Join Our WhatsApp Group

MALIKUSSAIFI IBNI ZIYAZZINUN Book 1 Complete Hausa Novel Document by MALIKUSSAIFI IBNI ZIYAZZINUN Book 1


MALIKUSSAIFI IBNI ZIYAZZINUN Book 1

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 14006



MALIKUSSAIFI IBNI ZIYAZZINUN Book 1

Reading Time: 1 Hours

Added On: 19, Dec 2023

Author: Aliyu Abubakar Sharfadi ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Adventure novels

File Size: 79.54 kb

File Type: txt

Views: 1223+

Download: 489+

Last download: 17 hours ago

Description/Story: MALIKUSSAIFI DAN ZIYAZZANUN
littafi na daya 1
part 1
post by Shuraih 99%

Godiya ta tabbata ga Allah madaukakin Sarki da manzon sa Annabinmu Muhammad tsira da amincin Allah su kara tabbata a gareshi,

wanda ya bamu iko ga jama'a domin su samu abin debe kewa da nishadantarwa yayin
karantashi.

Shi wannan littafin, fassarace daga harshen larabci zuwa na hausa domin jama'a Su amfaneshi.

Shi wannan littafi mafi yawancin mutanen yanzu basu sanshi ba, domin Malamai ne ada suke karanta wa jama' a shi idan sunajin nishadi.

Zakuji cewa Wannan littafin ya kunshi labaran soyayyaya, nishadi da kuma abubuwa iri daban-daban, wadanda suka kunshi sha'anin
bokanci da tsafe-tsafe wanda mutanen wancann lokaci suka kware a kai.

Za kuma aji yadda rayuwa take kasancewa ga
wannan sarki, tun tasowar sa da kuma girmansa, kama izuwa lokacin daya zama kasaitaccen Sarki da kuma mutuwar sa.

Kuma za aji cewa wannan littafin ya shafi bangaren addini da kuma ma'amaloli na rayuwar alumma. halakata. MAALIKUS-SAIF
Bin ZIYAZINUN a karan kansa an taba samu rayuwa irin tasa.

ldan muka duba tarihin masarautar BORNO zamu samu cewa daya daga cikin wadanda suka taba yin sarauta a wannan masarauta wadanda akeyiwa lakabi da Saifawa Dinas (Wato
Daular Saifawa), tayi kimanin Shekara dubu kafin ta gushe,

wannan zuria ta saifawa sun samo sunansu ne daga wannan babban Sarki kuma kamar yadda tarihi ya nuna shine ya kafata.

Don haka labari da aka bayar akan wannan Sarki SAIF yana iya zama kirkirerren labari ko
kuma shi Sarkin ya zamto antaba samunsa A hakikama yankin da wannan sarkin ya zauna wato HAMRA'U YAMEN ko YAMEN wato kamar yadda

wannan littafin tarihin ya nuna. A wani zamani mai tsawo daya wuce, zamanin Annabi Nuhu {Alaihissasatu wassalam yayi
wa 'ya'yansa addu'ar Allah yasa daya daga cikin 'ya'yansa a samun wanda zai mallaki duniya ya kuma yada addinin Allah.

Cikin ikon Allah sai wannan addu'a ta sa ta fada akan babban dansa SAMU, wanda shi SAMU a wannan lokaci zuriyar sa farare
ne {larabawa), shikuma karamin dansa HAMU zuriyar sa bakake ne.

Bayan Sun bar wajen Mahaifinsu, sai SAMU ya doshi gabashin duniya,yayin dashi kuma HAMU doshi yammacin duniya.

Bayan wani lokaci mai tsawo, sai akayi wani Sarki mai suna ZIYAZINUN shi wannan Sarkiire-iren zuriar SAMU ne, kumaya samu tarihin adduar da Annabi Nuhu {Alaihissasatuwassalam} ya yi wa kakansu na cewa "Allah yasa a irin zuriyarsa a samu wanda zai mulkiduniya, kuma a samu wanda zai yada addinin ibrahimiyya, da yake a wannan lokaci zamanin Annabi Ibrahim ne{Alaihissasatu wassalam}. Sarki ZIYAZINUN ya lashi takobin InAllah ya yarda a kansa wannan addu'ar zata fada, saboda haka ya yi ta yake-yake a gabashin duniya kuma ya murkushe kasashe da dama da yaki, har ya fado yammacin duniya.

Sai da takai hardai tsufa ya riskeshi. Wata rana Sarki ZIYAZINUN ya sauka a wanı guri, sai yaga yanayin wannan waje yana da kyau kuma yana da dadin zama, saboda haka sai yasa aka gina masa birni aka sa masa suna HAMRA'U YAMEN.
Shi wannan birni daya ginaa yana karkashin
masarautar HABASHA ne, wanda a wannan
lokaci ita wannan kasa tana karkashin wani sarki mai suna SAIFURRA' ADU su kuma ire- iren HAMU ne wato su bakake ne.

Sarki SAIFURRA'ADU ya samu labari cewa ga wani farin Sarki can ya sauka a kasar sa harya kafa birni ba tare kuma da izininsa ba. Dan haka sai ya tura yan leken asiri domin su gano masa irin shirin da Sarki ZIYAZINUN yazo dashi.

Suka je suka sanar wa da Sarkin su cewa ai Sarki ZIYAZINUN yazo da runduna ta sadaukai masu tarin yawa, kuma suka fada masa cewa bazai iya yakarsa ba.

Nan da nan Sarki SAIF yasa a ka tara masa bokayen kasar HABASHA domin su ba musulmai bane, taurari suke bauta mawa. Ya Ya

umarci bokayen nan dasu duba masa su gani idan ya yaki wannan Sarki akwai nasara ko
babu. Bokayen nan suka dukufa suka fara bincike kowanne yayi- yayi amman babu nasara, karshe dai suka sanar wada Sarki SAIF ya hakura babu nasara. Sarki ya sallamesu suka watse daga nan kuma Sarki yasa a ka kira masa wasu manyan bokayensa masu Suna SAKARADISA da SAKARAJUNA da Wazirinsa mai suna Waziri BAHARU.

Nan da nan wannan mutane guda uku
suka zo gaban Sarki SAIFI suka zauna. Sarki ya ce **Yana so ne su bashi shawarar yadda zai bullo wa Sarki ZIYAZINUN?".


Da bokayen nan suka ji wannan bukata ta Sarki sai sukace "Tauraruwa ta baka nasara, ai abinda zaka yi shine ka dauki daya daga cikin yardaddun bayin
ka ka bata guba, ka ce kana so ta boyeta a jikinta yadda kowa bazai iya ganinta ba, idan ta boye sai ka turata izuwa Sarki ZIYAZINUN a matsayin kyauta ta karramawa, ita kuma ka umarceta da idan ta tashi bawa Sarki ZIYAZINUN ruwa ko abinci da ta saka masa wannan gubar daya ci ko ya sha, sai ya mutu kaga shiken ba sai mun yakesa ba.

Sarki SAIF yayi murna da wannan shawara daga bakin SAKARAJUNA. Nan da nan yasa a ka kirawo wata kyakykyawar kuyanga wadda
tana daya daga cikin yardaddunsa
KAMRIYYA.

Aka kawo guba mai Suna
ya bata ya ce "Ta boye inda ba wanda zai ganta koda cajeta aka yi". KAMRIYYA ta karbi gubar nan ta cusa a gashin kanta yadda
inba wanda ya sani ba ba yadda za' ayi mutum ya gane. Daganan ya yi mata bayannin ce wa zaiyi Sarki kyautar ZIYAZINUN, idan ya karbeta ta ga suna tare to tasan yadda za tayi domin ta bashi wannan gubar ko dai a abinci ko kuma ruwan sha
yaci ko ya sha.

Ya ce "Idan ta aikata hakan zai 'yantata kuma zai bata dukiya mai tarin yawa,idan kuma ta kasa yin hakan to muddin ta dawo HABASHA to

sai ya halakata". Da KAMRIYYA taji haka sai ta ce "Zata aikata duk abinda Sarki yake so.

Shi kuwa Waziri BAHARU da yake musulmi ne, ya musulunta ne ba tare da sanin Sarki SAIF ba domin da yasan da musuluncinsa daya sa hallakashi, saboda da gudun abinda zai sameshi sai ya boye an musuluncinsa.


Saboda kishin addini, kuma ZIYAZINUN musulmine sai yasan Sarki
hankalinsa ya tashi, kuma yasan

saboda da gudun abinda zai sameshi sai ya boye musuluncinsa. Saboda kishin addini, kuma yasan Sarki ZIYAZINUN musulmine sai hankalinsa ya tashi, kuma yasan lallai Sarki ZIYAZINUN bazai iya gane makircin da aka kulla masa da KAMRIYYA ba.

Dan haka sai ya rubuta wasika zuwa ga Sarki ZIYAZINUN yayi bayanin ce wa "Shine Wazirin
Sarki SAIF, kuma shi Musulmi ne, ya kuma yi masa bayanin duk irin makircin da
aka kulla masa da KAMRIYYA duk ya rubuta a takardar, daya gama shine yayi kiran
wani yardajjen bawansa ya bashi wannan takardar, ya ce "Yayi sauri ya riga yan
aiken Sarki SAIF zuwa wannan birni na HAMRA'U YAMEN ya kai wa Sarki SAIF
wannan takarda ba tare da wani mutumin ya ganshi ba, sannan ya fada masa ce wa
"Idan har ya aikata hakan kuma ya dawo to zai 'yantashi, kuma zai bashi dukiya mai
tarin yawa'".

Waziri ya bashi takarda wannan bawa nasa ya daura sirdi ya sukani doki yabi ta wata barauniyar hanya ya nufi HAMRA'U YAMEN. Cikin dare ba tare da kowa ya ganshi ba...

Bayan kwana uku sai akayi sa'a wannan bawa na Waziri ya riga yan aiken sarki SAIF zuwa Hamrau Yameen.

Da zuwansa ya isa fada gurin Sarki ZIYAZINUN a kai masa iso gurin Sarki, ya fadi yayi gaisuwa yakuma isar da sakon Waziri BAHARU gurin Sarki ZIYAZINUN, yakuma ce wa Sarki ya sallameshi da wuri domin.

kada yan aiken Sarki SAIF suzo su taraddashi anan suyi tunanin wani abu. Nan da nan Sarki
yayi masa kyauta ya sallameshi ya juyo izuwa kasar Habasha.


Bayan kamar sa'a uku saiga yan aiken Sarki SAIF sun iso kasar HAMRA'UU YAMEN. Da zuwansu suma sai suka wuce fada, akayi masu iso gurin Sarki ZIYAZINUN, da isarsu suka fadi gaban Sarki suka gaidashi kuma suka bashi kyautar KAMRIYYA da Sarkisu Sarki SAIF yaba Sarki ZiYAZINUN.

Koda Sarki ZIYAZINUN yaga wannan sako sai ya sake gaskata bayanin da Waziri BAHARU ya fada masa, amman dukda haka sai Sarki ZIYAZINUN ya karbi KAMRIYYA ya nuna kamar baisan makircin da ake shirin kulla masa ba.

Yasa aka bawa yan aikennan masauki suka kwana kashe gari suka kama hanya izuwa kasar HABASHA.


Bayan ansamu kamar wata daya. Wata rana sai Sarki ZIYAZINUN ya kadaita da
kuyangar da aka kawo masa wato KAMRIYYA, a wannan lokaci ya zare takobinsa ya umarceta da ta fito da gubar da aka bata ta bashi in kuma taki to zai halakata, da KAMRIYYA taga zai halakata sai ta ciro gubar daga kanta ya karba, sannan suka kwanta tare a wannan dare dai Sarki ZIYAZINUN bai gushe ba saida kuyanga KAMRIYYA ta samu ciki dashi.

Da Sarki yaga ta samu ciki sai ya kira wani
malamin sa yace ya buga masa kasa yagani, sai wannan Malamin yaga ai wannan ciki
na KAMRIYYA namiji zata haifa kuma shine wanda zai mulki duniya.

Sai ya fada wa Sarki wannan labarin, Sarki yayi murna kwarai. Daga nan sai Sarki ZIYAZINUN ya rinka nunawa KAMRIYYA kauna yana tattalinta.

Lokacin da cikin KAMRIYYA ya cika wata na hudu sai Sarki ZIYAZINUN ya kwanta ciwon ajali, inda yayi wasiyya cewa idan ya nmutu KAMRIYYA ta hau karagar mulkinsa har ta haihu, idan Dan ya girma ta sauka tabashi mulkinsa.

Bayan yan Kwanaki ya cika inda KAMRIYYA taci gaba da mulki kasar HAMRA'U YAMEN. Da aka samu yan kwanaki KAMRIYYA tana kan gadon sarauta sai ta rika dauko mutanen HABASHA dai-dai da dai-dai tana kawosu majalisar kasar HAMRA'U YAMEN tana kuma korar mutanen Sarki ZIYAZINUN suna mutuwa.


Cikin dan kankanin lokaci duk ta kori mutanen Sarki ZIYAZINUN daga majalisa ta
mayesu da sababbi.

Ba dadewa cikin KAMRIYYA yakai wata tara, ta haifi yaro namiji kyakykyawa fari tamkar mahaifinsa.

Tun lokacin da KAMRIYYA ta haihu,
kuma taga ta haifi na miji sai wani abu ya dinga darsuwa a zuciyarta.


Bayan gari ya waye sai KAMRIYYA ta shirya jaririn ta fito dashi fada domin jama'a su ganshi, bayan ta zaunane a bisa karagar mulkinta sai ta ajiye jaririn daga
gefe bisa wata shimfida wadda ba kowanne jariri ake kwantarwa akai ba sai 'ya'yan
manyan Sarakuna.

A wannan lokaci sai jamaar wannan gari suka fara zuwa wajen wannan jariri suna kwasar gaisuwa suna cewa "Yaron kuwa kamarsu daya sak da
ubansa suna cewa munyi mubayi'a."

Bayan sun gama kwasar gaisuwa gaban jaririn
tare da masa adduar Allah ya raya sai kuma su juya kan KAMRIYYA suyi gaisuwa.


Gani cewa tun yanzu, tun ba'aje ko inaba gashi anfara mancewa da ita ta wannan
jaririn akeyi sai kishi ya kamata, anan sai tasan gaba tubeta zasuyi su nada yaron.

MALIKUSSAIFI DAN ZIYAZZANUN
littafi na daya 1
Part 2
post by Shuraih 99%
.
KAMRIYYA ta boye abinda ke damunta a zuci da dauki yaron ta koma cikin gida
jama'a kowa ya watse.

Da isarta gida ta zauna tayi shiru tana tunani, hankalinta yayi
kokoluwar tashi domin tasan lallai idan wannan yaron ya taso ya girma ya samu
wasiyyar uban sa to lallai sai ya tureta daga gadon sarauta ya hau, kuma gashi ita ta
dandana giyar mulki taji da dadi.

Saboda haka ta yanke shawarar kawai ta kasheshi
shiya fi. Ta dauko wuka zata yankashi amman saita fasa, ta sake yunkurawa zata
yankashi sai ta fasa, ana uku data yunkura zata yanakashi sai wata tsohuwar kuyanga
ta shigo dakin koda ganin abinda ke shirin faruwa sai tace kai! Keko mai wannan
jariri yayi maki da har kike yunkurin hallakashi?

Nan KAMRIYYA ta fada wa
wannan tsohuwar dalilinta da tsohuwa taji haka sai ta bata shawarar kada ta yankashi
ta bari sai dare ya tsala su hau dawakai su biyu su sulale ba tare da kowa ya gansu ba
suje can daji su yadashi, kana su ajiye dukiya tare dashi domin duk wanda ya tsincesa
yayi amfani da wannan dukiya wajen rainonsa, domin idan ya taso hannun wani bazai
taba tunanin shi dan Sarki bane balle ma har yayi wani tashin hankalı.


Sarauniya KAMRIYYA ta yarda da wannan shawara ta tsohuwa ta fasa yankashi
ta bari har dare ya raba sannan suka sulale kamar yadda tsohuwa ta fada, sukayita
tafiya, har saida suka fita daga cikin kasar kana suka ajiye jaririn a gindin wata
bishiya, kuma suka ajiye akwatun cike da kudi sannan sukayi komawarsu.


Can cikin dare jariri ya farka ya fara kuka shi kadai a cikin daji, can yanata kuka
sai matar Sarkin fararen aljanu tazo giftawa tana dauke da yarta mai suna AKISA,
wadda a wannan lokacin tana shayar da ita.


Da aljanan nan taga jinjirin nan sai
tausayinsa ya kamata, sai ta tsaya ta daukesa ta bashi nononta yasha ya koshi, daya
koshi sai ya koma bacci, ita kuma ta ajiyeshi ta dauki yarta tayi gaba.


Can da asuba tayi jaririn nan ya sake farkawa ya kama kuka yana cikin kukanne sai
ga wata barewa mai shayarwa tazo wajen, taga jaririn nan sai ta tsugunna ta kara
masa nononta yasha.

Yana cikin Shane kawai sai wani maharbi ya hango barewar
nan. Aiko ya lallabo ya na sanda saboda barewar bata ganshiba, koda ya matso kusa
sai yaga ai barewar nan jariri Dan mutum take bawa nono, sai ya tsaya ya na mamaki
hardai barewar nan ta ganshi ta gudu.


Maharbin nan ya matso kusa da yaron nan ya
tabbatar dan mutum ne, kuma ga wata akwatu kusa da shi, daya bude akwatun yaga
dukiya sai ya maida yarufe, ya dora akwatin a bisa Kai, yakuma dauki jaririn ya
rungumeshi ya na murna ga dukiya ga kuma Yaro sun samu.

Saboda haka ya juya
akalarsa zuwa gida.

Shi wannan mutumin mutumin kasar DUWAR ne, kuma ita wannan masarsuta ta
na karkashin Kasar HABASHA ne.

Da Isar wannan Maharbi gida tundaga waje ya
Fara kwala wa matarshi Kira harya shiga cikin gidan.

Da isarshi ya mika mata yaron,
kana ya sakko da akwatun da yake a kansa, sannan ya kwashe labari kaf! Ya bata.


Yace kinga shikenan daman bamu taba haihuwaba gashi Allah ya bamu d'a, sannan
kuma ga dukiya Allah ya bamu.


Da matar tajihaka sai tace "Haba! Mai gida kaika dubi irin.wannan kyakykyawan
yaron da ganinsa kasan dan sarakuna ne, KO kuma manyan attajirai ta yaya zamu I
ya rikeshi? Kuma kaga shi farine muko duk bakakene ai. Ana gani za ace satoshi
mukayi aje a samu a cikinwani hali, kawai yanzu ka daukeshi kaje ka Kai wa Sarki shi
domin wannan yaro yafi karfin mu.

Da mijin yaji haka sai ya zauna yayi tunani kuma

saiya aminta da shawarar matar tashi. Saboda haka saiya kinkimi akwatunan sannan
ya dauki jaririn ya nufi gidan Sarki. Yana isa bayan yayi gaisuwa ga Sarki ya kwashe
labari Kaf ya labarta wa Sarki.

Sarki ya karbi wannan jaririn daga hannun maharbin nan.
Shidai wannan Sarki sunan sa AFARA'U, kuma ya kasance karamin Sarki ne dake
karkashin babban Sarki SAIF na HABASHA. Sarki AFARA'U daman bai taba
haihuwa ba, sai yayi murna da samun wannan jaririn ya baiwa matarsa mai suna
DAHASHANATU yace ta rikeshi dukda su bakakene shikuma wannan yaron farine
{Balarabe) ne.



Ita kuma can wannan Aljanar da taba jaririn nan nono ya sha, data koma gida, sai
take bawa mijinta labarin cewa "Tagawani jaririn mutum kwance a daji shi kadai, ta
daukeshi ta bashi nononta yasha."

Da mijin yaji wannan labari sai yace "Ai tunda
kika bashi nononki ai ya zama danki sbd...


Read / Download MALIKUSSAIFI IBNI ZIYAZZINUN Book 1

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

2 Comments On MALIKUSSAIFI IBNI ZIYAZZINUN Book 1
avatar
haruna-dau

4 months ago

Reply

I really love to read this novel

avatar
abdullahi-isah-mika39i

4 months ago

Reply

Yeah

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album