Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

COMPLETED BY (itz B Y ebrerheem)

[9/26, 6:08 PM] Itz B Y ebrerheem: 💋💋💋💋💋
*MATAR DATTIJO*
💋💋💋💋💋

*©jeeddah Tijjani*
*Adam*
*(Jeeddahtulkhair)*

1

fitowa nayi daga daki ina shure-shuren kafa, "ni Allah baxan je ba innah" da kayana innata ta biyo ni tana rarrashina haba Niimatullah me yasa Kullum idan xaki makaranta sai an yi tsallen tsiya da ke, karbi kayan ki saka, kinga idan kika makara aka xane ki kada ki fara dawowa kiyi min korafi ko kin fada baxan kula ki ba, idanuna ne suka cika da hawaye, ni baxan je ba innata Kullum naje sai malam ya dake ni bansan me nayi masa ba ya tsane ni. ina maganar ina share guntun hawayen da na kalato shi da gan-gan, rarrashina ta shiga yi har sai da na saka kayan na tafi ina tafe a hanya ina mita, cin karo nayi da Babana da gudu na karasa wajensa ina sharar kwalla, cikin tashin hankali ya dube ni, me yasa min ke kuka Niimatullah? idanuna cike da hawaye na dube shi, innata ce tace sai naje makaranta ni kuma ban son xuwa, cikin kulawa tare da murmushi ya dafa kaina, kiyi hakuri yar lelen baba kije makaranta kin ji ko, ilimi shi ne gishirin xaman duniya, musamman ilimin addini, karbi wannan yasa hannu a aljihu ya miki min naira biyar, cike da shagwaba na tabe baki, ka barshi baba tausayinka nake ji, da dukkan alamu yaji dadin abinda na fada masa, dafa kaina yayi Allah yayi miki albarka yar lelen baba, Allah ya baki abinda kika tafi nema, amsa masa nayi da Ameen, na kwasa da gudu sai makaranta, cikin ikon Allah naci sa'a ba a fara dukan makara ba don haka cikin farin ciki na shiga Aji
Bayan an tashi na biyo ayarin kawayena muka taho muna tafe muna sha'anin mu irin na kuruciya, muna gab da shigowa ciki unguwa wata mota tayi parking a gaban mu, gaba daya muka ja da baya, saboda innata ta dade tana min gargadin idan naga mota na rika matsawa saboda masu satar yara, xuge glass din motar aka yi wani kyakkyawan dattijo ne ya leko da kansa, kallo daya xaka yi masa ka tabbatar da cewa kyakkyawa ne na ajin farko duk da ya fara manyanta hakan baxai hana ka fahimtar kyakkyawa bane, farin glass din da ke sanye a fuskarsa ne ya kara xayyana masa kyansa, sanye yake da farin voil wanda aka yi wa aiki da farin zare, kansa sanye yake da hula fara, babban mutum ne mai kamala duk inda ka kalle shi sau daya sai kayi marmarin sake kallonsa, saboda yadda Allah ya tsara masa halittar sa, cikin tattausar muryar sa ya kira mu, ku yaran nan ku xo, gaba daya muka fara ja da baya saboda mun tuna gargadin da iyayen mu suke mana, kwarjinin da yayi mana ne yasa muka kasa tafiya mu kyale shi, sake maimaita maganar da yayi a baya yayi, ku xo yara tambayar ku xan yi, daya daga cikin mu ce tayi karfin hali ta karasa inda yake cikin ladabi ta gaida shi, dagowa yayi tare da shafa kwantaccen farin gashin da ke kewaye a fuskarsa, kira min ragowar yan uwan naki xan tambaye ku gaba daya, da gudu ta karaso wajen mu, yace kuxo xai bamu sako ne, ba mu yi mata musu ba muka bita har wajen wannan mutum, murmushi yayi sannan ya fara yi mana magana, tsoro ku ke kada na gudu da ku ko, abinka da yara muka yi saurin amsa masa da eh. girgixa kai yayi to ku kwantar da hankalin ku ni ba irin wadanda ku ke zato bane, ke yarinya ya nuna ni da hannunsa ke nake son tambaya, hannu yasa ya dakko biron dake soke a jikin aljihun rigar sa sannan ya dakko takarda, tambayata ya fara yi ya sunanki gabana na dukan uku-uku na amsa masa da sunana Niimatullah, a wane unguwa kike, a nan bayan layi gidan mu yaje ba nisa daga nan, kafin na gama bashu amsa har hawaye ya cika idanuna, cikin damuwa ya dube ni, me yasa xa kiyi kuka Niimatullah, cikin kukan na bashi amsa, tsoro nake ji kada kaxo ka gudu da ni tsakar dare ni da innata, dariya na bashi sosai ki kwantar da hankalin ki ni ba haka nake ba, ku shige ku tafi gida kada a ga kun dade, wucewa muka yi kirjina na dukan uku-uku, ina shiga gida na fada jikin innata ina kuka, tambayata ta shiga yi me ya faru da ke yar lelen baba, cikin kuka nke bata labarin yadda muka yi da mutumin da muka hadu da shi, shiru innah tayi tana naxarin maganata, ki kwantar da hankalin ki Insha Allah alheri ne, tashu ki dauro alwalar magariba kinga lokacin sakkah ya gabato, tashi nayi na dauro alwala na dawo jikin innah na kwanta saboda fargaba ce fal a cikina.





*Jeeddahtulkhair😘*
[9/26, 6:08 PM] Itz B Y ebrerheem: 💋💋💋💋💋
*MATAR DATTIJO*
💋💋💋💋💋

*©jeeddah Tijjani*
*Adam*
*(Jeeddahtulkhair)*


*dedicated to Fatima sammani Alatu*

2

Sunana Ni'imatullah muhammad, iyayena yan asalin garin kano ne muna xaune ne a unguwar tarauni, ni kadai iyayena suka haifa, wannan dalilin yasa suke kaunata duk abinda nake so shi suke min matukar bai saba ka'idar shari'a ba, sai dai tafiya bata yi tsawo ba Allah yayi musu rasuwa sakamakon hadarin mota da ya ritsa da su,wannan dalilin yasa kulawata ta dawo hannun kakannina na wajen uba, suna ji da ni sosai saboda ni kadai ce jikar da suka mallaka kuma ni suke kallo a matsayin mahaifina, kasancewar babana shi kadai dan su a duniya. dangin mahaifiyata duk suna kauyen bichi idan an yi hutu nakan je musu xiyara.

ni yarinya ce kyakkyawa son kowa kin wanda ya rasa, Allah ya tsara min halitta ta dai-dai gwargwado idan ka ganni xaka iya cewa na fito ne daga salsalar buzaye ko larabawa. ni ba fara bace haka xalika baxa a saka ni a layin bakake ba, amma xa a iya kirana da (chocolate colour)idanuna manya ne kuma farare tas, hancina dogo ne wanda shi ne yake kara fito min da ainhin kyawuna, bakina kuwa dan karami ne, ga kuma dimple wanda yake kara bayyanar da asirtaccen kyauna, ni ba doguwa bace amma kuma baxa a saka ni a layin gajeru ba, xan iya kiran kaina da matsakaiciya, gashin kaina kamar auduga yake saboda santsi da laushi da ake da shi yasa bana yin kitso saboda ina yi yake warware wa, mutane da dama suna kirana da mai kyau, rayuwa mai dadi nake yi tare da kakannina sun hana ni kukan maraici babu abinda na nema na rasa a rayuwata.
Da gudu na fito daga bandaki ina kiran innah, a firgice ta fito daga dakinta tambayata ta shiga yi me ya same ki Niimatullah kuka nake ina nuna mata bandaki, kije ki gani innah na shiga uku, a raxane ta shiga bandakin ta fara lalube, ni ban ga komai ba Niimatullah, sake rushewa nayi da kuka ki duba pant dina ki gani innah, tana budewa taga ashe na fara jinin Al'ada ne, damuwa ce ta bayyana a fuskarta, bata so na fara da wuri ba saboda har yanzu ban gama mallakar hankalina ba, kwata-kwata shekaruna sha uku a duniya, gyara kayana ta shiga yi sannan ta jawo ni jikinta ta rungume ni, ni kuwa sai faman rusa ihu nake yi, lallabani ta shiga yi kiyi hakuri yar lelen baba haka Allah ya tsarawa kowace ya mace a rayuwarta, wannan ba wani abin damuwa bane ki kwantar da hankalin ki kin ji jikanyata, idona cike da hawaye na dubeta to yanxu yaushe xai tafi? shafa kaina tayi nan da sati daya ko kwana uku wata ma sai tayi kwana sha biyar bai tafi ba, xaro idona nayi kwana sha biyar fa kika ce innah, eh mana amma ya danganta da yanayin yadda Allah ya tsara miki, xai iya tafiya yau ma. bayan ta gama koya min yadda xan kula da kaina da jikina sannan ta yi min nasiha mai ratsa jiki, kinga yanxu kin xama cikakkiyar mace duk abinda yake kan tsohuwa yar shekara dari ya hau kanki don haka ki kula da ibada sannan ki daina guje-gujen da kike yi, kuma kada ki bar wani da namiji ya taba miki jiki ko da kuwa hannunki ne domin yana taba ki ciki xai iya shigar ki, saurin dagowa nayi na dubeta ciki fa kika ce innah, dama idan aka aurar da mace ba a ruwan randar gidan da aka kaita take sha ba? gyada kai innah tayi idan namiji ya taba hannunki ne kike daukan ciki don haka sai ki kula ki kiyaye. narai-narai nayi da ido xan yi kuka, ni dai ki bani magani nasha na daina yi innata, na karasa maganar tare da kwantar da kainaa jikinta, shafa bayana tayi kiyi hakuri Niimatullah xan yi miki addua xuwa gobe xai tafi, da murnata na dago na dubeta, da gaske xai tafi innah? xai tafi ke dai ki kwantar da hankalinki, da farin ciki na kwana a raina tun daga ranar kuma na kulke a rajna duk namijin da yayi min magana baxan sake kula shi ba.



*Jeeddahtulkhair😘*
[9/27, 3:04 PM] Itz B Y ebrerheem: 💋💋💋💋💋
*MATAR DATTIJO*
💋💋💋💋💋

*©jeeddah Tijjani*
*Adam*
*Jeeddahtulkhair)*


*dedicated to Niimatullah muhammad rafin dadi (miss rafin dadi)*


3

washe gari kuwa ko makaranta ban je ba, ina gida kan cinyar innah tana jinyata,da sallama Baba ya shigo dakin da muke hannun shi rike da ledar kayan miya mikawa innah yayi sannan ya samu guri ya xauna, sannu da xuwa inna tayi masa, har naxo yi masa magana na tuna da hudubar da innah tayi min a kan daina kula maza, juyo da kallonsa yayi gare ni, yar lelen baba ya na ganki kwance ko jikin ne ba dadi? shiru nayi masa sai da ya maimaita maganar kusan sau uku har sai da innah tayi min magana, baki ji abinda ake ce miki bane Niimatullah?.

turo baki nayi ina shusshura kafa, ba kince kada na kara yiwa namiji magana ba. kama baki innah tayi tana salati, to ai wannan kakanki ne baya cikin wadanda xaki 'ki yiwa magana kin ji ko? gyada kai nayi tare da gyara kwanciyata.

cike da mamaki baba ya dubeta, me ke faruwa ne naji kina mata wannan dogon bayanin? fuskar innah cike da damuwa ta bashi amsa, malam Niimatullahi ta fad'i, a raxane ya kalleta ta fad'i fa kika ce yaushe abin yaxo? jiya yaxo malam,ba karamar damuwa baba ya shiga ba da yaji abinda ya same ni, cikin damuwa yake magana, tunda ta fadi da wuri haka mu ma da wuri xamu aurar da ita tunda tana da saurin girma, ina ganin hankalin mu xai fi kwanciya.

tashi nayi daga kwanciyar da nake, aure fa kace baba tabdi ni dai wlh ba yanxu ba, kallona baba yayi yana min magana, to sannu babarmu tsayawa xa mu yi muna kallon ki ba aure, tunda kin girma me muke jira da ke? mikewa nayi ina duba kaina, ka ganni fa yar karama baba, Allah ban isa aure ba, haka muka rika muhawara da baba yana cewa na girma ni kuwa nace sam ba haka bane, tun daga lokacin nake ta tunanin ya xan yi idan aka aurar da ni yanxu ni da ko sanwa ban iya dorawa ba.

wata rana innah bata nan bayan na fito daga wanka na shiga dakinta, sanye nake da xani wanda nayi daurin kirji da shi, duba kaina na fara yi a mudubi naga yadda na fara xama cikakkiyar mace, kirjina har ya fara cika da dukiyar fulani, shape din jikina ma haka, komai yaji masha Allah ga kyawuna ya kara fita da yake makerin budurci ya fara tsara ni, murmushi nayi ina godewa Allah da kyawun surar da yayi min, lallai ban ga laifin su baba ba da suka ce xasu aurar da ni.

Bayan innah ta dawo daga unguwa na kwanta kan cinyarta ina mata shagwaba, nace a lallai sai tayi min tatsuniya ko ta bani labari mai dadi, ture ni nayi tana min fada, na gaji da wannan sa aikin naki Niimatullah ke kenan Kullum a cikin danne min tsohuwar cinyata, kallonta nayi ina murmushi yanxu idan ban danne ki ba wa xan danne innata? ke kadai fa kika rage min a rayuwata, tausayi na bata ta jawo ni ta kwantar da ni bisa cinyarta, haka ne Niimatullah kin fadi gaskiya.

Hirar mu muka cigaba da yi cikin nishadi, baba ne ya shigo hannunsa rike da carbi da butar alwala, kiran sunana yayi, Niimatullah tashi ki sanyo hijabin ki kin yi bako yana nan a soro yana jiran ki, da sauri na tashi xaune ina xare idanu, wane bako nayi baba, daure fuska yayi babu alamar wasa a tare da shi tashi ki kintsa idan kin je kya ga ko wane ne, jikina a salube na mike na shiga daki hijabi na sako sannan na sharbana silifas din innah xuciyata na tafasa na karasa soron.

dattijon da muka hadu jiya na gani, jingine yake da 'kyauran soron mu, yau ma sanye yake da fararen kaya wannan ya nuna min cewa shi ma'abocin son fararen kaya ne, saurin ja da baya nayi saboda ban taba xaton xai biyo ni gida ba, tambayarsa nayi, dama kaine bakon nawa me ka biyo ni gida kayi min? ina cikin maganar na tuna da alkawarin da na daukarwa kaina na daina yiwa maxa magana, a cikin xuciyata nace Allah na gode maka da ka tunasar da ni, ashe ban sani ba har maganar ta fito sarari.

tsare ni yayi da ido yana tambayata, me Allah ya tunasar da ke Niimatullah? sunkuyar da kaina nayi gaba daya na kasa dagowa saboda kwarjinin da yayi min, magana yake ta yi na kasa bashi amsa, har sai da ya gaji ya tambaye ni dalilin 'kin maganar da nake yi, idanuna a kasa na bashi amsa da innata ce ta hana ni magana da maxa, murmushi yayi tare da kad'a mukullin da ke hannunsa, lallai innar ki ta cika mai hikima, amma idan ta hana ki magana da maxa ai baxa ta hana ki magana da mijinki ba, a fusace na juyo na kalle shi mijina fa kace? Allah ya sauwake na aureka, dariya na bashi sosai. menene don kin aure ni Niimatullah shikenan kinga sai a rika kiran ki da *MATAR DATTIJO* tabe baki nayi ni ai matar yaro ce, kuma yaron ma sabon jini xan aura, shafa fuskar shi yayi tare da kallona.

A fuska nake dattijo amma a jiki nafi yaro kuruciya, baxa ki gane hakan ba har sai kin aure ni mun hadu a sunnah na fara baki soyayyar da baxa ki sameta a wajen yaro ba. shiru nayi na rabu da shi saboda bana son na rika yin doguwar magana da shi, naga alamar abinda yake so kenan, haka ya yi ta surutansa ya gama ba amsa, da ya tashi tafiya ya miko min ledar da yayi min shopping, da sauri na wuce gida na kyale shi da kayansa, sai yaro ya bawa ya shigo da shi gida, ina shiga na fada cinyar innah ina hawaye, tallafo fuskata tayi.

wa ya taba min ke niimatullah, share hawaye na shiga yi, innata wai wannan bakon da nayi sona yake yi ni gaskiya ya min tsufa Allah, rarrashina ta shiga yi, kada ki tada hankalin ki Niimatullah baxa mu aurar da ke ga wanda bakya so ba, sai kin xaba kin darje yar lelen mu.

kalaman innah su suka kwantar min da hankali nayi bacci mai dadi.

Alhaji Sadeeq Yusuf shahararren dan boko ne kuma tsohon minster na man fetur, ya rike mukamai da yawa wannan dalilin yasa ya tara dukiya mai yawa, gidansa a unguwar bompai yake titin durbin katsina, yayansa biyu ne duk maxa munir sai Hanif munir na da shekara talatin da biyar shi kuma Hanif na da shekara ashirin da biyar, tun daga kansu bai sake haihuwa ba, yana matukar son ganin kananan yara a gidan sa amma matarsa hajiya maryam ta dakatar da haihuwa kasancewar yar boko duk nacin da yayai akan kada ta dakatar da haihuwa taje tayi gaban kanta.

A hanyar xuwa islamiyya yaga Niimatullah, tunda ya ganta yaji ta kwanta masa a ransa kuma yayi niyyar mallakarta ko don ya gyara mata rayuwa.




*Jeeddahtulkhair😘*
[9/27, 3:04 PM] Itz B Y ebrerheem: 💋💋💋💋💋
*MATAR DATTIJO*
💋💋💋💋💋

*©jeeddah Tijjani*
*Adam*
*(Jeeddahtulkhair)*

4

Ina cikin bacci naji wayar innata tayi ringing, a cikin baccin na rarrafa na dauka, bakuwar number na gani, da farko har naki dauka sai aka dame ni da kira na saka wayar a kunnena, sallama nayi cikin dasasshiyar murya, wata iska naji an hura min cikin kunnena wanda har sai da sautin ya tsirga min cikin jikina, cikin sassanyar murya aka amsa min sallamata tare da cewa na tashe ki kina baccin ki ko??

shiru nayi ba tare da na bada amsa ba, cikin raina nace lallai dattijon nan ya fiye nacin tsiya.
shirun da yaji nayi ne yasa ya cigaba da magana.

kiyi hakuri gimbiyar mata, nasan dama dole xan dame ki saboda tunda na ganki kika kwance min tunanina, yanxu haka na kasa bacci saboda tunanin ki, nasan baxan iya lafiyayyen bacci ba idan ban ji muryar ki ba.
cikin tsiwa nake masa magana, to kaji muryar tawa sai me? murmushi yayi wanda har sai da naji sautinsa a kunne na, Niimatullah sarkin tsiwa, kiyi hakuri ki rage wannan tsiwar taki, idan ba haka ba kuma na kamaki a dakin mu xa kiyi bayani ne. hararsa na rika yi kamar yana kallona Allah ya sauwake naje dakin dattijo, na fada maka ni matar yaro ce ehe.

dariya yayi wannan tsiwar taki ba karamin burge ni take yi ba Niimatullah, haushi ya bani na kashe wayar, shi kuwa sai juyi yake bisa gado duk ta tayar masa da wani sabon kwadayi, shaawarta da shaukinta sun mamaye shi a ranar da kyar ya iya bacci saboda tunanin Niimatullah har sai da yayi ciwon mara, kasancewar matarsa bata damu da kulawa da hakkinsa ba, burinta a Kullum bai wuce ta karbi kudi a hannunsa ba, wannan ne kawai amfaninsa a wajenta amma duk wani hakki nasa tasa kafa ta shure.

washe gari da safe nake fadawa innata yadda muka yi da shi, murmushi tayi tare da ce min ke yanxu wane hukunci kika yanke a kan son shi, bata fuska nayi ni Allah bana son shi innah, baki ga gemunsa ba duk furfura, dariya na bata har sai da ta kusa tuntsirewa, menene da farin gemun nasa Niimatullah, indai xa a samu xaman lafiya ai babu wani abu, ke dai kiyi addu'a Allah ya zaba abinda ya fi Alkhairi.

tashi nayi na fara shirin tafiya makaranta, naxo daukan jakata kenan wayar innah tayi ringing a hankali na mika hannu na dauka, number da ta kira ni jiya na gani, wurgi nayi da ita gefe guda, innata ce ta lura da abinda nayi cikin tausasa lafazi take min magana.

ya kika jefar min da waya Niimatullah? turo baki nayi wannan mayen ne ya kira ni, ni dai tun wuri kiyi masa magana ya daina kula ni, ba aure xan yi yanxu ba sai na kara girma. kallona innah tayi banda wannan girman da kika yi wane girma kuma xaki kara yi Niimatullah? tabe baki nayi ni dai ban girma ba innata abinda ko girki ban iya ba, ajiyar xuciya innah tayi, har yanxu yarinta na damun ki ni'ima Allah ya kara miki nutsuwa.

ba Ameen ba innah indai don a aura min wannan dattijon ne baxan taba hankali ba, naira goma ta bani sannan na dauki flask din abincina, a damuwa na kasance a makaranta domin kwakwalwata ta daina karbar komai saboda maganganun da aka bijiro min da su.

yau ma da yamma yaxo gidan mu har tsakar gida ya shigo don gaisawa da innah, tarar da ni yayi ina ta sharawa jikina ruwa duk na jika kayana, kallona ya shiga yi ya kasa dauke idonsa daga kaina, da dukkan alamu ina burge shi, magana innah tayi min Niimatullah baki ga bakonki ba, shiru nayi mata na cigaba da abinda nake yi. A soro tayi masa shimfida komawa yayi ya xauna yana jiran fitowa ta, wajena innah ta dawo tayi min magana, ban saurareta ba na cigaba da tsallena ina shara ruwa a kaina, duka ta kai min Allah yasa na kauce bata same ni ba, fada ta shiga yi min

wuce daki ki kintsa kin bar bawan Allah a tsaye, dukan kasa na rika yi da kafafuna, ni Allah ki kyale ni innata. lallaba ni ta rika yi har sai da na cire jikakkun kayan da ke jikina na sanya wasu na tafi wajen shi.

xaune na tarar da shi ya hada kai da gwiwa, yana dago manyan idanunsa ya kalle ni naga ya tafi wani xuxxurfan tunani, shauki da begen Niimatullah ya cika masa xuciyarsa a duk lokacin da yaga yarinyar wata jaraba ce ta musamman ke kama shi ya rasa dalilin da yasa yake shaawarta haka, tsayawa nayi a kansa tare da cewa gani, wani tattausan murmushi ya sakar min gami da kashe min manyan idanunsa, Niimatullah!! ya kira sunana da tattausar muryar sa, guri na samu na xauna raina a bace yake saboda irin kallon da yake min, tsare ni yayi da ido har sai da na tsargu na rasa me yake kallo a

Please Login or Register in order to submit comment