Join Our WhatsApp Group

SUBUL DA BAKA 1, 2 & 3 Complete Hausa Novel Document by SUBUL DA BAKA 1, 2 & 3


SUBUL DA BAKA 1, 2 & 3

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 50187SUBUL DA BAKA 1, 2 & 3

Reading Time: 4 Hours

Added On: 28, Jan 2024

Author: Zainab Dahiru Daura ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 257.05 kb

File Type: txt

Views: 1980+

Download: 1529+

Last download: 2 days ago

Description/Story: Subul da baka 1 page 1
Posted by ANaM Dorayi on 08:41 AM, 20-May-15
Under: Subul da Baka
Lungu ne mai dauke da komatsen duwatsu,
robobi, leda da kuma fasassun kwalabe,
kana ketare Wadannan zaka yi karo da
katuwar bola mai dankaren wari,
musamman a lkc irin wnn wato damuna.
Gefe da bolar daga hnn dama Wani
kwarmatsattsen gidan kasane mai ' yar
guntuwar katanga yana dauke da daki daya
tak! sai makewayin langa-langa, daga bayan
dakin. Tsakar gidan murhun kasane da ' yar
guntuwar katanga yana dauke da daki daya
tak! sai makewayin langa- langa, daga
bayan dakin. Tsakar gidan murhun kasane
da. ' yar randar ruwa, sai igiyar shanya data
raba gidan biyu. Daga nesa kana hango
gwangwanayen alwala a jikin langa-langar
makewayin. Karamin gadon kara ne a
dakin, mai dauke da katifar Rimi, sai
jikunan kaya na gana ( Ghana must go ).
Daga bakin kofar akwai ' yar kujerar katako
ta zama, Kasa kuma an shimfida tabarma.
Gida ne na mabukata wnd rashi yayi wa ka
tutu.
katutu. Na yi saurin maida kwallar da ke
zubo min, tare da kara gyara fuskata.
mahaifina Allah ya karbi rayuwarsa tun
muna kanana kwarai, danginsa kuma sun yi
fatali da al'amuran mu, nice babba sai
kannena biyu Aisha da Sumayya. Allah ya
jarrabi mahaifiyar mu da ciwon asthma, shi
yasa duk talaucin mu baka ganin kura a
gidan mu, musamman kura. Kr2 na ya
tsaya tun shkr 2 da suka wuce, wato lkcn
da na gama aji uku. Da farko na fara talla
sai muka Ga cewa, hakan ba zai fisshe mu
ba, shi ne Wani aminin mahaifinmu ya
samo min aiki a gidan sari a matsayin
BAIWA cikin bayin da aka dauka sabbi.
Insha Allahu kuma gobe nake sa ran
farawa.
karfe 9 na dare muna shan garin rogo da
kuli a matsayin abincin darenmu kamar
kullum, Ina ta kalle ni tare da fadin.
"Abinda nake son ce miki shi ne, ki yi
addu'a Allah ya tabbatar miki da alherin
wnn aiki, sannan ya kawar miki da sharrinsa
kmr ydd na dage da tawa addu'a ba dare
ba rana. Kuma a dk inda kika shiga ki sanya
tsoron Allah a zuciyarki, ki tuna matsayin ki
dana iyayenki, banda daukar abinda ba a
baki ba, wlh ki guji abin hnn mutane ki
zauna Lfy. Ban yafe miki ba matukar ba a
baki abu ba kika dauka, ko kika roka. Aiki ya
Kai ki, shi za ki maida hnkl ki yi, banda
yawan surutun banza idan ba tmbyr ki aka
yi ba, do min yawan magana na haddasa
karya. kada ki manta ko ke wace ce, lkcn
da kike ckn gidan SARAUTA, to ki ringa
hango yanayin gidanku.
Yi na yi bari ya rabaki da kowa, wlh dk
wulakancin mutum dk izgilancinsa, matukar
zai ce ka yi ko ka bari kuma ka aikata
hakan, to lallai sai dai Wani abun,amma ka
wuce wulakancinsa. Da fatan kin ji abinda
na fada miki? " Na daga kaina Ina fadin, "
lnsha Allah inna zan kiyaye ". Tayi
murmushi, " Allah ya yi miki albarka, je ki
sha ruwa ki zo ki kwanta kada gobe ki
makara. Na ji shi mal. barau yace karfe 7
ake son ganinku a fada. ". Na mike Ina
fadin, " ko 6 ne inna Insha Allahu akan lkc
zamu je".Ta yi 'yar dariya, " ja'ira na sanki
da sammako, amma ai dole ki zo ki kwanta
din.
WASHEGARI A GIDANSARAUTA
Muka bi layi ana bamu kayan
sawa, wdnd zamu ringa amfani da su a cikin
gidan a matsayin " uniform". Yadi ne mai
Dan Karen kyau, Ga taushi ruwan sararin
samaniya (sky blue) dinkin riga da siket mai
kyau iri daya kuma kowacce za a bata dai-
dai ita, kowa kala bibiyu ya samu har aka yi
saura, don mu 26 ne sabbin dauka amma
duka babu wdd ta hour a shkr 22. Mafi
akasari sauran iyayensu a nan suke aiki
gidan sarauta, sai mu uku ne kawai wdnd
muka shigo ta hanyar ALFARMA! Abin
mamaki har 'yan kunne da sarkar wuya da
ta kafa tare da awarwaronsu aka rarraba
mana, irin kalar kayan, amman na duwatsu
mai haske. Musamman Wani fankacecen
daki aka bamu domin shiga, wai mu sanya
kayan da aka bamu yanzu. Duk wnn bidirin a
Wani bangare muke
cikin gidan ba mu isa inda ake son mu isan
ba hr ynz. "Allahumma arzukuna" kawai
nake nanatawa lkcn da nake zura kayan a
jikina, dk na rude sai kyarma nake yi.
Mutum kusan 6 suka hada baki wajen
fadamin cewa, NA YI KYAU!! Ni kaina nasan
kayan dole su yi min kyau, sbd klr ita ce
wdd na Fi so ckn kaloli, ba don komai ba
sai don kyan da kalar ke yiwa fatar jikina dk
lkc da ta rabu da ni. Muka biyo layi, dogarai
sun saka mu a tsakiya wasu gaba, wasu
gefenmu, wasu kuma a bayanmu. Inda dk
muka wuce bayi ne ke kara-kaina mana da
mata, haka na dinga raba ido Ina kallon
aljannar duniya a wnn masarauta, wuce
wnn tsuntsu, ruwa, filawowi babu abinda ba
mu gani ba har Allah ya Kai mu Wani
katafaren muhalli. A nan ne naga abin mamaki,
mata ce
kyakkyawa kishingide bisa Wani hadadden
gado, bayi kusan 12 gewaye da ita, wasu na
firfita, wasu matsar kafa, wasu na ba ta lbr
mai dadi don 'NISHADI' banda wdnd ke
bakin kofa da tsakar dakin suna kara- kaina.
Aka gaba tar da mu cikin wani irin yanayi
na girmamawa dk Ina lura da ydd suke yi.
Ta kalle mu ckn Dan murmushi kadan, ta
ce. "karasa da su wurin GIMBIYAR " Nan da
nan al'amarin ya daina bani mamaki da
fargaba gami da tsoro. Wani bangare muka
nufa, sashen da ya firgitani fiye da ckn inda
muka shiga, naji tmkr ba a duniya nake ba.
Can ma wasu bayin ne bila adadin suna
bauta. Mun fi mintuna 20 a tsaye ba tare
da wani ya kula da mu ba, dogarawan na
tsaye su ma kmr gani suka ba ni tausayi
(neman halak da wuya).
Zuwa can muka hng ' yanmata biyu da ' yan
kwanduna a hnn cake da filawoyi masu
kyau ga kamshi suna zubdawa a Kasa.
Mamakina ya karu ganin wasu nayin shara,
wasu na ba tawa. Ai ban karasa mamakin
ba na hng hadaddiyar budurwa ta biyo
sawun filawoyin ta sha kaya irin na alfarma,
Ga wata hadaddiyar alkyabba tana faman
jan Kasa, kanta cikin hular alkyabbar wdd
bazar kwaliyar ta boye rabin fuskarta,
amma kana iya hango kyallin zinaren da ke
falauniya a wuyanta da kunnenta. Har ta
zauna saman wata rantsattsiyar kujera ba a
bar zubda filawar nan ba. "GIMBIYA! !" Na
maimaita sunanan ta a ckn raina, Ina kara
yi mata kallo. kusan mintuna 15 da zamanta
amman
ko kallon inda muke ba ta yi ba. Tuni
kuguna ya soma rikewa sbd ni kam Allah ya
sani ba ni da jimirin tsayuwa. kafin na Kai
ga sarewa Allah ya taimakeni ta dago Kai a
hnkl kmr mai fama da ciwon sankarau, ta
wurgawa dogarawan nan wani mugun kallo,
nan da nan naga suna durkusawa suna
godiya tare da ficewa da sauri. Ta kalle mu,
tare da fadin. "ku zauna". Nan da nan muka
ciki umarni. " kafin na raba muku aiki zan
barku anan ku taimakawa sauran domin ku
ga ydd ake ya cikin kwana uku, daga safe
zuwa kr2 6 na marece. Jidda! " Ta kwada kira a
hnkl. Da gudu
ta karaso dattijuwa ta yi kusan kanwa ta 4
da ita, ko kallonta ba ta yi ba, ta ce. "A
kaisu ciki suna bukatar horo na kwana 3
kafin a raba musu aiki". Ta rusuna tare da
fadin. "An gama Gimbiya. Ku taso ku biyo
ni". Da sauri muka bita riii. .. ****"Inna
mutane na wahala a duniyar nan, kuma
mutane na jin dadi. Na ga mulki ni
HUMAIRA inna, a zage ka, a ci maka
mutunci snn kayi gdy, Kai SARAUTA wata
aba ce! Wlh inna kwana 2 nan ba ki ji ydd
jikina ke yi min ciwo ba."
Tayi murmushi tace dama
ai sai a hankali zaki saba kuma ai gobe ne kawai
ya rage da an raba muku aikin bashi ke nan ba
tunda kince akwai na safe akwai kuma na rana
dana dare kinga idan na safe Allah yaci da ke
karfe 7 kina can 2 kin dawo gida idan na rana ne
kuma 2 kina can 6 kin dawo idan kuwa na dare
ne 7 idan kika tafi sai safe bashi ke nan ba? Ke
dai ki sanya tsoran Allah a duk inda kike ki
kuma tuna yana ganinki a kowanne hali kika sami
kanki aikin nan mi wahala ne mutuka domin shi
ba wani share share ko goge goge ke gajiyar da
bayi agidan sarauta ba aa cin fuska da izgilanci
ke ba kowa wahala don haka sai an daure mai
nema yana tare da samu ki tuna idan baki daure
kika hakura ba ina zamu samu abincin da zamu
ci?ruwan sha har gagararmu yake yi a gidan nan
sai mu roko a makota ga karatun 'yan uwanki
tundda ke baki samu halin yiba sannan uwa uba
aurenki idan ya tasi wazai bamu?daga dangina
har na mahaifinki kin dai san yadda ake saboda
haka kiyi hakuri wata rana sai lbari"
Baku Murmushi kawai nayi domin a ganina
kamar
nafi inna sanin wadannan abubuwan kamar
kullum muka isa gidan cikin lokaci ni da Amira
wacce muke tafiya tare kwana 2 sakamakon
gidansu na bayan namu babu nisa kuma nice ke
biya mata safiya idan muka dawo zata rako ni
har kofar gida kafin ta koma nasu muna cikin
wankin gimbiya misalin karfe 12 na rana ina ta
alajabin wai har da wandunanta da rigunan nono
shin ita bata jin kunya mata bada wadannan
wurin wanki nawan haukan nake ganin kamar
wani sirrinta ne wanda ya kamata ace ita ke kula
da abinta kai wani abin sai gidan sarauta
HUMAIRA nayi saurin waigawa na'am bar musu
wankin kizo gimbiya na son ganinku ina kyarma
na dauraye hannaye na cikin gudu gudu sauri
sauri na karasa saboda na lura latti na saurin
hasala gimbiya duk abinda ta umarta lallai tana
son ayi mata shi da sauri acikin gaggawa
,Na iske su Amira a layi kamar ranar farko ni
mana bi sahu ta yatsina fuska tana kallonmu
daya bayan daya kamar mai kallon tsohon ciwo a
jikin kazamin mutum ku kasu gida 3 ta fada a
wahale ciki 'yan mintuna da basu wuce 2 ba
muka rabu kamar hanya abin haushi Amira bata
kusa dani don haka ya kasance bata cikin namu
gungun ma'ana nasu daban ta nuna su Amira da
baki daga yau zaku shiga cikin 'yan aikin rana
gabana ya fadi nan da nan na hau addu'ar zuci
kada Allah ya hadani da aikin dare saboda inna
bana tunanin zan iya barinta ta ringa kwana ita
kadai sai su sumayya saboda cikin dare asmarta
na iya tashi ta juyo garemu cikina ya bada wani
kugi kulululu kune masu aikin safe wadannan
kuma su shiga cikin masu kwana.
A hankali na furta alhamdulillah saboda haka
ku nadare kuna iya tafiya sai shida kwazo tare da
yan kwana na safe kuma kuyi sauri ku karasa na
ku 'yan rana su kar6a xa'a dinga biyan kowacce
dubu ashirin awata tana gama fadan haka ta kalli
masu bata abinci akawo mun kalaci na anan
mukai ta tsalle nida amira,saboda kwanan aikin
ne daman muke gudu,ga kuma makudan kudin
da
muka ji ta ambata fan ni ko rabunsusu wllhy
bansa rai ba.ina ta faman sauri babu ko waiwaye
shiga wancan lungun kurda wancan hanyar
saboda muna da dan nisa da gidan sarkin ban
ta6a kawo wa raina abin hawa ba saboda rashin
kudin biya.da zafina na isa gida ina dokin yiwa
inna albishir,tunda ga tsakar gida na fara jiwo
nishinta da kakari alamar ciwanta ya tashi na
wancakalar da takalman na karasa a guje tare da
tallabo ta a rude nake fadin ina kika ajiye
inhelar?
Sai neman san karewa take ta faman yi na ga
wawtata dana tsaya tambayarta,alhalin nadade
da sanin cewa ta kare. ,Haba a guje na fice gidan
kamar
mahaukaciya,nayi hayin kwalta kyamis din
dayyabu ,sai zufa nakeyi na fada shagon ina ta
haki, nace."Dayyabu ka dubi girman Allah kaba ni
bashin inhela,wallahi na sami aiki gidan sarki da
an biyamu zan kawo maka kudinka, bazan sa6a
ba insha Allah" kin tabbbatar?yafada yana
gargadina da hannu.na durkusa, wallahi dayyabu
zan kawo kaji na zantse"yadda ya miko min
maganin nace na gode"sai na kwasa a guje. Da
zuwa na isketa ta kai kasa warwas na shiga
shaka mata ina dan fesawa cikin mintuna 3 zuwa
4 komai ya tsaya.nayi ajiyar zuciya, Allah mai
yadda yaso yanzu da aikin rana nake fa? Nadaga
hannu sama nace, Allah na gode maka,Ubangiji
ka kara rufa mana asiri".
A hankali naji tace Ameen na kalleta nace
sannu inna"tace yauwa Ahankali,ya aka yi kika
dawo da wuri haka?na labarta mata yadda aka
tsara sai na ga tana murmushi, ni kuma na mike
zuwa tsakar gida na ga wacce dabara zan yi
mana a matsayin abincin rana.
****
Ina mamakin
mutane,gabanka faram faram,amma bayan
idonka
arinka zaginka ana gulmarka.su yanzu idan
gimbiya tajisu yazasuyi ko basu tunanin cewa
tunda naji zan iya kwarmata mata?naci gaba da
sauraransu "kinsan duk abin nan wlh ganin ita ce
bababba kuma sarki duk yafi ji da ita,sannan
kowa gidan tarairayarta yake yi ana
lallashinta".kware kuwa saboda ko wani abu ake
son mai martaba yayi,idan ta kife ciki wlh ba yayi
sai da ra'ayinta". "mts! Ni ina ganin harda da
rashin 'ya'ya
dayawa ga sarkin,kinga fasu duka shiddane a
gidan ita kadai ce wurin uwargida su ta sallah
kowa na da biyu biyu,sai Amarya da ke da daya
namiji shi yasa duk suka tsane ta sai kace ba
Allah ne ya bata ba"ke kuwa sun tabbatar ta
haifo MAGAJI.duk suka kyalkyale dariya harda
tafawa."Wai ni ya maganar auren
gimbiya?"Uhum!shu'umin mijin ne yaki zuwa har
yau,kin san idan sarauta ta hadu da sarauta dole
a baza MULKI.Amma naji an ce ya kusa zuwa
nan gidan zai yi wata 2 sannan iyayen su zo
maganar sanya rana"wannan wace irin al'ada ce
haka? "Ke ma kin gani,gidan nan ai sun yi bin da
yafi haka kawai tsabar ISA ce".kinsan abinda yafi
bani mamaki tace A'a". ,Wallahi kullum idan
muna tare da gimbiya ita
ce mai nemansa a waya,bai ta6a bugo mata
ba".suka kara dariya tace,"YARIMA!!! Wlh yarima
na wahalar da gimbiya,ina tunanin sarautarsu
tafi
wannan zafi".ko? Kware kuwa,ki ga fa mulki irin
na gimbiya da giman kai,amma wlh cikin kunnena
naji tana kwantar da murya tana rokonsa kada ya
ajiye mata waya". To ko bai sonta? Cikin sauri ta
kai mata duka."Yi shiru ban ce ba,domin ba a
jimutuwar sarki a bakina ba".yaushe zai zo? "An
ce talatar nan".kin san da maimartaba da
babanshi wasu irin abokai ne na kud-da-kud,kara
tu ma tare suka yi a kasar waje". ,ke a Ina kika
ji?""ya za ki tambaye ni bayan
kakar innarmu a nan ta yi aiki?""Uhm lallai, tashi
ki tayani kwaso wnk guga zan yi na zannuwan
gado".Na biyu da kallo a kaikaice Ina kara luliya
hirarsu ckn kwakwalwata, kafin daga bisani na
wancakalar da shi. Na dage ckn bada himma Ina
aiki na baji ba gani kmr daga sama naga Gimbiya
da tawagarta sun zagaye ni. ' Yarbaba Wacce ke
hnn damanta ta ce. " Allah ya ja da ran Gimbiya,
shin ko wnn kike magana? " Kafin ta yi yunkurin
magana tuni ' yan ' yan cikina sun kada, nan da
nan gudawa ta kusa kubuce min ckn wando,
tunani na ko laifi na yi. Ta kalle ni sama da Kasa
kafin tace, " a zo da ita daki ". suka juya. '
Yarbaba ta daka mini tsawa. " Saki wnn aikin
maza ki zo Kiran Gimbiya ". kwalla suka cika min
idona, muna tafe Ina addu'ar Allah ya tserar da
ni. Da shigarmu ta sallami kowa suka fice aka
barni da ita.Ta kalle ni a yatsune, "Me ye
sunanki? " Na ce,"Humaira".Ta rausayar da Kai,
"Na yaba da hnkl lki, Nutsuwa da kuma
kawaicinki. Kina da kyakkyawar trby kwarai da
gaske, sbd hk na daukeki a matsayin Wacce Zata
dinga kula da yarima idan yazo da safe kawai,
ckn masu aikin rana ma zan sami guda domin ba
zai so 'yan aikin dare ba sai dai wadanda ba a
rasa ba. In son da safe da kin zo ki Kai masa
ruwa a tasa kmr ydd al'adar gidan nan take, zai
wanke kafarsa kafin ya sakko daga gado ma'ana
bayan sallar asuba. Ke ce Zaki dinga wnke masa
kewaye da gyaran dakinsa tare da bashi kalaci.,
sa sauran kulawa har zuwa karfe 2 rana, kafin ta
ranar ta karba".Dadi ya kume ni na rusuna ckn
girmamawa na ce."Godiya...


Read / Download SUBUL DA BAKA 1, 2 & 3

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album