Join Our WhatsApp Group

MAZAN JIYA Book 2 Mujalladi na Biyu 2 Complete Hausa Novel Document by MAZAN JIYA Book 2 Mujalladi na Biyu 2


MAZAN JIYA Book 2 Mujalladi na Biyu 2

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 21417



MAZAN JIYA Book 2 Mujalladi na Biyu 2

Reading Time: 1 Hours

Added On: 19, Dec 2023

Author: Abdulaziz Sani Madakin Gini ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Adventure novels

File Size: 111.51 kb

File Type: txt

Views: 1190+

Download: 405+

Last download: 2 days ago

Description/Story: MAZAN JIYA
littafi na biyu 2
Mujalladi na biyu 2
littafin Abdulaziz Sani Madakin Gini
Typing by Shuraihu Usman.

Zamu tashi daga inda muka tsaya a Mujalladi na ɗaya 1, idan ba a manta ba, amma kafinnan a sani wannan typing mallakin shafin Taskar Novels ne kadai ba'a yarda wasu shafuka su dau typing ɗinnan ba ta kowanne hali kuwa, idan kuwa suka dauka zasu hanyo DMCA ya hau kan shafinsu wanda hakan zai yi sanadiyar lalata shafin nasu ya taba musu SEO, DOMAIN da HOSTING. Saboda tuni munyi registan content na shafinmu da hukumar DMCA, Digital Millennium Copyright Act amma kuna iya karantawa anan kyauta ko ku downloading duka daga shafinmu idan kunyi subscription na shafin Taskar Novels.

kike ciki na sani kuma na zo ne domin na taimakeki na biya miki bukatarki".


Koda jin wannan batu sai mamaki ya kama Zarifa kuma ta cika da dumbin farin ciki. Ba tareda fargabar komai ba Zarifa ta zauna daf da boka Ardusa ta kura masa idanu tana mai sauraron abinda zai fada ma ta.

Boka Ardusa yai murmushi gami da gyaran murya sannan ya ce, "Ya ke ma'abociyar kyawu,tauraruwar kyawawa, ina son ki sani cewa na san baki da wani buri wanda ya fi ki daukaka a duniya fiye da dukkan sauran mata, kuma kina son kimallaki dukiyar da babu mai kamarta.

Tabbas idan kika yi abubuwan da zan umarceki sai bukatarki tabiya.


Yanzu nazo gareki a sirrance lallai ki rike sirrin kada ki kuskura ki gayawa wani wannan sirri na zuwana wajenki koda bukatarki ta biyane idan kuwa kika fadi sai dan da za ki haifa yazamo sanadin ajalinki".


Koda jin haka sai Zarifa ta ja dogon numfashi ta ce,"Ai kuwa ba zan taba gayawa wani wannan sirri ba".


Boka Ardusa ya ce,"Na san kin yi mamakin yadda aka yi na kawo kaina wajenki, to amma ba abin mamaki bane idan kika yi la'akari da matsayina a yanzu na bokan da yafi dukkan bokayen duniyar nan karfin sihiri, amma kuma ina



daga cikin talakawan bokayen. Yau shekarata ashirin da biyar ina bauta a karkashin wannan masarauta ta birnin Kisra kuma akwai alkawari mai nauyi tsakanina da dangin su Sarki Kusaidu cewar ba zan daina bauta a garesu ba sai bayan shekara hamsin, kin ga ke nan a gaba akwai shekaru ashirin da biyar.

A ka'idar wannan alkawari ban isa na yiwa wani aiki ba face su idankuwa na kuskura na yiwa wani aiki mutuwa zan yi domin an yi alkawarin ne a cikin sihirin tsafi bisa amincewar mahaifina da mahaifin sarki Kusaidu.

Yanzu na zo wajenki ba aiki zan yi miki ba kawai zan gaya miki abubuwan da za ki yi ne a kanki domin bukatarki ta biya, ladana a wajenki abubiyu ne rak.


Abu na farko,bayan bukatarki ta biya za kibani kanki na sanki 'ya mace domin a rayuwata nayi alkawarin ba zan ta6a kwanciya da wata 'yamace ba sai wadda take da tsananin kyawu nagaban kwatance, kuma wadda ta kasance 'yar attajirin da babu kamarsa a wannan nahiya gabadaya,gashi kuma na yi dace na sameki.


Ladana na biyu shi ne, za ki raba dukiyarki gida biyu ki bani rabi bayan mutuwar 'yar uwarki Marifa domin a sannan ne za a baki gaba dayan dukiyar da mahaifinki ya bari.
Idan kin amince da wannan sharadi yanzu
take zan gaya miki abubuwan da za ki yi ki samu cikar burinki.


Sa'adda boka Ardusa ya zo nan a zancensa sai hankalin Zarifa ya dugunzuma ainun ta rasa abin da ke ma ta dadi a duniya ta mike tsaye dagakan gadonta ta kama kaikawo da tunani bisa hukuncin da ya kamata ta yanke akan ta yarda dashi.


Abin da ya fara fado ma ta a rai shi ne ya za ayi ta bayar da wannan kyakkyawan jiki na ta ga boka Ardusa tsohon da ya kai sa'an ubanta alhalin tana takama da tsananin kyawun da babu mai tabata face babban Basarake ko mashahurin attajiri.


Abu na biyu da ya fado ma ta a rai shi ne, yaza a yi ta raba wannan dukiya ta ta mai tsananin yawa ta baiwa wani rabi, wacce ta ishi mutum rayuwa a duniya koda zai shekara dubu

Lokacin da boka Ardusa ya ga Zarifa ta shiga halin rudewa da wasi-wasi sai ya mike tsaye yadubeta ya ce, "Wai shin kin manta ne da abin da bokaye da dama suka gaya miki cewa babu mai iya biya miki bukatarki face ni.

Idan zuciyarki bata gamsu da al'amarina ba shi ke nan ni zan yi tafiyata na barki da wayonki".

Koda jin haka sai Zarifa ta yi sauri ta shagaban boka Ardusa ta ce, "Ya kai wannan sakin bokaye ka yi sani cewa jikina da dukiyata ba abakin komai suke ba muddin zan sami biyan bukata Lallai na amince da dukka wanann sharadi naka don haka kayi sauri ka sanar da ni abubuwanda zan yi domin bukata ta biya".


Koda jin haka sai boka Ardusa ya yi murmushi ya ce, "Kafin nayi miki bayanin abubuwan da za ki yi kuma kika yi su kika sami nasara sannan daga baya kika yi min butulci, ma'ana kika ki cika mini alkawari, lallai zaki mutu a cikin kwanaki talatin cicif bayan yin aurenki.

Haka kuma dole ne ki ci gaba da bani kanki a duk sa'adda na bukace ki, idan kuwa kikaki asirinki zai tonu kuma ki rasa abin da kika samu a rayuwa. Yanzu sai ki saurareni da kyau domin kiji duk abubuwan da zan gaya miki wadanda za kiyi su bukatarki ta biya.

Abu na farko da za ki yi shi ne, dole ne ki fada mini tambayoyi guda uku wadanda mahaifinki ya fada miki ki tambayi masu neman aurenki gami da amsoshinsu domin nasanar da sarki Kusaidu su ya sami damar aurenki.Kin ga idan kika auri sarki Kusaidu za ki sami damar da babu wata mace da ta samu a duniya domin shi ne sarkin da a tarihi sarakan duniya babu masarautar da ta fi tashi tsohon tarihi da daukaka da karfin mulki.

Duk sarkin da ya yi zamaninsa har bayan shudewarsa ba a mancewada shi da matansa domin har a fadar sarkin Aljanun duniya ana rubuta tarihinsu a ajiye, atakaice dai sai sunanki ya bazu ko ina a duniya kinga ke nan ko ta nan kin yiwa 'yar uwarki Marifa fintinkau.

Abu na biyu da za ki yi shi ne, ki samo kasko ki yi fitsari a cikinsa sannan ki diga digon jininki a ciki, sai ki kira sunan 'yar uwarki sau uku ki tofa a ciki sannan ki wanke idanunki da shi amma a ranar da za a yi gasar neman aurenku. Dazarar 'yar uwarki Marifa ta hada idanu da ke awannan rana ba za ta yi wata goma sha uku ba aduniya za ta mutu, idan kuwa baki hada idanu daita ba to kece za ki mutu a cikin wata goma sha ukun.


Wannan shi ne iyakar abin da za ki yi. dukkan burinki ya cika.Da wannan furuci nake miki sallama sai mun hadu a ranar gasa.”


Kafin Zarifa ta bude baki ta ce wani abu tuni boka Ardusa ya yi girgiza ya bace 6at. Al'amarinda ya matukar baiwa Zarifa mamaki ke anan domin ya tafi ba tare da ta fada masa wannan tambayoyi uku ba, wadanda zai sanar da sarki Kusaidu gamida amsoshinsu.

Zarifa ta koma kan gadonta zuciyarta cike da sake-sake da tunani bisa wannan abu da ya faru tsakaninta da boka Ardusa. Ba wani abu take tunani da wasi-wasi ba face hadarin da ke cikin aikin da boka Ardusa ya sa ta.

Koda takwanta akan gadonta domin ta mike kafafunta tayibarci sai kawai tayi arba da wata takarda akangadon. Al'amarin da ya matukar ba ta tsoro damamaki ke nan domin a saninta babu wata takarda& cikin turakar ta ta koda guda daya kuma babu yadda za a yi a shigo da wani abu ba tare da saninta ba.Hannun Zarifa na karkarwa ta sa hannayenta biyu ta dauki takardar wacce ta kasance fara kal babu zanen komai a kanta.Koda ta dubi takardar sai ga hoton fuskar boka Ardusa ta baiyana akai yana mai murmushi a gareta sannan ya ce,"Maza kifadi wadannan tambayoyi uku gami da amsoshinsu."
Koda jin haka sai Zarifa ta karanto tambayoyin gami da amsoshinsu.

Bisa mamaki sai Zarifa ta ga an rubuta duk abin da ta fada akan wannan takarda ba tare da ta ga mai rubutun ba ko alkalamin da ke yin rubutun.

Nan take takardar ta6ace 6at tamkar bata taba wanzuwa ba a wajen.

Koda ganin haka sai Zarifa tayi murmushi sannanta kwanta. Kwanciyarta ke da wuya sai barci yasace ta,bata sani ba.


Abin da bata sani ba shi ne, kafin boka Ardusa ya bace daga cikin turakar ya busa mata hodar banju ta shaka, shi ya sa nan da nan barci yakamata in ba don haka be da ba za ta iya barcin basaboda tunanin gagarumin aikin da ke gabanta dakuma sharadin da ke tsakaninta da boka Ardusa.

DA RANAR gasa tazo sai fadar birnin Kisra ta cika ta batse da mutane duk inda mutum ya duba gabas da yamma, kudu da arewa sai dai ya ga kawunan bil'adama fululu babu masakar tsinke.


A tsakiyar fadar ne jaruman gasa suka taru wadanda gaba dayansu sun kasance sarakai da attajirai da ma manyan bokaye daga kowanne bangare a kasashen da ke nahiyar.


Sarki Kusaidu da sarkin Darul Mahabul ne suka shigo a karshe,bokayensu na take musu baya.

Maimakon su sarki Kusaidu su tafi izuwa inda karagar mulki take sai suma suka shiga tsakiyar fadar inda sauran jaruman gasar suke.


Saboda shakkar wanman gasa gaba dayan jaruman da suka tsaya a tsakiyar fadar su goma ne kacal su sarki Kusaidu ne suka zamo cikon na shabiyun. Ba wani abu bane ya janyo hakan ba face sauran jama'ar da suke son su shiga gasar wadanda adadinsu ya fi dubu dari bokayensu sun tabbatarmusu da cewa 6ata lokacinsu za su yi ba za su iyacin nasara ba.


Shi kuwa Sarkin Darul Mahabul ana i gobe za ayi gasar ne ya sami f
kwarin guiwar fitow awanann gasar bayan boka Sulbaini da boka Zaharu sun hakura da kiyayyar da ke tsakaninsu sun hada karfi da karfe sun binciki amsar tambayar da za ayi masa ya iya amsawa. Kuma a binciken da suka yi sai suka kasa gano tambayoyin da Zarifa za ta yi sai na Marifa suka gani. Koda suka ga tambayoyin sai suka kasa fahimtar amsoshinsu har sai da suka tara gaba dayan hadiman aljanunsu suka bazamasu izuwa cikin duniya wajen tsofafin mutane da aljanu masana ilimin tarihi. Da Kyar da sidin goshi aljanun suka samo amsar tarabayoyi biyu. Amsar tambaya ta uku kuwa ba a sameta ba sai a lokacim da suka fito filin gasar sannan wani hadimin boka Sulbaimi yazo da ita. Ai kuwa cikin gaggawa ya radawa sarki amsar a kunnensa.Koda jin amsar sai sarki ya cika da farin ciki kuma ya sami nutsuwar shigar gasar.
Jim kadan de shigar su sarki Kusaidu cikin jaruman gasa sai ga Zarifa da Marifa suka shigo cikin filin fadar.Kowacce daga cikinsu ta caba ado na ban mamaki kuma na kure adaka,kuyanginta na biye da ita gaba da baya suna watsa furanni masu kamshi akan hanyar takawarta.
Kamshin turaren da su Zarifa suka sanya a jikinsu ne ya fara dukan hancin kowa a fadar.Koda jama'a suka ji wannan kamshi sai suka waigo suka dubi masu shigowar,wohoho! Nan fa maza suka rude suka dimauce, wasu suka kama
dalalar da yawu, basu sani ba wasu kuwa sai suka kama yanke jiki suna faduwa kasa sumammu saboda sun ga abin da kwakwalwarsu ba za ta iya dauka ba.Masu Karfin hali ne suka rinka kuka suna zubar de hawaye saboda takaici bisa sanin cewa ba za su taba mallakar wadannan kyawawan 'yan mata biyu.
Tun kafn su Zarifa su shigo cikin fadar sai Zarifa ta ga Marifa ta sha lullu6i kuma ta sunku da kanta kas idanunta basa kallon komai face kasa inda take takawa. Alamarin da ya dugunzuma hankalin Zarifa ke nan domin ta san cewa idan har basu hada ido ba ita da Marifa kashinta ya bushe kuma ba za ta taba cika burinta ba. Nan fa Zarifa ta fara tunanin abin de za ta yi domin ta tabbatar cewa ta hada idanu da Marifa. Inda matsalar take shi. ne akwai tazara tsakaninta da Marifa kuma akwai kuyangin Marifa a tsakaninsu. Koda Zarifa ta ga fuskar Marifa a rufe take sai itama ta janyo mayafinta tayi lullu6i kuma ta sunkui da kanta kas amma zuciyarta sai bugawa take da karfi cikin tsananin tsoro.
Zarifa da Marifa suka ci gaba da tafiya suka nufi inda aka tanadar musu su zauna amma Zarifa na daga kai tana satar kallon Marifa ko za ta ga itama ta dago kai domin su hada idanu, amma bata dago din ba. Zarifa na cikin wannan satar kallo ne
ta hada ido da boka Ardusa,nan take ya yi ma ta nuni da idanunsa cewa lallai tayi duk iyakar kokarinta ta hada idanu da Marifa kafin su isa inda kujerun zamansu suke. Koda ganin wannan inkiya sai hankalin Zarifa ya kara dugunzuma ta shiga tunanin abin da za ta yi ya zamana cewa lallai ta hada idanu da Marifa kafin su kai mazauninsu. Sai da ya rage saura baifi taku goma ba su isa mazaunin nasu sannan dabara ta fado ma ta. Kawai sai tayi kamar tayi tuntu6e, cikin shammace ta tafi taga-taga ta fadi a gaban Marifa.Cikin mamaki da kaduwa Marifa ta sunkuya ta dubi Zarifa suka hada idanu. Suna hada idon sai Marifa taji wani abu ya soketa a kirji tamker an tsira ma ta mashi. Saura kiris tayi ihu kuma ta fadi kasa, amma sai ta daure ta mike ta ci gaba da tafiya. A sannan ne ta ga Zarifa ta dubeta tayi ma ta wani irin murmushi na mugunta. Nan take Marifa ta tsergu da cewa tabbas 'yar uwarta Zarifa tayi ma ta wani mugun asirin.
Zarifa da Marifa sun dade suna yiwa junansu mugun jifa na sihiri amma sihirin yaki ya yi tasiri akan kowannensu kuma duk wajen bokan da suka je yana gaya musu cewa sai dai su yi hakuri babu wani sihiri da zai iya huda jikinsu a yanzu,domin mahaifinsu ya yi musu tsari na musamman babu wanda zai iya karya wannan sihirin face bokan da
ya yishi kuma ba wani bane face boka Ardusa.
Cikin tashin hankali da mamaki Marifa ta karasa zuwa kan kujerar da aka tanadar ma ta ta zauna,itama Zarifa sai taje ta zauna akan ta ta kujerar fuskarta cike da murmushi,zuciyarta ta cika makil da farin ciki. Zamansu ke da wuya sai Alkalan gasar suka fara zartar da aikinsu aka ware jaruman da ke son Marifa da wadanda ke son Zarifa.
A zaton sarki Kusaidu Sarkin Darul Mahabul zai shiga cikin sahun masu son Zarifa amma sai ya ga ya shiga cikin sahun masu son Marifa. Nan take Sarki Kusaidu ya hau kan layin masu son Zarife ya tsaya daga Kanhe. Masu son Zarifa...


Read / Download MAZAN JIYA Book 2 Mujalladi na Biyu 2

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album