Join Our WhatsApp Group

RIJIYA GABA DUBU Complete Hausa Novel Document by RIJIYA GABA DUBU


RIJIYA GABA DUBU

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 30840



RIJIYA GABA DUBU

Reading Time: 2 Hours

Added On: 18, Jul 2023

Author: Abdulaziz Sani Madakin Gini ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Adventure novels

File Size: 164.89 kb

File Type: txt

Views: 4032+

Download: 1456+

Last download: 3 hours ago

Description/Story: RIJIYA GABA DUBU
Littafi na daya 1
Na Abdulaziz sani m gini
Ebook publish by - http://hausaebooks.cf

Typing:- Ibrahim S combatant
Post:- Shuraih Usman
@Shuraih 99%
Part 1A
.
Saurayin gudu yake iya karfinsa acikin dajin domin ya
ceci rayuwarsa,
.
yana gudu yana waigen bayansa cikin
tsananin tsoro,amma baya ganin komai kuma baya
jin sautin komai face na masifaffun karnukan dake
biye dashi.
.
Su dai wadan nan karnuka sun kai guda saba in da
doriya kuma sun kasance jibga jibga tamkar ba
karnuka bane kai kace kurayene sabo da girmansu da
kwarjininsu gami da ban tsoro,musamman aka
kiwata wadan nan karnukan kuma aka basu horo na
musamman domin suyi gadin babban kurkuku na
birnin Kisra.
.
A tarihin birnin na kisra tunda aka gina kurkukun
tsawon shekaru arba in ba ataba samun fursuna da
ya taba guduwa daga cikin sa ba sabo da karfin
tsaron da ke cikinsa sai wannan saurayi wanda ake
kira IMHAL IBN IMZANU,
.
sabo da tsananin karfin
gudun Imhal ne ya baiwa karnukan tazara ta kimanin
taku sittin amma sabo da nacin karnukan da mugun
horon da suka samu sai gashi sun fara hango shi,nan
fa suka kara kaimi,nan fa Imhal ya kara kaimin
gudunsa alokacin da ya waigo ya hango su yaci gaba
da falfala azababben gudu ta cikin kwazazzabai da
sarkakiya,
sabo da karfin gudun ma har tashi sama
yake yana tsallake duwatsu da karyayyun bishiyoyin
da suka fadi kasa
.
Shi dai Imhal gudun kawai yake yi acikin dajin amma
baisan inda yake dosa ba,sabo da baisan ma a inda
yake ba bare ma yasan hanyar da ya kamata yabi, a
duk sanda ya tuno da bakar wahalar da ya sha kafin
ya sami nasarar guduwa daga kurkukun sai ya kara
kaimin gudun nasa yana mai ayyanawa a ransa da dai
a kamasa a raye a mai dashi cikin kurkukun gwara a
sami gawarsa sabo da azabar da take cikin kurkukun
ta wuce tunanin mai tunani.
.
Asalin Imhal bin Imzanu mutumin birnin misira ne
kuma shi ba dan kowa bane kuma bai aikata laifin

komai ba,mahaifinsa wani makiyayi ne mai kiwon
dabbobi a daji,don haka rayuwar Imhal gaba daya a
cikin daji take,sai dai a karshen kowane sati ranar
Lahadi sukan shiga cikin gari suyi dan siye-siyen su
sannan su koma daji inda suka gina bukkarsu.
.
Imhal ya taso da Jarumtaka juriya da iya
farauta,sanan komai yawan dabbobi idan ya tafi kiwo
dasu yana iya sarrafa su
.
Lokacin da Imhal ya fara girma ya cika shekaru goma
sha shida ne ya tambayi mahaifinsa tsoho Imzanu
yace ya kai Abbana me yasa baka taba bani labarin
mahaifiyata ba?ban santa ba kuma bansan yanda
akayi ta mutu ba kullum sai kace dani kawai mutuwa
tayi,kayi sani cewa yanzu ni ba yaro bane karami na
mallaki hankalin kaina yakamata ka sanar dani
gaskiyar al amari,
koda tsoho Imzanu yaji wannan
batu sai hankalinsa ya dugunzuma ainun yayi shiru
yana mai sunkui da kansa kasa,kawai sai idanunsa
suka ciko da kwalla hawaye ya fara zubowa kas,
a sannan ne ya dago kai ya dubi Imhal yace yakai dana
kasani yau ka tambayeni wani sirri wanda dama nayi
alkawarin bazan sanar dakai ba sai bayan ka mallaki
hankalinka,don kada hankalinka ya dugunzuma
kwakwalwarka ta kasa daukar al amarin, koda imzanu
yazo nan a zancensa sai ya sake yin shiru kamar bazai
iya cewa komai ba,da kyar ya sake dago kai ya dubi
Imhal muryarsa na rawa yace ka gafarceni yakai dana
bisa abinda zaka ji daga bakina yanzu domin zakayi
matukar mamaki kuma zai iya girgiza ka,maganar
gaskiya ita ce ni ba mahaifinka bane na jini,koda jin
wannan batu sai zuciyar Imhal ta buga da karfi,nan
take idanunsa suka kada sukayi jawur,bai san sanda
hawaye ya zubo masa ba yace yanzu idan ba kaine
mahifina ba to wanene? Bansan kowa ba a rayuwata
sai dai kai kadai,
kaine kasan cina da shana tundaga
kuruciyata har izuwa yanzu,me yasa uban nawa ya
gujeni ya barni a wajanka cikin daji inda babu jin
dadi da tsaro?
.
lallai kuwa ashe babu soyayya tsakani
na da uban nawa tunda bai damu da rayuwata ba.
Koda Imhal yazo nan a zancensa sai tsoho imzanu ya
zubar
da hawaye sannan yace
Ni kaina bansan waye
mahaifinka ba,ka saurara dakyau kaji labarin da zan
baka yanzu,
wata kila idan kaji labarin zuciyarka tayi

sanyi ka rungumi kaddara a bisa halin da ka tsinci
kanka a ciki
....... ..¤¤¤¤¤¤¤
Wata rana da safe na fito kiwo acikin dajin nan ina
kada dabbobi na sai kawai na hango wasu mutane
bisa keken doki sanye da bakaken tufafi kuma sun
rufe fuskokinsu su biyu sun nufi bakin wani katon
rami mai zurfi da fadin gaske,cikin hanzari na kada
dabbobina izuwa cikin duhuwar bishiyoyi nima na
sami wuri na buya,
dama wadannan mutane basu
ganni ba,ina nan labe cikin duhuwa sai naga
wadannan mutane sun fiddo gawar wata mace daga
cikin keken dokin sun cillata cikin wannan
ramin,
kawai sai suka shiga cikin keken dokinsu da
sauri suka fice daga cikin dajin gaba daya,sai da na
tabbatar da cewa sunyi nisa da tafiya kuma babu
alamar cewa zasu dawo sannan na ruga izuwa bakin
wannan ramin na leka cikinsa kawai sai naga ashe
wata kyakkyawar mace ce aka yanka ta har a sannan
jini na bulbulowa daga cikin makogwaronta kuma
tana dauke da tsohon juna biyu,nan take naji na
kamu da tsananin tausayinta,
.
don haka sai na yanke
shawarar na shiga cikin ramin na dauko gawar
wannan mata domin na suturta ta sosai na haka
kabari mai kyau na binne ta,idan ma na barta acikin
ramin zata rube ne warinta ya dameni tunda ramin
yana kusa da inda bukkata take,nan fa na fara tunanin
dabarar da zanyi na iya shiga cikin wannan rami har
na iya dauko gawar,sai da nayi tunani na tsawon 'yan
dakiku sannan dabara ta fado mini,kawai sai na ruga
da gudu izuwa cikin bukkata,na dauko igiya mai tsawo
sannan na dawo bakin ramin,na daura igiyar a jikin
wata bishiya na wurgata cikin ramin sannan na kama
igiyar ina binta ina shiga ramin,sannu a hankali na isa
kasan ramin,koda naje kan gawar na duba ta sai naga
ashe da ranta bata mutu ba domin numfashinta na
fita kadan-kadan,cikin gaggawa na sunkuci wannan
mace na goya ta a bayana na daureta tamau,na sake
kama igiyar nayi iya kokarina na fito daga cikin ramin
goye da matar a baya na,hankalina a
dugunzume,sauri nake kawai na jarraba ceto
rayuwarta,ina fita daga cikin ramin na ruga da ita
izuwa cikin bukkata,na shimfide ta a kasa sannan nayi
sauri na dauko allura da zarin dinke fata na dinke
raunin wuyanta sannan na shafa magani akan
raunin,A sannan ne na kara hancina a dai dai hancin
matar don naji ko tana yin numfashi,amma sai naji
shiru alamar babu rai a jikinta,nan fa bakin ciki ya

lullube ni naji kamar na fashe da kuka sabo da
takaici,gashi nasaa wahalar dauko ta daga cikin
wannan ramin mai zurfi har ma tafin hannuwana sun
dade saboda kama igiya,cikin sanyin jiki na mike na
sunkuya da nufin daukar gawar na fita da ita waje
inda zan binne ta,kawai sai naji tayi tari,numfashinta
ya dawo,nan take murna ta kamani na ruga na dauko
wani ruwan magani na dura mata a baki dakyar tasha
mukurwa uku,jin kadan sai idanunta suka bude
dakyar,koda tayi arba dani sai naga ta firgita ta
yunkura zata tashi amma sai na danne kafadunta na
hana ta tashi,matar ta budi baki da nufin tayi magana
sai ta kasa,kawai sai naga tana dariya,wani lokacin
kuma sai ta hade fuska ta kama kuka tana fisgefisge,nan fa na gane lallai wannan mata ta samu tabin
hankali,al'amarin da yayi matukar bakanta raina
kenan domin naso ace ta iya yin magana acikin
hankalinta,domin na tambayeta ko ita wacece da
kuma wadannan mutane da suka kawo ta dajin acikin
keken doki a matsayin gawa,abinda zuciyata ta aiyana
min shine in ma basu bane to sun san wanda ya
kasheta,kuma akwai wani boyayyen al'amari akan
kisan nata,daga wannan rana naci gaba da jinyar
wannan mata har tsawon kwana ashirin da daya,A
tsawon wadannan kwanaki kullum a kwance take
kuma koda tayi yunkurin mikewa zaune sai ta kasa
sabo da raunin da yake makogwaronta,haka kuma
bata taba yin magana ba sai fisge-fisge da dariya
irinta mahaukata,abinci kuwa sai dai na dura mata
abaki tana ci tana kuka sabo da ciwo,da yake naga
tana dauke da juna biyu sai na dinga yawan bata
madarar shanu gami da abincin da yake gina jiki
domin abinda ke cikinta ya samu cikakkiyar lafiya,a
kwana a tashi har wannan mata ta shafe wata uku cur
a wajena,a sannan ne raunin makogwaronta ya
warke sumul har ya zamana cewa tana iya magana
sosai,amma a koda yaushe babu magana ta hankali
da nutsuwa a tare da ita sai maganganu irin na
mahaukata,nayi iya kokarina akan ta gayamin ko ita
wacece,daga inda take da kuma yadda akayi ta shiga
wannan hali sai tayi ta kyalkyala mini dariya,ganin
hakane yasa tausayinta ya karu a zuciyata,sau bakwai
ina nemo masana ilimin maganin mahaukata,wato
likitocin mahaukata suna zuwa su dubata kuma su
bata magani,amma duk a banza lafiya taki
samuwa,sau tari matar takan sulale ta nausa cikin
daji bansani ba,sai nasha wahalar nemota,bisa
wannan dalilin ne ma duk sanda zan fita kiwo ko
farauta sai na tafi tare da ita,wato na daina barinta a
gida.
Lokacin da cikinta ya tsufa sai tafiya da ita kiwo ko
farauta ya gagara,don haka nima sai na hakura da

zuwa ko ina,na tanadi abincina da na dabbobi na mai
yawa wanda zai kai tsawon kwana arba in,Ai kuwa
adaren kwana na talatin da bakwai nakuda ta kama
wannan mata acikin tsakiyar dare.Al'amarin da yai
matukar dugunzuma hankalina kenan tunda babu
halin in ruga cikin gari in nemo ungozoma,Da yake na
taba shiga irin wannan hali da nake tare da matata
wacce ta rasu a wajen haihuwa abinda ta haifa ma
yazo a mace,sai na shiga taimakon wannan mata,nine
na yankewa jaririn cibiya,na wanke shi sannan na
kimtsa mahaifiyar tasa,matar taci gaba da rainon
jaririnta tana shayar dashi ni kuma ina cigaba da fita
farauta da kiwona ina barinsu a gida,har tsawon
shekara daya da wata bakwai muna tare sannan
yaron ya fara tafiya da kafafunsa.
Kwatsam wata rana naje kiwo na dawo sai na nemi
wannan mata sama da kasa na rasa,kuma ga dannan
ta bar shi acikin bukka a zaune shi kadai yana ta tsala
kuka,cikin dimaucewa na dauki yaron na gaya shi a
bayana sannan na bazama neman wannan mata
wacce ko sunanta ban saniba bare na dinga kwalla
mata kira,Abu kamar wasa sai da na shekara daya da
wata tara ina nemanta amma ko alamunta ban gani
ba acikin wannan daji.A tsawon wannan lokacin ni
nake kula da wannan yaro da ta haifa dare da rana,ya
zama cewa na shaku dashi ainun shima haka
.Kwatsam wata rana da yammaci ina wasa da yaron a
kofar bukkata kawai sai na hango wannan mata daga
can nesa ta durfafo bukkata,cikin alamun tsananin
mamaki na mike tsaye na zuba mata idanu,matar ta
rame matuka,kuma duk rigar jikinta ta
yayyage,sannan tayi baki sabo da wahala da
kazanta,koda ta iso daf dani ta dubeni sai ta fashe da
kuka ta durkusa kasa bisa gwiwoyinta tana mai
neman gafarata tamkar mai cikakken hankali,nan take
naji na kamu da tsananin tausayinta don haka sai na
kama kafadunta na tasheta tsaye kuma na rungumeta
a kirjina a karon farko tun haduwa ta da ita,ita kuma
sai ta kankame ni ta da da fashewa da kuka,kawai sai
na janye jikina daga nata na dubeta nace me yasa
kika gudu kika barmu?shin kin manta ne cewa kin bar
danki a hannu na?koda jin haka sai matar ta dubi dan
nata ta girgiza kai tace ai ni kananin yaro na bar maka
bai kai wanan girma ba,da jin haka sai nayi dariya
nace to ai kullum mutum dada girma yake har yanzu
baki gaya min inda kika tafi ba kika barmu,Matar ta
bushe da dariya sannan ta hade fuska tace shan iska
na tafi na sake dawowa.Cikin tsananin damuwa nace
yau shekara hudu kenan muna tare baki taba gaya
min sunanki ba kuma baki gaya min sunan garinku ba
bare nasan asalinki da danginki shin bakya tausayin
wannan yaron da kika haifa ne?Koda jin wannan

tambaya sai matar ta sake bushewa da dariya tace
bansan kaina ba kuma bansan kowa ba sai kai,tana
gama fadin haka ta juya ta shige cikin bukka taje ta
kwanta ta kama bacci,tun daga wannan rana muka ci
gaba da zama tare,amma ko kadan wannan da nata
bai dameta ba,kuma bata yi masa komai sai dai ni
nayi masa,wani lokaci sai naga kamar hankalinta ya
dawo tana magana a nutse,amma da zarar na fara
tambayarta asalinta da garinsu sai ta birkice ta koma
hauka.
Wata biyu da kwana uku mukayi tare ranar kwana na
ukun ne matar ta wayi gari da tsananin rashin lafiya
wadda bansan sanadinta ba,cikin rudewa na shiga
hada mata magunguna iri-iri ina bata tana sha amma
duk a banza tamkar kara mata ciwon akeyi,kawai sai
naga idanunta sun fara lumshewa kuma numfashinta
na sarkewa,Al amarin da ya dugunzuma hankalina
kenan na fara zubar da hawaye,na shiga yi mata
tambayoyi akan ta sanar dani asalinta,matar na
kokarin bude baki tayi magana amma sai ta kasa,nan
take jikinta ya sandare,idanunta suka kafe ta daina
motsi.koda naga haka sai na rungumeta na fara
kuka,ganin ina kuka ne dannata wannan yaro dan
shekara kusan hudu ya rugo izuwa kaina shima ya
fashe da kuka.Hakika wanan rana nayi kuka mai yawa
sabo da shakuwar da nayi da matar nan sai da nayi
kwana ashirin da daya bana iya cin abinci
sosai,amma koda yaushe hankalina yana kan wannan
yaron ina kula da lafiyarsa sosai.
Koda tsoho Imzanu yazo nan a zancensa sai Imhal ya
tari numfashinsa suka dubi juna a lokacin da
kowannensu yake zubar da hawaye yace yakai
Abbana na gane cewa wannan yaro da mahaukaciya
ta haifa ba wani bane face ni dinnan,tabbas yanzu na
tabbatar da cewa ni marayane wanda bashi da uwa
bashi da uba kuma wanda baisan asalinsa ba,koda
Imhal yazo nan zancensa sai tsoho Imzanu ya
rungumesa suka fashe da kuka tare,can sai Imhal ya
janye jikinsa suka fuskanci juna ya dubi Imzanu yace
Bazan taba yarda bani d uba ba amma ni kai na sani
a matsayin ubana,ina son nayi maka wata tambaya
guda daya menene dalilin da yasa kake kirana da
suna IMHAL?
.
WASA FARIN GIRKI
.RIJIYA GABA DUBU
Littafi na daya 1
Na Abdulaziz sani m gini
Typing:- Ibrahim S combatant
Post:- Shuraih Usman
@Shuraih 99%
Part 1B.

Koda jin wannan tambaya sai hawaye ya zubowa
tsoho Imzanu yace Abinda yasa nasa maka suna
Imhal shine a iya zama na da mahaifiyarka har ta
mutu ban taba jin ta ambaci sunan wani mahaluki ba
face IMHAL,A kullum duk sanda za taci abinci sai naji
tana kiran sunansa tana cewa yazo suci abincin
tare,abinda na fahimta shine,koma wanene wannan
Imhal din lallai ya kasance babban masoyi a
gareta,zai iya kasancewa mijinta ne ko dan uwanta ne
ko mahaifinta,Abu na biyu da nake zargi shine,duk
yadda akayi mahaifiyarka ta fito daga babban gida
domin a ranar da na tsince ta acikin wannan katon
ramin mai zurfi sutturar dake jikinta mai matukar
tsada ce,babu mai sanya irinta face sarakai da
manyan attajirai,babban bakin cikina shine babu
wata shaida a tare da mahaifiyarka wadda zata iya
sawa a gano asalinta,koda tsoho Imzanu yazo nan a
zancensa sai suka sake rungume juna,daga can sai
Imhal ya dubi tsoho Imzanu yace,Lallai zan rike
sunana a zuciyata da bakina,lallai wata rana wannan
suna zai taimakeni na gano asalina.
Tun daga wannan rana Imhal da tsoho Imzanu suka
cigaba da rayuwarsu acikin daji kamar yadda suka
saba,amma sai ya zamana cewa kullum sai Imhal ya
shiga cikin garin Kisra kuma duk inda yaje si ya
tambayi mai suna Imhal,idan aka tambayeshi wane
Imhal yake nema sai ya kasa bayani domin baisan
wata inkiya ba ta Imhal din da yake nema,hakane
yasa suka dinga yiwa Imhal dariya suna cewa dashi
Bagidaje mutumin daji,saboda ganin yanayin
shigarsa ta makiyaya.
Wata rana Imhal yazo giftawa ta kofar gidan sarkin
kisra akayi sa a kuwa a lokacin sarki ya fito daga cikin
gidan sarautar zai fita rangadi kwatsam sai yayi arba
da sarki,Abinka da wanda baisan yadda ka idar
sarauta take ba sai kawai ya kurawa sarki
idanu,maimakon ya zube kasa gabansa ya kwashi
gaisuwa,ai kuwa sai dakarun sarki suka afkawa Imhal
da duka har suka kai shi kasa,cikin fushi ya yunkura
ya watsar dasu duka duk da cewar sunkai su
ashirin,nan take shima ya rufesu da duka,duk wanda
yayi wa naushi daya sai ya baje a kasa
sumamme,koda ganin haka sai ragowar dakarun
sarki suka zare takubbansu sukayi caa akan Imhal
zasu sassara shi,amma sai sarki ya daka...


Read / Download RIJIYA GABA DUBU

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

4 Comments On RIJIYA GABA DUBU
avatar
mlm

8 months ago

Reply

Next please

avatar
khadija-1-4

6 months ago

Reply

??????

avatar
muhammad-musa

5 months ago

Reply

Good book

avatar
ismail-9-8

2 months ago

Reply

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album