค๐”ธ๐”ธโ„โ„๐”ธโ„โœ๏ธ

๐Ÿ’ซ ๐— ๐—จ๐—ฅ๐—”๐——๐—œ๐—ก๐—” ๐Ÿ’ซ




An Imaginary Love Storyโค๏ธ



๐š‚๐šƒ๐™พ๐š๐šˆ ๐™ฐ๐™ฝ๐™ณ ๐š†๐š๐™ธ๐šƒ๐šƒ๐™ด๐™ฝ


๐™ฑ๐šˆ ๐™ต๐™ฐ๐šƒ๐™ด๐šˆ๐š‰๐™ฐ๐™ฐ๐™ท๐š๐™ฐ๐™ท



๐— ๐—œ๐—ž๐—œ๐—ฌ๐—” ๐—ช๐—ฅ๐—œ๐—ง๐—˜๐—ฅ'๐—ฆ ๐—”๐—ฆ๐—ฆ๐—ข๐—–๐—œ๐—”๐—ง๐—œ๐—ข๐—ก



Follow My WhatsApp Channel


https://whatsapp.com/channel/0029VaOeCGv42DcbctBrce2I



ุจุณู… ุงู„ู„ู‡ ุงู„ุฑุญู…ู† ุงู„ุฑุญูŠู…


๐™ต๐™ฐ๐šƒ๐™ด๐šˆ๐š‰๐™ฐ๐™ฐ๐™ท๐š๐™ฐ๐™ทโœ๏ธ



๐‘ƒ๐‘Ž๐‘”๐‘’ 2๐Ÿฆ‹








ฦ˜ara sa gyaran ษ—akin tayi da hanzarin ta kafin ta fito dan Indai ta fito ta tarar da ita sunan ta sorry a gidan. Tana gama gyara ษ—akin ta koma kitchen wanke-wanken ta ฦ™ara sa sannan ta fitar musu da Breakfast a dinning ta jera sai kafa-kafa take kar ta yarda wani abu ta sha faษ—a ษ—akin Ummu ta nufa nan ma aljannar duniya ce dan tafi ษ—akin budurwar kyau zaune ta tarar da ita ta hakimce akan kujera tana danna waya a ฦ™asa ta tsuguna "Ummu na gama aikin"

"Har ษ—akin Eshaal kin gyara"

"Eh na gyara"

"Kin haษ—a breakfast ษ—in"

"Shima na haษ—a Ummu"

"To sai gyaran ษ—akin nan, kar in dawo in tarar da shi haka"

"Dan Allah Ummu ki bani abinci inci kafin in gyara yunwa nake ji wallahi"

"Abinci? bayan baki gama aikin ki ba salon ina baki kiyi bacci Koh?"

"Wallahi ba zan yi ba, yunwa nake ji kamar na mutu Ummu baki ji cikina ba"

"Ai na fison ki mutu ko na huta da alakaฦ™ai, Kinga tashi ki ฦ™ara sa gyaran nan zaifi Miki" ta faษ—a tana make ta wucewa tayi ta barta a gurin durkushe tana riฦ™e da cikin ta.

Har wajen minti talatin bata tashi ba tana kuka ganin zaman ba zai amfane taba yasa ta tashi da kyar ta gyara ษ—akin sannan ta fito a palour ta tarar da su da alamu sun gama yin breakfast ษ—in kusa da Ummu tazo ta tsugunna tana
Domin cigaba da karantawa sai ku downloading.
Yadda ake downloading na littafin: ku tabbata kunyi register da shafinmu sanna kunyi login, idan bakuyi register a kasa zakuga maballai guda biyu daya an rubuta LOGIN dayan kuma an rubuta REGISTER sai ku taba su kuyi register, daga nan sai ku yi subscription koda na naira 1000 ne, domin sai kunyi subs dinann ne kadai zaku iya dauko littatafanmu.

Ya ya akeyin Subscription namu : Bayan kun yi Login ko register daga kasa zaku ga wani jan maballi (button) an rubuta SUBSCRIBE sai ku taba shi zai kaiku inda zaku zabi package wato tsarin subs na ku da mu. akwai na wata guda, watanni biyar da shekara guda. da zarar kun zaba zai kaiku inda zaku biya kudin, wanda daga nan sai ku cigaba da downloading kawai abunku

ABUN LURA : duk wani littafi da kuka gani a shafinnan kyauta ne, wannan tsari mun zo da shine don mu samu hanyar da zamu iya rike shafin muna managing na shi, izan ku kayi subs na mu tamkar DONATION ne ku ka yi mana, ku ka bamu kwarin guiwa don mu ciagaba da kawo muku sabbin littatafai, amma duk wanda ya ga bazai iya ba toh zai iya karanta littafin kyauta a cikin shafinnan namu batare da ya downloading ba, kawai ya yi kasa zai ga Koren maballi (button an rubuta) START READING sai ya taba zai kaishi inda zai karanta littafin.

Sannan duk wanda yaga kamn wannan process din zai bashi wahala kai tsaye zai iya min magana ta whatssApp +2348140419490, ya tura min kudin ni kuma zan dora mai subs din akan account na shi

NB: iya ta haka ne zaku iya karanta wannan littafi a shafinmu babu wata hanyar. DAN ALLAH KU DAINA MANA MAGANA AKAN MU TURA MUKU LITTAFI TA WHATSAPP, BAMA TURAWA HANYA GUDA MUKE TURA LITTATAFANMU SHINE WEBSITE NA MU https://taskarnovels.com.ng DUK MAI BUKATAR LITTAFINMU YA JE CAN YA KYAUTA NE, AMMA DOWNLOADING KUWA BA KYAUTA BANE SAI YAYI SUBSCRIPTION NA WEBSITE NAM
This is not the real Download Button


Read / Download MURADINA Book 1

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

This is not the real Download Button
Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album