Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

rarrashina, kiyi hakuri Niimatullah kin kusa samun lafiya kin ji, kuka na cigaba da yi innah kullum ji nake ciwon nan yana kara yin gaba,har yanxu bana samun sauki, ko da yaushe a cikin ciwon jiki nake shi ma dattijo har tausayi yake bani saboda kullum a cikin aikin yi min tausa yake. cike da kulawa ta dube ni

wai menene ma abinda yake damun ki haka? cikin kuka na amsa mata ciwon ciki da baya da xaxxabi sannan ga kasala kuma ina yawan jin yunwa sannan ina jin abu na min yawo a cikina kamar macijin ciki.

murmushi innah tayi kwarai kuwa babban macijin ciki ne da ke Niimatullah, xaro idanu nayi wane iri ne babban innah, ni dai Allah ku kai ni asibiti a raba ni da shi, dafa kafadata tayi ki kwantar da hankalin ki babban abin alkhairi ne ya same mu Allah ya axurta ki da juna biyu, rufe fuskata nayi saboda kunya shi kuwa dattijo sai murna yake.

Alhamdulillah Allah ya cika min burina ya bani abinda na dade ina nema, ashe ajiyata na da rabon xama a jikin ki Niimatullah Allah ya inganta ya sauke ki lafiya, ko kunyar innah bai ji ba ya matso kusa dani ya fara shafa cikin yana yi masa addu'a.

cike da soyayya ya dube ni, gobe xamu je asibiti don a kara tabbatar mana da lafiyar dan cikin mu.

A ranar naga tarairaiya kala-kala ko tsinke baya bari ya taba ni saboda soyayya.

*follow me on wattpad @jeeddahtulkhaeer Tijj*

*jeeddahtulkhair😘*πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹
*MATAR DATTIJO*
πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹

*Β©jeeddah Tijjani*
*Adam*
*(jeeddahtulkhair)*

*follow me on instagram @jeeddahtijjani*


*wannan shafin gaba daya sadaukarwa ne ga takwarata Khairaty marubuciyar 🌻🌸 YA SHEIKH 🌸🌻ana mugun tare*

37

jikin innah na koma na narke ina mata shagwaba, cikin marairacewa nace innah ni fa har yanxu ina dan jin motsin nan dan Allah ki bani magani na daina ji, cike da mamaki ta dago ta dube ni, kai Niimatullahi kiji tsoron Allah cikin da bai wuce sati biyu ba har kin fara jin motsinsa bana son raki fa, tun yanxu kin fara wannan tabarar ina kuma ga cikin ya girma,wannan ranar haihuwar ki da kallo sai an taro jama'a sun daddanne mana ke, murmushi dattijona yayi tare da cewa to ai don farin shiga ce shi yasa take jin haka innah, kuma kinga tana da kananan shekaru.

kallona tayi ta tabe baki, wallahi har da raki Alhaji amma ai cikin nan bai ci ya fara motsi ba kawai dai shirmenta ne, kaima kuma kana taya ta shi yasa take jin dadi, murmushi yayi kawai fita yayi ya barmu tare da innah ina ta mata shagwaba, bai dawo ba sai da wajen misalin karfe biyu na rana, da sallama ya shigo dakin mu ya ajiye mana ledodi kayan kwadayi ya siyo min da yawa, a gaban innah ya ajiye ledar kayan,cike da fara'a ta dube shi lallai Alhaji kai kake shagwaba Niimatullah shi yasa ma take yin wata tabarar, hannu nasa na dauki ice cream na fara sha, bayan na gama ya sake dawowa cike da girmamawa ya dubi innah, yanxu xamu tafi asibiti innah don a tabbatar da lafiyarta da ta abinda ke cikinta, tashi nayi na dakko mayafina muka nufi asibiti, ba tare da bata lokaci ba aka fara duba ni aka tabbatar da ina dauke da ciki na sati biyu, nan ma dai murna dattijo ya rika kamar xai hadiye ni saboda soyayya.

Gidan innah muka fara xuwa muka ajiyeta sannan muka wuce gidan mu, kallo daya xaka yiwa dattijo ka gane yana cikin farin ciki, bakinsa yaki rufuwa sai dariya yake yi, duk bayan minti biyu sai ya shafa cikina yayi godiya ga Allah.

muna isa gida ya dauke ni cak ya shigar da ni daki, saboda yace babu abinda xan rika yi da kaina indai yana raye a doran kasa, a kan gado ya dire ni yana bina da wani kallon soyayya, cikin jin kunya na sunkuyar da kaina ina masa magana, dama haka ciki yake da wahala dattijona, shi yasa tun farko nace kada ka taba ni gashi nan ka janyo min aiki, jawo ni yayi ya manna da kirjinsa cikin salon soyayya yake min magana, wannan ita ce albarkar auren Niimatullah ke kan ki idan kika xauna babu haihuwa baxa ki ji dadi ba, abin duniya damunki xai yi amma idan da dan babynki ko kallon shi kika yi sai kin ji sanyi a ranki, kuma na kara sonki saboda ajiyata ta kasance jikin ki,fatana dai ki kula min da kanki duk wani abu da xai cutar da ke kada ki rika yi, kuma daga yau na hana ki yin duk wasu aikace-aikacen gida xan samo miki mai aiki ta rika taya ki.

da sauri na dakatar da shi, a'a ka bar shi dattijona nayi komai da kaina, naji mutane na cewa masu aikin nan suna da matsala wasu munafunci wasu sata, kuma kaga bani kadai ce a gidan ba kada ta rika hada ni rigima da maman munir, ka bari nayi komai da kaina ko kuma ka rika taya ni abinda xaka iya, sauke ajiyar xuciya yayi gaskiya kin yi tunani mai kyau Niimatullah kinga ni da duk ban yi wannan tunanin ba, na hakura baxan dakkota ba.

Daukar waya yayi ya kira abokansa yana ta fada musu na samu ciki, ni abin ma har kunya yake bani sai kace a kaina ya fara samun haihuwa, dukan su sun taya shi murna tare da yi masa fatan alkhairi, yau ma a kan kirjinsa nayi bacci yana shafa dan cikinsa, washe gari shi yayi min wanka ya kintsa min gida ya hada min breakfast, xaunar da ni yayi a cinyarsa yana kallona, cike da ladabi na gaida shi, cikin kulawa ya amsa min da lafiya lau amaryar dattijo ya kwanan babyna?

sunkuyar da kai nayi saboda yanxu wani girmansa nake gani da kuma jin kunyarsa, kara kunnensa yayi a dai-dai cikina yana magana, ina kwana my baby da fatan ka tashi lafiya, kana dai cin abinci ko ya rigima?murmushi nayi Allah baka rabo da abin dariya dattijona dubi fa sai kace da mutum kake magana, dagowa yayi yana kallona to da wa nake magana idan ba mutum ba? kuma ya fada min cewa bakya cin abinci don haka duk abincin da na xubo miki yanxu sai kin cinye, don ina son naga babyna ya fito duniya da kuxari.

Bata fuska nayi xan yi kuka, Allah naci da yawa dattijona idan ka takura min na kara xan iya yin amai, kayi hakuri ka bari naci anjima.

daukan kwanon yayi ya mayar kitchen sannan ya dawo yasa cikina a gaba yana kallo yana murmushi, ji muka yi an danno kai cikin dakinmu gaba daya muka mayar da hankali don ganin abinda ke faruwa, ko ban fada muku ba nasan kun gane wacce ta shigo.

tsaye take a kan mu tana wani xare-xaren idanu, jikina gaba daya yayi sanyi saboda masifarta ta fara daga min hankalina, ita mace ce da bata gudun tashin hankali kuma bata gajiya da masifa, cikin tsawa dattijo ya fara yi mata magana, me kuma kika xo kiyi?me yasa ke bakya jin magana ne bakya gudun abinda xai kawo mana bacin rai, tun wuri ki fice kafin naci mutuncin ki.

Turo dankwalinta tayi ta gyara tsayuwa, bana gudun tashin hankali kuma indai a kan rashin adalcinka ne baxan taba gudun shi ba, yanxun nan nake samun labarin cewa wannan jahilar amaryar taka ta samu ciki shi ne don cin amana baka fada min ba a tunaninka kuma baxan samu labari ba, to wallahi baxa ta sabu ba sai an xubar da shi don baxai yiwu a haifawa yayana dan uba ba, idan kuma baka xubar ba ni xan xubar da kaina, shi yasa ashe kaxo ka nace mata saboda ka dura mata ciki ko?to tayi ciki hankalinka ya kwanta amma ka sani kamar an xubar da shi ne.

cikin tashin hankali ya dube ta maryam ba ki da hankali ne kike furta wadannan maganganun, ina tunaninki yake tafiya yaushe xaki san ciwon kan ki, ki fita daga wadannan abubuwan da basu shafe ki ba, wallahi xamu sa kafar wando daya da ke a gidan nan idan kika ce da wannan cikin xaki rika kishi, don xai iya sanadin mutuwar auren ki.

Harar shi tayi, tunda an yi maka asiri komai ma xaka iya fada, wallahi indai kana son xaman lafiya a xubar da shi idan ba haka ba kuma ka siya tashin hankali da kudinka, tana gama fada ta fice ta barshi tsaye yana naxarin maganganunta, ni kuwa ina kwance duk maganganun da take yi a kunnena amma na yi kamar ban ji ba saboda bana son na saka damuwarta a raina ya haifar min da wata matsalar.

A sanyaye ya dawo ya xauna ya kifa kansa a hannun kujera, cikin sassanyar murya na kira sunansa, dattijona! a hankali ya dago idanunsa wadanda suka yi ja saboda takaici, cikin tausasa harshe na fara yi masa magana.

Kayi hakuri mijina kada wadannan maganganun da tayi su sa gwiwarka tayi sanyi ko kuma su bata maka rai, indai wannan cikin rabon mu ne babu abinda ta isa ta hana sai abinda Allah ya kaddara mana, don haka ka manta da ita ka dawo cikin farin cikin ka.

Girgixa kai yayi haka ne Niimatullah, amma ina ji a raina kawai xan rabu da maryam saboda tunda na aureta ban taba samun farin ciki ba kullum kokari take taga na fada cikin matsala, don haka xan sauwake mata kawai yana gama fada ya mike.

Da sauri naja rigarsa idanuna cike da hawaye na dube shi, dan Allah kayi hakuri kada ka sake ta saboda ni, kayi mata afuwa ko don dadewar da ku ka yi tare da yayan da ta haifa maka, wallahi ina da tabbacin idan ka saketa abinda xai faru sai ya fi wannan kuma duniya xata xage ni tace ni nayi wani abin da har ka saketa,kayi hakuri ka rufa min asiri ka barta ta cigaba da xama da yayanata.

A sanyaye ya dawo ya xauna tare da kwantar da kaina a cinyarsa, na kyaleta albarkacin ki Niimatullah amma wallahi matukar ta yiwa cikin nan wani abu sai ta gane kuskurenta, tunda naga alamar bata son xaman lafiya.


mantar da shi tunaninta nayi, saboda bana son damuwarta ta hana shi walwala a mintuna kadan ya manta da ita muka cigaba da soyayyar mu.

*follow me on wattpad @jeeddahtulkheer*

*jeeddahtulkhair😘*πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹
*MATAR DATTIJO*
πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹

*Β©jeeddah Tijjani*
*Adam*
*(jeeddahtulkhair)*

*follow me on instagram @jeeddahtijjani*

*dedicated to Aysha Abdullahi yola (Aunty Admin mai kan doya😜)*

38

Tausa ya cigaba da yi min yana tambayata irin shirye-shiryen da ya kamata mu fara yi don tarbar babyn da xai xo, biro da takarda ya dakko ya fara rubuta dukkan abinda ya kamata ya siya, don gudun kada a manta da wasu abubuwan, dora hannuna nayi a wuyan shi ina yi masa godiya, dattijona ba karamin namijin kokari kake yi a kaina da babyn nan ba Allah ya taimake ka ya saka maka da alkhairi ni kuma Allah ya bani ikon yi maka biyayya. fuskarsa a sake ya amsa da ameen, har na kosa ranar taxo ki ga yadda xan baki kulawa da jaririn mu, nasan innah ma nan xata dawo ta cigaba da kulawa da ke, dagowa nayi ina murmushi Allah Baba baxai taba bari ta dawo ba sai dai ni a mayar da ni gidan na xauna idan nayi arba'in na dawo dama abinda ake yi kenan.

murmushi yayi tare da hararata ba inda xaki je kina cikin gidan nan, saboda ina son na rika lekowa ina ganin ki, amma idan kika koma gidan innah ai akwai matsala xan iya dawowa gidan da kwana gaba daya, da sauri na dago ina kallon shi, haba dai ai sai a yi da mu a ce ka xama mara kunya, lumshe idanu yayi, to menene don an yi da mu ai matata ce babu abinda maganar mutane xata yi min indai a kanki ne, shiru nayi na kyale shi saboda naga da gaske yake tsaf xai iya bina.

wayar da ke hannun shi ce tayi ringing, yana dubawa yaga number abokinsa ce, fuskarsa a sake ya dauki wayar tare da yin sallama, bayan sun gaisa yake shaida masa cewa yanxu xai xo wajensa, cike da farin ciki ya ajiye wayar ya juyo gare ni, kinga yanxu ma abokina xai xo ya ganki saboda ya san yadda nake ji da cikin nan.

rufe fuskata nayi saboda kunya, Allah ka iya tabara dattijona sai kace yau aka fara samun ciki a gidanka, jawo ni yayi jikinsa yana kallon fuskata kamar yau aka fara samu mana,tunda yau shekarata kusan ashirin da biyar rabon da a haihu a gidana, ni har na fidda rai ma xa a kara samun baby a gidan nan shi yasa kika ga ina rawar kafa, ko bakya so na rika yi?kaina a kasa na amsa da ina so mana dattijona.

Dada manna ni da jikinsa yayi yana murmushi yauwa amaryar dattijo ai nasan kina son kulawar mijinki, sake kiran wayar aka yi don haka yasa hannu ya dauka, sanar masa yayi cewa ya iso, don haka na tashi na shiga daki na sako hijab sannan na dawo na xauna, shigo da shi yayi parlour ya xauna, cike da ladabi na gaida shi, tunda ya shigo yake bin dattijo da kallo yana girgixa kai saboda yaga komai shi ya dakko ya kawo masa ni kuma ina xaune, yana dawowa ya xauna ya mika masa hannu suka gaisa sannan suka dan taba hira.

gyaran murya yayi tare da hade fuska sannan ya fara magana, wato naxo ne nayi maka magana a kan abubuwan da suke faruwa a gidan nan, da sauri dattijo ya dube shi wane abubuwa ne kuma suke faruwa?

murmushi mutumin yayi tare da cewa kwantar da hankalinka mana Alhaji menene na firgita haka, abin fa ba fada bane gyara naxo yi, kuma da naxo nima na tabbatar da abinda aka fada min.

Bata fuska dattijona yayi, okay ina sauraren ka, dafa kafadarsa yayi kayi hakuri Alhaji naga kamar ranka ya baci ka tsaya ka saurare ni, dan sakin fuskarsa kadan yayi tare da cewa, a'a ba komai kada ka damu cigaba da maganarka ina jinka.

gyara xama yayi, daxu ne Hajiya maryam matarka ta kira ni ta fada min matsalolin da take fuskanta tun lokacin da ka yi mata amarya, tace gaba daya ka kasa tsayar da adalci a tsakanin su, baka kulata baka kwana a dakinta duk wasu hakkonkinta kasa kafa ka shure, shi yasa naxo don nayi maka magana, kuma nima da naxo naga hakan domin komai kai kake yi ita kuma yarinyar nan na xaune tana xaro idanu, da sauri dattijo ya dakatar da shi.

Alhaji Hamxa sulhu ka xo yi ko sa min idanu a harkar gidana?naga ka fita daga maudu'in da muke tattaunawa, murmushi yayi tare da dafa kafadar dattijo, kayi hakuri kasan ita gaskiya daci ne da ita.

ni kuwa ina gefe na kifa kaina a kujera, xuciyata sai tafasa take yi wato yanxu har sharrinta ya kai ta rika yawo da ni a gari tana cewa na hana a yi mata adalci, wasu xafafan hawaye ne suka rika xubo min a idona.

magana dattijo ya fara yi duk abubuwan da ta fada maka xan iya cewa karya ne, domin ina kokarin bata hakkinta, ba nida burin danne wani hakki nata, sai dai a kullum naje wajenta da xagi da cin mutunci take rako ni, wannan dalilin yasa nayi xuciya na kyaleta saboda baxan rika bin ta ba kamar uwata, ko auren nan da kaga nayi ita ce sila da tana kulawa da ni babu abinda xai sa na kara aure.

Girgixa kai Alhaji Hamxa yayi gaskiya idan haka ne maryam bata kyauta ba,amma ni bata fada min abinda take yi kenan ba, shi yasa naxo da xafina ina maka fada, don haka yanxu kirata taxo nan a ji ta bakinta.

Dakatar da shi dattijo yayi a'a kyaleta bana so taxo nan saboda ba bangarenta bane, na hanata xuwa ne saboda kullum taxo sai tayi tashin hankali kuma ta nemi ta daki yarinyar mutane, taso mu je a yi maganar a wajenta, tashi suka yi suka fita.

Da sallama suka shiga wajenta, ta xaci dattijo ne shi kadai don haka ta watsa masa wata harara tare da juyar da kanta gefe guda, sai da taji maganar Alhaji Hamxa sannan ta dago tana borin kunya ta gaida su, murmushi dattijo yayi kaga irin abinda nake fada maka ka fara gani da idonka ko, dukkan abinda ke faruwa ita ta jawowa kanta babu wanda ya jawo mata.

cikin tsawa ta fara yi masa, kaga malam kada ka fara xuwa ka tayar min da hankali ina xaune lafiya, ka koma wajen amaryarka da ta shanye ka ta gama da kai,kayi mata amma ni baka isa kaxo kace xaka taka ni har cikin dakina ba, Alhaji wannan abokin naka ba adali bane kuma baya tsayar da adalci a gidansa, yanxu ma don ya ganka ne ya shigo wajena, saboda kada ka dora masa laifi, amma da baka xo ba sai nayi sati banga kyallinsa ba.

murmushi dattijo yayi kaga irin rashin da'ar tata da nake fada maka ko?
Girgixa kai Alhaji Hamxa yayi kwarai kuwa nima na tabbatar da hakan yanxu, cikin tausasa murya ya fara yi mata magana.

gaskiya Hajiya idan haka kike gudanar da rayuwar auren ki, sam bakya kyautawa kuma bakya kyautawa mijinki ke da xaki rika yiwa wasu fada a kan irin wannan amma a ce da kanki kike aikatawa wannan wace irin rayuwa ce, kamata yayi ki bawa mijinki hadin kai wajen tsayar da adalci a tsakanin ku, amma kya xauna Kullum ku rika rigima, baxa ku xauna ku fuskanci juna ba.

yatsina fuska tayi, wallahi wannan ba wani fahimtar juna da xa mu yi da shi, duk iya biyayyar da nake yi masa amma a ce ya rasa da sakamakon da xai saka min da shi sai na kishiya,ai bai min adalci ba.

Dakatar da ita Alhaji Hamxa yayi, kishiyar nan fa yar uwa ce a gare ki bai kamata ki riketa abokiyar gaba ba, ga shi da dukkan alamu yarinyar tana da saukin kai kuma ba tada hayaniya da kin kwantar da hankalin ki xaman lafiya xa ku yi, amma gaba daya kin tada hankali kin hana kan ki sukuni a kan yarinyar da kin haifeta.

kallon dattijo tayi tana hararar shi tare da mikewa tsaye, indai don na sassautawa yarinyar nan ne mu xauna lafiya wallahi baxai taba yiwuwa ba, kuna ma batawa kan ku lokaci ne, tafiya tayi ta bar su xaune.

cike da mamaki Alhaji Hamxa ya dubi dattijo, gaskiya kana namijin kokarin xama da ita, don da ni ne tuni na sallameta baxan iya xama da matar da bata ganin mutuncina ba, ita ko koyi da kawayenta bata yi nasan dai ba haka suke xaune da maxajensu ba, gashi wani abin ban haushi bata jin nasiha, lumshe ido dattijo yayi kaga dai abinda kake xargi ko? to don haka duk abinda ke faruwa ita ta jawowa kanta.

tashi suka yi suka bar dakin har bakin mota ya raka shi sannan suka yi sallama.

*follow me on wattpad @jeeddahtulkhaeer Tijj*


*jeeddahtulkhair😘*πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹
*MATAR DATTIJO*
πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹

*jeeddah Tijjani*
*Adam*
*(jeeddahtulkhair)*

*follow me on instagram @jeeddahtijjani*

*dedicated to Zee fulani*

*Bansan da irin bakin da xan gode miki ba aminyata ta kaina maijidda Bello naga abin arxiki na gode Allah ya bar xumunci*


39

A hankali ya rika jan kafa har ya isa wajen Niimatullah, duk ransa a bace yake saboda wulakancin da matarsa tayi masa a gaban abokinsa, nadama ya rika yi a ransa ba yasan abinda xata y masa kenan da bai bari sun je wajenta ba.

A sanyaye ya karaso wajena cikin sassanyar murya ya kira sunana, ni kuwa banda aikin kuka babu abinda nake yi, a hankali yasa hannu ya dago kaina ganin yadda fuskata ta jike da hawaye ne yasa hankalinsa ya tashi cike da damuwa ya dube ni, niimatullah kin manta akwai jaririn cikina a jikin ki kike kuka, baki san kuka yana illata mai ciki ba hannu yasa ya fara share min hawayen tare da yi min magana.

Kiyi hakuri amaryar dattijo Alhaji Hamza bai fahimci halin ki ba ne shi yasa ya fadi wannan maganar a kan ki, amma ko yanxu sai da ya Kara yabon ki ya kuma tabbatar min da cewa nafi kowane namiji sa'ar abokiyar rayuwa saboda yadda kike kula da ni kuma kike gudun bacin raina, kiyi hakuri ki daina kuka wallahi ina matukar kaunar ki.

Hawaye ya shiga share min, sai da ya tabbatar da hankalina ya kwanta sannan ya kyale ni, a ranar cikin farin ciki muka kasance.

Washe gari da sassafe dattijona ya fita Office, kasancewar yana da aiki da yawa a office, bayan na gyara gida na fito parlour na kunna TV ina sauraren wa'azi a tashar sunnah TV, turo kofar dakina aka yi da sallama aka shigo nayi mamakin jin sallamar saboda ban taba xaton wadda ta shigo xa tayi min sallama ba, cike da mamaki na dubeta tare da saurin mikewa tsaye don ban san da abinda taxo min ba.

cikin sakin fuska ta karaso gare ni tare da neman waje ta xauna, ganin yadda ta saki ranta ne yasa na gaida ita cikin sakin fuska ta amsa min, komawa nayi na tsaya saboda xuciyata bata amince na koma na xauna ba saboda ina tsoron kada ta turmushe ni tunda ta nuna a xahiri bata kaunar cikin da ke jikina.

ajiyar xucuya tayi tare da kiran sunana niimatullah,a hankali na dago na kalleta kirjina sai dukan uku-uku yake yi saboda tunda naxo gidan nan bata taba yi min kallon rahama ba ballantana har ta ambaci sunana.

Tsayar da idona nayi a kanta ina jiran jin abinda zai fito daga bakinta, cike da kulawa ta fara magana, hmm nasan xa kiyi mamakin ganina a wajen ki a kuma irin wannan lokacin, kaina a kasa na amsa mata da ina jin ki.

Murmushi tayi tare da cewa ya naga kamar bakya cikin nutsuwar ki ni fa naxo ne mu yi sulhu, mu ajiye dukkan makaman yakin da muka dauka, nasan nayi kuskure a kan abubuwan da na rika yi miki dan Allah kiyi hakuri mu tsaya mu nutsu mu kwantarwa da mijin mu hankalinsa.

wani sanyi naji ya ratsa xuciyata saboda ni bana son tashin hankali ina son naga muna xaune lafiya ko don mu farantawa dattijo, cike da sakin fuska na fara yi mata magana, ba komai aunty Allah ya yafe mana gaba daya dama ni bana jin dadin irin abinda muke yi insha Allah xaki same ni mai yi miki biyayya.

Cike da kulawa ta dube ni yauwa kanwata na gode dama dadyn Munir ya dade da fada min cewa kina da saukin kai ashe kuwa abinda ya fada haka ne, murmushi nayi kawai ba tare da na bata amsa ba.

Wani abin mamaki na gani tare da ita duk motsin da nayi idanunta a kan cikina har sai da na tsargu saboda kallon da take bina da shi ya shallake tunani, daki na shiga na sanyo hijabi sannan na dawo, a xuciyata na kosa ta wuce ta tafi tunda mun fahimci juna amma ta xauna tana bina da mayataccen kallo.

cikin kasalalliyar murya ta sake kiran sunana wanda har sai da naji gabana ya fadi, ba tare da na amsa ba na dago na kalleta, murmushi tayi bakya son na rika ganin cikin jaririn da xaki haifa mana ne shi ne kika sako hijabi ko, rufe fuskata nayi a'a ba haka bane aunty, rausayar da kai tayi haka ne mana kanwata, Allah dai ya kawo mana babyn nan lafiya ya sha lele. Murmushi muka yi gaba daya.

Mikewa tsaye tayi tana gyara mayafinta bari na tashi na koma wajena, akwai yan aikace-aikacen da ban karasa ba, tashi nayi na bi bayanta don yi mata rakiya sai da muka kai bakin kofa ta juyo ta dube ni.

Naji dadin yadda kika karbe ni hannu biyu ban taba xaton zan samu hakan daga wajen ki ba ganin yadda muka samu sabani da ke a baya na gode sosai, wani abu ta miko min aleda karbi wannan amaryar mu, hannu biyu nasa na karba.

kallona ta cigaba da yi, nasan baki san abinda na baki ba ko? Girgixa kaina nayi alamar eh, dafa kafadata tayi tana

Please Login or Register in order to submit comment