Join Our WhatsApp Group

RUDIN DUNIYA part 1 Complete Hausa Novel Document by RUDIN DUNIYA part 1


RUDIN DUNIYA part 1

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 89186



RUDIN DUNIYA part 1

Reading Time: 7 Hours

Added On: 05, Nov 2023

Author: Nafisat Isma'il Lawal ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : PERFECT WRITER'S ASSOCIATION

Author Phone : Not Inserted

Book License : Paid

Category: Love Novels

File Size: 448.97 kb

File Type: txt

Views: 584+

Download: 363+

Last download: 42 minutes ago

Description/Story: [07/07, 11:23 pm] OumƊahirah نفيسة: 🌍🌍🌍🌍🌍🌍

        *RUƊIN DUNIYA!*

🌍🌍🌍🌍🌍🌍


*NA_NAFISAT ISMA'IL LAWAL*
_UMMUDAHIRAH_

*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT🧝*



*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

                  *P.W.A✍️*





*Romantic Book ne, kuyi haƙuri sabida salon labarin ne ya zo a haka; babu yadda na iya.*










_________________________

*BABI NA ƊAYA*
_______________ *KADUNA ZARIA*
            A garin Kaduna ƙaramar hukumar Zaria; anguwan tudun wada. Malam Iro me kifi, sana'ar sa kenan siyar da kifi. Gado ne da yayi wajen mahaifinsa marigayi, tun yana saurayi yake sana'ar wadda ta kai yanzu har Aure yayi a cikin sana'ar, kuma alhamdulillah yana samu dai-dai gwargwado kuma har ya rufawa kansa Asiri. Mahaifiyar sa tana raye kuma shi yake kula da ita tunda shi kaɗai ne ɗa namiji da suka haifa, sai ƙannin sa biyu mata waɗanda yanzu haka sun yi aure da jimawa, sai dai Allah ya yiwa ɗaya rasuwa a lokacin da zata yi haihuwar fari. Shi ya ci gaba da kula da matafiyarsu tare da nasa iyalan, wanda a lokaci ɗaya jinyan mutuwa ta tarar da mahaifiyar tace ga garin ku nan.

              Shekaru da dama sun shuɗe, wanda har ga shi girma ya soma tarar da Malam Iro; amma har yanzu cikin sana'arsa ta gado yake. Yanzu haka Allah ya albarkace sa da Yara huɗu Mata; wacce matarsa Harira ta haifa masa. A cikin rayuwar Malam Iro akwai dogaro ga Allah da tsantsan tawali'u, duk abun da Allah ya ba shi yana ƙoƙarin karɓa da hannu bibbiyu sannan kuma ya yi mishi godiya. Sai dai kuma matsala guda ɗaya ce a rayuwar sa da yake samu, wanda kuma a yanzu ta zame mishi babbar matsala da yayi sanadin soma gurɓata rayuwar ƴaƴan shi

Harira Mace ce mai tsananin son abun duniya, haƙiƙa duniya tana matuƙar ruɗanta wanda ta kai har ba ta iya bambance abu mai kyau da mara kyau a rayuwarta, ita burin ta kawai tayi kuɗi, me zata taɓa ya zama kuɗi? Sannan aina zata samo hanyar da zai kawo mata kuɗi? Shi ne tunanin ta a koda yaushe. Tun farko Harira irin matan nan ne kyawawa da Allah ya zuba musu kyau; kasancewar ta bafulatanan nan cikin Zaria cikin anguwan Fulani, tallen fura da nono take kawo wa nan cikin kasuwan tudun Wada, wanda har Malam Iro ya ganta kuma tayi masa a zuciya, babu ɓata lokaci ya bayyana mata irin ƙaunar da yake mata, to, itama bata ja zancen ba ta amince domin a lokacin kaf cikin samarin ta shi ne wanda take ganin yana da ɗan kyan gani da sura me kyau, duk da a rayuwarta ta taso da burin auren shahararren me kuɗi; kasancewar yanda ake ce mata tana da kyau, irin su masu kuɗi suko so, domin irin su ne ake ajiyewa a gaban mota, to, ga shi kuma har ta kai wannan lokacin babu wani me kuɗi da ya taɓa cewa yana sonta, tun tana saka ran zata same su domin ta ƙi aure tana jiran irin su, amma kuma shiru kake ji sai irin ƴan iskan samarin nan da suke kawo mata hari ko yaushe. Haƙiƙa ta ji daɗin shigowar Iro cikin rayuwarta, wanda babu ɓata lokaci ta ba shi dama ya tura gidan su, aka yi komai na al'ada aka sanya musu ranan aure.

             Bayan lokaci yayi aka ɗaura musu aure ta tare a gidan su, tana zaune tare da mahaifiyar sa. Sai dai tunda aka yi auren ɗabi'un Harira waɗanda be san su ba suka soma bayyana, Mace ce fitinanniya ga shegen rowa, ko abinci tayi ba ta ba wa mahaifiyarsa, sai dai idan shi ya dawo ya nema mata abun da zata ci, sosai mahaifiyarsa take kuka da irin halin Harira saboda kasancewar ta Mace mai haƙuri, haƙiƙa tana ƙunsan baƙin ciki a wajen ta, ga shi ko kaɗan ba ta ganin girman ta har zagin ta take yi tayi ta gaya mata maganganu mara sa daɗi, shi kansa Iro haƙuri yake yi da ita sabida shima irin mahaifiyarsa ne, tun yana tanka mata yana tsawatar mata har ta zo ta fi ƙarfin sa yanzu, domin a yanzu ta sake kilewa rashin mutunci sai wanda ya daɗu a gunta, bare yanzu tayi ƙawaye matan masu kuɗi masu hannu da shuni, a wurin su take koyo duk wasu abubuwa da bata san su ba a baya, ita rayuwarta kawai tana hangen waɗanda suka fi ta ne shiyasa kullum fitina ba ya ƙarewa a gidan su, kullum da abun faɗan da zata yiwa Iro, ya gaji dai ya ƙyale ta ya fita harkan ta.

             A haka rayuwa ta ci gaba da tafiya har Harira ta haifi ɗiyarta Mace ta fari, aka sanya mata sunan Ƙanwar Malam Iro da Allah ya karɓi abun sa, Nana Firdausi. A lokacin da Harira take da cikin ƙanwar Firdausi har ta kusa haihuwa, sai kuma mahaifiyar Iro ta rasu, sanadin da aka maida wa yarinyar sunan ta, Ummu Kulsum, suna kiranta da Ummu, ita dai Harira da sunan ta gatsau take kiran ta babu ko kunya. Bayan kamar shekaru huɗu sai ta ƙara haihuwar Mace, itama aka saka sunan uwar Harira, Fatimah suna kiranta da Zahra, sai kuma Auta da aka haifa bayan shekaru uku da haihuwar Zahra, sai dai fa tunda aka haifi yarinyar nan Harira ta ɗaura buri na duniya a kanta sabida ganin yadda yarinyar ta fita daban da sauran ƴaƴan ta, tsananin kyawun ta da kaf ƴaƴan ta basu biyo ta ba, duk kyawun Harira ta ninka ta a kyau nesa ba kusa ba, shiyasa tunda aka saka mata suna A'isha Humaira, sai ita Hariran take kiranta da suna Arab sabida tsantsan kyawun ta, kuma sunan ta ji shi ne a wajen wasu masu kuɗi da suka sanya wa ɗiyar su, shiyasa itama take ce mata Arab, shiyasa sunan ya bi ta har girman ta, wanda daga ita ne kuma bata sake haihuwa ba. A wannan lokacin Harira wacce yaranta suke kiran ta da Inna; babu irin sana'ar da ba ta yi don kawai ta farfaɗo da rayuwar ƴaƴan ta, kuma ta sanya su a inda zasu yi gogayya da yaran masu kuɗi, shiyasa tun suna yara makarantar kuɗi suke yi, ita take biya musu kuɗi da komai bata damu da sai Malam Iro ya bayar ba, wanda a yanzu shi kuma yaran suke kiran shi da Baba, sai dai idan ya samu kuɗi yana taimaka musu sosai tunda zuciyarsa bata mutu ba, bazai iya gani yaran sa suna rayuwa be da amfani a tare da su ba, sai dai bai da wani iko dasu tunda sai abun da Harira tace a gidan ake yi, tuni ta mallake shi domin har biye-biyen Malamai take yi yanzu.

            Tunda yaranta suka girma bata da wani buri a yanzu sama da su samo mata masu kuɗi, kowanne iri ne idan yana da kuɗi; to, tana son yaranta su samu, shiyasa bayan sun gama secondary school; Ummu da Zahra, sai ta saka su a nan F.C.E Zaria, duk sanda suka je makaranta suka dawo zata ɗaura musu tallan shinkafa su shiga cikin kasuwa suyi talla, ita a ganin ta idan suna yawo kwararo-kwararo hakan ne zai sa masu kuɗi su gansu har su zo gare su

Yayinda ita kuma Firdausi tana zaune a gida ta ƙi makaranta, sabida ita bata da buri sama da tayi aure, kasancewar rayuwar gidan su yana mugun ɓata mata rai, kwata-kwata ta tsani halayyar da Innarsu take shirin jefa su a ciki, shiyasa ita kaɗai ce ta fita zakka a gidan su, wadda ita ta biyo halayen Mahaifin su ne sak, shiyasa yake tsananin ƙaunarta saboda tana bin maganar sa, yayinda ita kuma Inna Harira ta tsane ta kuma ta fita harkan ta, dalilin da yasa tace, "baza ta biya mata kuɗin makaranta ta ci gaba ba tunda ba ta mata biyayya." Ita kuma dama bai dame ta ba bare ta saka hakan a ranta, duk da Babansu yayi mata alƙawarin, "idan har ya samu kuɗi a wannan shekaran zai saka ta sai ta riƙa bin ƴan uwanta". Amma ita furr tace, "ba ta so." Tace mishi, "ita aure take so yanzu, kuɗin da zai saka ta makarantar gwara ya siyan mata kayan ɗaki." Kasancewar tana da saurayin da yake neman ta tun tana secondary school, sun shaƙu da shi sosai. Ɗan Kaduna ne amma yana zaune da Kakarsa a nan

To hakan ya yiwa Baba daɗi, shiyasa ya samu Nafi'u saurayinta yace mishi, "ya turo magabatan shi."

Abu kamar wasa har aka sanya ranan aure kusan shekara biyu, a haka Baba yayi kurɗa-kurɗan shi har ya samu ya yi mata komai da uba yake yiwa ɗiyarsa

Ba tare da ko sisin Inna ba, tunda ita tace, "ta ƙi bin umarnin ta sai abun da take so zata yi, to ta je tayi auren idan hakan shi ne zai fishshe ta."

Haka kuwa aka yi auren lokaci yana cika. Aka kai Amarya gidan ta da ke can Kaduna, alhamdulillah Nafi'u yana da rufin asiri dai-dai gwargwado tunda yana aikin sa kala-kala. Haka dai ya fi ma Firdausi tunda tayi aurenta ta baro gidan su, su ma ƙannin ta tana fatan ace wata rana sun gane gaskiya su gane cewa Inna tana saka su ne a cikin *RUƊIN DUNIYA!* wanda hakan babu inda zai kai su sai dana-sani.

        Ƙaramar ƙanwar su wato Arab, wacce a yanzu tana S.S 2 ne, ita kuma Inna Harira tana mata awara ne da yamma tana siyarwa a can bakin layin su. Gaba ɗaya yaranta ban da Firdausi ta ɗaura su a tirban da take buƙata, kuma su kansu sun tashi idanunsu a buɗe basu da buri sama da su cikawa uwar su burin ta, su kansu suna jin haushi musamman ganin su a gidan ƙasa gidan talakawa, ga ƙawayen su duk yaran masu kuɗi, shiyasa basu da aiki sai ƙarya, idan ka gansu baza kace yaran talaka bane sabida suturun da suke saka wa, kamar baza su taka ƙasa ba don yanga da iyayi. A duk cikin su ukun; Arab ta fi su fitsara da rashin kunya, domin ita halin mahaifiyarta ta ɗauka har ta zarta ta a son kuɗi, dalilin da yasa kenan ta soma ba wa maza kanta tun a wannan lokacin don kawai ta samu abun duniya, ga ta da samari ko ta ina, duk inda ta gibta sai ta samu saurayi, sai dai ita babu aure a tsarin ta a cewar ta, "sai nan gaba, sai ta gama karatu sannan zata yi aure". Dalilin da yasa take gara kan samari kenan, ga shegen wayon; sai ta ci kuɗin saurayi kuma ta hana shi abun da yake so sai ta gama jan mishi rai ko kuma ta gama wulaƙanta shi. Arab kenan yarinya mai zamani wacce take cin duniyar ta da tsinke a yanzu, a duk faɗin tudun Wada da kewaye babu wanda bai santa ba, har kirari ake mata da sunan, 'Arab Matar manya, kin fi ƙarfin Yaro'.








✳️✳️✳️✳️✳️✳️✳️✳️

          

         Yau ma kamar kullum yanda Inna Harira ta saba yiwa Arab awara domin ta fita mata dashi; hakan ne yau tayi mata, sai dai na yau ya fi na kullum yawa saboda ganin yanda ake ciniki sosai, ba ta daɗewa yake ƙarewa idan ta fita dashi, shiyasa tace wa Arab ɗin, "Autana yau da yawa zan yi miki tunda naga kina dawowa da wuri yana ƙarewa."

Arab tace, "ai kuwa Inna dama ina so in yi miki magana ki ƙara yawan shi don naga ba ya isan su suna son awara na wlh."

Baki Inna Harira ta washe ita kuma tana cewa, "ai dole ne su so awaran ki sabida daɗi, Ni na san na iya ai, ko kayan da nake kashe wa wannan awaran dole su riƙa santin shi."

Dariya daga Arab har Ummu da take jin su suke yi

Ummu tace, "Inna ai Ni ina ganin hannun ki ne mai albarka, ko abincin nan da muke fita dashi ba ki ga yanda ake wawa ba wlh, mu ma idan za ki sake yin mana sai ki ƙara yawan shi, ki haɗa ma har da kunun aya don shima ana yawan tambayar mu."

"To shikenan Allah ya kaimu goben za'a ƙara, dama ina ta tunanin siyan fridge wlh, to yanzu tunda kin ce haka kinga ban ga ta zama ba, yanzu ki taso ki shiga kasuwa sai ki siyo min abun kunun mu fara mu gani; Allah ya bamu sa'a."

"Amin AMin." Duk suka amsa daga Ummun har Arab

Sai Inna Harira ta kuma cewa, "yi sauri Auta ki shirya yanzu zan yanka miki ki wuce."

"To Inna." Arab ta amsa tana tashi daga bakin ƙofan da take zaune tana yankan ƙumba, ta wuce cikin ɗakin su, kayan jikinta ta cire ta ɗaura zani daga iya ƙirjin ta, kana ta fito kanta babu ɗankwali ta kamfaci ruwa a rijiya ta shiga wanka. Ta jima kafin ta fito tunda dama haka ta saba yin wankan ta, bayan ta shiga ɗaki ta gama shiryawa ta fito wajen

Ummu ta soma koɗata tana cewa, "iyen ba Ƙanwar mu, kin ga yanda kika tsatso kyau kuwa? Anya wannan baza ki haɗa gosilo a titi ba? Tirƙashi."

Dariya kawai Arab ɗin take yi tana duba jikinta

Yayinda itama Inna Harira sai washe baki take yi tana koɗa ta tana cewa, "ƴan matana ta fi na kowa kyau, iyee! Kin yi kyau sosai Auta na, na san yau akwai kasuwa kenan."

Fari tayi da manyan idanuwan ta tana taunan chewing gum ɗin bakin ta, yayinda ta furta, "sosai ma Inna, sai mun dawo kawai kiyi min addu'a."

"To Allah ya tsare Allah Ubangiji ya bada Sa'a, Allah yasa a samo mana rusheshen me kuɗi wanda zai kai Ni Makka bana."

"Amin AMin innarmu." Duk suka amsa suna dariya

"Ke ma tashi ki shirya ki wuce kasuwan nan kinga yamma tana yi." Tayi maganar tana kallon Ummu

Ita kuma Arab ƙaton farantin da aka jera mata komai, kama daga kan; icce, matsama, ashana, kalanzir, kafi-tankiya da Robbern zuba awaran idan ta tsame, duk suna kan farantin saboda ƙato ne, sai ta riƙe Robbern awaran a hannu tunda shi mai hannu ne, irin bokitin nan ne fari amma ƙato sosai, ta yiwa Innan sallama ta fice a gidan tana ci gaba da taunan chewing gum ɗinta, ƙararas-ƙararas kawai ake ji tana tafiya kamar zata karye tsaban yanga. Sai da ta ɗan yi nisa da gida sannan ta hangi Zahran su a cikin wata ƙatuwar jib ita da saurayin ta, shiyasa ta nufi wajen don ta ƙi wucewa sai ta kwashi rabon ta, tunda ta hangi wannan motan to akwai maiƙo a wajen, shu'umin murmushinta ta saki har da cije laɓɓa; tana wani gyara tafiyar...


Read / Download RUDIN DUNIYA part 1

START READING

OR

DOWNLOAD TXT NOW
Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album