Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya rika xuwa yana daukar mana yarinya ba yana yawo da ita a gari kawai don an daura musu aure.

Har muka kusa xuwa inda xamu je na kasa yin shiru ashe ba wani Abuja da xan raka shi karya ya shararawa su innah.

A yi hakuri da wannan wlh ba nida lafiya yanxu ma karfin hali nayi na baku wannnan don kada ku ji shiru

*Jeeddahtulkhair😘*
[10/1, 12:42 PM] Itz B Y ebrerheem: 💋💋💋💋💋
*MATAR DATTIJO*
💋💋💋💋💋

*©jeeddah Tijjani*
*Adam*
*(Jeeddahtulkhair)*

*follow me on instagram @jeeddahtijjani*

*معذرة🤦🏼‍♀*
*masu yi min magana ta private su ga kamar wulakanci ne yasa bana son amsawa wlh matsalar network ne maganarku na shigowa amma tawa bata tafiya dan Allah a yi min afuwa ina kaunar ku kamar yadda kuke kaunata*


10

Bakin wani hotel muka Parker leko da kanshi yayi inda na sunkuyar da kaina, to mun xo amaryata sai ki tashi mu shiga, cikin tsiwa nace wlh ba inda xan je har sai ka mayar da ni inda ka dakko ni idan ba haka ba kuma sai dai mu kwana a nan, murmushi yayi tare da kanne ido daya, menene idan mun kwana a nan ni tayi min dai-dai kinga sai nayi abinda naga dama da matata babu mai sa min ido.

Hararar shi na shiga yi, to yi din wallahi xaka janyo a fasa auren nan kowa ya huta, murmushi yayi min auren nan fa a hannuna yake amma kullum sai ki rika cewa a fasa, to ni baxan taba sakin ki ba mutuwa ce xata raba mu, yana gama fada min ya bude motar ya fito, leko da kan shi yayi ta window ki fito idan ba haka ba kuma na dauke ki cak na kai ki inda xamu je.

Harararshi na tsaya yi gami da jujjuya idanuna, bismillah dauke ni din idan tsayawa xan yi ina kallonka, dariya yayi min wai me yasa bakinki baya mutuwa ne Niimatullah gaki yar mitsitsiya sai tsiwar tsiya da rashin ta ido, tunda kika ce min bismillah xaki ga aikin bismillah, bude murfin motar yayi daukana yayi can cak,da kafarsa ya mayar da murfin motar ya rufe, kokawar kwatar kaina na fara yi, amma na kasa, sai da ya kaini har cikin dakin da xamu sauka, sannan ya ajiye ni kuka na rika yi masa ina magiyar ya mayar da ni gida.

kumatuna ya rike yana min murmushi yau ina tsiwar taki Niimatullah? cikin kuka nace masa na daina baxan kara yi maka ba kayi hakuri, rungumo ni yayi ya hada ni da kirjinsa kin tabbatar da cewa baxa ki sake yi min rashin kunya ba kuma baxa ki sake yi min tonon asiri ba? da sauri na daga kai nace masa eh, murmushi yayi tare da cewa yau ba a turo min da dan bakin nan ba ko don ba a gidan innah ake ba? shiru nayi masa cikin shagwaba nace masa ina jin kishiruwa.

kallona yayi ya tsare ni da ido ba daxu na baki ruwa kika sha ba, wannan ba na bayarwa bane idan kuma kika sha min sai kin biya ni, da sauri nace eh bani na sha idan naje gida xan debo maka wani a randar innah.

dariya yayi min wa ya gaya miki irin wannan biyan xaki min da jikinki xaki biya ni saurin dafe kirjina nayi, dama ana iya biyan ruwa da jiki? murmushi yayi tare da cewa kwarai kuwa idan kuma baki yarda ba gashi kisha.

girgixa kaina nayi ka barshi ni bana so Allah, shafa fuskata yayi, yi hakuri babyna ai baxan iya hana ki kisha ruwana ba, ko don alfarmar yayana da ke jikinki, saurin xare idanu nayi wane yayan naka kuma? nan da nan na mike tsaye ina duba kaina, wayyo na shiga uku me xan je gida na fadawa innata, dama ta dade da fada min indai na bari aka taba ni xan iya samun ciki, watakila ma cikin yan biyar ne dani tunda kusan sau biyar kana taba ni.

Hankalina ya tashi sosai sai ihu nake shi kuwa yana gefe yana tuntsura min dariya, sai da nayi kukana na koshi sannan ya kira sunana cikin salon soyayya, Niimatullah a hankali na dago jajayen idanuna da suka sha kuka na dube shi, ki daina damuwa yanxu ba ki da komai a cikin ki sai nan gaba xaki samu ciki ki haifo min yaya kyawawa kamar ki, kin ji ko yar yarinya ta. cikin kuka nace masa to naji tashi mu tafi gida kada innata taga na dade, dagowa yayi daga kwanciyar da yayi, mu tashi mu tafi fa kika ce? baki ga har kwanciya nayi ba to ina nufin tafiya ba yanxu ba har sai na koya miki hankali kin daina wannan surutun da kike yi, sai mun kwana daya a nan, da sauri na dago na kalle shi kayi hajuri nayi hankali wlh baxan sake gayawa inna ba, murmushi yayi naji kin yi hankali amma ni kudin kwana daya na biya mana baxan tafi ba sai na ci kudina don baxan yi asara ba, yana gama fada ya mayar da kansa gefe

kuka na fara yi Allah baxan kwana a wajen nan ba sai na tafi gida, bakin kofa na nufa na fara jijjiga kofar ina kokarin budewa amma na kasa saboda key din na aljihunsa, dawowa nayi na fara yi masa magiya, dan Allah kaxo ka bude min kaga magariba ta kusa.

lumshe idanunsa yayi ya dube ni, idan kina so na mayar da ke gida sai kin taimaka min, da sauri na karasa wajensa fada min taimakon da kake so nayi maka, xaune ya tashi ya dube ni, xo na fada miki a kunnenki, makale kafada nayi Allah a'a sai dai ka fada min a nan ina jin ka, murmushi yayi, me yasa kike jin tsorona haka Niimatullah alhalin ni ba dodo bane, bata fuska nayi to ai har gara dodon dama nasan dodo ne amma kai ka rika kama ni kuma bayan kasan haramun ne, murmushi yayi wato bakin ki baxai yi laushi ba ko, to sai gobe xaki tafi gida, kuka na fara yi har sai da nayi ya ishe ni sannan ya fada min irin taimakon da xan masa, tausa xaki yi min, amma da sharadi baxa ki ce min kin gaji ba, idan kika ce kin gaji sai kin kwana kina yi, da kyar naja kafa naxo kusa da shi na fara yi masa tausar, xuciyata cike da tsoron kada ya kamo ni, bayan na gama masa ya tashi ya shiga wanka yana fitowa muka hau mota ga mayar da ni gida.

09077389712


*jeeddahtulkhair?*??????????
*MATAR DATTIJO*
??????????

*©jeeddah Tijjani*
*Adam*
*(jeeddahtulkhair)*

*follow me on instagram @jeeddahtijjani*

*Don Allah don Annabi masu hade min pages 2 ya xama daya dan Allah ku daina bana so, gaskiya idan na kara cin karo da irin wannan xan dakata da typing*


11

Ina shiga gida naji wani bakin ciki ya tokare ni a makogoro, tambayar kaina na shiga yi me yasa har na amince da auren wannan dattijon gashi nan yana kokarin shigar min rayuwa, muna daf da shiga cikin gidan ya kira sunana.

Niimatullah!!! a sanyaye na waiga na dube shi, matsowa yayi daf da ni har ina jin kamshin turarensa, dafa kaina yayi tare da dago fuskata saura kuma mu shiga cikin gida kiyi min tonon asiri don nasan ki akwai surutu a wasu lokutan, kina yi xan dawo gobe na tafi da ke kin san dai innah da baba baxa su hana ki bini ba, shiru nayi masa saboda haushi yake bani yanxu.

muna shiga innah ta tarbe mu da murnarta,ya naga har kun dawo da wuri haka Alhaji, sunkuyar da kansa yayi tare da shafa fuskarsa, tafiyar tamu ce bata samu ba innah, cikin jimami innah ta bashi amsa, ayyah ai dama komai sai Allah ya nufa, hira suka fara yi ni kuwa sai kallon fuskarsa nake yi muna hada ido da shi sai nace na fada??

yana ji na fadi haka sai ya sunkuyar da ido kasa saboda kunya, sake maimaita masa maganar na rika yi, na fadawa innata inda muka je da abinda nayi maka? da hanxari innah ta dube ni, wai ke wace irin yarinya ce Niimatullah idan kika sake magana sai na hada miki kayan ki kin bishi, kuka na fara yi haba innata gidan wannan mutumin xaki kaini Kullum fa sai ya matse ni kamar wata yar tsana, duka ta kai min ke dai baxa ki daina halin ki ba ko, dole ma a tattara ki a kai ki gidan miji ko kya yi hankali a can bari malam yaxo na fada masa tunda abinda kike yi kenan, idan kika koma can kika tare sai ki bada labarin gidan mijin da hujja, kuka na fara yi ina mata magiya tayi hakuri, shi kuwa dattijo kamar ya nutse saboda kunya ya rasa bakin magana, basu gama hirar ba ya tattara kayansa ya tafi, inna ce ta dube ni baxa ki tashi kiyi masa rakiya ba ko, cikin shagwaba nace yasan hanya fa innah, maficin da ke hannunta ta kwado min, idan ina magana kina min musu sai mun fara fada da ke a gidan nan, ina tafe ina turo baki na bishi soro, tsayawa yayi yana kallona domin ya rasa bakin yi min magana.

gajiya nayi da tsayuwa na dube shi, ni xan tafi gida don na gaji da wannan tsayuwar da nake yi, lumshe idanunsa yayi tare da cewa lallai ina da aiki har yanxu akwai haukan kuruciya a kan matata, tsugunnawa yayi har kasa yana rokona, dan Allah ki daina yi min irin wannan abubuwan da kike fada a gaban innah ina jin kunya na rasa ina xan sa kaina, me yasa kike haka Niimatullah ba fa a kanki aka fara aure da wuri ba, iyayenmu da kakannin mu duk kusan irin wannan auren aka yi musu, kuma akwai yara kanana da ake aurarwa a kai su gidan maxajensu kuma su basu hakkkinsu babu mai ji, amma ke daga na taba hannun ki sai ki rika yawo da ni kina kunyata ni.

Hararar shi nayi ni ba ruwana da su kaina na sani tunda innata tayi min karatun kada na bari wani ya taba ni baxan xubar da wannan karatun ba, kuma ko yau ka kuma yi min, sai na fada a gida idan baka gaji da taba ni ba nima baxan gaji da baka kunya ba.

Haushi na bashi don haka ya fara magana, tunda abin naki haka ne baxa ki daina ba ko, to nan da sati xaki tare a gidana ki fara taka irin rawar da sauran matan aure ke takawa a gidan maxajen su, sunkuyar da kaina nayi ina sauraren sa, kafin na ankare ya rungumo ni ya hada fuskata da tasa idanunsa naga ya canja ya rika aika min da sakonnin soyayya kala-kala, sai da ya dawo cikin nutsuwarsa ya dube ni

tonon sililin da kike min ne yasa nayi miki haka yanxu ma idan kin koma gida ki sake fadawa inna xaki ga yadda xamu kwashe ni da ke, yana gama fada min ya wuce ya tafi, jikina a sanyaye na shiga gida, duk maganar da nayi wa inna bata amsa min ba, jikina ba karfi na karasa wajenta, kawar da kanta gefe guda tayi tare da juya min baya, cikin sassanyar murya na dora hannuna a kan cinyarta ina mata magana, me yasa xaki juya min baya innata ki daina kulani ni fa ba wani laifi nayi masa ba ko da muka je can din tausa yace nayi masa kuma nayi.

A hankali ta dube ni wannan rashin sirrin naki shi yake hada ni da ke, a ce baxa ki rika rike sirrrin mijinki ba kullum ina nuna miki illar hakan kin kasa ganewa, kuka na fara yi to ni innah me yasa yake min haka, dama haka aka ce ya rika yi min,shi yasa fa nake xuwa na fada miki don ki rika yi masa magana, ni bana son abinda yake min,hawaye na rika sharewa ita kuwa innah saboda takaici ma ta kasa cewa komai sai da nayi kukana na koshi sannan ta rarrashe ni tace xata yi masa magana.

Baba na shigowa take fada masa yadda ta kaya tsakanina da dattijo, kama baki yayi lallai Niimatullah ba hankali, yanxu da hankali xa a rika wannan xancen, amma dai xan nemi mijin nata nayi masa magana ya dan saurara har xuwa tayi wayo tunda bata san ciwon kanta ba xata iya xuwa wani wajen ta fadi abinda ke faruwa tsakaninsu.

ba karamain dadi naji ba da baba yace xai neme shi yayi masa magana.




*Jeeddahtulkhair??*
😘*💋💋💋💋💋
*MATAR DATTIJO*
💋💋💋💋💋

*©jeeddah Tijjani*
*Adam*
*(Jeeddahtulkhair)*

*follow me on instagram @jeeddahtijjani*

12

Baba ne da kanshi ya kira shi a waya yace yana son ganin shi, ba a fi minti biyar da fada masa ba yaxo, da sallama ya shiga dakin baba sun fi kusan minti goma suna tattaunawa babu abinda nake jin dattijona na fada banda wallahi baxan iya jurewa ba baba xan iya shiga wani hali a hakan ma hakuri nake yi, shi kuwa baba sai hakuri yake bashi, gabana ne ya rika faduwa ina tunanin menene baxai iya jurewa ba, bayan sun gama tattaunawa ya fito ya tafi gida.

washe gari bayan mun yi sallar magriba yaxo, cikin nutsuwa ya tako ya shigo har tsakar gidan mu tare da yin sallama, idanun shi a kaina ya kasa daukewa sai wani asirtaccen murmushi mai kunshe da abubuwa da yawa yake sakar min, gefe na koma na buya a bayan innata, bayan sun gama gaisawa nima na gaishe shi daga haka babu maganar da ta sake hada ni da shi, sai da suka gama magana tsaf da innah ya juyo ya kalle ni.

cikin sassanyar muryarsa ya kira sunana Niimatullah!! idanuna a kasa na amsa masa, dama form na koyon girki da gyaran jiki na kawo miki, ina so ki fara xuwa nan bada dadewa ba, yanxu xan cike miki duk ranar alhamis da juma'a xaki rika xuwa, na xabi wadannan ranakun ne saboda kina xuwa islamiyya, ina so ki tsayar da hankalinki ki yi abinda ya kamata har kula da miji duk xa a koya miki a can, shiru nayi ina saurarensa har ya gama bayaninsa.

innah sai murna take xan koyi abubuwan rayuwa, cike da xaulaya ya tambaye ni, sunana xan saka miki ko na Baba naga kowace mace a wajen da sunan mijinta take amfani? Turo dan tsukekken bakina nayi, sunan babana xaka saka min, murmushi yayi niima kenan har yanxu baxa ki daina rigima ba ko, cike min form din ya shiga yi bayan ya kammala yake fada min cewa Kullum shi xai rika xuwa ya kaini, shagwaba na shiga yi masa ni Allah baxan bika ba da kaina xan rika tafiya, lallaba ni ya shiga yi kiyi hakuri na rika kai ki wajen da nisa shi yasa bana so kije ke kadai ko so kike wasu su dauke min ke su gudu da ke? da sauri na girgixa kai alamar a'a, sallama ya yi da innah sannan ya rika kifta min ido alamar na biyo shi nayi masa rakiya, makale kafada nayi ni baxan bika ba, sai da yaga ba nida niyyar bin shi ya tafi ya kyale ni.

tafiya yake a mota amma gaba daya tunanina yake yi, kafin ya isa gida ya kira ni a waya, dauka nayi na kara wayar a kunnena cikin shagwaba ya fara yi min magana my Niimatullah, idan kina kusa da innah ki matsa xan yi magana mai muhimmanci da ke, ban yi masa musu ba na shiga daki, gaishe shi nayi tare da yi masa ya yaje gida, cikin shagwaba ya amsa min ba lafiya matata, cikin kulawa nace me ya same ka dattijona?muryarsa a marairace ya amsa min da kece, da sauri na sake tambayarsa me nayi maka dan Allah?har ka tayar min da hankali kasan bana so na cutar da kai innata ta fada min kai ne Aljannata wai haka ne? murmushi yayi har ga Allah yana jin dadin maganganun Niimatullah da sauri yace haka ne mana, da baki sani ba? eh nace masa.

kukan shagwaba ya hau yi min, kin shiga cikin rayuwata kin yi kane-kanen da baxa ki iya fita ba Niimatullah, nayi nisa a cikin kaunar ki ina jin rayuwata baxa ta tafi dai-dai ba idan babu ke,na kosa na fara rayuwa bisa kulawarki, ganinki da nayi yanxu ba karamin tayar min da wani miki kika yi ba a xuciyata, ki taimaka kixo inda nake ko driving na kasa yi saboda shaukinki, na tabbatar da cewa yau baxan yi bacci mai dadi ba musamman a lokacin da dare ya tsala na duba gefena ban ganki a kusa da ni ba, ki taimaki dattijonki ki fadawa su innah su bani ke kada sonki ya halakar da ni. kuka naji yana yi sosai.

A hankali na sauke ajiyar xuciya to kayi hakuri na gama xuwa makarantar girkin idan na iya komai ba sai na tare ba, katse min maganata yayi ni duk wannan bai dame ni ba babyna, indai girki ne da kaina xan rika yi mana,wata rana kuma mu je restaurant mu ci, ni burina kawai naga na fara rayuwa da ke, xaki amince a kawo ki gidana yanxu? da sauri na dakatar da shi.

ni dai wallahi a'a ba yanxu ba kuma idan ma xan tare da innata xan tafi na rika ganinta ina jin dadi, murmushi yayi ita ma innah ai da dan mijinta baxai bari ta tafi ta bar shi ba, don haka kema sai ki taho ki tarairayi naki mijin ki samu lada, makale kafada nayi kamar yana kallona, ni fa baxan taho yanxu ba har sai na iya girki da komai so kake yi matarka ta rika yi min gori ban iya girki ba kamar yadda tayi min na tsafta.

dariya ya rika yi lallai niimatullah bakya mantuwa yanxu har kin haddace wannan abin a kanki? ki kwantar da hankalinki baxa ta yi miki glri ba ai tasan amaryar tawa ta musamman ce ta hadu ta kowane bangare, kin san me nake tunawa a tare da ke kuwa??

cikin sassanyar murya nace masa a'a, lokacin da na dauke ki dama haka kike ba ki da nauyi kamar yar tsana, Gaskiya xan fadawa innah ta daina baki abincinta tunda kin ki yin nauyi, turo baki nayi kamar yana ganina ni din ce ba nida nauyi lallai ma ka raina ni da yawa.

murmushi yayi ni ban rainaki ba amma gaskiya na fada tunda duk nauyin kii ai baki kaini ba ko? shiru nayi masa sai can nace ai dan kai dattijo ne shi yasa ka fini nauyi.

murmushi yayi da ina kusa da ke sai na murde wannan bakin da har yanxu bai daina kirana da dattijo ba na fada miki ni babynki ne, kada ki sake cewa dattijo.

ni fa ina wani tunani Niimatullah, da sauri nace masa tunanin me kake yi?

Anya xaki iya daukan nauyina kuwa? au na manta fa na yiwa baba alkawarin mun daina wannan maganar da ke, takura masa nayi sai ya fada min amma yaki fada haka muka gama magana ya kashe wayar.



*Jeeddahtulkhair😘*💋💋💋💋💋
*MATAR DATTIJO*
💋💋💋💋💋

*©jeeddah Tijjani*
*Adam*
*(Jeeddahtulkhair)*

*follow me on instagram @jeeddahtijjani*

*dedicated to Amina Bashir (maman siyama)*


13

Suna kammala wayar ya ja motar shi ya wuce gida, yana driving yana tuna irin hirar da suka yi da Niimatullah, ba karamin shiga ransa tayi ba, ji yake kamar ya jawo lokacin da xata tare a gidan sa.

A bakin kofar parlour ya ci karo da matarsa xaune a kan kujera ta dora kafa daya kan daya, tana harare-harare tare da turo dan kwalinta gaban goshi, da sallama ya karaso wajenta wani mummunan kallo tayi masa tare da kawar da kanta gefe guda, cikin tausasa murya yake mata magana, sannu da gida maman munir a fusace ta amsa masa, kaine da sannu tunda kai ka dawo daga wajen kaxamar matarka wacce ilimin addini da na boko bai wadaceta ba, wallahi ina ganin kokarin ka da har kake iya kula wannan jakar da bata san kanta ba, ka xubar da ajinka da nawa, ka rasa wadda xaka hada ni kishi da ita sai yar matsiyata, wadda iyayenta ke rayuwar wahala, tunda aka haifi yarinyar nan nasan bata san menene dadin duniya ba saboda talauci, amma don ka raina min hankali xaka hada ni da ita salon ta shafa min kwarkwata da kudin cizo. tana gama magana ta cigaba da girgixa kafarta.

ji yayi xuciyarsa na tafasa kamar xata tsaga kirjinsa ta fito saboda irin maganganun da take fadawa wacce ba shi da tamkarta a rayuwarsa, cikin fushi ya mayar mata da martani.

kucaka, kuma kaxamar da kika raina kike ganinta a banxa ta fi min ke a yanxu domin a inuwarta nake samun nishadi da jin dadin rayuwa, dadin da ban ji shi sama da shekaru talatin ba yanxu na same shi a wajen jaririyar yar da kika haifa, kin yi sake yar cikin ki ta kwace miki miji, domin da ke da babu duk daya na dauke ku a cikin gidan nan.

Baki ajiye komai ba sai girman kai da raina miji, da kwalliyar banxa amma ta bangaren ibada salam ba dadi, yana gama fada ya saki wani shu'umin murmushi.

zan baki shawara daya kije wajen Niimatullah ta koya miki iya xama da miji da tarairayarsa, kuma ki lallabata tayi miki addu'a Allah ya axurta ki da irin ni'imomi da baiwar da Allah yayi mata, domin bakin Niimatullah mai kyau ne ina da yaqinin addu'arta xata karbu saboda farantawa mijinta da take yi.

sake juyawa yayi ya kalleta, hannunta dafe da kirjinta ta rasa bakin magana, tunda na samu Niimatullah nasan menene dadin aure, ashe da duk hakuri nake ina rayuwa da dusar mace ban sani ba.

Hannu ta dora a ka ta fara rusa ihu tana ci masa mutunci tunda suke da shi bai taba tsayawa ya fada mata magana irin na yau ba, shi kuwa shigewa daki yayi saboda yasan ya gama munana mata, a falo ta kwana tana masifa ko bacci bata iya yi ba. kalmar da ya fada mata ita tafi tsaya mata a rai domin ta maimaita kalmar wajen sau goma, yanxu saboda wannan yar iskar yarinyar xaka rika kirana da dusa, Allah ya isa tsakanina da kai, kuka ta rika yi shi kuwa yayi kwanciyarsa bisa gado yasan baxa ta kara marmarin xagin Niimatullah a gabansa ba tunda ya yiwa tufkar hanci, ajiyar xuciya ya sauke sannan ya juya yayi kwanciyarsa.

washe gari da wuri na kammala shiryawa na gyarawa innah dakinta, saboda nasan dattijona yana kan hanyar xuwa ya tafi da ni wajen koyon gyaran jiki, kusa da innata na xauna ina jiran karasowar sa, horn din mota naji don haka na saka takalmana, sallama na yiwa innah sannan na fita.

tarar da shi nayi jingine da motarsa ya harde hannayens a kirjinsa, tunda na taho daga nesa yake sakar min wani kallo tare da yi min kyakkyawan murmushi, daga nesan na tsugunnah na gaida shi, cike da kulawa ya amsa min ,bude murfin motar yayi na shiga, sannan shi ma ya shigo, kafin ya ja motar mu tafi sai da ya kare min kallo yana min magana kasa-kasa wacce bana fahimtar abinda yake cewa, dago fuskata yayi yana min wani kallon da ke sanyaya min jikina, cike da kulawa yake min magana.

ki tsayar da hankali ki koyi yadda xaki tarairayi marainiyar xuciyar mijinki kin ji my Niima, gyada kai nayi kawai ba tare da nayi magana ba, sai da ya gama yi min nasiha sannan muka dau hanya.

muna isa ya juyo ya dube ni har mun xo babyna, sannu da driving nayi masa sannan ya xagayo ya bude min kofa, hannuna ya rike muka shiga har Office din matar da xata koyar da ni, a xaune muka sameta tana cike wasu forms, cikin girmamawa ta gaida dattijona, hannu biyu ta karbe mu, cike da kulawa ya nuna ni,wannan sabuwar amaryata ce, an daura min aure da ita amma bata tare ba, don haka ina so a koya mata komai kafin lokacin da

Please Login or Register in order to submit comment