Subscribe for N1000/month for downloading access and an ad-free site. Contact WhatsApp +2348140419490 if you can't pay / subscribe. SUBSCRIBE

24 yin

GIDAN GWAURO Complete Hausa Novel Document by GIDAN GWAURO


GIDAN GWAURO

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 72686



GIDAN GWAURO

Reading Time: 6 Hours

Added On: 13, Aug 2024

Author: Asma Baffa ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : +2348061929616

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 373.99 kb

File Type: txt

Views: 870+

Download: 2732+

Last download: less than 1 second ago

Description/Story: [5/9, 9:55 PM] Sis Asma: 🏠🏠GIDAN GWAURO🏠🏠
COPY BY ZAINAB BULATAWA




FREE PAGE







BISMILLAH






1







Official






By
AsmaBaffa








INA GODIYA GA ALLAH DAYA BANI DAMAR SAKE RUBUTA SABON NOVEL,ALLAH YASA MU GAMA LAFIYA.

MASOYANA INA MIKO GAISUWA DA JINJINA ALLAH YA BAR KAUNA.




LITTAFAN DANA RUBUTA SUNE KAMAR HAKA

GASKIYA CE
MARAICIN RAHMA
MA'AIKACIYAR GOMNATI
CIRANIN AMANA
DUK INDA TA FADI
KAMARSU CE DAYA
KASUWANCI NA
JIN DADI SABO
HADIN KAI
ME MAGANI
TUBABBIYA

NA KUDI SUNE

RASHIN SA'A
TA GYARU
YAR KWANGILA
ADDU'AR KAWA.
GIDAN GWAURO.......






Ga masu bukatar siyen wannan novel ko wanne complt dari uku 300 ne.
RASHIN SA'A
TA GYARU
YAR KWANGILA
ADDU'AR KAWA

GIDAN GWAURO
masu bukatar shiga Group dinsa dari biyu 200 ne.

Masu siya ta Bank ga Accnt number

0175487861
Asmau Garba Muhammad
Gt bank.

Masu tura katin waya ta whatsApp, Vtu ko Transfer ga Number ta
08033933642.

'YAN NIGER ku nemi wannan number
+227 90 79 59 39.







Wannan page na masoyana ne Wanda novel Dina baya wuce su,Na Gode Allah ya bar kauna Musamman masu
Nemana Ina na shige.










Lokacin Damuna ne Gari yayi Dadi tare da sanyin Ni'ima,Iska tana kadawa kadan Kadan,a wani daji cikin wani Kogon dutse Wani ya fito kafarsa daure da sasarin sarka a Kafafunsa da hannayensa,Cike da rangaji Yana tangadi kamar yasha giya, a hankali yake iya tafiya Kafafunsa sunsha Dauri Har jini suke fitarwa,a hankali ya fito Yana rumtse Ido sakamakon Rana ta haske Masa Ido da yawa,alamar ya Dade Bai ga hasken Rana ba,cikinsa ne yayi kugi alamar yunwa,Ya Rasa Ina zai je a cikin Dajin,Jikin wata bishiya ya koma tare da kwanciya ya lumshe idanuwansa masu matukar kyau,Yana nishin yunwa kamar zai mutu.

Wata tsuntsuwa ce tayi kuka ai da sauri ya Ware daradaran idanuwansa a kanta,cikin Zancen zucinsa yace kwadayinta nake ji,harshe ya zaro tare da lasar jajayen lips dinsa Yana so yaci tsuntsuwa Amma Kash ba halin hakan, kwadayin tsuntsuwa yasa Ya Fara kokarin Balle sasarin dake Hannunsa a Dole sai yaci tsuntsuwa,idonsa yayi jajir sabo da yanda ya dage shi fa sai yaci tsuntsuwa Yana Haka yaji takun wani mutum a bayansa,da sauri ya juyo suka hada Ido da wani Babban Baushe masu farautar namun daji.

Baushen yace Samari waye ya daure ka haka? Daga Ina kake? Kyakyawan Saurayin ne ya bi Baushen da kallo,A zuciyarsa Yana cewa ko wannan sune mutane Yan Adam? To idan sune mutane Ni mene kenan? Baushen Ganin Saurayin Yana Maganganu shi kadai sai yace yaro ya sunanka? Kyawawan hakoransa ya bude jerarru kanana dasu farare tas yana Murmushi me matukar kyau,Baushe yace Kai yaro ko daga kasar larabawa akayi kidnapping dinka? Ko Kai Balarabe ne Wanda suke zuwa Nan aiki aka sace ka? Da gani Kai Balarabe ne sak hasken fatar da komai har gashinka na larabawa ne ya abin yake?

Matashin ya Rasa me zai cewa Baushen yace Ae kawai,Baki Baushe ya washe yace ai da ganinka kalar Hutu da Jin Dadi ne kalar Naira ne,Hannu ya mikawa Baushe alamar ya kwance Masa sasarin dake daure da shi,Ba musu Baushe yasa Karafansa yayi dabara ya sare sasarin har na Kafafunsa,Murmushi Matashin yayi na Jin dadi yace Na gode Sunana Alex,Baushe yace Uhm da ganin Sarkar Dake wuyanka an San Kai ba musulmi bane, ba komai ka mike wannan wannan hanyar zata kaika har babban titin Kaduna.
Matashin tafiya yaci gaba da Yi a hankali Yana tangadin yunwa.

A Haka Yana tafiya har ya Fara hango motoci suna yawo a Kan titi,gashi yaga wani kauye kusa da titin yace wato wannan sune mutane,Cikin kauyen ya shiga Ana ta kallonsa musamman kayan jikinsa masu daukan hankali,farar shadda ce dinki na Yan gayu cif cif jikinsa,Da wata sarka ta cross tafkekiya a wuyansa wannan ya nuna Christian ne ba musulmi bane,a jikin wata bishiya ya zauna Yana faman kallon duk abinda mutane sukeyi Yana Murmushi a hankali ya Furta dama Haka mutane suke abubuwansu gaskiya Nima sai na koma mutum Kamar su,Ruwa ya gani a rijiya Ana ja,har wajen ya taka yaje wani dattijo ne ya zuba a karamin kwano ya Mika Masa yasha ya koshi.

Tun daga wannan Rana Alex yake zuwa cikin kauyen kullum ya Sha kallon yanda mutane suke abubuwan su sai ya koma dajin Daya fito cikin Kogon dutsensa yayi ta gwadawa Yana koyon yanda mutane suke yin komai,Har Sallah yake gwadawa Amma Bai sai me akeyi ba ko ake cewa.
Abinci kuwa sai dai ya Kama tsuntsuwa ya gasa abinsa a dajin yaci,idan Kuma Bai Kama tsuntsuwa ba sai ya shiga kauyen ya tambaya a wani gidan a bashi yaci ya Kara gaba yayi ta Amai,ya rasa me yasa idan ba Nama yaci ba to Amai yakeyi har da Zazzabi,a Haka Har mutane Suka Fara ganowa Alex ba kalau yake ba amma ba Wanda ya kula shi,Yau ma Kamar kullum gani yayi Ana ta cin Abinci da cokali a Majalisa,yaga wasu Kuma da Sassafe suna motsa jiki exercise,ai komawa yayi daji ya dinga gwadawa sai da ya iya,har cin Abinci da cokali Haka ya ya dinga gwadawa da tsinke,har wanka sai da ya koya,Wasa Wasa sai ga Alex ya kwashe wata Biyar Yana koyon abubuwan da mutane suke Yi shima ya iya komai,Yaji kullum Ana Zancen kudi Amma ya Rasa mene kudin Nan da kowa yake magana kudi,sai na Samu kudi,ya gaji da jin Maganar kudi, ya kasa ganewa har ya yanke hukuncin tambayar mene kudi Wai.

Cikin kauyen ya shigo da Sassafe ya Fara tare wani Babban mutum yace Malam Ina da tambaya,Mutumin ya tsaya Yana jiran tambaya,Alex yace Wai Mene kudi ne? Naji Ana ta cewa kudi kudi Mene Wai kudi? Baki Bude mutumin ya kalli Alex lafiyayyen mutum zai Raina Masa hankali,tsaki yaja yayi tafiyarsa,Haka Alex yabi Wani Yana tambaya Babu Wanda ya saurare shi ma sabo da suna ganin ya Raina musu hankali da yawa,Da kyar ya samu wani Almajiri yace Masa malam kudi sune abinda ka siyi Shaddarka da su,kudi ake bayarwa a mallaki Abu,Alex yace mene mallaka? Uwarka ce malam cewar Almajiri,yace wayarka gata Nan katuwa a Aljihunka Ina gani itama kudi ce,Tsayawa Alex yayi Yana magana shi kadai waya Kuma? Aljihu? Yace ya kamata na shiga birni inda ake da wayewa a can Zan samu amsar tambayoyi na sai na koma mutum Nima.
Tsaki Almajiri yaja yayi gaba daga Nan Alex ya dauki Hanyar Shiga cikin garin Kaduna cikin birni Babba.

Dattijo ne ya kwada sallama a gidansa yace Ina Nabeela take Dan Ubanta yarinyar Nan Bata da mutunci Ni wallahi da Zan samu wani tsohon tuzuru Aura Mata shi zanyi,tabi ta Gama zubar min da mutunci a Unguwar Nan,Shekarun ta sun Kai ashiri taki fito da Mijin Aure so take sai kwayayen Haihuwarta sun Kare sun mutu a gida ba Miji,ace ban Isa da yata ba Ni Alhaji Hashimu na Haifi yarinya a cikina tafi karfi na,Kina gani tana Gama makarantar Secondary tace baza ta ci gaba da karatu ba ita Business zata Kama,har jari na Bata Amma ki duba kullum itace gantali da yawo gida gida,to gashi can ta tafi yawo ta bar kayan miyar a tabir dinta akuyoyin makwafta sun Zo sun cinye tumatur da Allayyahu tas, Baki Dattijuwa ta tabe tare da Furta Oh Ni Safiyya da ace Uwar Nabeela tana da Rai da tuni bakin cikin Nabeela ne zai Karasa ta,duk da kishiya ce kar ace na Fadi sharri,kasan Dan da ba naka ba.

Karar machine Suka ji an shigo gidan da Gudun tsiya,Baban Nabeela ne ya kalli me machine din sai ya ga Nabeela ce goye da kanwarta Yar Shekara bakwai a duniya a bayanta ga Kuma Kaya cikin katon buhunta,Babanta baiyi mamaki ba sabo da yasan Yarsa Nabeela ta iya abin Hawa kala kala,ta iya Keke,ta iya machine tun daga su Jin Chen,kanchen bare Kuma wani lifan da mota ta iya a garin yawonta da gwagwarmaya da Shiga cikin maza,Bata da tsinke Amma yanzu zaka ganta saman Machine,Keke ko mota ta mutane abokanta maza sabo da shige chigenta,Har a mota felleliya zaka ganta ciki tana tukawa ta aro.

Sakkowa tayi tare da sauke Yar kanwarta ta ajiye ta a saman Tabarmar da Babanta ke kwance,sannan ta koma ta dakko katon buhun data shigo dashi saman Machine ta ajiye a gaban Babanta tana huro hanci kamar zata doki mutane,Sabo da sun San halinta Babu Wanda yayi mamaki
Domin cigaba da karantawa sai ku downloading.
Yadda ake downloading na littafin: ku tabbata kunyi register da shafinmu sanna kunyi login, idan bakuyi register a kasa zakuga maballai guda biyu daya an rubuta LOGIN dayan kuma an rubuta REGISTER sai ku taba su kuyi register, daga nan sai ku yi subscription koda na naira 1000 ne, domin sai kunyi subs dinann ne kadai zaku iya dauko littatafanmu.

Ya ya akeyin Subscription namu : Bayan kun yi Login ko register daga kasa zaku ga wani jan maballi (button) an rubuta SUBSCRIBE sai ku taba shi zai kaiku inda zaku zabi package wato tsarin subs na ku da mu. akwai na wata guda, watanni biyar da shekara guda. da zarar kun zaba zai kaiku inda zaku biya kudin, wanda daga nan sai ku cigaba da downloading kawai abunku

ABUN LURA : duk wani littafi da kuka gani a shafinnan kyauta ne, wannan tsari mun zo da shine don mu samu hanyar da zamu iya rike shafin muna managing na shi, izan ku kayi subs na mu tamkar DONATION ne ku ka yi mana, ku ka bamu kwarin guiwa don mu ciagaba da kawo muku sabbin littatafai, amma duk wanda ya ga bazai iya ba toh zai iya karanta littafin kyauta a cikin shafinnan namu batare da ya downloading ba, kawai ya yi kasa zai ga Koren maballi (button an rubuta) START READING sai ya taba zai kaishi inda zai karanta littafin.

Sannan duk wanda yaga kamn wannan process din zai bashi wahala kai tsaye zai iya min magana ta whatssApp +2348140419490, ya tura min kudin ni kuma zan dora mai subs din akan account na shi

NB: iya ta haka ne zaku iya karanta wannan littafi a shafinmu babu wata hanyar. DAN ALLAH KU DAINA MANA MAGANA AKAN MU TURA MUKU LITTAFI TA WHATSAPP, BAMA TURAWA HANYA GUDA MUKE TURA LITTATAFANMU SHINE WEBSITE NA MU https://taskarnovels.com.ng DUK MAI BUKATAR LITTAFINMU YA JE CAN YA KYAUTA NE, AMMA DOWNLOADING KUWA BA KYAUTA BANE SAI YAYI SUBSCRIPTION NA WEBSITE NAM
This is not the real Download Button


Read / Download GIDAN GWAURO

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

This is not the real Download Button
Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album