Join Our WhatsApp Group

KULSUM Complete Hausa Novel Document by KULSUM


KULSUM

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 31556



KULSUM

Reading Time: 2 Hours

Added On: 04, Nov 2023

Author: Sumayya Abdulkadir Takori ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : 07030137870

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 162.76 kb

File Type: txt

Views: 4579+

Download: 2077+

Last download: 30 minutes ago

Description/Story:  KULSUM









1






Littafin


SUMAYYAH ABDULKADIR
takorikabara@gmail.com


SADAUKARWA
SADAUKARWAR littafin Kulsum bakidaya taki ce A'ISHAH SHAFI'I (MARUBUCIYAR ZANEN DUTSE, BAYAN NA MUTU, KOMAI NISAN DARE da WAYE SHI?). Sabida gudummuwar ki a dukkan al'amurana. Allah ya bar zumunci a tsakaninmu har 'ya'ya da jikoki.

Yayar ki, TAKORI
7/11/2020

GODIYA
Godiya ta musamman ga Nura Sada Nasimat sabida jimirin sa na bin rubutuna kafin bugawa da bada shawarwari. Allah ya raya mana Yusuf Nura Sada rayuwa mai albarka.

JINJINA
Ga daukacin mambobin TAKORI'S ONLINE FORUM, littafin Kulsum ya jinjina muku, ni da ku hadin Allah ne. Allah ya bar mana zumunci har gidan aljannah. You are my source of inspiration.

GARGADI
Ban yarda a karanta wannan littafi a kowacce kafa ta sadarwa ba batare da iznina ba, tun daga radio, facebook, whtsp idan har ban yi izni ba, yin hakan karya doka ne kuma abin tuhuma ne daga lawyer na Barrister Sadiq Rufa'i Wali.



TSOFAFFIN LITTATAFAN TAKORI
Ga masu bukatar tsofaffin litttafaina kuma basu iya hawa okadabooks ba zasu samesu a softcopy a kan farashi mai sauki. Ku tuntubeni a whtsp 07030137870.


















KULSUM 1
Safiyar garin Lahadin yau ta kasance mai dauke da hadari bakikkirin, iska na kadawa da karfi, kamshin kasa mai dadi na tashi sakamakon dan yayyafi da aka fara, alamu ne na cewa daga yanzu zuwa kowanne lokaci ruwa mai karfi zai iya sauka. Cikin tsakiyar watan Satumba, a cikin garin GAYA da ke cikin jihar Kano, a wata unguwa mai tsohon tarihi wai ita MAZA-GOMA. Sunan unguwar ya samo asali ne daga wata mace a shiyyar data haifi 'ya'ya maza goma a lokaci daya.
Gidan Malam Jibo, wanda aka fi sani da Baffa Jibo, sanannen gida ne a wannan unguwa, Malam Jibo mutumin kirki ne kuma manomi ne, wanda ya riki noma da daraja, ta kuma rike shi da iyalinsa cikin rufin asiri. Ya fi yin noman gyada, dankalin Hausa da makani lokacin rani. A duk shekara yana nome amfanin gona mai yawa, wanda yake sayarwa a nan cikin garin Gaya da makwabtanta ranar cin kasuwar kauyuka. Matarshi daya tun ta ladan noma, wato Aishatu da ake kira Goggo Shatu.
Baffa Jibo (Jibril) da matarsa Aisha (Goggo Shatu) Allah bai ba su haihuwa ba sai a shekarun girmansu, shekarun su ashirin da aure kafin su samu haihuwar Sugrah. Shekarun Sugrah goma sha hudu aka aurar da ita ga wani malamin makarantar sakandire a garin Yalleman ta jihar Jigawa. Duka-duka shekaru biyu da auren ta zo haihuwar diyarta ta fari, ko fuskar diyar Sugrah ba ta gani ba Allah ya amshi ran ta.
Malam AbdulHadi, wato mijin Sugrah, ya dauki jaririyar da Sugrah ta bari ya damka wa mahaifiyarsa Iyatu. Iyatu ta rike diyar tsayin shekaru biyar cikin tsananin kulawa, shi kuma Malam Hadi ya kara aure. A shekarar da yar ta shiga aji daya na firamare Allah ya karbi ran Iyatu, Malam Hadi ya so ya ci gaba da rikon yarsa a hannunsa, amma take-taken Lami na rashin tausayi da rashin kulawa ga 'Kulsumu' ya sa dole ya dauke ta daga gabanta ya dawo da ita wajen kakanninta na wajen uwa a garin Gaya, wato Baffa Jibo da mai dakinsa Goggo Shatu.

Rashin haihuwa da Allah bai wadata su da shi ba, da soyayyar diyar su Sugrah da bata yi tsawon rai ba, su suka taru suka haifar da soyayya mai tsananin yawa tsakaninsu da jikanyar su Ummu Kulsumu, daga Baffa har Goggo Shatu ba sa iya boye son da suke ma Kulsumu, wannan ya sa Kulsumu ta taso goyon kakanni, wautarta ta yi yawa, ga sokonci da tsokana, amma fa duk da haka Kulsumu na son karatu, daga na boko har na Arabi, komai na Kulsumu irin na mahaifiyarta ne, wannan ya sa suke masifar kama da Goggonta.
Malam Hadi na zuwa duk bayan wata uku ya duba Kulsumu, duk da Baffa ya dauki dukkan nauyin rayuwar Kulsumu mahaifinta ma na iyakar kokarinsa a kanta, in zai zo sai ya dinko mata sabon kaya ko kala daya ne ya sayo mata sabon takalmi ya dinko mata hijabi, in tana son wani abu na makaranta ya yi mata. Bayan Kulsumu ya haifi wasu yayan har biyar da Lami, amma tsammani za ka yi Kulsumu kadai ya haifa saboda son da yake yi mata.

Hadarin ya soma sauka yaf-yaf-yaf a kan rumfunan kwanon gidan Baffa Jibo bayan hadarin ya kai ya kawo, misalin karfe biyar da rabi na asubahi. Goggo Shatu da ke zaune tana lazimi bayan ta idar da sallar asubahi ta mika hannu tana tashin Kulsumu da ke bacci bisa gadon bononta. Kulsumu ta yi wani juyi ta yi mika tare da zumburo baki ta ce cikin muryar magagin bacci,
Goggo ko assalatu ba'a kira ba, don Allah ki bar ni in yi barcina.
Goggo ta sake dala mata duka a gadon bayanta, amma Kulsumu ko gezau, tayi mata dundu ta ki tashi, juyawa ta yi ta koma can karshen gadon ta ci gaba da baccinta.
Gyaran muryar Baffa da Kulsumu ta jiyo daga bakin kofa, ai ba shiri ta zabura ta dirgo daga gadon don ta san wannan dogon carbin nasa zai tsula mata muddin ya shigo ya ganta bata tashi ba. Ba ta tashi ta yi sallahr Asubah a kan lokaci ba.
Daga bakin kofa ya tsaya yayi gyaran murya, ya ce,
In ji dai Kulsumu ta tashi daga wannan barcin nata ta sauke farali?
Na tashi Baffa, har ma na yi alwallah, nasa hijabina na daidaita sahu, sallah kawai zan tayar. Kulsumu ta yi zaraf! Ta amsa kafin Goggo ta yi magana.
Ya wuce dakinsa yana fadin,
Kin taimaki kanki sarkin baccin banza da wofi.
Kulsumu na saukowa daga gadon Goggo, ta ji damshi yana malala a kasa, ga jikinta sharkaf da lema. Ta sa hannu ta toshe bakinta kafin wani kakkarfan kuka ya kwace mata.

Goggo, yau ma na yi fitsari!

Gaban Goggo Shatu ya yi mugun faduwa, ta mike a zabure ta kunna kwan lantarkin dakin, da yake gari bai yi haske ba. Fitsari ne sharkaf a tsakiyar gadonta, ga Kulsumu tsamo-tsamo ta jike tun daga saman rigarta har kasan zaninta. Wannan lalura ta Kulsumu sun dauka ta tafi kenan tun sanda wani mai bada magani da Goggo Shatu ta samo a kauyen Durbunde ya ba ta magani ba ta sake yi ba, yau wajen watanni shidda kenan.
Goggo Shatu ba ta ce komai ba, rigar ta kama ta taimaka mata ta cire, ga dan kirgan dangi har ya soma bayyana, amma Kulsumu ba ta daina fitsarin kwance ba.
Ta kama mata ta cire mata zanin da kamfai duka, ta ce ta dauki wani zanin ta je ta yi wanka da alwala. Ta wuce jiki a salube tana kuka da shessheka ta nufi bayan gida da ke can a tsakar gida. Goggo Shatu ta yaye zanin gadon, ta debo ruwa ta yayyafa sosai ta fidda yar yaloluwar katifar audugar waje tana tsiyaya ta shanya, ta dawo daki ta zuba uban tagumi. Tsoronta Allah, tsoronta kada wani a garin ya san Kulsumu tana fitsarin kwance, idan wannan labarin ya je kunnen wani, tana tsoron kada yarinyar ta ki auruwa, duk kyawun surar ta.

Tashi ta yi a sanyaye ta nufi turakar Baffa. Malam Jibo na karatun Alkurani mai girma lokacin da Inna Shatu ta shiga, bai saurara ba sai da ya kai karshen ayar suratul Ali-Imran, ya yi addua suka shafa a tare. Kallo daya ya yi wa matarsa ya tabbatar tana cikin tsananin damuwa. Tsufanta ya fara bayyana, domin ta wuce shekaru sittin, cike da kulawa ya ce,

Me ya faru Goggon Kulsumu?

Goggo ta sauke taguminta cikin alhini ta ce,
Baffa, fitsarin kwancen nan ya dawo.
Bai nuna damuwa a kan fuskarsa ba don ya kwantar mata da hankali, amma shi ma sai da zuciyarsa ta tsinke. Ya tausasa murya ya ce, Komai ya faru da bawa da sanin Allah Aishatu, tun da ana neman magani insha Allahu watarana za'a dace. Babu cutar da ba ta da magani a duniya sai tsufa sai ko mutuwa. Saboda haka mu ci gaba da addua, Allah zai yaye mata. Yanzu ku shirya ku koma Durbunde tunda nashin akwai alamun nasara wajen watanni bakwai ba ta yi ba tunda ya bada magani. Ga kudin mota ku fita da wuri don ku samu motar farko.
Hannu biyu Goggo ta sa ta karbi kudin daga hannun maigidanta, ya ciro wasu ya ce,
Ga wannan ku ba shi na sadaka, wannan kuma ku sha ruwa a hanya.
Sai da Goggo ta jira Kulsumu ta yi sallah, ta sanya kaya amma har zuwa lokacin Kulsumu ba ta bar kuka ba, duk da lallashin da Goggo ke mata na cewa, Allah zai ba ta lafiya. A ganin Kulsumu in wani ya san tana fitsarin kwance ta gama tozarta a idon duniya. Ita ba ta wani tunanin aure, wanda shi ne damuwar Goggo, ita a ce mata Kulsumu mai fitsarin kwance shi ne damuwarta. Shi ya sa ta ke nesa-nesa da kowa, ba ta yarda ta yi kawa ko aminiya, Goggo ita kadai ce kawarta aminiyarta, Baffa kuma abokin shawararta.
Bayan ta gama shiryawa Goggo ta sa ta a gaba suka tafi tasha inda za su hau motar Takai daga nan su sauka su hau ta kauyen Durbunde.
A cikin mota daga Goggo har jikanyarta babu mai magana, Kulsumu na jikin tagar kujerar farko, Goggo na gefenta. Sun yi saa sun samu motar farko amma motar ba ta samu cika ba sai karfe bakwai na safe. Goggo ta biya kudin mota, ta fita ta sayo wa Kulsumu kunshin kosai mai zafi na hamsin ta dawo motar. Ba ta dade da shigowa ba motar ta cika suka dauki hanya.

Ba yadda Goggo ba ta yi ba Kulsumu ta ci kosan nan, amma Kulsumu ta ki, hawaye kawai ta ke sharewa da gefen hijabinta. Goggo ta rabu da ita, ta ci gaba da jan cazbahar hannunta. Ba su tsaya ba sai a garin Takai, lokacin da suka hau ta Durbunde ne cikin Kulsum ya ishe ta da kugi, dole ta bude kosan ta soma ci. Bayan ya riga yayi sanyi. Zuwa lokacin ta gaji da kukan ta yi shiru ta goge idonta, sai kallon tseren da bishiyoyi ke yi bisa hanya ta ke yi, tana sake-sake a zuciyarta.
Kowa a duniya yana da damuwa, wani ta maraici, wani ta rashin gata, ita dai ba ta taba dandanar ko daya ba. duk da ba ta san mahaifiyarta ba, ba ta taba yin maraicin uwa ba. Iyatu da Goggo sun cike wannan gibin da kulawar da ko mahaifiya ba za ta yi mata ba. damuwarta a duniya wannan fitsarin kwancen ne wanda tun daga yarinta ya zarce har yau bai barta ba. Sai kuma matsalar gani; bata gane mutane daga nesa sai sun matso kusa. Ba ta taba gaya wa kowa ba, don ba ta so ta kara wa Goggo damuwa a kan tata. Ta sani Goggo ta fi ta damuwa a kan lalurar fitsarin kwancen ta. Ina ga ta zo ta gaya mata ba ta gani sosai, musamman da daddare? Wani lokacin sai ta hada da lalube a bandaki in babu wutar lantarki.
Tana wannan tunanin ta ji kwandasta ya ce,
An iso Durbunde, na Durbunde ku sauko.
Goggo ta kama hannunta suka fito, sannan suka samu mashin guda biyu suka hau wanda zai kai su har kofar gidan mai magani.
Layi cunkus suka tarar, haka suka zauna cikin jigata suka bi layi har bayan azahar kafin su samu ganin mai maganin. Gara Kulsum ta sanya kosai a bakinta, Goggo ko ruwa ba ta kurba ba duk sun galabaita. Sanda suka shiga Goggo ta gaishe shi, sannan ta dora da bayanin da ke tafe da...


Read / Download KULSUM

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

4 Comments On KULSUM
avatar
zainab-salisu-kasim

6 months ago

Reply

I luv dis book

avatar
zainab-salisu-kasim

6 months ago

Reply

I luv dis book

avatar
amina-abdul

5 months ago

Reply

love it

avatar
aysha-abubakar

3 months ago

Reply

I like the book

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album