Join Our WhatsApp Group

KAI MIN HALLACCI Complete Hausa Novel Document by KAI MIN HALLACCI


KAI MIN HALLACCI

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 100520



KAI MIN HALLACCI

Reading Time: 8 Hours

Added On: 09, Apr 2023

Author: Miss Xoxo ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : HASKE WRITERS ASSO

Author Phone : 09032345899

Book License : Paid

Category: Love Novels

File Size: 552.96 kb

File Type: txt

Views: 1838+

Download: 1520+

Last download: 1 hour ago

Description/Story: *............_KAI MIN HALACCI!_*
💕
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya

Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,

Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490

A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,

Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu

Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC

Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services

Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us

Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it

Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT

This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels


_*NA_*


_*©NANA HAFSAT_*
_*(MISS XOXO)_*


®_*HASKE WRITERS ASSO💡_*


*_SHAFI NA ‘DAYA_*


_بسم الله الرحمن الرحيم_
_In the name of Allah, the Gracious, the Merciful...!💕_


“Tsakanin d'an Adam..d'an Adam.. tsakanin d'an Adam da kud'i..! Kai..! Wayyo Allah na! Ooh! ya Subhan’Allahi Allah ka rabamu da babu ko ta mecece ma, na rantse da Allah idan aka ce yau baka dashi toh sunanka sorry Umma..”

Wani matashin saurayi dake sunkuye wajan rijiya yana wankin uniform d'insa shine yake wak'ar, yana kuma had'awa da addu'a duk da cewar yayi tane cikin takaici da jimami.

“Amin ya rabbil alamin Shamsu, ai talaka yana d'an-d'anawa a cikin k'asar nan, shi yasa muke son kayi karatu sosai, wata rana ka zama wani babban a k'asar nan.”

Matar dake zaune kan tabarma can nesa dashi take bashi amsa, tare da nuna masa burin su akan sa, nasan cigabansa nan gaba.

“Kai! Umma ni fa gaskiya wallahi na gama karatu daga secondary d'in nan, haba! hauka ake yi, ni yaushe zan zauna nayi ta cin boko kamar wani marar aikin yi? Ina.. billahil'azim babu inda zan d'ara daga wannan karatun kinji na rantse.”

Murmushi tayi tana girgiza masa kai,

“Shamsu kai yaro ne, ba zaka tab'a gane abinda muke son ka gane ba a yanzu, shin idan baka yi karatun ba ta yaya zaka cika burin ka a rayuwa nan gaba?”

Ya kad’e rigar uniform din, fara ‘kal da ita ya shanya a igiya kafin yace,

“Umma ba fa sai kayi mugun karatu kake zama wani a cikin k'asar nan ba, ki duba ki gani d'an majalisar jaharmu mai wakiltar mu iyakarsa sakandire, amma aka d'auki mulki aka bashi, shima sanatan mu iyakarsa NCE. Amman ki duba su Alhaji Aminu, su engineer Tijjani duk degree na biyu gare su, amman suna k'asa, saboda wad'ancan suna da kud'i shi yasa duk takarar duniyar nan sune suke cinye wa, dan haka na sawa raina wallahi daga wannan karatun ba zan d'ora wani ba Allah ya amfana wanda nayi.”

Tasan duk yadda zata nuna masa ba zai gane ba, Saboda abinda yake cikin zuciyarsa hakan yasa tayi masa fatan alkairi cikin ranta, can kuma ta d'ago tana kallan sa yana shanya wandon a jikin igiya tace dashi.

“Amman dai Shamsu ba harkar siyasa zaka fad'a ba ko? Ni wallahi bana son ta, Azo ayi ta zaginmu ana ambato ahalin mu wad'anda kai kanka baka sansu ba.”

Dariya yayi wanda kyakkywan dimples d'in sa suka lotsa, wushiyar sa ta bayyana, yana kallan Umman tasu yace.

“Kai Umma ke duk wata harkar samu sai kice bakya santa ki yi ta kushewa idan ki kaga anfi samu a ciki, toh bari dai mu gama makarantar sai muga abinda ya kamace mu muyi wanda zai yi dai-dai da ra'ayin ki.”

“Ah'ah ni ‘karya kake yi min Shamsu, yaushe na kushe abinda yake kawo samu ne? kawai dai ina nuna maka muhimman abubuwa ne da zaka yi ka cimma burin rayuwar ka, kaga da zaka samu ko NCE ko kuma 'yar diploma, kayi ka rike kwalin zai yi maka amfani nan gaba.”

Tsalle yayi ya dire kan k'afafunsa, kamar wani d'an k'aramin yaro, jin Umma tana kuma cusa masa son ci gaba da karatun da baya so, yana tafiya wajan bokitin da ya zuba ruwan d'auraya yace mata.

“Umma nafa gama yin karatu wallahi, indai wanda zai sanya na zauna wani malamin yazo ya koyar dani ne, haba Umma wai mai yasa kika dage sai nayi karatun boko ne? Ko Baba da yake malamin makaranta baya dagewa kan cewar sai nayi karatu, ki duba shi yayi har degree amma dubi albashin sa, kullum jiya i'yau gashi duk bashi ake biya dasu idan sun zo.”

Shiru tayi masa tasan tunda ya kafe toh ba zai yi ba, ko yayi ba zama zai yi ya fahimta ba tunda ya riga ya jahilci abin.

Jin ba tace komai ba yasa shima yayi shiru yana 'yar dariya k'asa-ka'asa, Umma ba ta san yadda ya tsani ci gaba da karatu ba musamman da yaga matsayin kwalinka a k'asar nan bayasa ka samu abinda kake so, dan haka yaki sanyawa zuciyar sa ‘kaunar yin karatu mai zurfi. ya gama wanke kayan ya shanya sannan ya shiga d'akinsu shi da yayansa ya d'akko sandal d'insa, zama yayi a kusa da ita yana goge su saboda baya son sai gobe yazo duk ya rasa yadda zai yi saboda Shamsu akwai tsafta.

“Umman mu ta kanmu, Allah dai ya barmu tare ya nuna min lokacin da zaki min aure.” Kallansa ta yi tana hararsa cike da mamaki kafin tace.

“Au dama saboda kayi aure shine baka son ci gaba da karatu ko? Toh wace yarinyar ce ma zata aure ka baka da sana'a gashi karatun ma kace ka gama yin sa? bari na gaya maka matan zamanin nan sunfi son auran mutum mai zurfaffan ilimin boko da arabi Shamsu kaje kayi tunani.”

D'an d'agowa ya yi yana kallan ta, yaga shi take kallo sannan ya gyara zamansa kamar wani babba yana cewa.

“Umma yanzu da kika dage sai nayi karatun gaba da sakandire shin Yaya Garzali da yake kanyin bokon nan mai yake dashi? Ina ce kullum sai yazo yace miki ki bashi da kud'in da zai sai handout ko biro ki d'auka ki bashi? gaskiya ni bana san wannan rayuwar ai ya kamata a ce idan ka girma kasan ka girma Ummah.”

“Shi kenan Shamsu Allah ya baka abinda yafi alkairi amin, amman ni bana son ka biyewa abokai suje su lalata min tarbiyarka, dan Allah ka tsare mana mutuncin mu Shamsu kaji?”

Yana matsar da takalman gefe yana amsa mata daga nan hira suka d'ora cike da shakuwa tsakanin su, suna hirar kamar ba uwa da d'ah ba, saboda yadda kowanne yake bawa abokin maganar tashi hakkin sa.

••• •••

Cikin yardar Allah kuwa yau gashi su Shamsu sun kammala makarantar gaba da primary(SSCE/Senior secondary school certificate) suna ta farin ciki, ko wanne da irin burin da yake a cikin ransa suna ta bankwana da juna kamar kada a rabu. Shamsu tsaye shi da abokansa Auwal shine babban amininsa sai Kabeer sannan Kamalu, suna ta faman maganar abin yi bayan sun bar makarantar. Auwal dake tsaye jikin bishiyar darbejiya yana gyara littattafan dake rike a hannunsa yace.

“Ai daga nan sai Bayero university kano, dan har na sanar da mutanan gidan mu kuma duk sun amince min, gaskiya ina son idan nayi karatun na samu wani babban office d'in na fara aiki a cikinsa.”

“Ni kam gaskiya ina sha'awar fannin lafiya kun sani dai ku ma, dan haka can zan ware na dinga yi muku allura idan an kawo ku babu lafiya.”

Kabeer ya fad'a yana yi musu dariyar shak'iyanci, suma duk suka kwashe da dariya, Kamal ya d'auki dutse yana jujjuya wa a hannunsa yace.

“Nima dai ina son yin gaba da karatun nan domin ina da burin son zama lecturer, abokai na ku ganni a gaban students ina zazzaga musu lectures wallahi abin yana bani sha'awa, ku dai kuyi mana fatan alkairi Allah ya cika mana burikan mu.'”

Murmushi Shamsu ya dinga yi jin yadda suke da burin zama cikakkun 'yan boko, wani irin kallo yake musu na baku da aikin yi shi kam ba zai iya aikin gwamnati ba duka government da Federal, Saboda gani yake tamkar wahala ce, har sai wata yayi zaka ji kararrawar kud'i, gashi nan Baban su har yanzu wahala yake sha d'an albashin ma ba isarsu yake yi ba, dan ma Umman su tana siyar da irin kayayyakin nan su daddawa, kanumfari, citta, barkono, kukar miya, busashiyar kub'ewa da dai sauran irin wad'annan kayan na buk'atar gida, kuma Alhamdulillah suna da rufin asiri dai-dai misali.

“Wai kai Shamsu kayi shiru, Ko har yanzu kana nan akan bakan ka, na yin aikin wahala ka samu kud'i?”

Kamalu ya tambayesa, kafin Shamsu yace komai Kabeer ya cafke maganar yana cewa.

“Yana nan wallahi akan bukatar sa, kasan ai banza ne shi, so yake kawai yaje yayi aikin da zai sashi yin baki da tsufa da wuri, ni wallahi ba zan iya ba shi yasa nake son yin karatu mai zurfi, ko irin aikin alhaji Tijjani na samu nake yi ai na warke, wallahi ace yau gashi Kamalu ya zama professor a wata babbar jami'ar wayyo Allah..”

Shamsu ya yatsina fuska tare da tab'e baki yana cewa.

“Kunsan Allah, ni duk harkar jira bana santa, haba ace kana namiji kuma lafiyayye har sai kajira wata yayi sannan za'a baka salary? Aji down wallahi, gara naje na nemi na kaina nima, ai duniyar akwaita da fad'i.”

“Toh mai zaka yi na neman kan naka Shamsu?” Auwal ya tambayesa cikin rashin walwala a fuskarsa.

“Ahh lallai ma ku d'innan, ga sana'o'i nan da yawa, zuwa zanyi Umma ta fara yi min kunun zaki ina kaiwa kasuwa na siyar.”

Kamar had'in baki duk suka kwashe da dariya, Kamalu harda bubbuga ‘kafa a k'asa yana rike cikinsa, kallan wani wawa gara suka dinga yi wa Shamsu, amman ya dake shima yana binsu da murmushi, ya kasa gano dalilin yi masa dariya har sai da Kabeer yace.

“Kunji gara, kai dai wallahi wani lokacin kamar ba wayis(wise)ba. Ya za'ai kana yaro da kai shekaru sha bakwai ka wani ce zaka yi tallar kunun zaki? ta ya har za kace talla tafi karatu Shamsu?”

“Ni fa gaskiya nafi sha'awar kasuwanci ne shi yasa nake ganin kamar idan na fara zanci riba, ku dai kuje kuci bokon ku amman gaskiya ni babu wata university da zanje.”

Duk rausayar da kai suka yi cikin jimami domin ba haka suka so ba, daga nan tashi su kai, suka yiwa juna sallama da abokai har suka baro cikin makarantar, a bakin titi duk suka rabu kowa yayi hanyar gida cike da farin cikin gama makaranta.

Shamsu na zuwa ya tarar da Umma tana ta faman aiki a kitchen, ‘kamshin da hancinsa ya dinga jiyo masa ne yasa shi nufar kitchen d'in, yana sake goge hancin sa dan ya sake jiyo k'amshin, fatan sa da burinsa ace a gidan ake yi ba wai a can makota ba.

“Alhamdulillah Umma wannan abin arzik'in daga ina yazo?”

Shamsu yayi tambayar yana d'aukar soyayyan naman kaza guda d'aya, k'ok'arin sawa a baki yake yi Umma tayi saurin zuwa ta ‘kwace tana dalla masa harara tace.

“Bana hanaka d'aukar abinda baka tambaya ba? Shamsu wai yaushe zaka san cewar girma kake yi ne? yanzu da ace banawa bane bafa kazo kaci nace dasu me? Ka dena bana so, nafi son ka dinga tambaya har sai nace ka d'auka tukunna.”

Fuska ya fara shafawa yana jiranta mik'a masa, idan ta gama yi masa fad'an dan ba wani damuwa yayi ba burinsa kawai yaji naman a cikin bakin sa, tana mik'a masa kuwa yabar gurin ya koma bakin ‘kofar d'akinta yana yagar tsokar fiffiken dake hannunsa, cikin jin dad'in gishiri da magin dake jikin naman ya fara magana.

“Toh Umma baki gaya min na waye ba, ko suya aka kawo miki ne daga gidan alhaji ishaq?”

Umma cikin ‘kosawa da tambayar da Shamsu yake yi mata tace dashi.

“Nace ban sani ba, koma dai na weye ka zuba ido kayi kallo mana.”

Shiru yayi dan tunda yaji a yadda take bashi amsa, ya tabbatar da cewar ya ‘kular da ita ya kaita har wuya, yana gamawa yayi cilli da k'ashin bayan ya tattaune sa kai kace dusa ce saboda tsabar iya tauna.

“Umma yau fa mun kammala sakandire ayi mana addu'a da fatan alkairi.” Murmushi yaga tayi tana yanka albasa yaji tace masa.

“Masha Allah Shamsu Allah yayi albarka ya bada ikon yin na gaba shima cikin yardar Allah.”

Yatsina fuskarsa yayi, ba tare da yace amin ba kasan cewar ta had'a da cewar yayi karatu. Jin yayi shiru yasa ta kallesa tare da komawa cikin kitchen tana yi masa fatan alkairi domin har yanzu tasan Shamsu akwai kuruciya a tare dashi. Sai da ta kammala soyawa tatas tayi pepper chicken, sannan ta d'akko ta kasa shi kwano-kwano, makotansu dake jikin katanga ta kullamawa, sannan ta d'ibarwa maigidan ta kuma d'ibarwa yayan Shamsu wato yaya Garzali, da kuma shi kansa Shamsun da idanunsa ke kan rabon da ake yi.

“Shamsu zo ka kai gidan malam Rayya, ka bawa Asabe kace gashi ba yawa.”

“Kai Umma sai nace musu wani babu yawa sai kace sun bada ajiya?”

Yayi maganar yana mik'a mata hannu dan ta bashi wanda zai kai d'in, hararar sa tayi, tare...


Read / Download KAI MIN HALLACCI

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album