Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ikon tafiya da ke duk inda naga dama a fadin duniyar nan,don haka ki shiga ki shirya ki fito.cikin gida na shiga na tarar da su innah fada musu abinda dattijo yace nayi basu yi min musu ba na dauki mayafina na fita.

Rike hannuna yayi har sai da muka shiga mota cike da kulawa yake min magana, amma kin fadawa su innah ba yau xamu dawo ba ko? Turo baki nayi ni ai baka ce min kwana xa mu yi ba kawai kace na dakko mayafina.

Lumshe ido yayi to sati guda xa mu yi ina so na huta sosai na mance da wannan damuwar da nake ciki, bata fuska nayi xan yi kuka, haba dattijona ba fa haka muka yi da kai ba sai ka janyo innah tayi fushi da ni.

Jan kumatuna yayi ba fa wajen sabawa Allah kika tafi ba Niimatullah farantawa mijinki kika tafi yi,nasan ma innah baxa tayi fushi da ke saboda tasan duk inda kike kina tare da mijinki ne, yana gama fada ya yiwa motar key muka tafi.


*Follow me on wattpad @jeeddahtulkhaeer Tijj*

*Jeeddahtulkhair😘*💋💋💋💋💋
*MATAR DATTIJO*
💋💋💋💋💋

*©Jeeddah Tijjani*
*Adam*
*(jeeddahtulkhair)*

*dedicated to Amrat makeover*

47

Kaina a sunkuye yake har muka isa bakin wani gida da ke unguwar hotoro, gidan ya hadu iya haduwa, amma da dukkan alamu gidan xaman mutum daya ne, key yasa ya bude mana gidan rike yake da hannuna har muka isa cikin gidan cigaba da bubbude kofofin gidan yayi, cike da mamaki nake tambayarsa, nan kuma gidan wane ne dattijona? murmushi yayi yana kallona nan ma gidana ne xuwa nayi mu shakata mu huta sannan mu koma, makale kafada nayi ina masa shagwaba, ni dai bana so mu dade dan Allah ka taimaka ka mayar da ni da wuri.kallona kawai yayi tare da jan hannuna muka shige parlour, a kan kujera ya xaunar da ni,tsayawa nayi ina karewa dakin kallo.

Komai na gidan a gyare yake kamar da mutane a ciki, rausayar da kaina nayi ina tambayarsa dattijona ya naga komai na gidan nan tsaf, kamar da akwai mutanen da ke rayuwa a cikinsa?kallona yayi tare da kanne min ido daya cike da xaulaya yake min magana, wata amaryar tawa ce a ciki, abinda yasa kika ga na kawo ki ta tafi xiyarar ganin gida ne.

Wani kishi ne ya taso min naji kamar na buge bakinsa a lokacin da yake fada min,bata fuska nayi ina masa magana, dama kana da wata matar bayan ni da maman munir gaskiya ka yaudare mu dattijo, me yasa xaka yi mana haka? nan da nan idanuna suka kawo ruwa hawaye ya rika xubo min ta ko'ina.

A hankali ya miko hannun shi ya dora bisa wuyana cike da rarrashi ya fara min magana kiyi hakuri tsokanar ki nake yi Niimatullah uwar kishi, ai daga ke ba kari amaryar dattijo kin min komai kuma kin wadace ni, babu gurin da xan je na samu nutsuwa idan ba naki ba.

ba karamin dadi kalamansa suka yi min ba, cike da shagwaba na dube shi.

Har ka bata min rai dattijona kasan bana son wata mace ta shiga xuciyarka idan ba ni ba,tallafo fuskata yayi yana sumbatata,babu mai shiga xuciyata idan ba ke ba Niimatullah ke kadai kike burge ni duk cikin mata.

Kwantar da kaina ni yayi a jikinsa har cikin raina nake jin wani dadi na ratsa xuciyata, hira muka cigaba da yi cikin nishadi bayan mun huta muka shiga toilet muka yi wanka, muna fitowa ya fara bina da fitinannen kallon shi,ko ban fada muku ba kun san abinda dattijona ke so, bayan mun kammala mun dawo cikin nutsuwar mu muka sake sabon wanka, sannan muka nufi restaurant don cin abinci.

*****

Hajiya Maryam ce tsaye a bakin kofar shiga falonta, sanye take da doguwar riga ta atamfa ta nade kanta da mayafi, da dukkan alamu daga unguwa da ta dawo, cikin sassanyar murya ta kwalawa danta munir kira wanda yake daki yana karatu, da hanxari ya karaso wajenta cike da ladabi yake mata sannu da dawowa, mika masa kayan da ke hannunta tayi tare da cewa shigar min da su ciki saura kuma ka tsaya bincikawa kaga abinda ke ciki,karba yayi ba tare da yace komai ba ita kuma ta bi bayansa.

Fadawa kan kujera tayi ta xauna duk ranta babu dadi ta rasa ina xata saka ranta saboda mijinta ya juya mata baya, tayi duk abinda xa tayi amma kullum dada karkata yake yi wajen kucakar yarinyar da ya auro mata, mugun tunani ne ya rika bijiro mata, a cikin xuciyarta ta fara tunanin hanyar da xata bi ta kwato yancinta.

Munir ne ya lura da halin damuwar da take ciki, a hankali ya karaso kusa da mahaifiyar tasa cike da nutsuwa ya fara yi mata magana.

Mama lafiya naga kwana biyu bakya cikin walwala, ko bakya jin dadin jikin ki ne?a hankali ta dube shi da farko kamar baxa tayi masa magana ba, sai kuma can bayan yan mintuna ta amsa masa da lafiyata kalau, amma wannan uban naka yana son gadar min da hawan jini da ciwon xuciya.

Bai ji dadin maganar da ta fadawa babansa ba, amma ya daure ya cigaba da yi mata magana, kiyi hakuri mama rayuwar aure yar hakuri ce,kuma komai na duniya sai an yi hakuri, wata rana sai kiga komai ya xama tarihi.

A fusace ta dube shi, kai saurara ba wa'azi na kiraka kayi min ba idan xaka bani shawarar yadda xan samu mafita, na sanu damar barar da cikin yarinyar nan,kuma na koreta a gidan nan shi ne abinda nafi bukata, amma bana bukatar kasa ni a gaba ka rika yi min maganar banxa.

Kansa a kasa ya fara yi mata magana, subhanallah dan Allah ki tsaya ki saurare ni mama, ki daina furta wadannan maganganun, duk abin nan da kike tunani ba shi xai xama mafita a gare mu ba, kuma wannan ba shi xai sa dady ya rabu da matarsa ba tunda don yana sonta ya aureta.

Abinda xamu duba mama gaskiya duk wani gyara daga wajen ki yake kece kika bada kofar faruwar duk abinda yake faruwa a yanxu, mama ke da dady kun wuce a ce ana jin kanku kuna fada, amma har yanxu dady bai wuce xagi a wajenki ba, ba ki daina fada masa duk abinda kika ga dama ba,kinga wannan matsalar dole ta tsayawa dady a rai har yayi tunanin kara aure, sannan yarinyar nan da aka auro bata xo miki da fitina ba,ina ji Aunty take kiran ki sannan duk ladabin da ya kamata tana yi miki, bai kamata a ce kin nuna bakya sonta ba, sannan har ki rika fitowa fili kina cewa xaki xubar da cikin da ke jikinta a ganina duk wannan bai kamata ba, matsalar da dady ke fuskanta ne ma yasa ya bar gidan nan ya tafi da matarsa tunda yaji irin abinda kike fada, gaskiya ki gyara mama ki nemi gafararsa tunda kinga aljannarki a karkashinsa take,har fitar nan da kike yi ba da ixninsa ba duk ki nemi yafiyarsa ya yafe miki.

Tun jiya nake kiran number shi taki shiga, amma xan cigaba da kira insha Allah sai na yi muku sulhu.

Sai da ta gama saurarensa tsaf sannan ta watsa masa wata harara tare da daka masa tsawa.

Ban taba tsammanin kai mahaukaci bane sai yau munir, dama ashe baka kaunata duk xaluncin da ake yi min baka gani ba sai ramuwar da xan yi, to baxan ji nasihar taka ba kaje ka nemi uban naka kace ya sake ni tunda dama ba sona kake yi ba,ka fi son wannan jakar matar uban naka kaje na barka da su, kada ka kara shiga harkata ko abinci na dafa baxan sake baka ba,sai dai kaci na kaxamar matar babanka, tashi tayi ta shige daki.

Bin ta yayi yana bata hakuri, kiyi hakuri mama ban fada miki wannan maganar don ranki ya baci ba, dan Allah ki yafe min wucewa tayi ta bar shi yana mata magiya.

Daki ya koma ya rika tunanin irin wannan hali na mamansa da yadda xai yi ya shawo kan matsalar gidan su don abin ya dade yana ci masa tuwo a kwarya fargabar abinda xai biyo baya ne ya hana shi magana.

****

A bayan dattijo nake ya Goya ni da towel yana rarrashina kamar wata baby saboda gajiyar da ni da yayi a daren jiya,kuka na rika yi masa a kan ya mayar da ni wajen innah na cigaba da rayuwar da babu takura a cikinta, rarrashina yake yi yana min albishir da xai mayar da ni a lokacin, wayar dattijona aka kira hannu yasa ya dauki wayar tare da karata a kunnen shi, gaisawa naji suna yi ashe innah ce ta kira take tambayar lokacin dawowar mu
Cike da girmamawa ya bata amsa da mun dan yi nisa innah nan da sati biyu xamu dawo sallama suka yi ya kashe wayar.

A firgice na kalle shi, haba dattijona yanzu har sai mun yi sati biyu a nan Allah guduwa xan yi, sakko da ni yayi ya xaunar da ni a cinyarsa, jan kumatuna yayi indai kinga mun tafi daga wajen nan sai dai idan na tabbatar baba xai mayar min da ke dakina,idan ba haka ba kuma sai dai mu shekara a nan, kuka na fara yi masa ina masa magiya ya mayar da ni.

Wayar shi aka sake kira ta dade tana ringing sannan yasa hannu ya dauka, yana duba wayar yaga sunan maman munir, jifa yayi da ita gefe ya cigaba da yi min magana.

Rausayar da kai nayi ina masa magana bai kamata kayi watsi da wayar da tayi maka ba ka sani ko kiranka tayi ta roki gafararta, lumshe idanu yayi sannan ya fara min magana.

Nasan da cewa alkhairi baxai sa maryan ta kira ni ba don haka baxan dauki wayarta ba,lallaba shi nayi har ya dauka sai dai yana dauka ya ji...........


*follow me on wattpad @jeeddahtulkhaeer Tijj*


*jeeddahtulkhair😘*💋💋💋💋💋
*MATAR DATTIJO*
💋💋💋💋💋

*©jeeddah Tijjani*
*Adam*
*(jeeddahtulkhair)*

*Follow me on instagram @jeeddahtijjani*


*dedicated to Suhaimah M Bello*

48

Muryar dan shi munir yaji wani sanyi yaji a ransa, saboda yayi missing yayan nasa yana son kasancewa da su amma halin uwar su yasa ya bar su, cike da ladabi yake masa magana tare da gaishe shi, murmushi naga yana yi sai abin ya bani mamaki, ganin yadda yake magana yana fara'a ne yasa na gane ba Hajiya maryam bace, cike da walwala suka kammala wayar ya dawo da kallonsa gare ni, matsowa yayi daf da ni tare da kwantar da kansa a jikina,cike da xaulaya yake min magana nasan har hankalin ki ya tashi ko amaryar dattijo kin xaci ogarki ce ta kira? Murmushi nayi ni hankalina bai tashi ba don ta kiraka, xan fi so a ce ta dawo hanya madai-daiciya don ta samu yardar mijinta, wannan rashin xaman lafiyar gaba daya bana jin dadinsa, kwanto da ni yayi yana min kallon kauna.

Hankalin ki yana burge ni Niimatullah idan kika yi wani abin kamar babba ce tayi, kina da hangen nesa kuma ba ki da kyashi, duk da cutarwar da maryam ke yi miki amma kina so ta dai-daita da ni, gaskiya kin cika mace ta gari Allah yayi miki albarka, kaina a sunkuye na amsa masa da ameen.

Dago fuskata yayi yana kallona, kin son da wa muka yi waya yanxu? Girgixa kaina nayi sannan na amsa masa da a'a, gyaran murya yayi sannan ya fara yi min magana, munir ne ya kira ni yake bani hakuri a kan abubuwan da suke faruwa, kuma ya roki na koma gida amma ni gaskiya baxan koma ba sai na huta sosai da matata.

Kamo hannun shi nayi na rike kayi hakuri mu koma dattijona kaga kada a shiga hakkinta da yayanta, kuma kaga danta ma baya goyon bayan abinda take yi, tunda har ya shigo maganar ya kamata ka koma gida ko a yanxu nasan ta gane kuskurenta, murmushi yayi lallai har yanxu baki san wacece maryam ba Niimatullah shi yasa kike fadar haka, wallahi ina tabbatar miki baxa ta fasa abinda take yi ba, ni fa nasan halin kayana.

Sauke ajiyar xuciya nayi, duk abinda xata yi mana ya kamata ka rika hakuri dattijona tunda kaine shugaban gidan kai xaka tsara abinda xai fi xama daidai a gidanka, a ganina tahowar da muka yi nan baxai xama maslaha ga xamantakewar mu ba sai dai ma ta kara tsanata saboda tunani xa tayi na mallake ka na janye ra'ayinka.

Shafa kaina yayi xan yi naxarin maganarki amaryata, hira muka yi sannan na raka shi ya shirya ya tafi office, bai fi 2hours da tafiya ba ya dawo, cike da mamaki nake tambayarsa.

Me kuma ya dawo da kai dattijona, marairaicewa yayi yana kallona ba tare da yayi min magana ba, karasowa yayi ya narke a jikina cike da tausayawa na dube shi,me yake damunka mijina? rausayar da kai yayi sannan yayi min magana, soyayyarki ce ta dawo da ni har na fara aiki na gudo na taho wajenki, Allah ya sani bana koshi da soyayyarki amaryata, bata fuska nayi xan yi kuka.

Dan Allah kayi hakuri dattijona yau a gajiye nake kaga nayi maka aiki da yawa jiya ka taimaka ka kyale ni yau na huta, jawo ni jikinsa yayi ki taimaka min amaryata kin san da cewa a wajenki kawai nake samun nutsuwa, duk hakurin da na bashi bai karba ba sai da yayi abinda yake so,sannan ya sake shiryawa ya koma office.

Da ya tafi ma bai saurara da kirana a waya ba,bayan mintuna kadan yake kirana mu yi magana, yaji lafiyar babynsa.

****

Munir ne ya fito daga daki da sauri ya biyo bayan mamansa yana mata magana, ina xaki je mama? A yatsine ta dube shi gidan ubanka xan je babana, cike da tausasawa yake mata magana kinga irin abinda nake fada miki mama ki daina irin wadannan abubuwan saboda kina shiga hakkin dady kina fita ba tare da ixninsa ba, a fusace ta juyo ta wanke shi da mari, na fada maka ka fita daga cikin idanuna na rufe kafin ranka ya baci,tunda ka nuna baka kaunata na fita a harkar ka, don haka nima ka bar tawa kafin na saba maka, wucewa tayi ta barshi hannunsa rike da fuskarsa, kaninsa ne ya hango shi cike da tausayawa ya karaso wajen da yake kama hannun yayan nasa yayi tare da jansa gefe daya.

Kayi hakuri yaya a bisa dukkan abinda mama xata yi maka a kan amaryar dady, dole mu jajirce mu ga mun tsamota daga halin da take son jefa kanta har ma da mu, dan Allah kada kayi fushi ka cigaba da nuna mata gaskiya wata rana xata gane, ni kaga ko gaskiyar xan fada mata ma baxa ta tsaya ta saurare ni ba, kai din da kake yi ka cigaba da yi Allah ya baka lada.

Hirar xumunci suka cigaba da yi tare da tattauna matsalar da suke fuskanta a wajen mahaifiyar su.

Kai tsaye gidan kawarta ta xarce da kuka ta shiga gidan, cikin tashin hankali ta tarbeta tare da tambayarta abinda yasa take kuka, kasa bata amsa tayi saboda kukan da take yi, sai da tayi ya isheta sannan ta dubeta.

Wallahi ina cikin tashin hankali tunda dadyn munir yayi aure ban kara samun farin ciki ba, wannan yarinyar taxo ta raba ni da shi, yanxu xancen nan da nake miki kusan kwanansa uku baya kwana a gida, ni duk wannan ba shi ne ma abinda yake tayar min da hankali ba illa yadda ta shiga malamai ta raba ni da su munir yanzu yaran nan gaba daya a bayanta suke basa ganin laifinta, dan Allah ki taimaka min kawata ta karasa maganar tana kuka.

Girgixa kai tayi tana jimamin abinda Hajiya maryam ta fada mata, gaskiya kina cikin tashin hankali kwarai da gaske, amma me yasa kika bari har aka yi auren wannan shi ne kuskure na farko da kika yi, da kin fada min wallahi ko tarewa baxa tayi ba abin xai lalace, yanxu ma dai ba a makara ba kawo kunnenki kiji wata magana, rada tayi mata bayan sun gama ta mika mata hannu suka tafa, sannan suka dauki mayafansu suka fita.


*follow me on wattpad @jeeddahtulkhaeer Tijj*


*jeeddahtulkhair😘*💋💋💋💋💋
*MATAR DATTIJO*
💋💋💋💋💋

*jeeddah Tijjani*
*Adam*
*(jeeddahtulkhair)*

*follow me on instagram @jeeddahtijjani*

49

Fitowa suka yi daga gidan suna tafe suna tattaunawa a kan yadda xasu bullowa halin da hajiya Maryam ke ciki, sun yi tafiya mai nisa, sannan suka fara tunanin inda xasu nufa don warware matsalar, kasancewar dukannin su suna cikin damuwa da al'ajabin yadda niimatullah ta rikita maryam dare daya ta kasa gane kan mijinta, kawarta ce ta dube ta, yanxu so nake na kai ki inda xa a baki shawarwari da kuma hanyar da xaki bullowa wannan shaidaniyar amaryar taki,saboda idan kika barta illah mai yawa xata yi miki watan wata rana ma korarki xa a yi daga gidan gaba daya, ke da mijinki sai kallo. mai adaidaita sahu suka tare inda suka fada masa suna bukatar ya kai su unguwar farawa, gidan kawar su suka nufa suna zuwa suka fada mata abinda ya kawo su, shawarwarin yadda xata cutar da niimatullah ta bata da irin musgunawar da xata yi mata, har ta koreta daga gidan sannan kuma cikin da take takama da shi ya xube, ba tare da sun shirya faruwar hakan ba.

bayan sun gama kulle-kullen da xa su yi suka ci abinci suka yi hira,Hajiya maryam bata dawo gida ba sai bayan sallar isha.

A waje ta ci karo da yayanta tun daga nesa suka hangota, da fara'a suka karaso suna yi mata barka da zuwa, wani mummunan kallo ta watsa musu gaba daya suka koma gefe jikin su a sanyaye, kai tsaye daki ta shige ta dauki waya ta fara kiran dattijo don ta shirya masa makircin da xai sa ya dawo gida bai shirya ba. sai dai tana kiran wayar ta ji ta a kashe, cike da bacin rai tayi jifa da ita tana mayar da numfashi xuciyarta har tafasa take saboda takaici.

Bandaki ta shiga don yin wanka ko xata ji saukin bacin ran da ke damunta, tana shiga taji wani jiri yana dibanta, rike kofar bandakin tayi don kada ta fadi, gaba daya ta daina ganewa saboda jirin da ke dibarta, fasa wankan tayi ta koma ta xauna a hankali ta rarrafa ta fito waje,kiran yayanta ta shiga yi da hanxari suka karaso don ganin abinda ke faruwa da ita.

ganinta suka yi kwance har ta fara galabaita cike da damuwa suka karaso suna tambayarta abinda ya faru da ita, sai dai bakinta ya kulle ta kasa magana, kinkimarta suka yi suka kaita asibiti don gano abinda ke faruwa da ita.

Bayan likitoci sun gama bincike ne suka tabbatar da cewa tana fama da matsananciyar damuwa wanda idan ta cigaba da kasancewa a wannan halin xai yi sanadiyyar rasa rayuwarta gaba daya, cikin kuka yayanta ke mata magana ki taimake mu mama ki raba kan ki da wannan damuwar, ki daina tashin hankalin ki a kan abinda bai kai ya kawo ba, ki mikawa Allah lamarin ki komai yayi xafi maganinsa Allah, nasihohi masu ratsa jiki suka rika yi mata,suna kwantar mata da hankali tun daga wannan lokacin kullum cikin rashin lafiya take yau da dadi gobe ba dadi kuma duk da haka xuciyarta cike take da jin haushin niimatullah ko kadan bata jin kaunarta a ranta.

******
Tsaye nake na jingina kaina a jikin dattijona ina masa kuka, Allah ni babu inda xaka je yau sai ka mayar da ni gidan innata,kai kuma ka tafi gidanka na gaji da wannan xaman yau satina biyu ban ga innata ba sannan ga damuna da kake yi da yawan bukata, ni gara mu koma gida ka sasanta da matarka a raba kwana kowa ya rika shan aiki, ga shi innah ma har tayi fushi ko kiran mu bata yi tasa mana ido ta ga yadda xa mu yi.

tsayawa yayi yana kallona yana murmushi, cike da kulawa ya dube ni, yanxu kina so ki fada min cewa kin gaji da dawainiya da mijinki ne niimatullah, cikin marairaicewa na amsa masa ba gajiya nayi da kai ba, amma hidimarka tana da yawa ni kadai baxan iya kulawa da kai ba, dan Allah yau mu koma gida ka sulhunta da aunty kaga ita ma tana da hakki a kanka.

rausayar da kai yayi yana dubana, xamu koma amma ba yanxu ba ki bari na dawo daga office xa mu yi magana, bakin kofa na raka shi muka yi sallama sannan na dawo, kayana na shiga xubawa a akwati don yau nayi alkawarin baxan sake kwana a wannan gidan ba sai a gidan innah ko a gidansa.

Kaya ya gani na tare a gabana ina buntsure-buntsure a hankali ya tako har inda nake tare da cewa yau ko sannu da xuwa baxa ki yi min ba Niimatullah? Rausayar da kai nayi kaina na sunkuyar sannan na far yi masa magana, ni gida xaka mayar da ni nayi alkawarin baxan sake kwana a gidanka ba, cike da kulawa ya dube ni, idan baki kwana a gidana ba a gidan wa xaki kwana amaryar dattijo?kiran wayar shi da aka yi shi ya katse mana maganar da muke yi, don haka yayi saurin saka hannu a aljihu don dakko wayar.

Number Hajiya maryam ya gani tana kiran shi, mayar da ita aljihu yayi ya dawo da kallon shi gare ni, cikin sanyaya murya na fara yi masa magana, ko baka fada min ba nasan wacce take kiranka amma baka dauka ba, ka daina irin wannan dattijona ba kyau, matsowa yayi daf da ni tare da jan hancina ban san lokacin da kika fara wa'azi ba Niimatullahi kullum sai kin yi min magana a kan matar nan da ita ce fa ko tunawa da ke baxa tayi ba.

Muna cikin maganar ya sake jin shigowar text message, a hankali yasa hannu ya dauki wayar number dan shi munir ya gani, karanta text din ya shiga yi.

```innalillahi wa innah Ilaihi raji'un Allah ya yi wa mama rasuwa yanzu```

Hannun shi na gani yana karkarwa, saurin mikon min wayar yayi bakinsa na rawa ya kasa magana, karba nayi na fara karantawa, Aunty ta mutu dattijo?? wani jiri naji ya debe ni a take na fadi sumammiya.

*Follow me on wattpad @jeeddahtulkhaeer Tijj*

*Jeeddahtulkhair😘*
💋💋💋💋💋
*MATAR DATTIJO*
💋💋💋💋💋

*jeeddah Tijjani*
*Adam*
*(jeeddahtulkhair)*

*follow me on instagram @jeeddahtijjani*

50


Fadawa kaina yayi yana jijjiga ni ki, taimake ni ki tashi Niimatullah kada ki mutu ki bar ni, na rasa Maryam ke ma na rasa ki ina xan tsoma rayuwata, ruwa ya tafi ya dakko ya hau yayyafa min a hankali na fara bude idona abu na farko da ya fito min daga bakina shi ne, da gaske Aunty ta mutu dattijona, ka tabbatar min da abinda nake tunani a xuciyata, idanunsa cike da kwalla ya dube ni, maryam ta mutu Niimatullah sai dai mu yi hakuri na kira wayoyin yaran duka a kashe, kukana ne ya tsananta tausayinta ne ya kama ni, ban so ta mutu yanxu ba naso a ce ta dai-daita da mijinta.

Cikin kuka na cigaba da yi masa magana, kaga abinda nake fada maka ko dattijo, ka kyale matar nan ka dawo wajena watakila ma damuwa ce ta kasheta, yanxu ta mutu baka nemi gafararta ba me xaka ce da Allah idan kaje lahira.

Shiru yayi yana saurare na a hankali ya dago yana dubana, tabbas nayi kuskure Niimatullah kuma ina fatan Allah ya yafe min, ba a son raina na kyale maryam ba sai dai baxan iya jurewa masifarta ba, hannuna ya rike tare da mikar da ni tsaye, tashi mu tafi gida fitowa muka yi daga, a mintunan da basu wuce goma ba muka isa gidan.

Da sauri yayi parking muka fito don ganewa idanun mu abinda ke faruwa, abin mamaki gidan ba kowa kamar wani abu bai faru ba, cikin gidan muka cigaba da sa kanmu tarar da su munir muka yi a falo suna kallo, suna ganin mu suka mike suna yi mana barka da xuwa, ganin yadda suke murmushi yasa muka gane babu abinda ya faru, cike da mamaki dattijo yake tambayar su ina maman ku, a ladabce suka amsa masa da tana daki tana bacci sake jefa masa tambaya yayi munir ina wayarka da sauri ya amsa masa da tana hannun mama, a nan ya gane cewa makirci ta shirya masa.

Xaunawa nayi a wajen

Please Login or Register in order to submit comment