Join Our WhatsApp Group

MAGAJIN WILBAFOS book 2 Complete Hausa Novel Document by MAGAJIN WILBAFOS book 2


MAGAJIN WILBAFOS book 2

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 56893



MAGAJIN WILBAFOS book 2

Reading Time: 4 Hours

Added On: 11, Nov 2023

Author: Dr Abdullahi Muhammad Ibrahim ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Adventure novels

File Size: 313.27 kb

File Type: txt

Views: 642+

Download: 327+

Last download: 20 hours ago

Description/Story: MAGAJIN WILBAFOS
Fita na biyu 2
Marubucin littafin
Dr Abdullahi Muhammad Ibrahim
Ebook creat by Shuraih Usman
Ebook publish by www.hausaebooks.cf
Ebook din nan yazo maku ne daga shafin www.hausaebooks.cf
Kuna ziyartar shafinmu don samun sababbin littatafai
Ga duk wanda ke bukatar ebooks nashi ya samu shiga cikin wepsite namu sai ya turo mana da littafin ta Email namu hausaebooks@gmail.com
MAGAJIN WILBAFOS
Marubuci: Dr Abdullahi Muhammad Ibrahim
Babi na 51: Umarnin Ururu
Post by: Shuraih Usman
@shuraih 99%
www.facebook.com/hausaebooks
.
Daga:- Taskar Magajin Wilbafos
___
SHEKARU DA SUKA GABATA (ALAƘA TSAKANIN HIDAYA
DA ALJANI JIDAIME)
___
Hidaya ta ɓata rai tana duban aljani Jidaime wanda ke
tsaye yana lilo akan iska, "Kasan mai yasa Ururu suka fi
kowacce ƙabila ƙarfi a wannan zamani, ba komai bane
saboda su basu dogara da aljanu ba. Saboda haka babu
wata farar-laya da zata iya aiki a kansu. Sun dogare ne
kachokam da ƙarfin Izzar dake cikin baƙaƙen
idanuwansu. Haka nake so Armad shima ya dogara da
ƙarfin jininsa na Wilbafos. Bana son ya dogare dakai a
matsayinka na aljaninsa, domin hakan bazai kaishi ko'ina
ba."
Aljanin najin haka ya murtuke fuska, "Kina nufin kin raina
ƙarfina ne. Kuma kema ai kina amfani da aljaninki,
danme yasa kike so ki hana shi amfani da nasa."
Hidaya ta ɗanyi murmushi sannan ta amsa da cewa
,"Bawai ina cewa ban yadda da ƙarfin ka bane, Jidaime.
Kawai dai nasan akwai ƙarfin Izza irin wadda ni kaina ban
san iyakacin ta ba acikin ruhin ƙani na, saboda haka ina
so yayi amfani da ita maimakon ya dogara da ƙarfin
aljaninsa. Saboda haka kayi haƙuri zan ɗaure ka ta yadda
babu yadda Armad zai iya amfani da haƙiƙanin ƙarfinka.
Kuma ina mai yi maka gargaɗi na ƙarsge da kada wani
tsautsayi yasa ka ƙara haɗa kanka da aljani na domin yin
hakan zai jawo maka hukunci. Aljani na bai taɓa biyayya
ga Ururu ba kuma Ururu basu isa su baahi umarni ba. Kai
kasan mai nake nufi."
Tana rufe baki Aljani Jidaime ya fara jada baya yana
neman guduwa, amma ina tuni Hidaya ta saukarda
al'amudan Farar-laya akansa.
Tun daga wannan rana yake a ɗaure, kuma basu samu
wata damar ganawa da Armad ba sai a wannan lokaci.
Hasalima Armad baisan cewa aljaninsa a matsayi ɗaya
suke dana Ikenga ba. Kuma bawai kaɗai Walƙiya aljanin
nasa yake sarrafawa ba. Kai a taƙaice ma wannan walƙiya
ba daga aljanin nasa take fitowa ba. Tana fitowa ne daga
ainahin cikin ƙarfin ruhin Armad wanda aka haifeshi
dashi. Irin ƙarfin da yayarsa Hidaya take so yayi amfani
dashi.
_____
Acikin filin Jinzidal kuwa, har wannan sadauki mai
muƙamin kyaftin ya ɗauki Armad a sume da niyyar tafiya
dashi sai Uznu Ururu ya dakatar dashi.
Uznu na tafiya taku ɗai-ɗai ya iso ga jikin Armad ya kuma
saka hannunsa akan zuciyar Armad. Haka na faruwa wani
haske ya fara fita daga jikin hannunsa yana shiga jikin
Armad.
____
Acikin duniyar aljanun nan kuwa Armad yana tsaye yana
tunani wacce shawara ya kamata ya yanke kawai sai yaga
duniyar ta fara cika da wani baƙin haske. Lamarinda yasa
shi ajiyar zuciya. Amma tun kafin ya gama gane maike
faruwa yaga fuskar aljaninsa Jidaime ta canja.
"Armad ko ka kwance ni yanzu ko kuma baza ka iya ƙara
amfani da fasahar walƙiya ba." Aljanin ya faɗa cikin sauri
da alamun tsoro.
Idanun Armad suka cika da mamaki a lokacin da yaga
canjin yanayin da aljanin ya samu kansa aciki. Nan take
ya buɗe baki ya tambayi aljanin, "Mai yake faruwa?"
"Uznu Ururu ne yake neman ƙara ƙarfin ankwar dake
ɗaure dani. Ban san tayaya ba, amma da ƙarfin baƙaƙen
idanun sa yana iya gani har cikin ruhinka. Wato dai a
taƙaice yana ganinmu a halin yanzu. Kana da ƙasa da
daƙiƙa biyar ka yanke shawara akan abinda zakai."
Aljanin na rufe baki ya fara karkarwa lamarinda ya ƙara
ruɗa Armad, domin har a wannan lokaci ya kasa yanke
shawara.
Abu ɗaya dai da Armad ya sani shi ne ba dukkan
maganganun da aljanin ya faɗa zai yadda dasu ba, yasan
cewa lallai ba'a raba aljanu da ƴan ƙarairayi nan da can.
Amma a halin da yake ciki bashi da wani zaɓi face ya
bawa wannan aljani dama yaga kozai iya kuɓutar dashi
daga halin da yake ciki.
Saboda haka Armad yayi tsalle izuwa wannan aljani, ya
kuma ja ankwar da ƙarfin tsiya. Abun mamaki bai taɓa
tsammani ba, amma kawai sai yaga ankwar tana
murmushewa tana sakar wannan aljani. Wanda a iya
lissafinsa cire ankwar zai ɗau lokaci kuma yana buƙatar
makami kafin ya faru. Amma koda Armad ya tuna cewa
ai ankwar ta tsafi ce, sai kuma ya gane yadda abin yake.
Aljani Jidaime yai ƙaraji tare da miƙe hannayensa sama
bayanda yaji shi a sake. Ranar daya daɗe yana jira tazo.
Amma kafin ya fara komai yana buƙata ya kashe Uznu
Ururu dake waje, wanda idan baiyi saurin yin hakan ba
wannan baƙin hayaƙi zai iya ƙara ɗaure shi ya maida shi
gidan jiya.
Nan take ya finciko ruhin Armad daga wannan duniya ya
dawo dashi izuwa jikinsa a wannan fili. Shi kuma ya
bayyana a gaban Uznu Ururu yana mai riƙe da farin
al'amudin aljanu a hannunsa na dama.
Koda bayyanarsa sai dukkanin kyaftin guda biyar ɗinnan
dake biye da Uznu sukai tsalle suka dira a gabansa domin
su kare shi. Amma suna dira aljani Jidaime ya kawo wata
muguwar wafta da al'amudinsa inda ya share su baki
ɗayansu a lokaci guda. Sannan kuma yayi kan Uznu
gadan-gadan. Lallai ƙarfin aljanu da bil-adama da
banbanci.
Nan da nan fuskar Uznu ta canja, yanayin firgici ya
bayyana akanta. Amma a wannan lokaci ne ya ciji
ɗanyatsansa na dama, inda jini ya fara ɗisa. Uznu baiyi
wata-wata ba wajen saka wannan jini acikin idanunsa
baƙaƙe guda biyu. Ai kuwa haka na faruwa wani baƙin
haske ya fara ɓulɓula daga ciki, sannan Uznu ya fara
magana, "Ina mai umartarka da ƙarfin Ururu dake jini
na, da ƙarfin Ururu dake bisa ƙasa ta farko daka tsaya a
inda kake."
Abin mamaki yana rufe baki wani irin ƙarfin izza marar
misaltuwa mai cike da buwayar Ururu ya fara ambaliya
acikin filin. Kan kace meye wannan aljani Jidaime ya tsaya
a inda yake cak ya kasa motsi. Sannan kuma Izzar Uznu ta
fara hawa tana ambaliyar har saida takai Shekaru dubu
huɗu da ɗari tara da casa'in da tara. Uznu ya cafi
takobinsa yayi kan aljani Jidaime.
Tun kafin ya ƙarasa akaji muryar aljanin na cewa, "Idan
ka kashe ni kasan ƙabila ta baza suyi shiru ba. Kuma
babban sarki Ururu Kuyurussa'ayi yayi mana katanga
daku..." Yana magana yana karkarwa, kuma ganin cewa
Uznu baya saurarensa kawai sauri yake ƙarawa yasa tsaya
ya kasa ƙarasa abinda yake faɗa tare da fara karkarwa.
Uznu na ƙarasowa yasa takobinsa ruwan toka ya tsarge
aljani Jidaime gida biyu. Aljanin yai wata ƙara mai
firgitarwa, inda daga bisa ya fara narkewa izuwa toka
yana murmushewa.
"Da kasan da tsakanin da akai mana da baka tunkare ni
ba. Ko ba komai ina da hujja idan aka je gaban babban
sarki Ururu Kuyurussa'ayi." Uznu na magana yana goge
takobinsa.
Sannan nan take ya ɗau Armad ya ɓace daga wannan filin
gasa.
___
A can gefe guda kuwa sarki Deniz Iluru da dakarunsa
suna tsaye suna kare duk wani hari da yayo kan ƴan kallo
a lokacin da ake wannan fafatwa tsakanin Uznu da su
Armad.
Duk da kuwa cewa tunda Uznu ya buɗe idonsa dukkan
ƴan kallon suka sume, amma bayan da aka gama komai
hankali ya dawo jikinsu saida hukumar yaƙin garin tayi
amfani da rahoton ƙarya na cewa girgizar ƙasa ce tasa
aka tsayar da gasar wannan shekara. Amma ta ƙarƙashin
ƙasa sarki Deniz Iluru ya rubuta ƙara izuwa fadar Ururu
dake ƙasa ta biyu mai kula harkokin Jinzidal akan su
hukunta Uznu Ururu saboda cikas ɗin daya kawo a gasar
Jinzidal ɗin. Cewa kuma suna fata ai musu adalci.
To haka dai aka kawo ƙarshen wannan gasa ta Jinzidal ta
wannan shekara.
____
To ALLAH ya kawo mu ƙarshen Jinzidal. Yanzu zamu shiga
wani sabon sashi na wannan littafi. Duk mai tambaya ko
kuma wani abu da bai gane ba a babika 50 da suka wuce
ya rubuto a comment.
Nidinne dai Shuraih Usman inkiya
99%
Daga taskar magajin wilbafos
MAGAJIN WILBAFOS
Marubuci: Dr Abdullahi Muhammad Ibrahim
Babi na 52: Dordor mai waka
Post by: Shuraih Usman
@shuraih 99%
www.facebook.com/hausaebooks
.
Daga:- Taskar Magajin Wilbafos
Doron ƙasa na huɗu
Shalkwatar Mayaƙan Ururu
____
Sahu-sahu ne na mutane ɗai-ɗai har sahu ɗari, kowanne
ɗaya daga cikin wannan sahu yana ɗauke da mutane
guda ɗari. A taƙaice dai mutanen dake cikin wannan sahu
su dubu goma ne. Dukkaninsu na sanye da baƙaƙen kaya.
Babu mai ko magana acikinsu. Kai ko tari babu maiyi.
Dukkanin wannan mutane ba kowa suke jira ba illa
kwamanda Uznu Ururu. Uznu Ururu dai yaje ƙaro ilmi a
jami'a mafi girma a duniya dake bisa doron ƙasa ta farko.
Jami'ar da ake kira da Namibiya da yaren Aldurish na
Ururu. Saboda daɗewar da yayi nema baya nan suka
shirya masa wannan gagarumar tarya.
Amma bisa mamaki Uznu yana bayyana kawai tsayawa
yayi kimanin daƙiƙa ɗaya, inda ya kyaɗa musu kai
alamun jinjina sannan yai ɓangaren inda ofishinsa yake.
Koda yake baza a iya kiran wajen na Iznu Ururu da ofishi
ba kaɗai, tunda iya girman wajen kaɗai yakai wani ɗan
ƙaramin gari. Sannan kuma ga shirye-shirye na
musamman na al'amura da suka shafi Izza da ake
gudanarwa a wajen. Kusan zaka iya cewa duk wani
sinadari da za'a iya samu a ƙasa bakwai akwai a wannan
ɓangare na Uznu Ururu, kasancewar shi ɗin yawanci
kayansa daga doron ƙasa ta farko yake tahowa dasu.
Amma dukkanin wannan abubuwa basu suka dami Uznu
ba, a yayin da cikin sauri ya shige wani ƙaton ɗaki na
bincike-bincike inda yana shiga ya turo ƙofa ya rufe,
tunda dama babu kowa acikin ɗakin. Sannan ya zaro
wani ɗan irin Ayrid na musamman daga aljihunsa ya
karanta wasu ɗalasimai, wanda nan take wannan Ayrid ya
fara ƙara girma yana girma har saida ya kai girman ƴar
ƙaramar ƙofa, inda nan take wannan irin Ayrid yai aman
Armad ta cikin wannan ƙofa.
Uznu ya fizgi Armad ya kwantar dashi akan wani ƙaton
taburi na aiki. Sannan kuma ya fara karanta wasu
ɗalasimai wanda suka saka wani farin haske ya fara cika
ɗakin.
Nan take wasu Rauhanan aljanu guda biyu, ɗaya mai
ƙaho ɗaya mara ƙaho, suka bayyana, suna bayyana suka
zube a gaban Uznu, kana gani kasan alaƙar dake
tsakaninsu bata wuce ta bawa da ubangidansa ba.
Uznu ya amsa sannan ya fito da wasu fararen takardu
daga aljihunsa guda biyu ya miƙa musu. Sannan ya fara
jawabi da cewa, "Kunga wannan shi ne karo na biyu da
muka shigo da Littafin takobi wannan ɗaki acikin shekaru
ɗari da suka wuce, saboda haka haka ina fata zamu
kiyaye duk abubuwanda suka sa a wancan lokaci bamuyi
nasara ba."
Ya kalli aljanin mai ƙaho daga cikin guda biyun yace,
"Kalkutu kasan mai zakai."
Sannan ya juya izuwa mara ƙahon, "Kaima Netti kasan
meye aikinka."
Uznu ya ci gaba da bayani a yayinda wannan aljanu biyu
suka nutsu suna saurare, "A bisa bincike na na gano cewa
Littafin-takobi yana da rai yana kuma da hankali nasa na
kansa. Kawai dai ba irin yadda mutane da aljanu suke ba.
Kuma ta hakan nema na gano cewa indai akwai ma'aboci
Ururu a waje to Littafin-takobi bazai taɓa baƴyana kansa
ba. Kuma hakan ba abin mamaki bane tunda shi wanda
ya samarda Littafin takobin ɗan adawar gidan mune na
Ururu.
"Saboda haka a lokacin da za'ai wannan aiki dole ne ya
zamanto bana kusa da wannan yaro, in ba haka ba
wannan Littafi bazai taɓa bayyana kansa ba.
"Sannan kuma a wani binciken da muka gudanar a
jami'ar Nimibiya mun gano cewa wannan Littafin ya zaɓi
ƴan zuri'ar Wilbafos har a karo biyar daga cikin karo
bakwai da ya taɓa zaɓar wani. Kuma shima wannan
yaron daya zaba ɗan zuri'ar wilbafos ɗinne. Amma
babban abinda zaku riƙe ku kiyaye shi ne, Littafin-takobi
yana bayyana ya taimaki waɗanda ya zaɓa. Saboda haka
hanya ɗaya da zamu tabbatar ya bayyana shi ne mu
tabbatar da cewa mun azabtar da wannan yaro ta
kowacce hanya ƙololuwar azabatarwa tayadda Littafin zai
fito da kansa ya taimakeshi. Da zarar ya fito kunsan
abinda zaku yi na gaba, saboda haka ku fara aiki.
"Zan shiga shalkwata na fara shirye-shiryen sarrafa
wannan Littafi tayadda kuna zaƙulo shi kawai aiki zamu
fara akansa. A tafiya ta zuwa doron ƙasa ta farko na samu
dama na tattautana da Babban ɗan sarki Kuyurussa'ayi,
yarima mai jiran gado Níwajítu Dúmaƙísu Kuyurussa'ayi.
Kuma ya bada koyon bayansa ɗari bisa ɗari akan abinda
muke niyyar yi da wannan Littafi. Saboda haka lallai sai
mun tabbata munyi nasara a wannan karan."
Bayan Uznu ya tabbatar da cewa aljani kalkutu da Netti
sun fuskanci halinda ake ciki sai ya fita ya barsu domin su
fara aiki akan Armad.
________
A can wani sashin duniya dake ɓangaren Ikwatora na
doron ƙasa ta shida kuwa wata mace ce kwatsam ta
bayyana cikin jini kuma a sume. Lallai kana ganinta zaka
san gab take da mutuwa, kuma lallai idan ba'ai wani abu
akanta ba, to babu makawa mutuwa zatai. A tsakiyar inda
wannan mace ta bayyana kamar wata daula ce ta Dordor
launi-launi. Domin kuwa duk inda ka duba su zaka gani.
Babu gida gaba babu gida baya a wannan daji da take,
babu kuma abinda kake ji sai kukan tsuntsaye da
maganganun jinsin halittar nan da ake kira da Dordor.
To kamar masifar da wannan mata take ciki bata isa ba,
sai kurum wasu daga cikin Dordor dake wajen suka
hange ta. Ai kuwa nan take manyansu suka fara isa wajen.
Amma bisa mamaki kowanne Dordor idan yazo ya
shanshana wannan mace sai kawai yai tsaki ya juya kai ya
tafi. Kuma dukkanin waɗannan dordor da suke zuwa
kanta suna da kai sama da biyar. Kuma kowannensu fatar
jikinsa nada launi na daban. Babu kuma wanda keda Izza
ƙasa da ɗari biyar acikinsu. Lallai koda wannan mace na
cikin hayyacinta bata ishe su kallo ba.
To abu ne dai sananne a duniya cewa Dordor mai kai
biyar zuwa sama shi ake cewa Babban Dordor, sannan
kuma babban Dordor baya cin naman halittar da Izzarta
bata kai ɗari biyar ba. Saboda haka dai ga dukkan alamu
wannan mace ta taki sa'a.
Sai dai kuma ana haka bayan waɗannan manyan Dordor
masu kayika da yawa sun bar kanta sai ga wani Dordor
nan mai kai biyu ya gabato, yana tafiya a hankali kana
ganinsa kasan a yunwace yake. Tun daga nesa ya hangi
wannan mace ya kuma fara murmushi da kansa na
dama, sannan kuma yana dariya da waƙa da kansa na
ɓangaren hagu.
*Abinci ya samu
Yau yau abinci ya samu
Abinci har da kalace
Abinci ya samu
Abinci ya samu*
Haka dai wannan aljani ya wanzu yana gudu-gudu sauri-
sauri yana waƙa har ya isa inda wannan mace ke kwance.
Abune sananne ansan cewa jinsin fararen Dordor sha'irai
ne ma'abota waƙa, kuma sukan rera waƙa musamman a
lokacin da suka samu abinci.
Hakan nema yasa waƙa taƙi ƙarewa a bakin wannan Farin
Dordor wanda kaf komai a jikinsa fari ne fat tun daga
gashin kansa har zuwa fatar tafin ƙafarsa.
Dordon ya miƙa farin hannunsa wanda yafi farar-ƙasa
fari ya juyo da fuskar wannan mace. Sannan ya zaro wata
ƴar ƙaramar wuƙa daga aljihunsa da niyyar ya fara
yankar naman wannan mace yana kaiwa bakinsa-na-
waƙa. Amma kafin ya fara komai ya ɗaga hannu ya fara
da addu'a, "Godiya ga ubangijin daya jefowa da farin
Dordor naman bil-adama. Muna fata gobe ma a bamu!
Ameen!" Wannan Dordor ya shafa wannan addu'a
sannan yai azama wajen fara yankan naman jikin wannan
mace.
Idan ka kalli fuskar wannan mace zaka ga ba wata bace
illa Nusi ƙawar Armad wilbafos, wadda kwamanda Uznu
Ururu yai cilli da ita aka nemeta aka rasa tsahon lokaci.
Nidinne dai Shuraih Usman inkiya
99%
Daga taskar magajin wilbafos
MAGAJIN WILBAFOS
Marubuci: Dr Abdullahi Muhammad Ibrahim
Babi na 53: Bakar guguwa
Post by: Shuraih Usman
@shuraih 99%
www.facebook.com/hausaebooks
.
Daga:- Taskar Magajin Wilbafos
___
A kowanne yanki na Ikwatora dake kowacce ɗaya daga
cikin ƙasashe bakwai na duniya, akwai wani tsibiri wanda
shi ne waje da ma'abota wannan yankin suke gani a
matsayin tsarkakakken waje. Wannan tsibiri shi ake cewa
Tsibirin-guguwa.
A duk bayan kowacce shekara sittin wata guguwa mai
ƙarfin gaske na tasowa daga Tsibiri. Wannan guguwa ita
ake kira da Baƙar guguwa. Duk lokacin da aka fara ta
akanyi watanni kamar biyar ana yinta, kuma anyi ittafaƙi
wannan iska tana da ƙarfin da zata iya tarwatsa duwatsu
da ƙarafa da al'amudai komai girmansu.
Amma acikin wannan...


Read / Download MAGAJIN WILBAFOS book 2

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album