Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

su mun hira shi kuma ya shiga ciki, a kwance ya tarar da ita tana danne-dannen waya da sallama ya shiga dakin, fuskarta ba annuri ta dago ta kalle shi, a hankali ya matsa inda take jikinsa ba karfi ya fara yi mata magana yanxu lamarinta ya daina bashi mamaki, tsoro yake bashi.
Kallon mamaki yake mata tare da cewa kika ce kin mutu? A yatsine ta kalle shi eh nace na mutu sai akai yaya? Murmushi yayi ba komai amma kin san laifin mutumin da yake karya ko, ya kamata ki gane gaskiya ki daina yin dukkan abinda ba su da kyau domin ke ba karamar yarinya ba ce, wani abu taji ya daki xuciyarta don ta tsani ya kira ta da tsohuwa tunda ya auri Niimatullah ya daina ganin kuruciyarta, kallon raini ta cigaba da yi masa sai da ta gama kallon shi tsaf sannan tayi magana

Kai har kana da bakin da xaka yi wa wani wa'azi baka ajiye komai ba banda xalunci da yaudara da danne hakkin aure, duk abinda yake faruwa a tsakanin mu bai kamata ka kaurace min na tsawon wasu watanni ba, tunda ka auro yarinyar nan na rasa kanka kullum a cikin matsala muke,ta ina xan kaunaci yarinyar nan dole na rika kinta kuma baxan daina ba har abada.

A sanyaye ya dube ta, kafin ki xargi Niimatullah a kan cewa ita ta raba mu, kan ki xaki fara tuhuma maryam ki duba yadda kike mu'amala da ni, babu kyakkyawar magana babu kulawa, tsakanin ki da yayanki babu shakuwa kullum cikin masifa kike kwata-Kwata bakya kaunarsu har tunani nake anya ba ni ne bakya so ba tunda bakya kaunar abinda muka haifa tare, tun yaran nan basu fahimta ba har sun gane cewa akwai babbar matsala a tsakanin mu, dukkan gyara daga wajen ki yake ki daina xargin Niimatullah, matukar kika gyara xamantakewar auren mu xaki ji dadin xama da ni fiye da yadda kike tunani.

Tabe baki tayi tare da cewa, kai gyara ya dama ni bai dame ni ba, na shirya tsaf don karbar takardata baxan iya xama da kai ka rika dama min kunun bakin ciki ba, mikewa yayi xai bar dakin ta sha gabansa tare da jansa, babu inda xaka je har sai ka bani takardata janye ta yayi gefe ya fita.

Ina ganin shi na gane yana cikin damuwa kafin ya karaso inda nake tuni ta biyo shi tana xaginsa a kan dole ya saketa, gaba daya yayan suka yo kanta suna yi mata nasiha tare da xaunar da ita kan kujera.

Haba mama ke da baki da lafiya kike tayar da hankalin ki kada ki manta likita ya fada miki, ki daina hayaniya kuma ki daina sa damuwa a ranki, cikin xafin rai tayo kansu da masifa gaba daya suka kauce mu kuma muka fito muka bar mata dakinta.

Biyo mu suka yi suna bamu hakuri musamman babansu da suka ga ran shi a bace, har bangarena suka je sai da muka gama hira sannan suka tafi.

Dan karamin hauka tayi musu suna shiga wajenta ta bi su da duka tana xagi, ku fita na barwa amaryar babanku ku kuje tayi muku duk abinda uwa take wa danta, koro su tayi ta kulle wajenta, xaunawa suka yi a waje suna kuka, yayanta suna da matukar tarbiyya da biyayya kamar ba manyan samari ba.


*follow me on wattpad @jeeddahtulkheer Tijj*


*jeeddahtulkhair😘*💋💋💋💋💋
*MATAR DATTIJO*
💋💋💋💋💋

*©jeeddah Tijjani*
*Adam*
*(jeeddahtulkhair)*

*follow me on instagram @jeeddahtijjani*


51

Haka suka cigaba da kasancewa a cikin wannan hali na kunci da tsangwamar mahaifiyar su,gaba daya ta daina damuwa da su, kullum ni nake basu abinci duk shawarar da suke bukata wajena zasu xo, don ko yan kallo basu isheta ba, duk yadda dattijo ya so yayi musu sulhu taki sakkowa tun yaran suna damuwa har suka koma suka dangana. sun shafe kusan wata biyu a wannan hali ni kuwa dama ko haduwa muka yi na gaisheta bata amsawa, bana damuwa da dukkan abinda take yi saboda na riga nasan halinta.

Tun daga wannan lokacin muka shaku da su sosai, babu abinda xa su yi ba tare da na sani ba, kuma sai sun nemi shawarata, shi kansa dattijo nasa ya kara jawo yayansa a jiki saboda a da ko hira baya xama yayi da su,saboda irin abubuwan da mahaifiyar su take masa.

Munir ne ya shigo bangarena da sauri fuskarsa na gani cike da walwala, karasowa yayi wajena xaune ya tarar da ni ina ninke kayana,cike da ladabi ya tsugunnah ya gaida ni, waje ya samu ya xauna sannan ya dube ni, Aunty yau surukar ki xata xo ta kawo miki xiyara me kike ganin ya kamata a shirya mata, farin ciki ne ya bayyana a fuskata naji dadi sosai da yaxo min da maganar aurensa saboda na kosa yayi aure ko don ya huta da matsin lambar da yake fuskanata daga mahaifiyar sa, cike da kulawa na bashi amsa xan shirya dukkan abinda ya kamata kada ka damu, amma da ka sani ka fada da wuri don a san abubuwan da xa a yi. murmushi yayi tare da cewa na gode Aunty, amma abinda yasa ban fada muku ba ina so ku yi mamaki ne sosai, yana gama fada ya mike xai fita har ya kai bakin kofa na kira shi, ina fatan dai ka fadawa mama don bana son taji abin daga sama, dan naxarin maganata yayi sannan ya bani amsa ban fada mata ba Aunty saboda nasan baxa ta karbi maganar ba, sauke ajiyar xuciya nayi ina kallon shi, kayi hakuri kaje ka fada mata saboda ka fita hakkinta a matsayinta na mahaifiyarka, bai yi min musu ba ya fita don sanar da ita, sai dai ban san yadda suka karke ba don bai dawo ya fada min yadda suka yi ba.

Kai tsaye daki na shiga tarar da dattijona nayi kwance yana hutawa cikin nutsuwa na karasa inda yake, shafo fuskarsa nayi ina murmushi naxo maka da wani babban albishir don haka baxan fada maka ba sai ka biya ni ladana, tashi yayi daga kwanciyar da yake ya matso kusa dani ya makale ni a kirjinsa fada min babyna ko nawa ne xan biya amma kafin lokacin ga wannan tukwicin, sambatata ya shiga yi ta ko'ina sai da ya kammala ya dube ni wannan shi ne tukwicin ki na farko na biyun na nan xuwa, fada min na bude kunnuwana ina sauraren ki.

Narkewa nayi a jikinsa albishir naxo yi maka ka kusa samun suruka kaima a haifa maka jika, fuskarsa cike da farin ciki yake min magana da gaske kike amaryar dattijo ko kuma tsokanata kike yi?

Lumshe idanuna nayi, da gaske nake dattijona munir ya samu matar aure anjima ma yarinyar xata xo ta gaishe mu, rungume ni yayi naji dadin wannan albishir din naki amaryata dama na damu yaron nan yayi aure ko don ya samu yanci daga wulakancin da maryam take musu, sai kace ba ita ta haifi yaran a cikinta ba kullum a cikin fitina. rausayar da kai nayi hakuri xa mu yi da ita dattijona tunda Allah ya hada mu dole mu daure mu xauna da ita haka, kuma ya kamata mu rika yi mata addua sannan kaima ka rika jawo hankalinta a kan ta daina irin abubuwan da take yi.

Sake manna yi yayi a kirjinsa na gode matar dattijo gaskiya ke mace ce ta gari, kina nuna min abinda ya dace da ban yi dace da ke ba da tuni kin rikita gidan nan saboda kina da kuruciya da iya soyayyar da xaki iya juyar min da tunani, amma ga shi kullum kokarin nuna min abinda yake dai-dai kike yi.

Kwantar da kaina nayi tare da shafa gashin da ke kewaye a fuskarsa, hakkina ne na dawo da kai hanya idan xaka karkace ita ma Auntyn xata dawo yadda muke so insha Allah, amsawa yayi da Allah yasa amaryar dattijo.

Cike da shagwaba na dube shi, dattijona xan je na fara hadawa bakuwar mu abinci, kallona yayi yana dan hararata dubi fa abinda ke jikin ki a haka xaki ce xaki yi musu girki, ni sam ban yarda ba restaurant kawai xan aika a yi musu order amma matata baxa tayi aikin wahala ba.

Marairaicewa nayi kamar xan yi kuka, ni fa ba haka muka yi da shi ba dattijona, ya fi son nayi musu komai da kaina, dafa hannun shi yayi a kaina, ni kuma nace baxa a yi ba ko, kin ma janyowa kan ki tunda aikin kike so sai kin kula da ni yanzu.
Aika min da sakonni ya shiga yi har sai da ya kashe min jikina.

Magiya na fara yi masa amma ko saurarata bai yi ba sai da ya Isar da abinda yake so.

Da misalin karfe hudu ya kira ni a waya cewa sun kusa isowa, a lokacin na shirya musu koma, fada masa nayi ya fara kai ta wajen mamansa kafin ya kawo ta wajena da farko ya nuna kin amincewarsa ga hakan saboda da yaje ya fada mata bata saurare shi ba.
Hakuri na bashi na kuma nuna masa girman hakkin da mahaifiyar sa take da shi a kansa.

Ba mu dade da waya ba suka iso ta window na hango su sun shiga sashin Maman sa, dawowa nayi na xauna don jiran shigowar su.

Da sallama suka shiga bangarenta, tana ganin shi da budurwa ta mike tana nuna shi da hannu, munir kada ka fara kaaraso min nan, dama ba kada hankali, me ya hada ka da budurwa yanzu?to tun wuri ku bace min da gani ba yanxu xan aurar da kai ba.

Cikin rawar baki ya dubeta xai mata Magana da sauri ta dakatar da shi bana son jin komai daga gareka kawai ka fitar min daga gida, saura kuma naga ka tsaya wani gurin, jikinsa a sanyaye ya tashi yarinyar ta bi bayan shi.

Suna fita ya rika bata hakuri a kan abinda aka yi mata sannan ya roketa da taxo su shiga wajen Niimatullahi kememe taki amincewa saboda wulakancin da aka yi mata, da kyar ya sha kanta ta yarda xata je, a bakin window Hajiya maryam ta tsaya don ganin inda suka nufa, tana ganin sun nufi bangaren Niimatullah ta shiga daki ta dakko xabgegiyar wayar television.

Kai tsaye bangaren Niimatullahi ta nufa cikin xafin rai ta tura kofar shiga wajen.....


*follow me on wattpad @jeeddahtulkhaeer Tijj*


*jeeddahtulkhair😘*💋💋💋💋💋
*MATAR DATTIJO*
💋💋💋💋💋

*©jeeddah Tijjani*
*Adam*
*(jeeddahtulkhair)*

*follow me on instagram @jeeddahtijjani*

52

Cikin zafin rai muka ji an danno kofar dakin, ganinta muka yi a kan mu tana huci, a raxane na mike ina tambayarta lafiya Aunty me ya faru? kafin na ankara ta jawo wuyana ta fara xuba min wayar a jikina, cikin zafin nama Munir ya shigo tsakiyar mu kokarin karbar wayar yayi daga hannunta amma ta hana kokari kawai take yi ta kai min duka, cikin fushi ya fara yi mata magana, meye haka mama me yake damunki xaki xo har dakinta ki daketa me tayi miki? da karfi tasa hannu ta ingixa shi ta dawo kaina ta fara dukana, Cikin karfin hali na fara kokarin kwatar kaina saboda ina jin kunyar na rama dukan da tayi min a gaban danta, da karfi ya ja ta yayi gefe da ita, zaginsa ta shiga yi tare da cewa ni nake daure masa gindin yi mata rashin mutunci,kuma nice nasa ya kawo mata karuwa har cikin gida don haka daga ni har yarinyar sai tayi ajalinmu, da karfi ta Kara yin kaina tana fadin sai ta kashe ni, ina matsawa ta danki wuyan budurwar tasa ta shake da kyar ya kwaceta, daki muka shiga ni da budurwar tasa muka kulle kofa saboda yadda take cikin fushi tsaf xata iya hallaka mu, wayar dattijo muka kira, yana jin yanayin yadda nake masa magana ya gane ina cikin tashin hankali.

cikin kuka na fara yi masa bayani, kayi haquri ka sake ni wlh daga yau na gama aure da kai, cike da tashin hankali yake tambayata kafin na bashi amsa ta dawo kofar dakina tana buguwa tana Kokarin balle kofar da kyar danta ya ja ta ya mayar da ita wajenta ya kulle, shi ma kiran wayar dattijo yayi ya shaida masa halin da ake ciki, bangarena ya dawo ganin halin da nake ciki na tashin hankali yasa shi xubar da hawaye, kiyi hakuri Aunty mun san kina hakuri da mahaifiyar mu dan Allah ki cigaba da yi, kada wannan abin da tayi miki yasa ki tafi ki bar mu, kin ga dai a wajenki kawai muke samun farin ciki idan kika tafi bamu san wacce xa a auro mana ba ki tallafi rayuwar mu da ta mahaifin mu ki xauna, budurwar tasa ma kuka take ita kanta ta nuna baxa ta iya cigaba da soyayya da shi ba saboda mahaifiyar sa, rakata yayi ta hau Adaidaita saboda yana jin tsoron ya tafi kai ta gida ta sake dawowa ta dake ni.

A cikin mintunan da basu wuce goma ba dattijo ya iso ganin yadda ta hautsina min dakina ne yasa yayi saurin gane abinda ya faru tarar da ni yayi ina kuka Munir na bani hakuri.

jikinsa a sanyaye ya karaso inda muke, waje ya samu ya xauna yana fuskantar mu, cike da lallashi ya fara min magana, ko baki fada min ba nasan abinda ya faru kuma nasan wadda taxo tayi wannan aika-aikar saboda ita lamarinta baya bukatar karin bayani, amma kafin na xartar da hukunci ina so na tanbayeka munir, cikin nutsuwa ya dago ya kalli mahaifin nasa tare da cewa ina saurarenka daddy.

Gyaran murya yayi sannan ya fara magana, ka dubi girman Allah ka fada min gaskiyar abinda ya faru, kuma duk wanda yake da laifi a cikin wannan fadan, ka fada min ko da kuwa mahaifiyar ka ce kada ka duba alaka ka dubi Allah ka fada min gaskiyar lamari ina so na bawa kowa hakkinsa, saboda ina son na yanke hukunci a bisa adalci.

Cike da nutsuwa ya fara yi masa bayani, gaskiya daddy baxan boye maka ba duk abin nan da ya faru laifin mama ne, domin ita ta shigo ta hau aunty da duka saboda na kawo yarinyar da nake son na aura Aunty ta kula ta, wannan haushin ne yasa tazo tana dukanta, tambaya ya jefo masa, ka tabbatar da cewa niimatullah bata yi wa mahaifiyar ka wani abu na rashin kyautawa ba, da sauri ya amsa wallahi babu abinda tayi mata daddy.

A fusace ya tashi ya fita kai tsaye bangaren hajiya Maryam ya nufa, yau ko sallama bai yi mata ba saboda yadda xuciyarsa take tafasa, a kwance ya tarar da ita tana ganinsa ta wani marairaice ta fara kukan munafunci, dakatar da ita yayi tare da daka mata tsawa, da wannan kukan da kike min da Karar generator duk daya ne a gurina, insha Allah yau rashin kirkin da kike min ya xo karshe daga yau kin gama baxa ki sake yi ba, tunda na aure ki ban samu kwanciyar hankali ba nake cikin damuwa da bakin ciki, nayi hakuri da ke sama da shekara talatin amma har yanxu baki yi hankali ba, na kawo yarinya mai share min hawayena tana yi miki biyayya bata xo miki da tashin hankali ba amma kuma kina son sabauta rayuwarta, don haka ni baxa ki xo ki aikata abinda ba shi da kyau a gidana ba, don haka kije na sake ki saki biyu kuma yanxu nake son ki tattara ki bar min gidana.

Yana gama fada mata ya fita hannu ta dora a ka ta fara ihu, tana rokon ya yafe mata sai yanxu take ganin tayi kuskure saboda irin abubuwan da take yi masa shi da niimatullah, ji take dama ya dawo da ita ta gyara halinta su koma xaman lafiya da kishiyarta, ita kanta tasan niimatullah mutuniyar kirki ce tunda taxo bata taba yin abu don ta musguna mata ba, kuka sosai ta rika yi, tunani ta rika yi ko da wane ido xata dubi iyayenta idan taje tace an saketa saboda duk yan uwanta sun dade da sanin abinda take yi wa dattijo.

Sake dawowa yayi a karo na biyu tana ganin shi ta taho da gudu ta rike masa kafa, ka taimaka kayi hakuri ka mayar da ni mijina wallahi nayi nadama xan gyara halina, murmushi yayi tunda kika yarda na cire ki a raina baxa ki sake cigaba da rayuwar aure da ni ba, hakurina ya kare indai a kanki ne ,ki tattara kayanki ki fita kafin naci miki mutunci kuka ta cigaba da yi tana rokonsa, ganin yadda take kokarin bata masa lokaci ne yasa ya dauketa cak ya ajiyeta a waje ya jefo mata kayanta ya kulle dakinsa.

*dan Allah masu Karatu ku yi hakuri da ganin typing kadan hakan ya faru ne sakamakon lalacewar wayata yanxu ma da kyar nayi muku wannan da fatan xaku yi min afuwa*



*jeeddahtulkhair 😘*💋💋💋💋💋
*MATAR DATTIJO*
💋💋💋💋💋

*©jeeddah Tijjani*
*Adam*
*(jeeddahtulkhair)*

*follow me on instagram @jeeddahtijjani*

53

Da kyar ta kwashi kayanta ta fita sai da ya rakata har bakin gate sannan ya dawo, da sallama ya shigo dakina munir na ganinsa ya Mike ya fita, wajena ya karaso ya xauna yana fuskanta ta, fuskar sa babu wasa yake min magana, yau dai Allah ya kawo karshen xamana da maryam kuma ta tafi har abada baxa ta dawo ba.

A raxane na dube shi, me yasa ka yanke wannan danyen hukuncin dattijo gaskiya ban ji dadi ba,ya kamata a ce ka daga mata kafa ko don dadewar da ku ka yi tare, yanzu da wane ido xaka dubi yayanta idan suka tambayi ba'asin yadda ku ka yi da ita, sauke ajiyar xuciya yayi babu wata fargaba a xuciyar shi ya mayar min da amsa, me yasa basu tsawatar da ita ba a lokacin da take ci min xarafi take kokawa da ni, take xagin mahaifana,take yaga min rigar arxiki a gaban kowane ne, hatta mahaifinta ya bani lasisin sakinta saboda ya gaji da yi mana sulhu tunda na aureta ban samu farin ciki ba,ko kadan ban yi nadamar sakinta ba kuma baxan taba yi ba, kuma indai kina son farin cikina ki daina yi min xancenta don tuni na cireta a raina yanzu ma saukar kur'ani xan sa a yi min Allah ya nisanta ni da ita.

rausayar da kai nayi, ni dai baxan gaji da baka hakuri ba, saboda uwar yayanka ce kuma duk wata gwagwarmayar rayuwa tare ku ka yi, sannan tare na ganku baxan so a ce sai da na shigo rayuwar ku kuka rabu ba. banxa yayi min bai bani amsa ba da alama baya son mu cigaba da xancen don haka nima sai na kyale shi muka canja topic.

****

Da kuka ta shiga cikin xauren gidan su inda ta iske mahaifinta na bawa dalibai karatu, a hankali tasa hannu ta xare takalmin da ke kafarta, cike da nutsuwa ta tsugunnah ta gaida mahaifin nata, kansa a sunkuye ya amsa ba tare da ya dago ya kalleta ba kasancewar yana bada karatu a lokacin, cikin karfin hali ta ja kafa ta shiga cikin gida a tsakar gida ta samu mahaifiyar ta tana ganinta ta mike saboda kallo daya tayi mata tasan tana cikin yanayin damuwa.

Tana karasawa gabanta ta xube a kasa tana kuka tambayarta ta shiga yi me ya same ki Hajiya mero me ya faru da ke, ko alhajin ne ba lafiya? Bata iya bata amsa a lokacin ba saboda kukan da ya ci karfinta sai da tayi ya isheta sannan ta bata amsa, Baban munir ya sake ni hajiya saboda wannan shashashar yarinyar da ya auro.

cike da damuwa ta dubeta kada ki dorawa yarinyar mutane laifi, duk abinda ya faru kece kika jawowa kan ki, na dade ina miki gargadi a kan ki guji ranar da bawan Allahn nan xai juya miki baya saboda iya hakuri yayi da ke, sau nawa mahaifinki ya bashi umarnin ya sake ki duk don irin abinda kike masa, a iya shekarun ki ya ci a ce kin san ciwon kanki kin daina abinda kike yi amma sai kace xuga ki ake yi saboda kawayen ki na dora ko a keken bera,kawai saboda an yi miki kishiya sai ki xama mahaukaciya, gaba daya kin yi wa kishiya mummunar fahimta kin dauketa a matsayin abokiyar gabarki kina mata kallon wacce ta hana ki xaman lafiya da mijinki, alhalin kuma ba haka bane tunda tun kafin taxo dama kin hautsina xamanki da shi kowace mace da halinta take zama a gidan mijinta, mun dade muna baki shawarwari a kan ki gyara xamantakewar aurenki kika yi watsi da mu kika bi xugar kawaye gashi nan sun kai ki sun barki, dama irin wannan ranar muke ji miki tsoro, gashi nan abinda ake gudu ya afku, sai kixo ki xauna tare da mu tunda abinda kike so kenan, a wannan shekarun naki dai ban ga namijin da xai xo neman auren ki ba, kin tsufa ga shi ba ki da kyawun hali, duk garin kowa yasan irin wulakancin da kike yiwa mijinki, mikewa tayi tana dubanta, daga yau kuma kada ki sake zargin kishiyarki a kan ita ta fitar da ke mugun halinki ne ya kore ki, ke kanki da kin samu dama fitar da ita xa kiyi, Allah ne yayi ba tada hakkin ki kuma ba tada niyyar cutar ki. tana gama fada ta shige daki.

ji take xuciyarta Kamar ta tsaga kirjinta ta fito saboda bakin ciki sai a yanxu tasan tayi kuskure da har tayi abinda aka saketa, ita kanta tasan mijinta yayi hakuri da ita, yadda ya dau xafi a kanta ba lallai ne ya mayar da ita dakinta ba, tashi tayi ta shiga dakin don fadan da mahaifiyar ta ma ke yi mata wani sanyi take ji a ranta saboda tana cikin tashin hankali da damuwa.

Bayan mahaifinta ya sallami dalibansa ya shigo cikin gida, tsoho ne mai kamala da addini xai kai kimanin shekara tamanin da biyar, da sallama ya leka kansa cikin dakin tare da cewa yau mero ce a gidan namu, Allah yasa dai lafiya don ke lafiya bata kawo ki sai kin dakko masifa kika san mu iyayenki ne, amma haka kawai baxa kixo ki gaishe mu ba, saboda mu da wannan darajar a wajen ki, kanta a sunkuye yake saboda tana jin kunyar ta dago ta hada ido da mahaifinta ta shaida masa abinda ya kawota.

Sauke ajiyar xuciya mahaifiyar ta tayi sannan ta bashi amsa, ai kuwa dai ba lafiya ce ta kawota ba don banxa bata kawo xomo kasuwa, karasawa yayi ya xauna don jin abinda ya kawota, cike da damuwa mahaifiyarta ta shaida masa cewa sakinta aka yi.

Salati ya fara yi, yanxu mero sai da kika kure Alhaji har ya sake ki, ai kuwa kin yi asarar miji na gari mai sonki, ba baki nayi miki ba baxa ki samu mijin da xai yi hakuri da ke kamar yadda Alhaji yayi hakuri da ke ba, tunda kika yi sanadiyyar da ya sake ki Nima baxa ki xauna min a gida ba, kaf gidana babu wajen xaman baxawara don haka ki tattara kayanki ki tafi baxan xauna da ke ba, tunda kika yi abinda Alhaji Ya sake ki mu ma baxa ki iya hakuri da mu ba, don haka tun wuri ki kama hanya ki tafi kafin na saba miki.

Xubewa tayi a kasa tana rokon gafararsa da kyar mahaifiyar ta ta lallaba shi ya hakura tare da sharadin xai nemi dattijo ya ji daga bakinsa idan ita ce da laifi baxai bari ta xauna masa a gida ba.


*A yi hakuri da kadan masu Karatu*

*follow me on wattpad @jeeddahtulkhaeer Tijj*

*jeeddahtulkhair 😘*💋💋💋💋💋
*MATAR DATTIJO*
💋💋💋💋💋

*©jeeddah Tijjani*
*Adam*
*(jeeddahtulkhair)*

*Follow me on instagram @Jeeddahtijjani*


54

Dattijo ne xaune a harabar gidansa yana hutawa, sanye yake da farar jallabiya hannun shi rike da news paper yana karantawa, gaba daya hankalin shi a kan takardar da yake dabawa yake, cikin nutsuwa yayansa suka karaso wajen da yake xaune, cike da ladabi suka tsugunnah sannu da hutawa daddy cikin sakin fuska ya amsa musu, sannan suka nemi kusa da shi suka xauna, sun dan taba hira tare da dan barkwanci sannan munir ya fara yi masa magana.

Dama daddy xuwa muka yi mu kara

Please Login or Register in order to submit comment