Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

baka hakuri a kan abinda mama take maka, mun san kana hakuri da halayenta amma ka kara yi, saboda hannunka baya rubewa ka yar daddy, sannan kuma idan tana tare da kai da Aunty tana ganin yadda ku ke mu'amala da kyakkyawar dabi'a ina ganin xata canja wasu dabi'un nata.

A hankali ya dago ya dubi yaran nasa har cikin ransa yake jin kalaman sa na ratsa duk wani jini da tsoka na jikinsa, tabbas shi kansa yasan yayi sa'ar yara masu hankali da xurfin tunani, kuma xai so a ce da mahaifiyar su suke rayuwa amma halinta ya janyo ya rabu da ita, sauke ajiyar xuciya yayi sannan ya bashi amsa.

Tabbas dukkan abinda ku ka fada gaskiya ne, amma lamarin mahaifiyar ku yana bukatar dogon naxari ba abu ne da xa a yi shi da gaggawa ba, naji dadin wannan tunatarwar da ku ka yi min, Allah yayi muku albarka kuma xan duba wannan maganar taku da idon basira insha Allah, amsawa suka yi da ameen sannan suka mike, bin su yayi da kallo har suka shige bangaren su ba karamin tausayi suka bashi ba, amma yana ji a ransa baxai iya cigaba da rayuwar aure da mahaifiyar su ba.

Har ya mayar da hankali kan takardar yana karantawa yaji baxai iya cigaba da karatun ba, saboda tunani da tausayin yayansa, tashi yayi ya nufi wajen Niimatullah.

A kulle ya tarar da kofarta don haka yayi sauri ya tura don ya san bacci take yi indai yaji kofarta a kulle, saka kanshi yayi ya shiga dakin tare da sallama.

Ina jin maganar shi na narke a cikin bargo ina dan numfarfashi, saboda nasan matukar ya shigo ya tarar da ni a xaune tara min gajiya xai yi. Jin ban amsa sallamar bane yasa shi shigowa cikin bed room din, a cikin bargo ya iske ni ina ta faman numfarfashi, maimakon naga damuwa a ransa sai naga yana murmushi, bata rai nayi xan masa kuka.

Kana ganin ba nida lafiya shi ne xaka yi min dariya, karasowa yayi yana murmushi tare da jan kumatuna nasan abinda kike gudu fa amaryar dattijo shi ne xaki shirya min wannan law din ko? to ai na gane nufin ki. Langwabar da kai nayi tare da dora hannuna a jikinsa Allah da gaske nake bana jin dadi dattijona taba ka ji, hannunsa ya dora a wuyana ni ban ji komai ba Niimatullah kawai don kada ki kula dani ne, kuma dole a bani hakkina saboda yanzu ne lokacin da ya kamata mu ci amarcin mu tunda wannan jarababbiyar bata nan.

Kukan shagwaba na fara yi masa ni Allah baxan yarda ba, idan kuma kaje kayi abinda cikin ya xube ba ruwana, cike da xaulaya ya bani amsa to menene idan ya xube sai na kara yin wani tunda dama na farkon ma ni nayi abuna.

Tashi nayi xan gudu da sauri ya riko ni ya manna ni da kirjinsa, ina xaki je amaryar dattijo? Bata fuska nayi wani dakin xan tafi tunda nan ka takura min, murmushi yayi tare da rike hannuna haba Niimatullah me yasa har yanzu kika kasa sabawa da halin dattijon ki, ni fa haka Allah ya halicce ni da tsananin bukatar ki baxan iya rayuwa ba tare da soyayyar ki ba, hawaye na fara yi wlh yau a gajiye nake dattijona babu abinda xan iya yi, sumbatar goshina yayi tunda kin gaji na hakura amma fa ki sani bashi kika ci akwai ranar da sai kin biya gaba daya.

Da sauri na amsa da eh na yarda xan biya, cika ni yayi na koma na xauna wayar shi ce tayi ringing hannu yasa ya dakko yana dubawa ya hasko min kalli number wa kike gani? cikin sassanyar murya na amsa masa da number Aunty ce, ajiyeta yayi a gefe tare da cewa baxan duba ba don ni yanxu na kulle babin rayuwarta.

Rarrashin shi nayi a kan ya dauki wayar amma yaki dauka, sai da tayi masa missed calls sama da goma, tana sake kira na dauka ina yin sallama naji muryar namiji kuma da alama ya manyata, da sauri na mayar da wayar kunnensa cikin ladabi naji yayi sallama magana suka fara yi wani abin yana bada amsa wani kuma naji yayi shiru, bayan sun kammala ya fada masa cewa xai xo yanzu.

Bayan sun gama magana yake fada min cewa baban maman munir ne, yana min magana ne a kan abinda ya hada ni da maryam na fada masa yanxu xan je nayi masa bayani, ;amma wlh baxan dawo da ita ba saboda shi ma yasan halinta.

Lallaba shi na shiga yi don Allah kayi hakuri hubbyna ka dawo da ita dakinta ko yanxu ai ta gane kurenta idan har aka ce xa a yi muku sulhu kada ka vki amincewa saboda sulhu alkhairi ne, kuma na tabbatar da cewa baxa ta kara aikata kuskuren da tayi a baya ba.

Murmushi yayi kina bani mamaki Niimatullah ina rasa wace irin xuciya ce da ke, ke da xaki ce kada na dawo da ita amma ke kike bani hakurin na mayar da ita dakinta, lallai a gaishe ki amaryar dattijo.

Hular shi ya saka, tashi nayi xan masa rakiya ya dakatar da ni yace nayi xamana, sallama muka yi ya tafi addu'a na rika yi wa maryam Allah yasa ya mayar da ita, saboda ina son yayanta su cigaba da rayuwa da ita.


*follow me on wattpad @jeeddahtulkhaeer Tijj*


*jeeddahtulkhair😘*💋💋💋💋💋
*MATAR DATTIJO*
💋💋💋💋💋

*©jeeddah Tijjani*
*Adam*
*(jeeddahtulkhair)*

*follow me on instagram @jeeddahtijjani*

55

Kai tsaye gidan su Hajiya maryam ya nufa, a bakin kofa ya tsaya ya aika yaro a sanar musu cewa ya iso, da fara'a mahaifinta ya fito ya tarbe shi tare suka shiga har cikin gida, yana shiga ya tarar har an yi masa Shimfida ana jiran isowarsa.

A ladabce suka gaisa da babanta bayan sun dan yi hira ya dubi dattijo, nasan baxa kayi mamakin kiran da nayi maka ba Alhaji, domin tatsuniyar gixo bata wuce ta koki, murmushi dattijo yayi tare da cewa gaskiya ne baba.

Gyara xama yayi sannan ya fara yi masa magana, abu na farko da xan fara cewa shi ne Allah ya baka hakuri Allah ya huci xuciyarka domin xama da Maryam sai an kai xuciya nesa, kayi namijin kokari da har ku ka kai wannan lokacin tare ba tare da kun rabu ba, bana bukatar jin musabbabin abinda ya janyo rabuwar ku domin nasan duk laifin daga wajenta yake, don haka ina kara baka hakuri Allah ya huci xuciyarka, sannan baxan maka dole a kan ka dawo da ita ba, idan kaga akwai matsala kuma xaka fi samun kwanciyar hankali to ka bar mayar da ita.

Duk kunya sai ta kama dattijo ganin yadda mahaifinta yake fadar laifinta da kansa, kansa a sunkuye ya bashi amsa, ina nan ina tunani a kan haka indai ta gyara halinta ba komai sai mu cigaba da xama dama ai sulhu nake so a yi. Cike da farin ciki ya dube shi gaskiya ne Alhaji to idan da alkhairi Allah ya dai-daita, amsawa yayi da ameen suka yi sallama.

Kwance Hajiya maryam take tana tuna irin rayuwar jin dadin da ta yi a gidan dattijo, addua ta fara yi a kan Allah ya gyara tsakaninta da mijinta ta koma dakinta yanzu ta gane muhimmancin da mijinta yake da shi, da duk bata ganin amfaninsa.

Bayan tayi wanka ta shirya ta saka hijabi don yanzu sam ba tada nutsuwar da xata tsaya ta gyara sosai, gidan abokin dattijo ta nufa tunda dama matarsa kawarta ce.

Tana isa bakin kofar gidan hawaye suka cika idanunta, ji take dama ita ma ta koma dakin mijinta ta rika cin gashin kanta kamar kowace mace, da kuka ta shiga gidan hankalinta a tashe ta fara tambayarta dalilin kukanta daki suka shiga saboda kada yara su fahimci halin da take ciki.

Suna shiga ta kara rushewa da kuka, zayyana mata yadda suka yi da dattijo tayi, ta tausaya mata sannan tayi mata nasiha sosai a kan irin abubuwan da take yi masa, ita kanta ta dade tana bata shawarwari a kan ta nutsu ta kama mijinta, wayar maigidanta ta kira ta shaida masa cewa yayi bakuwa, saboda idan ta fada masa kai tsaye cewa ita ce taxo baxai xo ba, saboda shi ma ta taba ci masa mutunci a kan Niimatullah.

Basu dade da yin waya ba ya iso gidan, yana yin ido biyu da Hajiya maryam ya bata rai, fuskarsa ba annuri ya karaso inda suke tare da cewa, kika ce nayi bakuwa ina bakuwar take? Jikinta a sanyaye ta nuna Hajiya maryam.

Fuskar shi a daure ya fara magana dama a kan wannan matar da bata san mutunci ba xaki dakko ni daga wajen aikina? amma baki kyauta min ba wallahi saboda tuni na fita daga shaaninta tunda naga bata san mutunci ba, a fusace ya fita ya bar dakin, bin sa tayi tana bashi hakuri a kan ya dawo amma kememe yaki dawowa.

Ba karamin xafi duniya tayi mata ba, duk inda take tunanin xata ra6a ta samu alfarma a bawa dattijo hakuri ta ci musu mutunci duk a kan auren Niimatullah, da kuka ta fito daga gidan.

Bayan ta koma gida ta kira wayar Niimatullah domin ta bata hakuri a bisa abubuwan da ta rika yi mata a baya.
sai duk kiran da tayi bata samu ta dauka ba, wannan abin ya kara jefeta a cikin damuwa.

Cikin kankanin lokaci ta canja tayi baki ta rame ga damuwar da take fuskanta na rashin muhalli mai kyau da abinci mai kyau, sannan ba damar tayi kuskure sai mahaifiyarta ta hau yi mata fada da gorin abincin da take ci, wannan dalilin ya kara sawa taji duk xaman gidan ya isheta ta kosa ta koma dakinta.

*follow me on wattpad @jeeddahtulkhaeer Tijj*


*jeeddahtulkhair😘*💋💋💋💋💋
*MATAR DATTIJO*
💋💋💋💋💋

*©jeeddah Tijjani*
*Adam*
*(jeeddahtulkhair)*

*follow me on instagram @jeeddahtijjani*


56

Ina shigowa daki na dauki wayata na duba, kiranta na gani kusan missed calls biyar ban samu damar bin ta a lokacin ba, kasancewar bana jin dadi ko na kirata baxan samu damar yi mata magana ba.

Kwantawa nayi don baxan iya cigaba da xama ba saboda ciwon da jikina ke yi, tun daga lokacin da ta dake ni ban sake jin karfin jikina ba nayi shiru ne kawai ban fadawa dattijo ba,don kada ya kara daukan xafi yaki dawo da ita, kiran wayar shi nayi na fada masa yanayin da nake ji a jikina, cike da tausayawa yake min magana tare da cewa xai dawo ya kula da ni, dakatar da shi nayi don bana son ya dawo gida ya bar aikinsa, rokon shi nayi a kan ya bari na tafi gidan innah, hana ni tafiyar yayi don baya son ya ga ina xirga-xirga, kiran innah yace nayi taxo taga jikin nawa.

Ina kiranta ta dauka, cike da shagwaba nake fada mata abinda ke damuna a cikin mintuna kadan ta iso, cike da mamaki ta shigo dakina tare da tambayata ina uwar gidanki take naga wajenta a kulle kuma alamu sun nuna babu mutum a ciki.

Sakkowa nayi na dawo inda take xaune, kwantar da kaina nayi a kan cinyarta ina kallon fuskarta nake magana, dattijo ya sallameta innah, a raxane ta dube ni yaushe wannan al'amarin ya faru Niimatullah amma baki sanar da ni mun shiga cikin maganar ba?

Wallahi innah nayi shiru da xancen ne saboda naga baya son maganar shi kansa bai fadawa kowa ba, cike da tausayawa take magana amma ban ji dadin faruwar wannan abu ba idan aka fara tara iyali hakuri ake yi, amma xan same shi nayi masa magana gara ya dawo da ita saboda yayanta.

Hirar da muka rika yi kenan ni kaina ina so ta dawo saboda baxan iya da hidimar dattijo ni kadai ba, yamma nayi ta fara shirye-shiryen tafiya.

Riko kafarta nayi tare da cewa ina xaki je innah? Kallona tayi tana murmushi ya naga kin rike ni Niimatullah ko so kike tsohuwar kafar tawa ta karye? Langwabar da kaina nayi xan yi kuka, ni Allah babu inda xaki je innah a nan xaki kwana kina ganin har yanzu ban warke ba amma xaki tafi ki barni. Kuma ai kin ce xaki tsaya kiga dattijo ku tattauna a kan dawo da Aunty idan kika tafi yanxu yaushe xaku yi maganar?

Dawowa tayi ta xauna, dafa kafadata tayi, ban fadawa malam xan kwana ba Niimatullah idan na xauna kin ga ban yi dai-dai ba.

A shagwabe nake mata magana haba innah indai baba ne nasan baxai hana ki kwana ba, wayarta na dakko bari na kira shi nayi masa magana nasan Allah baxai ki yarda ba.

Kira daya nayi masa ya dauka, fada masa nayi innah xata kwana ai kuwa naci sa'a bai hana ba, innah bata so ya yarda ta kwana ba saboda bata son dattijo ya rika yin rashin kunya a gabanta.

Innata na kalla ina dariya naji dadi baba ya bari ki kwana yau a dakina xaki kwana kuma a kan cinyarki, ture ni tayi tun wuri gara ma ki sani baxa ki kwana tare da ni ba dakin mijinki xaki tafi.

Bata fuska nayi haba innah yaushe rabon mu kwana tare, ni gaskiya da ke xan kwana, tabe baki tayi sai ki kwana mu gani, ni fa idan kika takura min kika ce sai kin kwana tafiya ta xan yi, gara ma tun wuri ki canja shawara shiru nayi tare da kwantawa a kan cinyarta.

Sallama muka ji gaba daya muka mayar da hankali ga mai yin sallamar, Hajiya maryam muka gani gaba daya ta canja wahala ko ta ina ta bullo mata, da fara'a ta karaso inda muke, cike da mamaki nake kallonta ko menene ya dawo da ita?

Karasowa tayi ta xauna gaisawa suka yi da innah sannan nima na gaisheta, hawaye naga yana sauka a fuskar ta cikin kuka ta fara magana, dan Allah kiyi hakuri ki yafe min Niimatullah duka abinda nayi miki kiyi hakuri, insha Allah hakan baxa ta kara faruwa ba.

Cike da tausayawa innah ta dube ta, komai ya wuce Hajiya kuma nima yau naxo gidan nan naga bakya nan nake tambayar Niimatullah ko kina ina sai tace wai kun rabu da Alhaji, gaskiya ban ji dadin faruwar hakan ba, kuma insha Allah xan shiga ciki mu sasanta.

Godiya tayi sannan ta tashi ta tafi, wajen yayanta ta nufa inda ta roke su da su bata mukullin bangarenta ta shiga, da kyar suka bata budewa tayi ta shiga ciki.

Dattijo na isowa yaga wajen Hajiya maryam a bude cike da mamaki ya bude kofar don ganin wanene a ciki.


*Follow me on wattpad @jeeddahtulkhaeer Tijj*


*jeeddahtulkhair😘*💋💋💋💋💋
*MATAR DATTIJO*
💋💋💋💋💋

*©jeeddah Tijjani*
*Adam*
*(jeeddahtulkhair)*

*follow me on instagram @jeeddahtijjani*

57

Saka kanshi yayi cikin dakin don ganewa idanunsa abinda yake xargi, yana dosar dakin yayi saurin ja da baya domin abinda yake tunani dai shi ya gani, cike da tuhuma ya fara magana da iznin wa kika dawo min gida har kika bude daki kika shiga ba tare da amincewata ba, a marairaice ta fara magana.

Na bi Allah na bi ka mijina dan Allah kayi hakuri ka yafe min a bisa dukkan abinda ya faru na aikata ne a bisa kuskure, naje wajen niimatullah ma na nemi yafiyarta kuma ta yafe min, saurin dakatar da ita yayi wannan yafiyar da tayi miki tsakanin ku ne ni bata shafe ni ba, kuma niimatullah ba tada hurumin baki umarnin ki xauna min a gidansa domin ba gidanta bane kuma ba xamanta kike yi ba, xamana kike yi don haka tun wuri ki tashi ki koma gidan ku ki cigaba da cin kwaki da xogale tunda haka kika xabar wa kan ki, yana gama fada ya fice a fusace. kifa kanta tayi jikin kujera tana kuka a xahiri take fadar ta cuci kanta tayi watsi da damarta da har ta kai mijinta bangon da baya jin rarrashinta.

A fusace dattijo ya shigo bangarena ganin yadda ya turo kofar falona da karfi nasan akwai maganganu a bakinsa sai dai yana shigowa ya ci karo da Inna sai kuma jikinsa yayi sanyi, a kunyace ya gaida ita sannan ya tashi ya shiga daki, har na share naki bin shi innah ta harare ni tare da cewa tashi ki bi mijinki, ban so ba na shiga dakin saboda bana son yayi min maganar hajiya maryam, cikin kasalalliyar murya nayi masa sallama a hankali ya dago ya kalle ni ba tare da ya amsa min ba kasancewar ran shi a bace yake, karasawa nayi kusa da shi na sake maimaita masa sallamar da nayi masa a wannan karon ya amsa sai dai bai dago kai ya kalle ni ba.

shiru muka yi na wani dan lokaci saboda ban san ta inda xan fara magana ba, don naga mutumin nawa yau a cikin xafi yake, a hankali na kira sunansa dattijona me yasa na ganka a haka ko wani ne ya bata min ranka? kansa a sunkuye ya amsa min kece kika bata min rai tunda kika sa wannan matar ta xauna min a gida ba tare da iznina ba.

Muryata a sarke na amsa masa wallahi ba ni bace dattijona innah ce taga halin da take ciki shi ne ta tausaya mata tace ta koma dakinta idan kaxo sai tayi muku sulhu, share xufar da ta cika masa fuska yayi tare da cewa babu sulhu tsakanina da Maryam ni kadai nasan irin axabar da na dandana a wajenta don haka har abada baxan so Allah ya kara maimaita min irin wuyar da na sha a hannunta ba.

cike da rarrashi nake masa magana, haba dattijo ya xaka kafe a kan magana daya kamar fadar Allah, tunda tayi kuskure a baya yanxu kuma ta dawo xata gyara kuskurenta ya kamata ka yafe mata, ko don yayan da ku ka haifa tare, mikewa yayi yana kallona da kin hakura kin rike maganarki niimatullah baxan taba jin wannan rokon naki ba, ke kan ki matar nan ta kusa kashe ki amma kokari kike yi a dawo da ita wai ke mai kyakkyawar niyya ko? To ni dai take aure kuma nace bana yi ta tafi ta samu wani mijin mai irin halinta watakila xasu dai-daita ni dai na gama xama da ita, yana kammala maganar ya fita wajen innah yaje don su yi hira.

Tambayarta lafiyar jikina yayi da jaririna cikin sakin fuska ta amsa masa da lafiyar mu kalau, a cikin hirar tasu ta jefo masa tambaya wadda sai da tasa ya dauke wuta gaba daya, Alhaji ashe haka abu ya faru yau nake samun labarin cewa ka rabu da Maryam me yayi xafi haka? Kansa a sunkuye ya fara magana wallahi matsalolin ne suka ki ci suka ki cinyewa innah, kullum a cikin tashin hankali nake ni da niimatullah, gata nan, ya nuna ni da hannunsa duk tasan halin da ake ciki, kullum kokarinta ya xa a yi ta ga bayana wannan dalilin yasa na sallameta saboda tashin hankalin da nake ciki da yawa.

girgiza kai innah ta shiga yi, kayya abu ba dadi Alhaji amma da anyi hakuri kuruciya ce wata rana xata daina, kuma ko yanxu nasan tayi laushi ta gane abinda take yi ba mai kyau bane baxa ta Kara maimaitawa ba, kuma Alhaji idan aka fara tara yara ba a son saki duk abinda xai faru hakuri ake yi wata rana sai kaga ya xama labari.

cike da nutsuwa ya amsa da haka ne innah sai dai ita abin nata ya wuce lissafi, nayi hakurin har sai da ta kai ni bango.

Hakuri innah ta cigaba da bashi har sai da ya hakura ya sakko, umarni innah ta bani da naje na kirata, tashi nayi na nufi bangarenta inda na fada mata innah na kiranta.

*follow me on wattpad @jeeddahtulkheer Tijj*


*jeeddahtulkhair😘*💋💋💋💋💋
*MATAR DATTIJO*
💋💋💋💋💋

*©jeeddah Tijjani*
*Adam*
*(jeeddahtulkhair)*

*follow me on instagram @jeeddahtijjani*

58

Bata yi gardama ba ta biyo ni, jikinta a sanyaye take tafiya har muka isa dakina, da sallama muka shiga dakin gaba daya suka amsa mana na lura da dattijona sai hararta yake yi, ita kuwa yi tayi kamar bata ganshi ba sai muxurai yake yi, gefe muka samu muka xauna gaba dayan mu sunkuyar da kai muka yi muna jiran jin abinda xai fito daga bakin su innah.

Shiru suka yi na dan lokaci sannan innah ta katse shirun da aka yi tare da cewa, Hajiya kiyi hakuri na taso ki kina hutawarki, kanta a sunkuye ta amsa da ba komai innah, magana ta fara yi abinda yasa ku ka ga na tara ku a nan don na kawo karshen matsalar da ke faruwa a gidan nan saboda xaman ku babu dadi a haka, juyar da kanta tayi wajen dattijo Alhaji ina baka hakuri Allah ya huci xuciyarka dan Allah ka dawo da Maryam kayi mata afuwa Insha Allah xata gyara halayenta.

Sauke ajiyar xuciya yayi Shikenan innah ba komai na dawo da ita albarkacin ki wallahi da baki shiga maganar nan ba baxa ta dawo ba na rabu da ita har abada.

Godiya innah tayi masa tare da sa masa albarka juyawa tayi wajen hajiya maryam tayi mata nasiha sosai a kan biyayyar aure sannan ta umarceta da yin kawaici abisa dukkan abinda ta gani na rashin dadi.

hawaye ne ya rika sauka a kan fuskarta cikin rawar baki ta fara magana, na gode innah ashe dama abinda wasu mutanen ke fada gaskiya ne kishiya yar uwa ce ba abokiyar gaba ba, gashi nan na gani da idona sanadin niimatullah na dawo dakina na gode innah Allah ya saka da alkhairi Insha Allah duk nasihar da kika yi min xan yi amfani da ita.

Riko hannuna tayi niimatullah na gode dan Allah ki yafe min a bisa dukkan abinda ya faru a baya, ashe da nake gudunki ke alkhairi ce a gare ni na gode Allah ya hada kanmu hakuri ta juya ta bawa dattijo shi ma a nan take ya yafe mata tashi tayi ta nufi bangarenta tana kuka.

Tana shiga ta dauki waya ta kira kawarta zainab, bayan sun gaisa ta fara yi mata magana Gaskiya a yanxu na gano kishiya yar uwa ce yanxu ta sanadin niimatullah na koma dakina, tabe baki tayi tare da turo dankwali gaban goshi, wannan munafunci ne kawai tunda tasa a kore ki dole tasa a dawo da ke, tayi haka ne fa ba don Allah ba sai don kissa da kisisina ke ina kwakwalwarki take tafiya ne gaba daya kin manta da sharrin kishiya ko? Sauke ajiyar xuciya tayi

Wallahi sis zee Niimatullahi da iyayenta mutanen kirki ne mu ne muka yi musu mummunar fahimta da na tsaya na nutsu tun farko da abubuwan da suka faru a baya basu faru ba, da tana da mummunar niyya a kaina baxa ta yarda a dawo da ni, tunda babu kalar rashin kirkin da ban yi mata ba,kashe wayarta tayi don tana jin baxa ta iya jurewa sauraren dukkan abinda take fada mata ba domin ita duk a matsayin soki burutsu ta dauki xantukanta, duk kiran da tayi mata a lokacin bata dauka ba ashe shiryawa take xata xo gidanta.

Bata dade da ajiye wayar ba ta iso, tun daga bakin kofa ta fara xaxxaga mata masifa, a kan me yasa xata amince da makircin da Niimatullah tayi mata,duk kokarin da tayi don ta ganar da ita taki ganewa a ranar baran-baran suka rabu.

Tun daga wannan lokacin xamantakewar mu ta canja, kanmu ya kara haduwa duk abinda xai janyo mana fitina ina kokarin kauce masa sannan shi kansa dattijo ina kara saita shi a hanya wajen tsayar da adalci a gidansa bana yarda ya danne mata hakkinta ko yaya yake, ba karamin ji da ni take yi ba yanxu na xama masoyiyarta duk abinda xata yi sai ta nemi shawarata yanxu ta kai ta kawo ko unguwa xata je sai ta tafi da ni duk irin xugar da kawayenta ke mata ta toshe kunnenta muna xaune lafiya, dattijo kuwa kullum cikin saka min albarka yake saboda a yanxu ya fi jin dadin rayuwar gidan.

Innah bata dade ba ta koma gida ganin yadda xaman gidan yayi daidai don komai maman munir ke shigowa tayi min ko girki bata bari nayi, yayanta kuwa sun xama kamar nawa komai zasu gabatar sai da shawarata.

*follow me on wattpad @jeeddahtukhaeer Tijj*

*jeeddahtulkhair😘*💋💋💋💋💋
*MATAR DATTIJO*
💋💋💋💋💋

*©jeeddah Tijjani*
*Adam*
*(jeeddahtulkhair)*

*follow me

Please Login or Register in order to submit comment