Join Our WhatsApp Group

SAKATARIYA TA Complete Hausa Novel Document by SAKATARIYA TA


SAKATARIYA TA

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 154237



SAKATARIYA TA

Reading Time: 12 Hours

Added On: 06, May 2024

Author: Azizat Hamza ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 757.44 kb

File Type: txt

Views: 372+

Download: 1133+

Last download: 10 minutes ago

Description/Story: *SAKATARIYA TA*
......(My Secretary).......

__
*©Azizat......✍*
*Wattpad @000Azee*


*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*


*Ban yarda wani ko wata su yaɗa min wannan labari ta ko wani siga ba, ban yarda a karantashi a youtube channels ba, ban yarda a kwafa ko a juya wannan labari ba. Wannan labari Hakkin Mallakan Azizat Hamza ce*


*Free page*


0️⃣0️⃣1️⃣



Idon sa ya rintse, lokaci guda kuma ya daka tsawa "get the hell out of here!" Gigicewa yarinyar ta yi, jikin ta na rawa.
Sai da ya sake ma ta magana cikin tsawa " out of my office!" Sannan ta fita daga office ɗin a bircike, yai tsaki tareda jawo wayar landline ya danna kira, cikin muryar shi mai ɗauke da amo ya ce " Anas, i need another secretary"
Bai saurari mai zai ce ba ya ajiye phone ɗin. Ya ja tsaki sannan ya fara latsa laptop da ke gaban shi...



"Ene what happened?" Matashin saurayin ya tambayi yarinyar da ke harhaɗa files ta na yi ta na share ƙwalla.
Ta ɗago jajayen idanun ta ta kalleshi ba tareda ta ce komai ba sannan ta cigaba da abinda ta ke yi.

A hankali ya ce " please stop crying, i'll talk to him" ya wuce cikin katafaren ofishin da ya fi kowanne girma acikin kamfanin.


Har yanzu aiki ya ke yi, shi ya sa ko da ya ji alamar buɗe ƙofa bai ma ɗago ya ga waye ba. Ya san sarai mutum ɗaya ne zai iya shiga ma sa office karangatsau haka.

" what exactly is your problem, wai kai for once ba za ka iya haƙuri da juriya da zama da mutane ba. Yanzu mi ta ma ka dan Allah?"

Ya fi minti biyu bai ce komai ba kuma bai ɗago ba.

"Najeeb magana fa na ke yi"

Sai a lokacin ya ɗago kykykyawar fiskar shi ya ce " Oh na ɗauka ƙara ka kawo ai"

Ya ja kujera ya zauna sannan ya kalli Najeeb ya ce " wannan kuma mi ye matsalarta?"

Kamar abin da Najeeb ɗin ke jira kenan ya fara kwarwa " the girl is so dumb, imagine jiya na ba ta report ba ta yi ba, wai ta manta. Yau kuma na ba ta wani, ta je ta yi min shirme....."


" ya isa haka ba sai ka kai ƙarshe ba, na san ƙarshen labarin. Yanzu ya ka ke so ayi?"

"Change her, May be wannan karon ka kawo namiji"

" kamar da gaske, Secretary biyu kafin wannan ba maza ba ne, su ma ba korar su ka yi ba"


Najeeb ya ɗan haɗa rai yace " look dude, ka san yanda na ke son aiki na, you either work perfectly or you leave. Ba na son shirme"

"Na ji za a nemo wani, but gaskiya Najeeb this time around ka yi haƙuri da koma wanene"

"Yallaɓai Anas na ji na amince. Sai me kuma?"

Anas yai dariya ya ce " duk yadda ka ce Engineer"




...............................................



Waya ce ɗare a kunnen ta lokacin da ta tsaida mai keken. Sai da ta zauna sannan ta ce Muda-Lawal ta ci gaba da waya wanda duk rabi masifa ta ke yi.
Ta na ajiye wayar ta kalli ƙeyar mai keken ta ce " nawa ne?"

"Ɗari da hamsin" ya faɗi hankalin sa na tuƙin da ya ke.


" hala ka fara fashi da makami ko?"

Mai keke ya tunzura ya ce" ban gane maganar ki ba"

"Idan na baka tamanin ka sa makami ka ƙwaci sauran kuɗin"

" gaskiya 'yan mata idan ba za ki ba da ɗari da ishirin ba ki sauka" ya na magana ya na rage gudun keken.

" sai ka zo ka fitar da ni ai"

Mai keke ya ja keken sa ya tsaya "sauka dan ba zanje a naira tamanin ba"

" duniya da 'ya'yan ta. Idan na sauka a keken nan na zama turmi" ta daka ma sa tsawa "za ka ja keken ka mu tafi ko dai!"

Mutumin da ke gefen ta ya ce " mai keke mu je zan biya kuɗin"

Sai a lokacin ta kalli mutumin. Saurayi ne dan a ƙalla ba zai wuce shekara ishirin da tara zuwa talatin ba. Ta ce "yawwa shishshigi. An gaya ma ka ban da ɗari da hamsin ɗin biyan sa ne?"

"Allah ya ba ki haƙuri" ya faɗi ya na kauda kai gefe saboda yadda ta tsare shi da manyan idanun ta.
"Ba zan gaya ma ka sunana ba hakanan ba zan ba ka numbata ba dan na san dalilin shishshigin kenan"

Murmushi yai ba tareda ya kalleta ba. Mai keke ya cigaba da tafiya, a hankali mutumin ke satan kallon ta sai dai ita hankalin ta ya karkata ne kan wayan ta. Chan ta lura ya zuba ma ta ido. Ta ɗago idon ta da sauri ta ce "Malam kallon yai yawa, idan idon ka bai faɗo ba zan ƙwaƙwaleshi da kai na"
Mai keke ya fashe da dariya a zuciyar shi ya na mamakin masifar budurwan nan.
Har aka iso inda za ta sauka ba wanda ya tanka ma ta. Ta na sauka ta fito da naira ɗari biyu ta miƙawa mai keke ta ce ban ɗari da Ishirin. Mai keke ya ce "Oga ya biya mi ki duka kuɗin"
" chan ta matse mu ku " ta faɗi tareda maida kuɗin ta cikin purse.

Ta ƙarasa wajen park ɗin ta na tafiya ta na waya. Yayinda hayaniyar masu mota ke tashi a tashar.

"Dan Allah baiwar Allah ki saurare ni" ta ji an faɗi a bayan ta, ta juyo a tsanake.

"Sai aka yi ya?"

Yadda ta yi maganar da faɗa-faɗa ya sa ta ƙara burgeshi. Yai Murmushi ya ce "suna na Rayyan, kar ki min fassara amma idan ba za ki damu ba ko zan iya sanin sunan ki? Please" yai maganar yana haɗa hannun sa alamar roƙo.
"Ai da ma na san dalilin biya min kuɗin kenan. To ba zan faɗi sunan....."
Chak ta tsaya lokacin da aka ƙwala sunan ta
*'Aisha mai gwanjo'*

ta juya ba ta ga mai kiran ba, ta yi tsaki.
Wani saurayi ne ya ƙaraso akan machine ɗin sa ya na murmushi
" Allah ya ja zamanin ki 'yar kasuwa"
Sai a lokacin ta gane shi.
"Sabi'u Inuwa Manzo" ta faɗi ta na maida hankalin ta gareshi.
"Aka ce kina Yola, ya na ganki a Bauchi"

"Wallahi na je gida biki ne yanzu ma na ke son komawa Yolan. Kai fa ina aka turaka?"

"Sun turani Ilorin amma na relocating na dawo Bauchi, kin san mutum mai iyali sai a hankali"

'Yola...Yola..Yola mutum ɗaya' ake kira ta yi saurin sallama da Sabi'u Inuwa Manzo ta wuce wajen motar.
Har Sabi'u zai wuce Rayyan ya tambayeshi sunan Aisha da numbarta. Sai da Sabi'u ya sha dariya kafin ya bashi numbar bayan da Rayyan ɗin yai ma sa bayanin masifar da ya sha shi da mai keke. Sabi'u ya ce ai indai Aisha Farida Salihu ne to kaɗan ka gani.


................................

Tana shiga makarantar aka ce principal na neman ta ta sani saboda tafiyar da tayi ne dan haka hankali kwance ta wuce office ɗin sa. Da mamakin ta sai taga ashe neman saboda wasu 'yan mata 'yan aji shida da ta daka ne kafin ta tafi.

Ba ta bashi haƙuri ba balle ta nuna ta yi nadamar abinda ta yi sai da ta bari ya gama masifar shi ta ce " Mr principal dududu saura sati uku na bar makarantar nan. Yara kuma na dake su ne saboda raini da izgilanci da su ke min, ko gobe su ka sake zan dake su dan ni ba sa'ar su ba ce"

"Idan ba dan Yasir ba ai da tuni mun rabu da ke. Aisha tunda ki ka fara bautar ƙasa a makarantar nan koyaushe ana complain ɗin ki"

"Zan iya tafiya?"

Principal ya girgiza kai "kai kai kai, wannan mijin ki ya shiga uku wallahi"


Lokacin da aka tashi break ta haɗu da Yasir a staff room.

"Tawan ya ki ke, gida ya ƙarɓe ki fa sai wani ƙyalli ki ke"

"To miya fi raina"

Kujera ya ja zuwa kusa da ita kamar kullum ya na ƙoƙarin shawo kan ta. Sai dai kamar kullum ɗin zancen ta ɗaya ne.

"Mun kusa gama bautar ƙasan nan fa Farida ki taimakeni ki amince da ni" ya faɗa haɗe da haɗa hannunwan sa biyu alamar magiya.

"Yasir kenan, soyayyar talaka da maikuɗi a Nigeria its a nonono option for me. Wahala kawai zan sha ni kuma ban shirya ba. Balle kai da ka ke ɗan bare-barin nan ina zaman zama na iyayenka su turomin Yasin mai walƙiya na bi duniya"

Yasir ya sa dariya sai da ya yi mai isar sa ya ce "wallahi shiyasa na ke ƙara son ki, ba kya rabuwa da abin dariya. Yanzu miye kuma Yasin mai walƙiya"

"ka fini sani sarai"
Yasir ya cigaba da dariya.


......................

*Wacece Aisha Farida Salihu?*

Malam Salihu ɗan ƙaramar hukumar Wase ne da ke jahar Plateau. Sai dai tun yana ɗan shekara sha takwas da ya ƙare sakandare ya dawo cikin Jos da zama. Sana'ar sai da kayan gwari ya fara kuma Alhamdulillah yana samu. Su biyar ne a wajen mahaifin su wanda ya jima da rasuwa tun yana shekara bakwai a duniya, shi ne na huɗu a gidan kuma su biyu ne maza. Babban yayansu Musa shi yana Kano inda yake kasuwancin sa acan sai yayun sa mata Halimah, Asma'u da ƙanwar sa Fatima, wanda a lokacin duka sun yi aure Shekarar sa biyar a Jos yai aure.

Aminah 'yar Jos ce domin iyayen ta anan su ke da zama tun shekara da shekaru sai dai asalin su Fulanin Dukku ne da ke Jihar Gombe.
Shekarar Aminah shabiyar aka yi auren wanda a lokacin JSCE kawai ta kammala. Suna zaune da Salihu lafiya cikin so da ƙauna har wata takwas kafin mummunan ala'amari ya faru. Tana zaune ta shirya abincin rana ta tsara kwalliya tana jiran sa, saboda ko yaushe Salihu a gida ya ke cin abincin rana, taji sallamar mutane daga waje. Ta sa mayafi ta fita inda taga Alhaji Nuhu ne wanda su ke haya a gidan sa da kuma Yusufu wanda rumfar sa ke kusa da na Salihu a kasuwa. Yanayin su kaɗai ya tabbatar ma ta akwai matsala. A hankali Alhaji Nuhu ya sanar ma ta Salihu ke asibiti ya yi hatsari. Cike da tashin hankali ta bisu asibitin inda Salihu ke kwance rai a hannun Allah. Da asuba Salihu ya cika wanda sanadiyyar haka ya sa Aminah suma. Da ta farfaɗo ma dai rikicewa ta yi wanda da ƙyar Nanna wato mahaifiyar Aminan ta shawo kan ta. Sai da aka yi bakwai ɗin Salihu Nanna ta fahimci Amina ciki gareta wanda ko Aminan ba ta san da shi ba. A hankali Aminah ta dinga renon cikin ta wanda Inna mahaifiyar Salihu ta ke matuƙar farin ciki da cikin. Tsakar daren ranan Alhamis Amina ta tashi da naƙuda,aka kira wata nurse da ta ke ƙasan layin su, zuwa asuba ta haihu, ta samu ɗiya mace. Aisha Farida aka sa ma ta saboda sunan da Salihu ke cewa zai sawa 'yar sa ta fari kenan saboda sunan innar sa Aisha ya ce zai haɗa da inkiyar Faridah.

Amina ta cigaba da renon Aisha Farida a gidan su. Tana son ɗiyar ta sosai, ko kaɗan ba ta ma ta karan 'ya'yan fari irin na fulani. Shekarar Aisha Farida biyu da rabi Baba ya fara yiwa Amina maganar aure saboda a lokacin akwai manema dayawa da suke son ta. Duk ciki ba ta da zaɓi dan ita tun Salihu ba ta kuma sa soyayyar wani namiji a ranta ba. Cikin maneman ta Baba ya zaɓa ma ta Malam Haruna wanda shima mutumin Dukku ne yana ɗin ki a Terminos. Matar sa ɗaya da yara shida. Lokacin da Amina za ta tare Inna ta so a bar ma ta takwarar ta sai dai Amina ta nuna batason hakan dan a ganinta Farida ta yi ƙaranci a raba ta da uwarta. Ba laifi Haruna na ƙoƙarin nuna adalci tsakanin matansa sai dai Laraba sam ba ta da haƙuri kullum cikin tsangwaman Amina da 'yarta ta ke yi. Amina za ta lamunci komai amma idan akan Farida ce to ba za ta bari ba. Watarana Amina ta dawo daga unguwa lokacin watan ta takwas a gidan ta samu Laraba na dukan Farida tsabar wahala sai da yarinyar ta suma amma haka Laraba ta cigaba da jibgar ta. Da gudu Amina ta yi kan 'yar ta tana ihu. Daga asibiti dai Amina gidan su ta wuce ta yi yaji. A ranan Haruna ya zo biko sai dai ta nuna ma sa matuƙar za ta zauna da shi to dole ne ya raba mu su gida. Yai-yai da ita ta ƙi chanja ra'ayinta, daga baya ya yarda da hakan. Har ya kama ma ta haya ɗaki ɗaya a wani gidan haya a tudun Fera. Ana saura kwana ɗaya tak ta tare saboda har an je an jera ma ta kayanta sai ga Haruna ya zo neman ta da yamma, ta fita ta sameshi a ƙofar gida. Bai amsa gaisuwarta ba ya damƙa ma ta takardar saki ɗaya. Ba dalili ba komai. Ƙarshe dai yadda aka je aka jera kayanta haka aka dawo da su gida. Ta ƙare iddar ta ta cigaba da zaman gida. Da tanada hali ma makaranta za ta koma sai dai iyayenta ma su ƙaramin ƙarfi ne. Kuɗin makarantar Farida. Baffanta Musa ke aikowa tareda kuɗin buƙatunta duk wata, ya so ya ɗauketa sai dai Amina ta ƙi musamman da ya maida Inna zuwa gidan sa a Kano.
Ganin zaman gidan shiru ya sa ta fara yin su kunun zaƙi da zoɓo tana siyarwa. Shekararta ɗaya tana zawarci Ibrahim ya fito neman ta shima dai yanada mata, ba ta bashi dama ba sai dai ganin Haruna ya dawo yana son maida auren su ya sa ta yi saurin amincewa da Ibrahim. Haruna yai nadamar sakin ta acewar sa bai san ya akayi ya saketa ba.

A Saminaka Ibrahim ya ke da zama da shi da matarsa da yaran su uku. Watannin farko an tafi lafiya-lafiya sai daga baya Matar sa Kubura ta fara nuna halin muguntar ta, ƙarshe sai raba mu su gida Ibrahim yai Lokacin Amina na laulayin ciki. Sai da su ka raba zama Amina ta samu sakewa ita da 'yar ta. Da cikin ya cika wata tara Amina ta haifi ɗa namiji. Hakan ya farantawa Ibrahim rai saboda yaran Kubura duka mata ne. Wannan haihuwar ya jawo Kubura ta sake jin tsanar Amina. Da daɗi dai ba daɗi su na zaune har Faruƙ ya shekara biyu. Kasancewa abubuwa sun fara ja baya wa Ibrahim ya sa su ka bar gidan haya su ka koma gidan sa. Zama tareda Kubura dai sai ma abin da ya ƙaru.

Watarana Farida da Safiya 'yar Kubura su ka yi faɗa. Kubura na kitchen ta ji kukan Safiya aikuwa ta fito da gudu, ba tareda bin bahasi ba ta kama jibgar Farida daga ƙarshe ta kaita kitchen ta sa wuƙa a cikin...


Read / Download SAKATARIYA TA

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album