Subscribe for N1000/month for downloading access and an ad-free site. Contact WhatsApp +2348140419490 if you can't pay / subscribe. SUBSCRIBE

24 yin

NAGA TAKAINA Complete Hausa Novel Document by NAGA TAKAINA


NAGA TAKAINA

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 106417



NAGA TAKAINA

Reading Time: 8 Hours

Added On: 20, Aug 2023

Author: Sadnaf ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : PURE MOMENT OF LIFE WRITERS

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 565.75 kb

File Type: txt

Views: 1526+

Download: 1918+

Last download: 9 hours ago

Description/Story: *NAGA TAKAINA*

*NA SADNAF*🌸🌸🌸🌸🌸


®️ *_PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*
_{We Don't just entertain nd educate we also touch the heat of readers P.M.L}💪🏻_


*Free Novel*


*Tun kafin nayi nisa a rubutu nake da burin rubuta wanan labari Allah bai nufa ba sai yanzu labarin Nan ya faru a gaske tun 19's wahalar rubuta shi nake gani Sabida yanda xan na had'a present da past Amma a yanzu Allah ya nufa zanyi insha Allah zai na zuwar muku sau uku a sati idan na samu sarari ma zaku iya samun pages fiye da haka labarin Nan ya bambanta da sauran novels Dina na baya za'a ga abubuwa da za'a ga Anya dagaske zai faru kuwa ya faru dagaske zaka iya aikata Abu da baka d'aukeshi a bakin komai ba sai bayan shekara da shekaru sai abun ya dawo maka Allah ya tsare mu da tsarewarsa ya tsaremu da imanninsa Ameen*


*Page 1*

*1992*

Da Sauri na shige d'akina na rufo k'ofa a lokacin da Umma ta hangoni ta biyoni a guje ko nauyin cikin dake jikina banji ba sabida tsabar tsoronta da nakeji.

Jingina nayi da k'ofar d'akin Ina sauke numfashi Umma kuwa sai tura k'ofar take Tana auna min zagi iyayena da kasa ta Dade da rufe musu Ido da take ta Kiran sunansu Tana zaga yasa naji wani irin hawaye na zubomin Sanin na riga da na kulle k'ofar yasa naja k'afana na nufi Kan gadona Sabida kaina danaji Yana neman fad'owa sabida tsananin ciwo rabona da abinci har na manta lemon kwalba da bredi su kawai suka zama abincina a matsayina na Mai tsohon ciki nida gidana ban Isa na fita ba sai uwar mijina ta nada min duka bredin ma da lemo sai na fakaici Bata palon nake fita na siya kamar yanda yanzu na faki idonta na fita Ina dawowa ta gani ta biyoni a guje sabida kawai na fita siyan abinda zan sawa cikina.



Dan cikina dake ta mutsu mutsu yasa na tuna da yunwar da nakeji na tashi na mik'e dak'yar na jawo ledar bredi da lemo Dana siyo na fara tusa bredin Ina hawaye Dan ko kad'an ba dadinsa nakeji ba ci kawai nake.

Abban Zahira daya fad'omin a Raina yasa naji na k'asa ma had'iyar bredin bansan lokacin da kuka ya k'wacemin ba na fara magana a fili cikin tsananin kuka

"Nasiru Mai nayi maka haka Dana cancanci haka daga wajen Kai da mahaifiyarka?laifine Dan na zab'eka a cikin dumbin masoyana na aureka ka raboni da dangina da kowa nawa ka kawoni wani garin kana wulakantani Mai nayi Dana cancanci haka daga wajenka"?

Kukan dayaci k'arfina yasa na kasa cigaba da maganar da nake a fili na koma na kwanta sabida rawar da jikina keyi na cigaba da kukan da ya zame min jiki ko da ba'a min komai ba fuskata Bata rabo da hawaye sosai nake k'ewan yarana Amma uwar mijina ta hanani ganinsu Mahaifinsu kansa sai dai na jiyo muryarsa rabon Dana saka shi a idona wata hud'u kenan da sunan muna gida daya.

Mahaifiyarsa ta zama tamkar itace matarsa Dan komai ita ke masa kwana ne kawai Bata yi a d'akinsa.


"Mommy Mommy"

Naji siririn muryar Zahira Tana tab'a k'ofata

Zumbur na mik'e nayi hanyar k'ofa har Ina cin tuntub'e rabon dana ga ita da Nadiya har na manta Dan k'arfi da yaji Umma ta hanani ganinsu a d'akinta suke kwana ko d'akinsa da ta ga sun nufo d'akina zata daka musu tsawa tasa kanwar Nasiru Safiyya ta d'aukesu ta maidasu daki ta kulle tun yaran Ina jin suna kukan hanasu da akayi su zo wajena har suka zo suka Saba

Idona ya rufe sosai da San ganin yarana hakane yasa ko kad'an ban tuna da wata Umma na palon ba Dan inajin tashin muryar ita da Safiyya da kanwar Safiyya Lami a palon suna Hira.

Da Sauri na bud'e k'ofar banyi wata wata ba na d'aga ta Sama na rungume ta a jikina inajin wani irin Sanyi a zuciyata Wai ace Kai da danka karfi da yaji a nemi rabaku itama zahiran lamo tayi a jikina Tana sauke ajiyar zuciya ko damuwa banyi da yanda naji cikina ya dunkulle ba sabida yanda na Dora Zahira a jikina wuwurga Ido na fara yi ko zan hango Nadiya Amma Banga alamarta ba da Sauri na sauke Zahira na ruk'o hannayenta nace Mata "Ina Nadiya"?

Cikin maganar Yara tace min "dazu Yaya ya rik'e hannunta suka fita Ni Kuma inasan ganinki Dana ga Umma Bata kallona shine na taho wajenki mommy Dan Allah zan kwana a dakinki Aunty Safiyya Tana yawan dukana ta mitsini na har da tsintsiyar kwakwa take Zane Ni"

Zahira ta karasa fada tana Kara fad'awa jikina


Rungumeta nayi kukan da nake d'annewa ya k'wacemin Wanda hakan ne ya jawo hankalin su Umma da kallo ya d'aukewa hankali kaina

Wani irin Ashar Umma ta lailayo tayo wajenmu har zaninta na neman fad'uwa

Kara rungume Zahira nayi a jikina ko kad'an banji tsoron yanda ta taho wajena gadan gadan ba Dan gani nake kamar Zahira na iya taremin dukan da zata kawo jikina Tana isowa ta fusge Zahira da k'arfi daga jikina ta wancakalar da ita daga Ni har Zahira ihu muka saka lokaci guda Dan Zahira ta Bugu Ina k'ok'arin mik'ewa Umma ta jawo hannuna ta murd'a Tana "Bana hanaki tab'a yaran Nan ba kin Raina Ni ko toh wlh Kika Kara tab'a yaran Nan sai na saka waya na zaneki babu ruwana da cikin jikinki shegiya Yar mayyu jikar mayyu gidan uban wa ma Kikaje dazu"?

Duk maganar da take sheshek'a kawai nake Ina kallon hannun Zahira daya kumbura sabida bugawar da tayi ko kadan banji zafin yanda take murd'amin hannu ba

Kamar numfashina zai d'auke na fara magana Ina "Umma idan Wani Abu nayi Miki Dan Allah Dan annabi kiyi hakuri ki yafemin Dan Allah ki daina azabtar Dani banida kowa sai Allah sai ku Dan Allah kiyi hakuri kibarni Naga yarana"


"Kinci ubanki Naeema ba dai kin dage sai kin zauna da Nasiru ba azaba yanzu na fara gana miki nace miki bana sanki bana kaunarki tunda Kika Haifi wanan faratun Yar Taki nace ki tafi Kika k'i sabida maita kafin ma tayi shekara Kika Kara k'unsar wani cikin ke gaki kin Samu gidan arzkiki Zaki baje ki cike Mana gidan da Yaya itama Nadiyar ko shekara biyu batayi ba Kika Kara d'aukar wani cikin Zakici ubanki Dani kike magana wlh azabar da zan gana Miki a gidanan sai kin roki mutuwa da kanki Nasiru kuwa sai dai ki hangoshi daga nesa ya Miki nisa wanan tsinanan cikin jikin naki Kuma ki haifeshi nagani"


Ta karasa Tana wancakalar da hannuna tare da juyawa ta fusgi hannun Zahira dake ta tsunduma ihu har lokacin tayi hanyar dakinsu da ita ta wurgata Kan katifa ta jawo k'ofar ta rufe.

Ni kuwa kukan ma kasawa nayi na koma na zuci

Ina kallonta ta dawo zauna ta cigaba da kallo ita da yaranta da duka suka girme min Dan banfi Sha takwas ba lokacin Dan inada shekara Sha hud'u Mukayi aure da Nasir shekara hud'u kenan da auren mu.


"Ke Naeema zo ki wuce kiyi wanke wanke zan Dora Mana girkin dare kafin Yaya ya dawo"


Safiyya tace Tana jefomin harara.

Ban tashi ba sai da Umma ta juyo ta Kara zabga min wani mugun harara na mik'e jikina na rawa cikin dafa bango na Isa kitchen din na fara tattara lodin kayan wanke wanke Wanda wasu Dan keta ba amfani akayi dasu ba aka jibgashi wajen wanke wanke Dan kawai a bani wahala.

A hankali na fara wanke wanken hawaye nata zubarmin har da majina ban damu duk na hanasu zubowar ba Dan gani nake zan samu sa'ida idan suka zubo zuciyata datamin nauyi zata ragemin nauyi

Guntattakin abincin da suka rage na hada naci Dan banida abinda xan sawa cikina anjima bredin Kuma na gaji da ci Yanzu wajen sati kenan bana iya ba haya sabida Basir daya sakoni gaba.

Bani na fito daga kitchen din ba sai da na musu jajjagen kayan Miya na Dora musu farar Shinkafa sanan Umma ta umarceni da na fito na koma d'akina Dan danta ya kusa dawowa Bata San yayi arba Dani zuciyarsa ta tashi.

Ahaka na koma d'akina inajin duk gabobin jikina na min ciwo sallah ma kasawa nayi sai kwanciya kawai da nayi Ina tunanin shekara biyu da.suka wuce da nake rayuwa da mijina Naseer dake balain Sona kamar ya goyani da irin soyayyar daya shayar Dani daga Kan haihuwar Nadiya zuwa Kan cikin jikina Naga ya fara sauyamin tunda
Domin cigaba da karantawa sai ku downloading.
Yadda ake downloading na littafin: ku tabbata kunyi register da shafinmu sanna kunyi login, idan bakuyi register a kasa zakuga maballai guda biyu daya an rubuta LOGIN dayan kuma an rubuta REGISTER sai ku taba su kuyi register, daga nan sai ku yi subscription koda na naira 1000 ne, domin sai kunyi subs dinann ne kadai zaku iya dauko littatafanmu.

Ya ya akeyin Subscription namu : Bayan kun yi Login ko register daga kasa zaku ga wani jan maballi (button) an rubuta SUBSCRIBE sai ku taba shi zai kaiku inda zaku zabi package wato tsarin subs na ku da mu. akwai na wata guda, watanni biyar da shekara guda. da zarar kun zaba zai kaiku inda zaku biya kudin, wanda daga nan sai ku cigaba da downloading kawai abunku

ABUN LURA : duk wani littafi da kuka gani a shafinnan kyauta ne, wannan tsari mun zo da shine don mu samu hanyar da zamu iya rike shafin muna managing na shi, izan ku kayi subs na mu tamkar DONATION ne ku ka yi mana, ku ka bamu kwarin guiwa don mu ciagaba da kawo muku sabbin littatafai, amma duk wanda ya ga bazai iya ba toh zai iya karanta littafin kyauta a cikin shafinnan namu batare da ya downloading ba, kawai ya yi kasa zai ga Koren maballi (button an rubuta) START READING sai ya taba zai kaishi inda zai karanta littafin.

Sannan duk wanda yaga kamn wannan process din zai bashi wahala kai tsaye zai iya min magana ta whatssApp +2348140419490, ya tura min kudin ni kuma zan dora mai subs din akan account na shi

NB: iya ta haka ne zaku iya karanta wannan littafi a shafinmu babu wata hanyar. DAN ALLAH KU DAINA MANA MAGANA AKAN MU TURA MUKU LITTAFI TA WHATSAPP, BAMA TURAWA HANYA GUDA MUKE TURA LITTATAFANMU SHINE WEBSITE NA MU https://taskarnovels.com.ng DUK MAI BUKATAR LITTAFINMU YA JE CAN YA KYAUTA NE, AMMA DOWNLOADING KUWA BA KYAUTA BANE SAI YAYI SUBSCRIPTION NA WEBSITE NAM
This is not the real Download Button


Read / Download NAGA TAKAINA

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

This is not the real Download Button
5 Comments On NAGA TAKAINA
avatar
huda

1 year ago

Reply

Chapter 21

avatar
ibrahim-7-2

1 year ago

Reply

Masha Allah

avatar
ibrahim-7-2

1 year ago

Reply

Masha Allah

avatar
ibrahim-7-2

1 year ago

Reply

Masha Allah

avatar
ibrahim-7-2

1 year ago

Reply

Masha Allah

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album