Subscribe for N1000/month for downloading access and an ad-free site. Contact WhatsApp +2348140419490 if you can't pay / subscribe. SUBSCRIBE

24 yin

MATAR DATTIJO Complete Hausa Novel Document by MATAR DATTIJO


MATAR DATTIJO

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 70386



MATAR DATTIJO

Reading Time: 5 Hours

Added On: 05, Sep 2024

Author: jeeddah Tijjani ,

Ebook Compiler : itz B Y ebrerheem

Author Group : Unknown group

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 365.46 kb

File Type: txt

Views: 627+

Download: 1121+

Last download: 12 hours ago

Description/Story: COMPLETED BY (itz B Y ebrerheem)

[9/26, 6:08 PM] Itz B Y ebrerheem: 💋💋💋💋💋
*MATAR DATTIJO*
💋💋💋💋💋

*©jeeddah Tijjani*
*Adam*
*(Jeeddahtulkhair)*

1

fitowa nayi daga daki ina shure-shuren kafa, "ni Allah baxan je ba innah" da kayana innata ta biyo ni tana rarrashina haba Niimatullah me yasa Kullum idan xaki makaranta sai an yi tsallen tsiya da ke, karbi kayan ki saka, kinga idan kika makara aka xane ki kada ki fara dawowa kiyi min korafi ko kin fada baxan kula ki ba, idanuna ne suka cika da hawaye, ni baxan je ba innata Kullum naje sai malam ya dake ni bansan me nayi masa ba ya tsane ni. ina maganar ina share guntun hawayen da na kalato shi da gan-gan, rarrashina ta shiga yi har sai da na saka kayan na tafi ina tafe a hanya ina mita, cin karo nayi da Babana da gudu na karasa wajensa ina sharar kwalla, cikin tashin hankali ya dube ni, me yasa min ke kuka Niimatullah? idanuna cike da hawaye na dube shi, innata ce tace sai naje makaranta ni kuma ban son xuwa, cikin kulawa tare da murmushi ya dafa kaina, kiyi hakuri yar lelen baba kije makaranta kin ji ko, ilimi shi ne gishirin xaman duniya, musamman ilimin addini, karbi wannan yasa hannu a aljihu ya miki min naira biyar, cike da shagwaba na tabe baki, ka barshi baba tausayinka nake ji, da dukkan alamu yaji dadin abinda na fada masa, dafa kaina yayi Allah yayi miki albarka yar lelen baba, Allah ya baki abinda kika tafi nema, amsa masa nayi da Ameen, na kwasa da gudu sai makaranta, cikin ikon Allah naci sa'a ba a fara dukan makara ba don haka cikin farin ciki na shiga Aji
Bayan an tashi na biyo ayarin kawayena muka taho muna tafe muna sha'anin mu irin na kuruciya, muna gab da shigowa ciki unguwa wata mota tayi parking a gaban mu, gaba daya muka ja da baya, saboda innata ta dade tana min gargadin idan naga mota na rika matsawa saboda masu satar yara, xuge glass din motar aka yi wani kyakkyawan dattijo ne ya leko da kansa, kallo daya xaka yi masa ka tabbatar da cewa kyakkyawa ne na ajin farko duk da ya fara manyanta hakan baxai hana ka fahimtar kyakkyawa bane, farin glass din da ke sanye a fuskarsa ne ya kara xayyana masa kyansa, sanye yake da farin voil wanda aka yi wa aiki da farin zare, kansa sanye yake da hula fara, babban mutum ne mai kamala duk inda ka kalle shi sau daya sai kayi marmarin sake kallonsa, saboda yadda Allah ya tsara masa halittar sa, cikin tattausar muryar sa ya kira mu, ku yaran nan ku xo, gaba daya muka fara ja da baya saboda mun tuna gargadin da iyayen mu suke mana, kwarjinin da yayi mana ne yasa muka kasa tafiya mu kyale shi, sake maimaita maganar da yayi a baya yayi, ku xo yara tambayar ku xan yi, daya daga cikin mu ce tayi karfin hali ta karasa inda yake cikin ladabi ta gaida shi, dagowa yayi tare da shafa kwantaccen farin gashin da ke kewaye a fuskarsa, kira min ragowar yan uwan naki xan tambaye ku gaba daya, da gudu ta karaso wajen mu, yace kuxo xai bamu sako ne, ba mu yi mata musu ba muka bita har wajen wannan mutum, murmushi yayi sannan ya fara yi mana magana, tsoro ku ke kada na gudu da ku ko, abinka da yara muka yi saurin amsa masa da eh. girgixa kai yayi to ku kwantar da hankalin ku ni ba irin wadanda ku ke zato bane, ke yarinya ya nuna ni da hannunsa ke nake son tambaya, hannu yasa ya dakko biron dake soke a jikin aljihun rigar sa sannan ya dakko takarda, tambayata ya fara yi ya sunanki gabana na dukan uku-uku na amsa masa da sunana Niimatullah, a wane unguwa kike, a nan bayan layi gidan mu yaje ba nisa daga nan, kafin na gama bashu amsa har hawaye ya cika idanuna, cikin damuwa ya dube ni, me yasa xa kiyi kuka Niimatullah, cikin kukan na bashi amsa, tsoro nake ji kada kaxo ka gudu da ni tsakar dare ni da innata, dariya na bashi sosai ki kwantar da hankalin ki ni ba haka nake ba, ku shige ku tafi gida kada a ga kun dade, wucewa muka yi kirjina na dukan uku-uku, ina shiga gida na fada jikin innata ina kuka, tambayata ta shiga yi me ya faru da ke yar lelen baba, cikin kuka nke bata labarin yadda muka yi da mutumin da muka hadu da shi, shiru innah tayi tana naxarin maganata, ki kwantar da hankalin ki Insha Allah alheri ne, tashu ki dauro alwalar magariba kinga lokacin sakkah ya gabato, tashi nayi na dauro alwala na dawo jikin innah na kwanta saboda fargaba ce fal a cikina.





*Jeeddahtulkhair😘*
[9/26, 6:08 PM] Itz B Y ebrerheem: 💋💋💋💋💋
*MATAR DATTIJO*
💋💋💋💋💋

*©jeeddah Tijjani*
*Adam*
*(Jeeddahtulkhair)*


*dedicated to Fatima sammani Alatu*

2

Sunana Ni'imatullah muhammad, iyayena yan asalin garin kano ne muna xaune ne a unguwar tarauni, ni kadai iyayena suka haifa, wannan dalilin yasa suke kaunata duk abinda nake so shi suke min matukar bai saba ka'idar shari'a ba, sai dai tafiya bata yi tsawo ba Allah yayi musu rasuwa sakamakon hadarin mota da ya ritsa da su,wannan dalilin yasa kulawata ta dawo hannun kakannina na wajen uba, suna ji da ni sosai saboda ni kadai ce jikar da suka mallaka kuma ni suke kallo a matsayin mahaifina, kasancewar babana shi kadai dan su a duniya. dangin mahaifiyata duk suna kauyen bichi idan an yi hutu nakan je musu xiyara.

ni yarinya ce kyakkyawa son kowa kin wanda ya rasa, Allah ya tsara min halitta ta dai-dai gwargwado idan ka ganni xaka iya cewa na fito ne daga salsalar buzaye ko larabawa. ni ba fara bace haka xalika baxa a saka ni a layin bakake ba, amma xa a iya kirana da (chocolate colour)idanuna manya ne kuma farare tas, hancina dogo ne wanda shi ne yake kara fito min da ainhin kyawuna, bakina kuwa dan karami ne, ga kuma dimple wanda yake kara bayyanar da asirtaccen kyauna, ni ba doguwa bace amma kuma baxa a saka ni a layin gajeru ba, xan iya kiran kaina da matsakaiciya, gashin kaina kamar auduga yake saboda santsi da laushi da ake da shi yasa bana yin kitso saboda ina yi yake warware wa, mutane da dama suna kirana da mai kyau, rayuwa mai dadi nake yi tare da kakannina sun hana ni kukan maraici babu abinda na nema na rasa a rayuwata.
Da gudu na fito daga bandaki ina kiran innah, a firgice ta fito daga dakinta tambayata ta shiga yi me ya same ki Niimatullah kuka nake ina nuna mata bandaki, kije ki gani innah na shiga uku, a raxane ta shiga bandakin ta fara lalube, ni ban ga komai ba Niimatullah, sake rushewa nayi da kuka ki duba pant dina ki gani innah, tana budewa taga ashe na fara jinin Al'ada ne, damuwa ce ta bayyana a fuskarta, bata so na fara da wuri ba saboda har yanzu ban gama mallakar hankalina ba, kwata-kwata shekaruna sha uku a duniya, gyara kayana ta shiga yi sannan ta jawo ni jikinta ta rungume ni, ni kuwa sai faman rusa ihu nake yi, lallabani ta shiga yi kiyi hakuri yar lelen baba haka Allah ya tsarawa kowace ya mace a rayuwarta, wannan ba wani abin damuwa bane ki kwantar da hankalin ki kin ji jikanyata, idona cike da hawaye na dubeta to yanxu yaushe xai tafi? shafa kaina tayi nan da sati daya ko kwana uku wata ma sai tayi kwana sha biyar bai tafi ba, xaro idona nayi kwana sha biyar fa kika ce innah, eh mana amma ya danganta da yanayin yadda Allah ya tsara miki, xai iya tafiya yau ma. bayan ta gama koya min yadda xan kula da kaina da jikina sannan ta yi min nasiha mai ratsa jiki, kinga yanxu kin xama cikakkiyar mace duk abinda yake kan tsohuwa yar shekara dari ya hau kanki don haka ki kula da ibada sannan ki daina guje-gujen da kike yi, kuma kada ki bar wani da namiji ya taba miki jiki ko da kuwa hannunki ne domin yana taba ki ciki xai iya shigar ki, saurin dagowa nayi na dubeta ciki fa kika ce innah, dama idan aka aurar da mace ba a ruwan randar gidan da aka kaita take sha ba? gyada kai innah tayi idan namiji ya taba hannunki ne kike daukan ciki don haka sai ki kula ki kiyaye. narai-narai nayi da ido
Domin cigaba da karantawa sai ku downloading.
Yadda ake downloading na littafin: ku tabbata kunyi register da shafinmu sanna kunyi login, idan bakuyi register a kasa zakuga maballai guda biyu daya an rubuta LOGIN dayan kuma an rubuta REGISTER sai ku taba su kuyi register, daga nan sai ku yi subscription koda na naira 1000 ne, domin sai kunyi subs dinann ne kadai zaku iya dauko littatafanmu.

Ya ya akeyin Subscription namu : Bayan kun yi Login ko register daga kasa zaku ga wani jan maballi (button) an rubuta SUBSCRIBE sai ku taba shi zai kaiku inda zaku zabi package wato tsarin subs na ku da mu. akwai na wata guda, watanni biyar da shekara guda. da zarar kun zaba zai kaiku inda zaku biya kudin, wanda daga nan sai ku cigaba da downloading kawai abunku

ABUN LURA : duk wani littafi da kuka gani a shafinnan kyauta ne, wannan tsari mun zo da shine don mu samu hanyar da zamu iya rike shafin muna managing na shi, izan ku kayi subs na mu tamkar DONATION ne ku ka yi mana, ku ka bamu kwarin guiwa don mu ciagaba da kawo muku sabbin littatafai, amma duk wanda ya ga bazai iya ba toh zai iya karanta littafin kyauta a cikin shafinnan namu batare da ya downloading ba, kawai ya yi kasa zai ga Koren maballi (button an rubuta) START READING sai ya taba zai kaishi inda zai karanta littafin.

Sannan duk wanda yaga kamn wannan process din zai bashi wahala kai tsaye zai iya min magana ta whatssApp +2348140419490, ya tura min kudin ni kuma zan dora mai subs din akan account na shi

NB: iya ta haka ne zaku iya karanta wannan littafi a shafinmu babu wata hanyar. DAN ALLAH KU DAINA MANA MAGANA AKAN MU TURA MUKU LITTAFI TA WHATSAPP, BAMA TURAWA HANYA GUDA MUKE TURA LITTATAFANMU SHINE WEBSITE NA MU https://taskarnovels.com.ng DUK MAI BUKATAR LITTAFINMU YA JE CAN YA KYAUTA NE, AMMA DOWNLOADING KUWA BA KYAUTA BANE SAI YAYI SUBSCRIPTION NA WEBSITE NAM
This is not the real Download Button


Read / Download MATAR DATTIJO

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

This is not the real Download Button
Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album