Subscribe for N1000/month for downloading access and an ad-free site. Contact WhatsApp +2348140419490 if you can't pay / subscribe. SUBSCRIBE

24 yin

TAME GARI Complete Hausa Novel Document by TAME GARI


TAME GARI

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 100716



TAME GARI

Reading Time: 8 Hours

Added On: 30, Sep 2023

Author: Khadija Usman ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 535.96 kb

File Type: txt

Views: 7259+

Download: 7005+

Last download: less than 1 second ago

Description/Story: [: TA ME GARI*

NA
khadija usman

*BISMILLAHIR RAHMANIRRAHIM*

1⃣

Na rantse da Allah bazan yadda ba sai an biyani nikana tun

kin isa ma wlh kika sake kika je kika fadawa innata yaseen sai kinci ubanki cewar dije dake kara tattake garin dake zube a kasa kuma an barar din duk ranar da kika qara cemin dijan gala tame gari tuwon gidanku ma zanje in barar wlh

su Shatu dake gefe suna kallo ba damar suyi magana dije taci uwarsu dan haka sukayi gum ko yi hakurin sun kasa fada hafsi kuwa sai rizgar kukanta takeyi dan tasan yau idan taje gida kashinta ya bushe gurin delu dan saita mata dukan mutuwa kuma tasata nemo mata wani garin koda ta tuna ai saita kara bare baki dije ce ta kalleta tace wai ke uwar me nayi miki da kiketa min wannan kukan danma ban faffasa miki baki ba hegiya me idon gyada

shatu ce ta karaso kusa da ita tace kin san delu dukanta zatayi idan taje gida kin san dai ba imani ne da ita ba

shuru dije tayi na dan wani lokaci kamar wadda ta tuna wani abun sannan kuma tace toh kinga ke kika jawo wa kanki tunda kika tsoka ne ni amma kiyi haquri kinji tahi nasan yadda zamuyi amma sai kin bani hakuri

da sauri hafsi tace yi haquri dan Allah

toh naji ya sunana

Anti dije

wani farin ciki ne ya mamaye zuciyarta dan tana masifar son sunan nan na 'yan binni dan haka da sauri tacewa hafsi taso muje gidanmu in baki dawar ki kara kaiwa nikan

da sauri hafsi ta mike dan tasan ko yanzu takai nikan sai ta ci ubanta dan ta jima dan haka da sauri suka je gidansu dije koda suka je dije bata boyewa inna saudi komai ba aikuwa ta basu dawa suka kai nika har gida dije suka raka hafsi aikuwa delu kamar ta ari baki taita jarabar ta dayake 'yan dukan basa kusa sun dai samu rabon zagi amma bata daki hafsi ba

********
mota ce kirar honda Accord LC ta shigo cikin garin Gawo kasancewar rashin kyawun hanyar ga kuma da alama wanda ke cikin motar yasha tafiya mutum biyu ne ciki matasan samari kyawawa daka gansu kaga wadanda hutu da nera suka zauna a wajen tuki yakeyi kamar wanda aka yiwa dole kafin ya waiga ya kalli dayan yace cikin kasalalliyar muryarsa

Habeeb wlh nagaji dayawa na matsu mu qarasa cikin garin nan in yada zango kan gadon tsohon nan

wanda aka kira da habeeb yayi murmushi kafin yace hmm kaima kenan bare kuma ni dana sha tafiya kwana nan gashi yau ma son ganin wannan me ran karfen yasa na biyoka

hmmm kai dai bari ai wannan tsohon inaga rokon Allah yakeyi mana shiyasa bama iya daukar lokaci bamu ganshi ba ko daddy ma fa kullum shi batun shi baba malam kusan koyaushe yana kan hanya

toh Allah yaja da kwana dai

Ameen ya Allah

kam bala'i ta fada yayin da taga motar na kokarin shigewa alamar ma na ciki besan me yayi ba giginyar dake hannunta ta dauka ta saita glass din motar ta wurga cikin sa'a kuwa ta daki glass din side driver sannan taje ta hada da bakin habeeb wanda yagama amsawa da ameen yanzu

wani wawan birki ya taka tare da kiran ya Allah sbd ganin abun da yayi kamar a mafarki dubansa yakai inda habeeb yake yaga nan da nan bakinsa ya haye ya wani kumbura kamar bakin jaba ga kuma jini na zuba yaso yayi dariya harga Allah amma ba hali dole ya ambaci kalmar subahanallah ya fara kokarin bude motar ya fito danya zagaya gurin habeeb dan shi har yanzu baisan ta inda abin yafaru ba amma dai kawai yaga wulgawar abu

tsaye take ta rike kugu da hannu daya dayan kuma wata katuwar giginyar ce datafi ta farko girma
kwalliyar fuskarta kawai yagani yaji gabansa ya fadi dan wlh babu tantama wannan aljana ce

wa'innahu sulaimanu wa'innahu bismillahir rahmanir raheem ya fara ambata cike da tsoro da faduwar gaba domin dai babu tantama wannan aljana ce duba da yanayin ta gata fara sol saika ce zabiya ga kuma uban bakin kwalli data shafa a bakin nan kamar 'yar auta ga jagira cinku ta hade da kwallin dataja hawayen masoyi

jikinsa ne ya hau kyarma inda ita kuma dije take ta fahimci meyake nufi aikuwa a zuciyarta tace anzo gurin

harara taci gaba da wurga masa tanata juya ido inda shikuma hakan ke kara firgita shi cikin karkarwar jiki ya qarasa inda habeeb yake ya sunkuyar da kansa kasa sakamakon nauyin daya yi masa sbd giginyar ta bugi kansa ga haqorinsa guda daya daya fita ga bakin ya kumbura yayi tsayi kamar shantu cikin rawar jiki Nasir yakarasa inda yake ya bude murfin motar yana me karanta duk addu'ar data zo bakinsa dago kansa yayi ya dubeshi jin yanata kwarara addu'a sai ya fahimci lallai gamo sukayi domin ya hango aljanar tsaye da irin tasu giginyar ta Aljanu tanata juya ido duk da jirin dayake ji hakan bai hanashi rudewa ba shima ya kama kokarin fitowar nan suka kankame juna shida nasir wanda har kwalla yafara yi dan tsoro musamman duba da yayi da yanayin gurin babu komai sai tarin bishiyoyi da besan kona meye ba amma dai yasan harda na kuka kuma sune gidan aljanu

cikin wata irin murya da malkwada harshe dije tace ku bil adama daga ina

wani irin fitsari ne ya kufcewa naseer shiko habeeb ji yayi kamar ya suma dan kanshi saida ya amsa

ko bakwa ji ne ina tambayarku?

cikin in i na nasir yace yi....yi..ha.k..uri.daga Abuja Abuja wlh muka zo

shine aka ce dan kunzo daga binni kubi takan 'ya'yana suna tsaka da yin wasan su wato sbd kun raina mu ko

ah ah wlh ba...bahaka bane wlh ku kuke ganinmu bamu muke ganinku ba dan girman Allah kiyi haquri wlh bamu sani ba

toh naji zan hakura amma sai dai kubar abin hawanku anan ku qarasa da kafarku inda zaku ko kuma ni inkai ku

ah ah wlh mun gode suka fada a tare zamu karasa da kafarmu ina ke ina wahala akanmu

hahahahahaha
tayi dariya sannan tace saini dije uwar aljanu ku wuce amma fa bazan kyaleku ba duba da yadda kuka raunata 'ya'yana yanzu haka suna bangon duniya wajen me magani dan haka sai naje naga yadda jikinsu yake tukunna kafin in san wanne hukunci zanyi muku

kuuuuu cikin nasir yayi wata kara dan girman Allah kiyi hakuri wlh bamu san dasu bane ina mu ina aikata haka muna sane

toh naji ku tashi ku tafi gobe kuzo ku dauke wannan motar amma ba yau ba

to toh toh mun yadda wlh

sam habeeb yakasa tafiya yayin da naseer ne ya kamashi da kyar yasaba a kafada ya miki hanya bako waiwaye harda hadawa da dan gudu bako waiwaye

tunda dije taga haka ta zube a gurin tanata dariya harda hawaye a irin wannan yanayin su shatu suka qaraso suka risketa nan suka shiga tambayarta sam kin fada musu tayi gashi ba damar su matsa ta dankari banza dan karfi ne da ita kamar yaki inji su duk ta fisu karfi

sai da tayi me isarta kafin ta mike tace mu tafi

hafsi ce tayi karfin halin tambayarta ina gyadar da kika samo ?

ban sani ba tafada tana harararta

ai kuwa tayi gum suka ci gaba dactafiya da zarara ta tuno yadda bakin habeeb ya koma da kuma yadda taga Naseer yayi fitsari saita kuma kyalkyalewa da dariya sudai su hafsi nasu ido amma ba damar tambaya sai uwar gayyar ta so bada labari dakanta

*****
tafiya yakeyi ya hada zufa ga habeeb na cikin wani hali da taimakon Allah da taimakon wasu matasa daya sansu a gidan baba malam suka qarasa da shi gida

🌀🌀🌀🌀🌀🌀



*TA ME GARI*


2⃣

*ina neman afuwarku sakamakon jina shuru da kukayi a littafina ZARGI NE SILA Insha Allahu shima zan karasa muku shi nan kusa uzuri ne yasha kaina*


ba karamin tashin hankali baba malam ya shiga ba ganin halin dasu habeeb suka shigo cikin rudewa ya shiga tambayarsu lfy ko hadari sukayi

sam naseer baya cikin nutsuwarsa abinda kawai yake iya fada shine gamo mukayi malam aljana wlh aljana ce

subahanallah!!!

malam ya fada kafin ya ce aje a kirawo muntari me chemist don ya duba habeeb domin yaga yana jin jiki da alama


bayan an gama masa duk abinda yakamata ayi masa harda allura malam kuwa rubutu yayi musu tare da tofa musu addu'oi sbd dukansu sun firgice daga baya suka samu bacci su duka kowa yanata al'ajabin abun wai aljana toh ko a ina suka ganta oho

****

da wakarta ta shigo tana rerawa inda ko sallama batayi ba ta shigo innah dake zaune
Domin cigaba da karantawa sai ku downloading.
Yadda ake downloading na littafin: ku tabbata kunyi register da shafinmu sanna kunyi login, idan bakuyi register a kasa zakuga maballai guda biyu daya an rubuta LOGIN dayan kuma an rubuta REGISTER sai ku taba su kuyi register, daga nan sai ku yi subscription koda na naira 1000 ne, domin sai kunyi subs dinann ne kadai zaku iya dauko littatafanmu.

Ya ya akeyin Subscription namu : Bayan kun yi Login ko register daga kasa zaku ga wani jan maballi (button) an rubuta SUBSCRIBE sai ku taba shi zai kaiku inda zaku zabi package wato tsarin subs na ku da mu. akwai na wata guda, watanni biyar da shekara guda. da zarar kun zaba zai kaiku inda zaku biya kudin, wanda daga nan sai ku cigaba da downloading kawai abunku

ABUN LURA : duk wani littafi da kuka gani a shafinnan kyauta ne, wannan tsari mun zo da shine don mu samu hanyar da zamu iya rike shafin muna managing na shi, izan ku kayi subs na mu tamkar DONATION ne ku ka yi mana, ku ka bamu kwarin guiwa don mu ciagaba da kawo muku sabbin littatafai, amma duk wanda ya ga bazai iya ba toh zai iya karanta littafin kyauta a cikin shafinnan namu batare da ya downloading ba, kawai ya yi kasa zai ga Koren maballi (button an rubuta) START READING sai ya taba zai kaishi inda zai karanta littafin.

Sannan duk wanda yaga kamn wannan process din zai bashi wahala kai tsaye zai iya min magana ta whatssApp +2348140419490, ya tura min kudin ni kuma zan dora mai subs din akan account na shi

NB: iya ta haka ne zaku iya karanta wannan littafi a shafinmu babu wata hanyar. DAN ALLAH KU DAINA MANA MAGANA AKAN MU TURA MUKU LITTAFI TA WHATSAPP, BAMA TURAWA HANYA GUDA MUKE TURA LITTATAFANMU SHINE WEBSITE NA MU https://taskarnovels.com.ng DUK MAI BUKATAR LITTAFINMU YA JE CAN YA KYAUTA NE, AMMA DOWNLOADING KUWA BA KYAUTA BANE SAI YAYI SUBSCRIPTION NA WEBSITE NAM
This is not the real Download Button


Read / Download TAME GARI

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

This is not the real Download Button
Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album