Subscribe for N1000/month for downloading access and an ad-free site. Contact WhatsApp +2348140419490 if you can't pay / subscribe. SUBSCRIBE

24 yin

HAUWA KULU WOMEN LEADER book 1 Complete Hausa Novel Document by HAUWA KULU WOMEN LEADER book 1


HAUWA KULU WOMEN LEADER book 1

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 19015



HAUWA KULU WOMEN LEADER book 1

Reading Time: 1 Hours

Added On: 03, Oct 2024

Author: Oum Yasmeen ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : 09061890481

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 106.54 kb

File Type: txt

Views: 395+

Download: 181+

Last download: 2 days ago

Description/Story: 
*HAUWA KULU WOMEN LEADER*

Oum yasmeen




Da sunan Allah me Rahman mejinkai

Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfanar da al'umma





*Perfectly pen's*

*King and queen writing chamber*



Story and writing

*Oum yasmeen*


https://whatsapp.com/channel/0029VaLdFeg4SpkQ9xyW5c0k

Domin samun cigaba kuyi following din channel dina


Book 1

page 1 🔞



Ji tayi an buge'ta da sauri ta dago zata zuba uwar tijara sai kuma taga baraka tace



"Baraka ina zuwa haka...da tsakar ranar nan..?,


ke kai zan tambaya ina zaki ai ni kinsan inda nake zuwa



Haɗa rai tayi tace



"Baraka kin san halina sarai bana son rashin arziƙi ina tambayar ki kina tambaya ta...,


dariya tasa tace



"Maida hukar gidan gwamnati zani....,

washe baki hauwa tayi tace


"Dan Allah aikuwa nima gobe in zaki zani..,

Tsalle baraka ta daka tace

"Dan Allah gwaggo ta barki...?,



guntun tsaki taja tace




"Ai ita gwaggo bata da matsala inhar ina so to itama tana so kahu hamisu ne matsalata amma shima a sannu zan maganin sa..,





kai baraka ta jinjina tace



"Wallahi hauwa in kika shiga gidan gwamnati zaki iya da ko wanne shege barin shegun woman leader ɗin nan da basu da mutunci....


turo daurin ta gaba tayi tace




"Ke nima ai woman leader zan zama...,



dafa kafaɗar mara tayi tace


"Uhmmm kin san kuwa zaki iya...,

dariya ta sheƙe da ita baka ganin dariyar hauwa in ba mugun'ta ba zata yi ba tace




"Dan Allah ai kuwa kaf garin geza sai an san da zamana ke har fadar shugaban kasa sai naje...... siyasa sanadi..,



Jinjina kai Baraka tayi tace





"Allah ya nufa kin ga tafiya ta...,


To sai kin dawo ai zanzo kai kurun baraka ta gyada mata tayi gaba itama ta ci gaba da tafiya har ta isa gun me kayan miya washe baƙi yayi yace


"A'a rabebe arnan daji kece yau a gun nawa...,



haɗa rai tayi ta miƙo mai hamsin tace





"Bani attaruhu......na hamsin..,





da rawar jiki ya amsa saurin ja da baya tayi ta ya mutsa fuska tace




"haba jolu ka dinga tsabta gaka warin da kake kaga bani kuɗina in kara gaba in siya...,



ransane ya ɓaci yace


"To yar hau in baki ba ai ace bake bace shegiyar jikar masifaffiyar tsohuwa.......ai kafin ya ƙarasa ta daddage ta zabga mai kasa baki diɓar attaruhun'ta tayi ta fita a guje


kasa haɗe baƙin sa yayi


ya shiga tofar da yahu haɗe da kasa ya bita a guje da gudu ta shiga cikin gidan su ta rufo kofar langa langa dafe gwuiwoyin'ta tayi tana mai da numfashi tasan tun da tazo gida ta tsira zuwa gobe kuma zata ƙara shammatar sa ta rama zagin da ya yiwa gwaggon'ta yar aljanna tana jin irin zagin da yake yi


nan zuciyarta ta har zuƙa ta shiga gida ajiye attarun da ta siyo tayi yafi na dari......
ta shiga ɗakin da mage yake ajiye karan..... farautar mage



ta kunto da yake sun saba da karan in ya kace yabi mutum binsa yake duk inda ya shiga sai ya bi wan da kanuna mai buɗe kofar tayi ai jolo yana ganin karan a guje ya fita bama takai da sakin sa ba dariya ta sheƙe da ita ta kamosa


mai dashi ma'ajiyar'sa tayi



gurin kahu musa ta nufa buɗe wajan da yake kiwon zaɓin'sa tayi ta kamu uwar garken'sa ta mai da ta kulle jikake tana kuyat kuyat kuyat


Da saurin kama baƙin zabuwar nan tayi ta salallaɓa ta fito sai ta kanta tayi a rariya zata ta yanka saita kan tayi ta yanka ta murɗe kanta a fuka fuki ta ƙari burburwar'ta


Wanke hukar tayi ta wanke gun


daman kafin ta dawo gwaggo ta dora ruwa fige'ta tayi tsab ta sa gashin a baƙar leda duk bidirin nan da take ba wanda ya sani a gidan





hakan kuwa baƙaramin dadi yayi mata ba dan haka ta cikin sauri take komai gwaggo tane gefe tana jajjage tace





"Amma wannan attaruhu yayi araha...,



ta gefen ido ta kalli gwaggo tace





"In ana cin ɓaure ba'a tone tone...kawai ki ci gaba da daka,





banza tayi mata har ta gama ta kwashe ta koma ɗaki



tafasa zabuwar nan tayi sannan soya zabuwar nan tayi sannan ta soya attaruhun nan tayi tare albasa yaji kayan kamshi saka ta tayi a cikin soyayyan attaruhun nan ta juja'ta nan fa kamshi ya baza ko ina





gafaran ku dai masu gida gaban jidda ne ya waɗi sai ta dake ta washe baki tace







"Kahu musa barka da dawo wa..,



mamaki ne ya kama shi to jidda hankali tayi ne ......har tana mai barka da zuwa in kana da rai zaka sha kallo ya raya a zuciyarsa yace





"yauwa kululu me kike dafawa haka...kamshi ya ƙaraɗe ko ina..na garin ɗurma..,


Sosa keya tayi tace



"yauwa kahu zo kai ma ka kwashi rabon ka biyan bashi akai min da kaza shine nace mun dade bamu motsa baki ba bara nayi mana dabgee muciiii...yau kowa ya mai da mugun yahu....,





tattare malin malin ɗin'sa yayi zuciyarsa tayi fari kal yau zai washe baki....da jajjaja..an dade ba ahaɗuba ƙaraso kujera ya samu ya zauna







dariya ce ta kusab kubbucewa jidda gashi dai yana giwo amma ba wanda ya isa yaci shima ba ci yake ba sai dai su mutu ba wanda ya isa yaci aikuwa yau tasan ladan kowa na gidan nan domin sai sun tauna kashin uwar garken kahu musa tace



"Kahu lafiya naga kayi hurjajan da kai kaga fuskar ka kuwa...? yawa kwan lantarki duk ta motsi...,



haɗa rai yayi kome ta tuna sai kuma ya saki yace


"Am kululu bara in samo kwano ki zuba min nawa naga kamar ya dahu...,





Da sauri gwaggo ta fito tace


"Wallahi baka isa ba ko ni ban ciba sai kai daga zuwan ka da kafa yawa katafila kana cewa a zuba maka da sai miƙe huya kake yawa murriƙen lema...anya kuwa musa kana so kaga annabi...?,





me jidda zata yi inba dariya ba haɗa rai yayi ya kasa magana saukewa tayi ta zubawa gwaggo nata sannan ta zuba nata ta miƙowa haku tukunya da huya da kafafuwa zaman dirshan yayi yana ci yace



"Amma kululu wallahi baki da kirki jibi wanda kika bani me maƙon ki raba dai-dai ni da gwaggo ki dau karami shine kika nuna wariyar launin fata ko....?,





Kut gwaggo ta haɗe naman bakin ta taci



"Kululu dauko min tukunyar nan tun da bashi da godiyar Allah....duk wanda be godewa Allah ba zai godewa azabarsa..,




saurin jan tukunyar yayi ya zuge huya yace



"Haba gwaggo agaban yarinyar nan kike min haka..,





gyara zama tayi tace



"Wato jidda anya akwai tsuntsuwar da takai zabo dadi...?,


kasa haɗiye yar tsokar da ya cira yayi besan lokacin da ya zunduma ihu ba yace





"Wayyo Allah na shiga uku gwaggo me kike faɗa..,



saurin tashi kululu tayi ta sheƙe da dariya tana kallon kahun nata sai zare ido yake yawa wanda ya yiwa sarki karya ga dalalal da yahu da yake ya kasa haɗiyewa tace


"Wayyo Allah gwaggo kahu musa bashi da lafiya abin mahaukata yake....mu gudu...kar ya murɗe mana huya kamar yarda ya murɗewa zabuwar....sa,




Baba lami ce ta fito tana lasati tace



"Malam ban ga uwar garken ka ba...kuma kamar kwai zata fara Allah isa ɓarayi ne suka shigo ba...,





da hannun'sa ya shiga nuna su kululu yama rasa bakin magana





Karab jidda tayi tace





"Kar ka doramin jakar tsaba kaji su dinga bina biyan bashi akai min na zabuwa...,



malin malin ɗinsa ya cire yayo kan jidda a zafafe gwaggo ta jawo shi tace



"Wallahi ka taɓa ta zan ɓatar maka jidda ce tace tana son cin dabgee shine ni kuma bani da kuɗi nace ta zaɓo mana me tsoka da maiƙo a cikin zabin ka muci tun da nasan kai in na tambaye ka ba bani zakai ba shi kuma maraya ba a hanashi a bu...,



wani irin tukuƙi zuciyar kahu musa take kai ya gyaɗa yawa kadangare ya dauki malin malin ɗinsa bal yayi da tukunyar cikin daga murya gwaggo tace




"Kayi ball da ɗuwawun Rabi'u...,





tsalle jidda tayi ta dinga dariya ran baba lamine ya ɓaci ta bar gurin .....



fakar idon gwaggo yayi ya dauki kwanon jidda ya tafi


ihu jidda tayi tana ta zauna a kasa tana rusar kuka kai kace mahafin'ta da ya rage mata shine ya mutu



tsaki gwaggo tayi tace



"Na dawo gareki shine kika zuba naki yafi nawa Allah shiƙara da ya dauke miki..,







dakata wa tayi da kukan ta zaro manya manyan idanuwanta.....,







********


Cikin sauri ta ballo magani ta watsa a bakin ta ta dauki glass cup ɗin dake kan table ta sha daga shi sai trouser milk colour sai singlet ya shigo saurin boye



raguwar maganin tayi da sauri ya ƙarasa cikin haɗa rai yace



"Bani abin da kike sha...,



gaban tane ya waɗi kut ta
Domin cigaba da karantawa sai ku downloading.
Yadda ake downloading na littafin: ku tabbata kunyi register da shafinmu sanna kunyi login, idan bakuyi register a kasa zakuga maballai guda biyu daya an rubuta LOGIN dayan kuma an rubuta REGISTER sai ku taba su kuyi register, daga nan sai ku yi subscription koda na naira 1000 ne, domin sai kunyi subs dinann ne kadai zaku iya dauko littatafanmu.

Ya ya akeyin Subscription namu : Bayan kun yi Login ko register daga kasa zaku ga wani jan maballi (button) an rubuta SUBSCRIBE sai ku taba shi zai kaiku inda zaku zabi package wato tsarin subs na ku da mu. akwai na wata guda, watanni biyar da shekara guda. da zarar kun zaba zai kaiku inda zaku biya kudin, wanda daga nan sai ku cigaba da downloading kawai abunku

ABUN LURA : duk wani littafi da kuka gani a shafinnan kyauta ne, wannan tsari mun zo da shine don mu samu hanyar da zamu iya rike shafin muna managing na shi, izan ku kayi subs na mu tamkar DONATION ne ku ka yi mana, ku ka bamu kwarin guiwa don mu ciagaba da kawo muku sabbin littatafai, amma duk wanda ya ga bazai iya ba toh zai iya karanta littafin kyauta a cikin shafinnan namu batare da ya downloading ba, kawai ya yi kasa zai ga Koren maballi (button an rubuta) START READING sai ya taba zai kaishi inda zai karanta littafin.

Sannan duk wanda yaga kamn wannan process din zai bashi wahala kai tsaye zai iya min magana ta whatssApp +2348140419490, ya tura min kudin ni kuma zan dora mai subs din akan account na shi

NB: iya ta haka ne zaku iya karanta wannan littafi a shafinmu babu wata hanyar. DAN ALLAH KU DAINA MANA MAGANA AKAN MU TURA MUKU LITTAFI TA WHATSAPP, BAMA TURAWA HANYA GUDA MUKE TURA LITTATAFANMU SHINE WEBSITE NA MU https://taskarnovels.com.ng DUK MAI BUKATAR LITTAFINMU YA JE CAN YA KYAUTA NE, AMMA DOWNLOADING KUWA BA KYAUTA BANE SAI YAYI SUBSCRIPTION NA WEBSITE NAM
This is not the real Download Button


Read / Download HAUWA KULU WOMEN LEADER book 1

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

This is not the real Download Button
Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album