Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yayi.

cike da gadara take masa magana, naje na lalata auren yar iskar yarinyar da kake so, saboda baxan taba iya sharing dinka da wannan kaxamar yarinyar ba, kuma wlh ka sani na rika yi maka haka kenan Har abada ba kai ba kara aure, duk inda kaje neman aure sai na rika xuwa ina ci musu nutunci a haka har su yi xuciya a fasa auren, mutumin banxa Kawai mara alkawari, a fusace ya dubeta.

ni kike kira da mutumin banxa Hajiya Maryam? tsare shi tayi da ido tana harararsa na fada duk abinda xa kayi sai dai kayi, karya nayi maka ba mutumin banxan bane kana tsoho ka auro yar cikinka saboda son xuciya da kwadayi an girma ba a san an girma ba, lalata aure yanxu na fara idan xaka nemi yan mata dari ni kuma sai na lalata auren har sai ka hakura ka daina.

komawa yayi ya xauna saboda idan ya cigaba da tsayawa tsaf xai fadi wani bakin ciki ne ya cika xuciyarsa cike da fushi ya mayar mata da amsa wlh ba dan arxikin yayan da kika haifa ba da xamana ya kare da ke yau,a matsayina na uban yayanki kike kirana da mutumin banxa saboda ba ki da hankali, auren Niimatullah ne bakya so kuma kisa a ranki kamar amarya ta tare a dakinta ne, kuma ki shirya ganin wulakanci kala-kala Allah dai ya kawota da alkhairi, da sannu sai na ganar da ke kuskurenki sai kin yi nadamar kirana da mutumin banxa shashasha mara amfani, sai kin xama tamkar shara a gidan nan dama ba ki da wani amfani a wajena banda bata min rai babu abinda kike yi mahaukaciya kawai, yana gama fada mata ya wuce dakinsa.

Yana shiga daki ya jawo waya ya kira Niimatullah, ina kallon wayar na ringing na kyaleta, sai da ya kira ni wajen sau biyar sannan na dauka, ina jin yanayin yadda yake magana nasan yana cikin matsananciyar damuwa, mun kai kusan minti daya ba tare da mun cewa juna komai ba, nice nayi karfin halin kiran sunan shi.

Dattijona!! cike da damuwa ya amsa min da na'am my Niimatullah, cike da damuwa nake masa magana, idan har akwai wani abu da xan roka a wajenka bai wuce na rokeka a kan, ka amince mu kasance tare ba har abada, domin tabbatuwar mafarkin da ya jima yana bayyana a cikin baccina, ina sonka amma dole na barka tunda iyayena sun hango min matsala a tare da Kai.

Cikin sanyin murya yake min magana yanxu baxa ki tausayawa mijinki ba niima, ina cikin damuwa ko abinci na kasa ci, yanxu babu taimakon da xaki neman mana a wajen baba ya taimaka ya kyale mu muyi rayuwar farin ciki da juna,shikenan duk ginin da muka yi a baya ya rushe my Niimatullah, ki duba halin da xan shiga ki tallafi rayuwata, ji nayi hawaye sun fara xubo min hannu nasa na goge.

ina sonka dattijona amma baxan iya aurenka ba saboda mugun halin matarka saurin dakatar da ni yayi, tsaya Niimatullah bana son kina kawo tunanin wannan matar a ranki, babu abinda ta isa ta hana game da auren mu rayuwa mai dadi xa kiyi da mijinki, ki tallafi rayuwata ki shawo min kan innah da baba su yarda da ni, a sanyaye na amsa da to xan yi insha Allah sallama muka yi da shi ya kashe wayar.
ina ajiye wayar bai fi da minti biyu ba naji shigowar message din shi, a hankali nasa hannu na bude.

*Ina fatan xuwan ranar da xan kasance shinfide a saman kafadun ki na kwana a cikin dakin Ki, na kasance a tallafe bisa hannuwan ki,wato ranar da xa a kirani da angon ki. Ki duba kaunar da nake miki ki shawo min kan baba, ina sonki ki huta abar alfaharina*

Ina gama karantawa naji wani hawaye ya xubo min na tabbatar da cewa mijina yana sona idan na bar shi ban yi masa adalci ba.

Wajen innata na koma fadawa nayi jikinta ina kuka, cike da tausayawa ta dube ni, me ke faruwa da ke Niimatullah? cikin kuka na amsa mata da dattijona innah kada ya mutu ta sanadina na samu alhaki, yana cikin damuwa yace na roke ku, ku janye maganar nan dan Allah.

cikin kulawa inna ta dube ni tare da girgixa kanta, kiyi hakuri Niimatullah xan samu malam nayi masa magana nasan xai janye idan yaga halin da kuke ciki,ni kaina bana son auren nan ya tarwatse saboda Alhaji mutumin kirki ne Kuma tsakani da Allah yake sonki kiyi hakuri Insha Allah xai sakko, rarrashina ta rika yi har sai da hankalina ya kwanta.
wayar da ke gefen mu ce tayi ringing, hannu innah tasa ta dauka,sallama tayi cikin kulawa aka amsa mata tare da cewa dan Allah ina neman Niimatullah ne, da sauri innah ta miko min wayar na kara a kunnena tare da yin sallama

muryar matar da take min gyaran jiki naji cikin ladabi na gaida ta, tambayata dalilin da yasa kwana biyu banxo makaranta ba ta fara yi, muryata na hardewa na bata amsa saboda bakin cikin da ke cike a raina, an fasa auren shi yasa na daina xuwa.

A raxane ta tambaye ni me kike fada min haka Niimatullah bana son shirme fa, ina innar ki?cikin kuka nace gata nan kusa da ni, da sauri tace min mika mata wayar xa mu yi magana.

cikin girmamawa take wa innah magana, sannu baba ya gida ya yara, nice matar da nake gyarawa Niimatullah jiki naga kwana biyu bata xo ba shi yasa na kira nasan jiki da jini, sai kuma yanxu da na tambayeta dalilin rashin xuwanta naji tana min wata magana wai an fasa auren nata menene gaskiyar abinda take fada min baba? kana ganin Innata xaka gane tana cikin damuwa don damuwar har a maganarta ta bayyana, bayani ta fara yi mata ba karya Niimatullah ta fada miki ba gaskiya ne abinda ta fada, cike da mamaki take tambayar innata, to menene dalilin hakan baba?

sauke numfashi Innah tayi mun fasa ne saboda muna ganin hakan shi ne abinda xai fi xama Alkhairi a gare mu da kuma ita, mijin Niimatullah yana sonta nasan kema kin san haka, amma kishiyarta ce ba tada kirki xuwanta biyu gidan nan tana ci mana mutunci har tana ikirarin xata hallaka Niimatullah wannan dalilin yasa muka fasa.

cikin nutsuwa malama ta fara yiwa Innah bayani, ina ganin ba haka ya kamata a yi ba baba, tufkar kawai xa a yi hanci, amma batun a fasa ma bai taso ba, saboda xa a cutar da xuciyoyi biyu da suka dade suna son juna, tunda matsalar nan ba daga wajen bawan Allahn take ba bai kamata a fasa ba, saboda idan aka fasa an ji tsoro kuma an bata damar ta cigaba da yin haka nan gaba, ita wacece da xata ce ita kadai xata rayu da mijinta,tunda Allah ya bashi dama kuma yana da ra'ayin kara aure dole yayi, baxai yiwu a ce duk gyaran da muka yi ya tashi a banxa ba baba, gobe insha Allah xan xo tare da Alhajin duk inda matsalar nan take sai an warwareta, godiya Innah tayi mata sannan suka yi sallama.

ba karamin dadi naji ba da jin kalaman malama nasan tana xuwa komai ya xo karshe insha Allah.


*jeeddahtulkhair๐Ÿ˜˜*
[10/18, 11:22 PM] It'z B Y ebrerheem: ๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹
*MATAR DATTIJO*
๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹

*ยฉjeeddah Tijjani*
*Adam*
*(jeeddahtulkhair)*

*follow me on instagram @jeeddahtijjani*

*dedicated to Asma'u sharif Gambo yako (maman Sharifa)*

*Ya Allah ga yar uwata abar alfaharina sister Suhaima M Bello ba tada lafiya, ya Allah ka bata lafiya kasa ya xama kaffara a gareta๐Ÿ‘๐Ÿผ*

21

Baba na dawowa innata ta sanar da shi yadda suka yi da malama, shiru yayi na wani dan lokaci yana naxarin maganarta a hankali ya dago da kansa yana duban mu ni da innah, ni kuwa gabana sai faduwa yake saboda ban san irin amsar da xata fito daga bakin sa ba, cikin nutsuwa ya fara yi mana magana.

ina so ku fahimci wani abu ko kadan ban taba jin na tsani auren Niimatullah da Alhaji ba, hasali ma xan fi kowa farin ciki idan aka ce sun yi aure saboda nasan kyakkyawan hannu na kai ta, baxa mu taba yin da na sani ba, amma abinda xa a duba matsalar matar nan da irin furucin da take yi a kanta, nasan irin wadannan matan ba tun yanxu ba idan suka yi yaki da baki suka ga bai ci ba komawa suke su bi mutum ta kasa, shi yasa bana son abinda xai xo ya tayar mana da hankali muna cikin xaman mu lafiya.

ji nayi kamar nayi kuka wata sabuwar soyayyar Dattijona ce take dada bijiro min ban ki a ce na tashi na koma gidansa da rayuwa ba, duk wata matsala da baba yake hango min ni a yanxu bana ganinta,saboda ko kadan Allah ya cire min tsoron matarsa kuma ina jin xan iya yin fito na fito da ita ba tare da wata fargaba ba, nasan nayi nisa a xuciyar mijina wanda bata isa ta kamo ko rabin son da yake min ba, kaina a kasa na fara yiwa baba magana.

ni dai baba idan da yadda xa a yi dan Allah ka bari na aure shi wallahi ina son mijina, cike da mamaki innah ta dube ni, inye Niimatullahi har kin san dadin mijinki, lallai yaran xamani sai dai a barku kawai, shi kuwa baba kallona kawai yake y rike baki Innah ce take ta bayani.

malam tunda har Niimatullah ta furta mana tana son mijinta ina ganin ba mu da wani xabi wanda ya wuce mu tattara ta mu kai ta dakinsa, girgixa kai baba yayi, nima tunanin da nake yi kenan shi yasa kika ga na kasa magana, amma xan nemi Alhaji yaxo ya tattara ta su tafi

kuka na fara yi cike da shagwaba nake magana a tattara ni fa kace baba sai kace wata kayan wanki ni Allah sai ma na fasa auren, murmushi baba yayi ko kin fasa sai an kai ki tunda ina yi miki gata har kina cewa kina son mijinki ni ba ruwana dole sai kin tare, kuka na fara yi a kan ni baxan tare ba na fasa tashi baba yayi ya bar mana wajen, kan cinyar innah na fada ina cigaba da kukana.

Washe gari Dattijo da malamar mu suka iso gidan mu a tsakar gida suka same ni ina hada kwanuka, sauri nayi na sanya hijabina saboda baxan iya jure kallon da yake bina da shi ba, a dakin innah nayi musu shimfida, shiga malama tayi ta xauna shi kuwa dattijona a tsakar gida ya tsaya yana cigaba da kare min kallo, cike da tsiwa nake masa magana.

menene ka tsura min ido kamar baka saba ganina ba, murmushi yayi tare da matsowa daf da ni riko hannuna yayi cikin sigar shagwaba yake min magana shi ne don kin ganni kike wani saka hijabi ko,naga dai komai na jikin ki mallakina ne to me xaki boye min?

Harar shi nayi tabdi wallahi ba mallakinka bane nawa ne ko innah xa a tambaya tasan da haka, murmushi yayi gami da jan kumatuna kina da dabaru na sanya ni murmushi my Niimatullah ko da a ce ina cikin fushi idan kika yi magana sai naji wni snyi a raina,kin zamo wata ta daban a gare ni, shi yasa ina ganin ki dukkan shaukina yake tashi,bana gane cewa ni namiji ne sai ina tare da ke, don haka ki daina tuhumata idan ina kallon ki, tunda kina sona ko matar dattijo?a hankali na gyada kaina alamar eh, murmushi yayi sannan ya cigaba da magana nasan da cewa tunanin ki a kullum bai wuce neman hanyar da xaki inganta rayuwata ba ki bani farin ciki mara misaltuwa,wannan dalilin yasa na sadaukar miki da soyayyata kuma nake fatan kasancewa da ke har abada my Ni'ima, baxan iya daina kallonki da begenki ba har sai ranar da numfashina ya kare

duk maganganun nan da yake yi kaina na kasa saboda kunyarsa gaba daya ta kama ni,maganar da innah tayi masa ne yasa ya dawo hankalinsa, a sanyaye ya cika ni tare da sumbatar hannuna, sai na fito my Niimatullah
na sake ki ne ba dan na koshi da ke ba,sai dan xuwa na samo mana mafitar yadda xamu rayu da juna har abada, sakina yayi na koma gefe na xauna.

Tattaunawa suka fara yi a kan maganar tarewa ta a gidan dattijo, kwala min kira innah tayi da hanxari na karasa dakin cikin ladabi na tsugunna tare da cewa gani innah, cike da kulawa ta dube ni kira mana malam a waje, takalmana na saka ina fita naci sa'a na same shi, yana shigowa malama ta fara magana.

mun xo ne baba a kan maganar tarewar yarinyar nan, naji ana cewa kun fasa shi ne naxo na baku hakuri a kan bai dace a yi saurin yanke hukunci haka ba,tunda dai suna son junansu, kuma maganar kishiya baxa ta tsoratar da mu ba tunda yarinyar nan mijinta na sonta duk wani abu da xai cutar da ita xai yi kokarin kawar mata da shi.

gyara xama baba yayi, ni dama ban xafafa ba Hajiya fatana dama yaxo ya fada mana irin matakin da xai dauka a gidan sa saboda ina jin tsoran abinda xai je ya dawo ko ba haka ba.

cike da xumudi dattijo ya fara magana, wallahi baba babu wata matsala da xa a samu duk wani matakin da ya kamata na dauka naje na dauka, na yi mata magana a kan ba ita ba Niimatullah idan kuma ta cigaba xa tayi a bakin aurenta.

saurin dakatar da shi baba yayi, a'a ba a haka Alhaji kada auren nan yayi sanadin rabuwar ka da uwar yayanka idan kayi haka baka yi adalci ba sannan duniya xata xage ka mu ma xata xage ma, a xaci don ka auri jikar mu ne kayi mata wannan wulakancin, baxa a duba girman laifin da tayi ba namu xa a gani, don haka kada ka fara aikata haka, kawai kai dai kayi niyyar tsayar da adalci a gidanka sai kaga Allah ya taimake ka amma batun kace xaka saketa ma bai taso ba.

cike da ladabi dattijo ya amsa da insha Allah xan kokarta baba, na gode da wannan shawarar da ka bani, haka suka cigaba da tattaunawa daga karshe aka tsayar da lokacin tarewar mu nan da sati biyu masu xuwa, ba karamin dadi dattijo yaji ba, nima farin cikin ne ya kama ni saboda duk kusan hirar da suke yi a kunnena ake yinta.

tashi suka yi xasu tafi, a tsakar gida dai suka kara tarar da ni, kirana malama tayi ta fara yi min nasiha.

kinga yanxu tarewar ki ta matso don haka gyaran jiki xamu rika yinsa ba dare ba rana idan kuma baki tsaya an gyara ki ba kin xauna kina gaddama kishiya ta raina ki,ni ba ruwana don haka yanxu duk abubuwan da na baki ki mayar da hankali ki shanye, idan kin xo gobe xan baki wasu ki kara sha,so nake ki rikita mijin nan naki ya kasa gane hanyar garin su, dariya muka yi gaba daya har mun yi sallama ta tafi ta dawo ta kira ni, kije mijinki na son magana da ke, makale kafada nayi ni Allah bana son xuwa, hararata tayi kinga irin abinda yake hada ni da ke ko wuce mu je nace miki.

wucewa nayi na tafi a cikin mota na same shi don haka ya bude min motar na shiga tare da rufo murfun motar.



*masu karatu ku nemi littafin kalubale na juwaira domin fadakarwa nishadantarwa da kuma wa'axantarwa kada ku bari a baku labari*


*jeeddahtulkhair๐Ÿ˜˜*
[10/18, 11:22 PM] It'z B Y ebrerheem: ๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹
*MATAR DATTIJO*
๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹

*ยฉjeeddah Tijjani*
*Adam*
*(jeeddahtulkhair)*

*follow me on instagram @jeeddahtijjani*

*dedicated to Salma Nura*

24


Washe gari ma sai da aka sake gyara ni sosai kyawuna ya kara fita duk inda ka kalle ni sau daya sai kso ka kara kallona, shi kuwa dattijona kullum yana kan hanyar xuwa ganina, a lokuta da dama idan yaxo da kyar yake tafiya, saboda yadda yake yaba kyauna kullum da rigima muke rabuwa.

yau da sanyin safiya na shirya don xuwan wajen kunshi, soro na fita na xauna na hada kaina da gwiwa saboda kaina yau ya dau caji, ina jin ciwo sosai a raina idan na tuna gobe xan bar gida, wasu xafafan hawaye ne suka rika kwarara a fuskata tambayar kaina na shiga me yasa har na amince da auren dattijo gashi nan yana son raba ni da rayuwar gidan innata, ji nayi an kira sunana a hankali na dago kaina, dattijona na gani tsaye yana min murmushi fuskar sa cike da damuwa yake tambayata lafiya kike kuka my Niimatullah?lumshe idanuna nayi cikin kuka na bashi amsa, ina ji a raina kawai xan fasa auren nan bana son rabuwa da innata, rarrashina ya shiga yi gami da kawo min hadisan da suke magana a kan muhimmancin aure a haka har hankalina ya kwanta xuciyata tayi sanyi.

Hannu yasa ya tayar da ni tsaye, ina rungume a jikinsa har muka isa bakin mota, bude min murfin motar yayi na fara shiga sannan ya shigo, kallona ya rika yi a xahiri naji yana godiya ga Allah,Allah na gode maka da wannan babbar kyautar da ka bani Allah ka bani ikon riketa amana, shafawa yayi sannan ya dube ni yana min murmushi

Kece kaddarar da na jima ina tsimayin tarar da ita a rayuwata, zan kasance a duk inda kike Niimatullah,zan tsaya a duk inda kika tsayar da ni. Ina sonki, adadin son da kalmomi ba zasu iya siffantawa ba,
xan kasance mai
baki kulawa da kuma kaucewa dukkan abinda zai sanya ki a damuwa fatana ki tabbata a cikin farin ciki,ban son irin dadin da xan ji ba idan na ganki gobe a dakina, fatana dai Allah ya bamu xaman lafiya.

amsa masa nayi da ameen muna xuwa ya sauke ni a kofar gidan,kudi ya dakko ya bani, cike da shagwaba nace masa baxan karba ba, dago fuskata yayi yana min murmushi ki karba my Niimatullah kinga ba a yin kunshi kyauta, langwabar da kaina nayi to ka rage kudaden sun yi yawa, murmushi yayi tare da cewa ban san me yasa kike tausayina ba Niimatullah, kaina a kasa na amsa masa saboda ka xama mijina kuma innah ta fada min tausayin miji abu ne mai kyau, girgixa kai yayi yana murmushi gaskiya innah ta iya tarbiyya Allah ya saka mata da aljannah da take kokarin saita min uwar yayana. fitowa nayi na shiga gidan kunshin.

ba tare da bata lokaci ba aka fara yi min, gaskiya kunshin yayi kyau domin ya dace da kafata sosai, da misalin karfe hudu ya iso daukana, tun daga nesa yake min murmushi jikina a sanyaye na karaso wajen sa tare da cewa an gama, shafa fuskarsa yayi tare da cewa miko min hannun na gani, makale kafadata nayi a'a baxan bayar ba, jan hancina yayi me yasa kike min rowar jikinki kin xama tawa fa Niimatullah babu abinda yayi saura. cike da tsiwa nace Allah da akwai abinda yayi saura tunda saura kwana daya naje gidan ka, murmushi yayi tare da jan hannuna to naji taho mu tafi bana son wannan rigimar taki.

A kofar gida ya ajiye ni ya wuce gidansa, ina shiga gida nayi sallah na fada bandaki nayi wanka sannan na koma dakin innah na kwanta kasancewar yanxu bana son hayaniya nafi son na kebe ni kaina na rika tunanina, yau ko baccin kirki ban samu nayi ba saboda bakin cikin xan bar gidan innah cikin dare na tashi ina kuka ina bankwana da gadon da nake kwana.

rana bata karya sai dai uwar diya taji kunya, A yau lahadi 14-10-2018 ta kama ita ce ranar da xa a kaini dakina, da kyar aka yago ni nayi wanka saboda duk wata gwiwa ta jikina tayi sanyi, yan uwa da abokan arxiki daga gurare daba-daban sun halarci bikina, duk wanda yaji labarin irin son da dattijo ke min sai yayi mana fatan alkhairi da samun xuri'a ta gari, anci an sha duk abincin da aka ci a wajen dattijo ne yasa aka kawo mana daga 10 to 10 restaurant, an yi komai cikin rufin asiri.

xaune nake a daki na xuba uban tagumi ina tunani, cikin nutsuwa aka yi sallama a hankali na dago don ganin mai sallamar daya daga cikin kannen mahaifiyata ne, gefena ta samu ta xauna, tashi ki kintsa Niimatullah an kawo motocin tafiya gidan ki, a xabure na dago na kalleta, tun yanxu xa a tafi ni gaskiya yayi wuri a bari sai an yi sallar magariba, cikin kulawa take min magana ki tashi mu je ga ruwa can an kai miki bandaki gara ki shirya da wuri yanxu xaki ga magaribar tayi, hawaye ne suka cika idona cikin kuka nake mata magana, wai dama da gaske ne sai an kai ni gidan mutumin nan Aunty, ni wlh ba inda xan je. lallaba ni ta shiga yi har sai da na tashi na tafi ina wankan ina kuka.

Bayan na kammala na fito na sanya kayana, wajen baba aka kaini inda ya fara yi min nasihohi masu ratsa jiki a kan biyayyar aure da kuma kyautatawa miji bayan ya gama aka kaini wajen innah don sallama da ita da kuma yi min nasiha.

muna hada ido da ita ta fara kuka da sauri na fada jikinta muka rungume juna, cikin kukan take min nasiha ki bi mijinki sau da kafa Niimatullah, duk abinda yace kiyi masa kiyi banda gaddama, sannan kuma ki xama mai hakuri da kau da kai, kada kice duk abinda kika gani sakin yi magana, kiji ki qi ji, ki gani ki qi gani, ki xama mace mai kawaici da hakuri, kada ki bari mijinki yaji wani abu mara dadi daga gare ki, ki kiyaye masa ganinsa da jinsa da hancinsa, abinda nake nufi da ki kiyaye masa ganinsa shi ne kada ki bari yaga wani abu na aibu a gare ki, abinda nake nufi da ki kula masa da jinsa,kada ki bari ki fada masa wata magana mara dadi da har xata bata masa ransa, duk abinda xai ji daga gare ki ya xama mai dadi ne, abinda nake nufi da ki kiyaye masa hancinsa kada ki bari yaji wani wri daga gare ki kullum ki kasance cikin tsafta da kamshi ki kula da tsaftar hakoran ki, Allah ya baki sa'a yasa kin shiga a sa'a Allah ya kare ki daga dukkan sharri yasa ki xama tsohuwar gidansa.

kuka sosai muka rika yi ni da innah da kyar aka raba ni da ita aka saka ni a mota, gidansa da ke unguwar bompai aka kaini bangare biyu ne a gidan, don haka bangaren kishiyata aka fara kaini inda aka damka mata amanata, a wulakance ta karbe mu amma duk da haka ba wanda ya kula da abinda tayi mana.

kai tsaye bangare na aka wuce da ni, ina shiga na godewa Allah da irin namijin kokarin da dattijona yayi min,ko iyayena masu hali ne iya abinda xa a saka min kenan a dakina komai yaji, daya daga cikin dakunana aka shigar da ni inda aka xaunar da ni bisa gado, bayan an yi addu'a an shafa kowa ya watse ya bar ni ni kadai, kuka na ne ya tsananta na rika kiran innata, tashi nayi na fara kewaye gidan dakuna ne guda uku gaba duyan su an saka masu kayan gado na alfarma, kujeru na ma duk masu kyau ne wadanda aka yi musu ado da yadi launin orange sai kuma pillow din su da suka kasance launin baki, kitchen dina ma cike yake da kaya gwanin sha'awa, taku naji alamar xa a shigo wajena da sauri na koma gado na nade kaina a mayafi.



*jeeddahtulkhairi๐Ÿ˜˜*
[10/18, 11:22 PM] It'z B Y ebrerheem: ๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹
*MATAR DATTIJO*
๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹

*ยฉjeeddah Tijjani*
*Adam*
*(jeeddahtulkhair)*

*follow me on instagram @jeeddahtijjani*

*dedicated to Ummy xie ina godiya da abin arzikin da kika yi min*


23

kwanci tashi asarar rai, komai aka sawa rana wata rana sai yace, yau ya rage saura kwana uku na tare a gidan dattijona, tun safe na tashi ina kukan rabuwa da innata nice har da su birgima, wani irin kaunar gida ne naji ya kamani sai na tsinci

Please Login or Register in order to submit comment