Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

nayi tare da cewa ba wani nan tunda ka xalunce ni komai ma sai ka fada, ni daga yau na daina kula ka tunda haka kake, rarrashina ya fara yi gami da bani hakuri, ni kuwa wani haushinsa ke kara kama xuciyata. kifa kaina nayi jikin pillow ina cigaba da kukana saboda a halin yanxu shi ne kadai abinda xai sanyaya min raina.

tashi yayi ya nufi toilet, yaje ya kintsa kansa sannan ya dawo, muna hada ido da shi na kawar da kaina gefe saboda a yanxu kallon axxalumi nake masa, kiran sallar asubah aka yi don haka na rika kokarin mikewa amma na kasa tashi, wani kuka na saki tare da cewa, gashi nan ka karya min kafa na kasa tashi, cike da kulawa ya karso gare ni kiyi hakuri Niimatullah ki yiwa mijin ki uxuri na fada miki komai nayi sonki ne ya jawo mini.

taimaka min yayi ya mikar da ni tsaye ya kai ni har bandakin inda ya hada min ruwan dumi na gasa jikina da shi,bayan na kammala na fito yaja mana jam'i muka yi sallah.

muna idarwa naji wani xaxxabi ya rufe ni jikina banda rawar dari babu abinda yake yi, hawaye ne ya shiga fita a idona cikin kuka nake yi masa magana, ni dai ka kira min innata mu yi magana, na fada mata xaxxabi nake yi taxo ta tafi da ni, matsowa yayi kusa da ni tare da kwantar da kaina a kirjinsa, kiyi hakuri Niimatullah kin ga yanxu safiya ce idan aka kira innah a irin wannan lokacin aka fada mata baki da lafiya hankalinta ne xai tashi, ki bari gari ya kara wayewa sosai sai na kira miki ita.

cike da shagwaba nake masa magana, ni dai Allah yanxu xaka kirata idan ba haka ba kuma na dauki jakata na tafi gida, shiru yayi ba tare da ya amsa min ba, wayar da ke gefensa ya dakko ya fara kiran waya, duk a tunanina innah ya kira kawai sai naji salon hirar tasa ya canja.

wani doctor ya kira inda ya shaida masa cewa bana jin dadi, ya fada masa dukkan abinda yake damuna daga karshe ya fada masa cewa yaxo asibiti ya karbar min magani.

cike da mamaki na dube shi, haba dattijona dama ba innata xaka kira min ba sai ka tashi kira wani doctor ni ko ya bani maganin ma baxan sha ba tunda baxa ka kira min innata na fada mata ba.

cike da kulawa ya dafa kafadata kiyi hakuri gari ya waye sosai Niimatullah, yanxu idan innah taji ba ki da lafiya xata iya tahowa yanxu saboda yadda take ji da ke.

shura kafata nayi ina kuka har sai da na hargitsa shirin gadon gaba daya, cikin kuka nake masa magana, ni dai sai ka kira min ita Allah, rarrashina ya shiga yi to kiyi hakuri ki daina kuka yanxu xan kira miki innarki.

ringing daya wayar tayi naci sa'a innah ta dauka, muna fara magana taji na rushe da kuka, Haba innata tunda na tafi kika manta da ni yau kwanana shida amma baki taba xuwa kin ganni ba, gashi nan yanxu haka ba nida lafiya.

A raxane innah take tambayata me ya same ki Niimatullah, cikin kuka nace mata xaxxabi nake kuma............ina maganar dattijo na kallona yana min warning a kan kada na fadawa innata abinda ya faru.

tambayata ta cigaba da yi kuma me Niimatullah?kin fara magana kuma kin yi shiru, cikin sarkewar murya na bata amsa ni dai kixo innah xan fada miki dukkan abinda ke damuna a gidan dattijo, sallama muka yi da ita sannan ta kashe wayarta.

murmushi yayi sannan ya dube ni, Niimatullah kenan sarakan tonon silili, idan innah taxo kika fada mata sai na kara maimaita miki abin jiya, turo baki nayi Allah sai na fada wa yace ka rika takura min.

lallaba ni ya shiga yi saboda yasan wannan kadan ne a cikin karamin aikina babban aikina ya fi gaban haka. tashi yayi ya shiga kitchen ya hada mana breakfast sannan ya dawo ya fara bani har sai da naci na koshi, tashi yayi tsaye yana dubana.

Amaryar dattijo, a hankali na dago ido na kalle shi tare da cewa na'am dattijona, lumshe kyakkyawan idanunsa yayi sannan ya fara yi min magana, xan je yanxu na karbo miki maganin ki, saboda bana son xaxxabin yayi karfi a jikin ki, ki kula min da kanki kinji amaryar dattijo, dago kaina nayi tare da cewa to a dawo lafiya.

Bai dade da fita ba ya dawo hannun shi rike da ledar magani, cikin kulawa ya ballo maganin ya bani amma naki karba, sai da rigima nasha guda daya saboda a rayuwata na tsani magani da allura.

Da misalin karfe sha daya na rana innata ta iso, tun daga nesa na jiyo muryar dattijo na mata sannu da xuwa, ina jin alamun shigowarta dakina na rushe da kuka, karasowa dakin tayi ta same ni ina kuka har da su majina.

cike da damuwa ta karaso inda nake, tambayata ta fara yi, me yake damun ki Niimatullah, kishiyar ki tayi miki wani abu kike wannan uban kukan ko kuma mijin ki,ni dai naga alamun ki baki da wata matsala a tare da ke, kuka na cigaba da yi naki bata amsa har sai da ta fusata.

baxa ki amsa min maganata ba sai na bata miki rai, cikin kuka nace dattijo ne, tana ji na ambaci shi ne ta dakatar da ni, to ya isa kada ki fada min abinda ya hada ku don nasan kwanan xancen, turo baki nayi dan Allah ki bari na fada miki abinda ke faruwa innata.

shi ne Kullum yake...........hannu tasa ta toshe bakina, nace bana bukatar ji ko Niimatullah idan kika kara magana xan dauki takalmana na tafi duk wata mace da kike ganinta a gidan aure hakuri take, saboda aure ibada ne, kuma duk abinda ya xama ibada dole sai an yi hakuri an jure an kuma jajirce wajen yin aiki tukuru, don haka kema ki dage wajen kulawa da mijin ki ta haka ne xaki xama mace ta gari, wacce mijinta xai yi alfahari da ita.

kalaman innata sun shiga kunnena sosai kuma na kudiri niyyar cigaba da amfani da su indai xan xama mace ta gari a wajen dattijona, hirar da muka rika yi kenan har xuwa lokacin da xata tafi gida.

yau ma da riguma muka rabu ji nayi kamar na bita mu tafi, wata kaunarta ce ta kama ni a ranar wuni nayi ina kuka ban iya aikata komai ba wannan dalilin yasa xaxxabina ya kara tsananta saboda kukan da na sha.




*follow me on wattpad @jeeddahtulkhaeer Tijj*

*jeeddahtulkhair😘*💋💋💋💋💋
*MATAR DATTIJO*
💋💋💋💋💋

*©jeeddah Tijjani*
*Adam*
*(jeeddahtulkhair)*

*follow me on instagram @jeeddahtijjani*

*wannan shafin gaba daya sadaukarwa ne gare ku masoyana wallahi a jiya na tabbatar da irin son da ku ke min babu abinda xan ce da ku sai dai godiya da fatan gamawa da duniya lafiya*

My daughater Aysha yar london, Queen maryam (maman surayya),Maijidda saleh, mabaruka Lawal, Billy santaly, Bilkisu mai gado(maman irfan)Hafsat muhd, Rukayyat muhd, Mom Habib....
Ummieee..........
Kaltuma bala Muhammad.
Sadiya Abdulahi....
Fateemah.............
Aisha.............
Habiba dakare........
Hussaina Junaid......
Haleemah Ibrahreem
Bilkisu Basheer...
Fatima m Sani ummu tauheeder...
Subai'at U Sarki....
Maman Khalid
Maman ikraam
Zaynab Adam
Ummu Nur
maman haneepa
Hajjo Ahmed
(beauty)
Ummita❤
Ummu Muhseen
Hauwa Muazu
Farida sani
Waleeda sani
Fatima dutse
Mmn yesmeen
Aysha h waziri
Mmn intisar
Teemash❤❤ Saudat sanee yero
Dafseeyya Ameen
Jzaynerb umman amal
Ummi
Afnan &Afrah
.meerah luv
zainab rimi
.hafsat rimi
.Queen billy,Aysha Ahmad Muhammad
Amina jafar Ahmad jby,ShareefahUmmu farouk,Faiza jibril
Maman safwan ( fauxee)
Zainab Ahmad Ameena medabeeno
Ummuo serjeederh
.Nana Khaslim
.zainab
.Hannatu abidjan
sauran masoya ku yi hakuri da sannu xaku ji sunayen ku.

32

Haka na kwana jikina duk ba dadi banda tunanin innata ba abinda nake yi, Allah-Allah na rika yi gari ya waye na tambayi dattijona xuwa gidan innata.

yau ta Litinin kuma a yau din kwanakin amarcina da dattijo ya kare a yau xai koma wajen abokiyar xamana da kwana gaba daya bana jin nishadi saboda ko kadan bana so nayi nisa da mijina, gari na wayewa na kintsa ko'ina na gidana, shiryawa nayi cikin wasu tsadaddun English wears na nufi wajen dattijona, cike da nutsuwa nake taku dai-dai tare da sakar masa murmushin da a koda yaushe yake saka min shi nutsuwa da nishadi, cikin salon soyayya ya bude min hannunsa na fada jikinsa kwantar da kaina nayi a kirjinsa ina kashe masa idanu,cike da shagwaba na dube shi dattijona!!

cikin nutsuwa ya dago kyawawan idanunsa tare da jan kumatuna na'am my Niimatullah?

cikin siririyar murya na fara yi masa magana, dan Allah alfarma naxo nema wajenka angona, shafa gashin kaina yayi, wace alfarma kike nema yar lelen dattijo? kara narkewa nayi a jikinsa sannan na fara yi masa magana. ka bar ni naje gida naga innata yau da tunaninta na kwana na tashi idan ban ganta ba baxan iya bacci ba. cikin kulawa ya bani amsa gaskiya baxan bari ki fara fita yanxu ba amaryar dattijo, satin ki daya fa rabonki da gidan innah amma har kin kosa ki koma, kuma naga jiya innah taxo ta ganki, baba ma da kanshi ya fada min kada na bari ki fara fita sai bayan wata shida, Allah ya sani ina sonki kuma ina kishinki baxan bari ki fara fita yanxu ba, saboda har yanxu kina nan a budurwar ki babu wani kala da matar aure da kika yi baxan barki fita ba wani ya kwace min ke.

turo baki nayi tare da kara kwantar da kaina a jikinsa haba dattijona duk abin nan da ya faru kace ban xama matar aure ba Allah ni dai na xama kawai wayo kake so kayi min, murmushi yayi tare da kanne min ido, baki xama ba fa Niimatullah da saura saboda sau daya abin ya faru idan kina so na barki sai na kara yi kamar sau uku.

da sauri na dago na kalle shi sau uku fa kace,Allah ni dai a'a murmushi yayi min sannan ya cigaba da magana, tunda baxa ki yarda ba sai ki yi ta xama a gida,na rika xuwa ina dakko innah tana ganin ki amma ke dai baxa ki rika fita waje ba har sai kin xama matar aure sosai. kuka na fara yi masa ina masa magiya amma yayi shiru yaki bani amsa, na lura dattijo mutum ne mai kulle, magiya dai nake masa amma har yanxu yana nan a kan bakansa na mayar da ni matar aure.

cike da kulawa ya dube ni my Niimatullah bari na tashi na tafi wajen maman munir tunda yau a dakinta nake, amma gaskiya kafin na tafi ki bani kulawa saboda nasan xan yi missing din ki kafin na dawo, hawaye naji ya fara xubo min daga idona, yanxu tafiya xa kayi ka bar ni dattijona sai da ka bari na saba da kai sannan xaka tafi ka kyale ni, ni gaskiya baxan iya kwana ni kadai ba sai dai ka mayar da ni wajen innata, hannu yasa ya shiga share min hawayen.

kiyi hakuri my Niimatullah kwana uku kwai xan yi a wajenta sai na dawo gare ki,ina son kwatanta adalci a tsakanin ku ne shi yasa bana son na dannewa kowa hakkinsa, banda wannan dalilin babu abinda xai sa nayi nisa da ke, amma har cikin xuciyata nafi son xama a dakin ki domin shi ne aljannar duniyata, kina min duk abinda nake so kina bani kulawa shi yasa bana son na bar ki ko da na minti daya ne.

cike da shagwaba nace to don yau a dakinta kake sai ka tafi da wuri haka, ai bari xa kayi sai dare xaka je, shafa fuskata yayi ya kara manna ni a kirjinsa, haka ne ka'ida Niimatullah yanxu ya kamata na tafi wajenta naga ya ta kwana ita da yaran mu, tunda dai lokacinta ya shiga kada ki damu xan rika xuwa wajen ki ina ganin ki, Niimatullah ki sani ko da kin yi nisa da jikina soyayyar ki na nan a cikin xuciyata, duk inda naje a duk inda na kasance ina tare da tunanin ki.

rarrashina ya shiga yi tare da romancing dina har sai da na manta dukkan damuwata, kwanciya nayi a wuyan shi ina jin radadin barina da xai yi, don a yanxu na fara sabawa da soyayyar dattijona, ban jin xan iya jurewa rashin shi.


A dai-dai lokacin muka ji an bude kofa an shigo, da sauri muka daga kai don ganin wane ne, matar dattijo ce rike da kugu take kare mana kallo, cikin fushi ta fara masa magana, yau fa xaka dawo dakina amma gashi har kusan karfe goma ban ga keyarka ba saboda tsabar rashin adalci me kake nufi da hakan? saboda ka auro wannan kaxamar yarinya karuwa xaka samu damar wulakanta ni.

shiru dattijona yayi yana naxarin maganganunta, ba karamin xafi kalamanta suka yi min ba, ganin ba shi da niyyar cewa komai yasa nima na mike, cike da tsiwa na bata amsar maganarta, kada ki sake ce min karuwa domin kula da mijinki kika kasa naxo na taya ki kula da shi, kaxawar ki ita ta janyo har ya ganni yaga na dace da rayuwarsa sannan ya aure ni, da kin cika cikakkiyar mace da baki yi sake an yi miki kishiya ba, ki dube shi ki gani da lokacin baya da yanxu daya yake?daga xuwana gidan nan ya canja yayi kiba hankalin sa ya kwanta saboda yana samun abinda yake so. juyawa nayi na koma jikin dattijona na kwantar da kai bisa kirjinsa.

Dattijo yayi mamakin maganganun da Niimatullah ta fadawa Hajiya Maryam, a cikin xuciyarsa kuma yayi nadamar kwancewa uwar yayansa xani da yayi a wajen Niimatullah da har ya fada mata cewa rashin kulawa da shi da bata yi ne yasa ya aureta,(don haka ya kamata maxa su hankalta idan sun je neman aure su daina fadar aibun iyayen gidan su ko don kaucewa samun raini tsakanin uwar gida da amarya).

A fusace ta karaso wajena ta dalla min mari, wata kara mai firgitarwa na saki, cikin masifa take min magana, ni xaki fadawa wannan maganar dan uban ki yaushe kika xo duniya har kika yi wayon da xaki fada min bakar magana, da sauri dattijo yaja hannunta ya fitar da ita,ni kuwa banda aikin kuka babu abinda nake yi.

har falo ya kai ta ya ajiye ta, rarrashinta ya shiga yi kiyi hakuri momyn munir ban auri Niimatullah don na toxarta ki ba, kina da matukar muhimmanci a wajena saboda kece uwar yayana, na auri Niimatullah ne don ta taimaka miki ki gyara rayuwar auren ki da kika bari a baya, idan kika yi kokarin raba ni da yarinyar nan xan iya shiga matsala,ko kina so na fada halaka ne, na rika bin matan banxa? kuma dan Allah ina rokonki ki daina kokarin xagin yarinyar nan kinga tun yanxu ta fara ramawa, sannan ga marinta da kika yi wanda hakan babban kuskure ne tunda dai ba yarki bace, ba kuma kanwarki bace, shawara nake baki ki nisanci yin hakan ko don gudun wata rana kada ku yi doke-doke da ita domin na lura hakurinta ya fara karewa.

shiru tayi tana saurarensa daga bisa ni kuma ta sauke ajiyar xuciya tare da cewa, gaskiya ne abinda ka fada dadyn munir kuma nima naga kuskuren da nayi a baya kuma xan yi kokarin gyarawa, amma ni wannan tsinanniyar yarinyar ce baxan taba kauna ba, kuma wlh mu xuba ni da ita a gidan nan sai ta gudu saboda tsabar wahalar da xan bata.

Godiya yayi mata sannan suka cigaba da hira cikin farin ciki.

Har bayan sallar magariba banga dattijona ba babu shi babu alamar shi, ga shi ba ni da wayar da xan kira shi, kukana ne ya tsananta, a fili nake magana tun yanxu dattijona ya fara wulakanta ni saboda wannan tsohuwar matar tasa wallahi baxan sake kwana a gidan nan ba, bakin kofa na fita inda na tarar da ita a kulle don haka na hakura na dawo, kan gado na fada na rika aikin kuka, a fili na rika fadar da nasan haka aure yake da ban yi shi ba, ji nake kamar na haura katanga na gudu saboda xafin da gidan yayi min, tunanin nasihar da innata take min nayi inda take fada min cewa aure ibada ne dole akwai jarrabawa a ciki, kuma duk inda ibada take tana bukatar hakuri da juriya, wanda idan aka yi hakuri aka jure sai Allah ya bawa mutum dukkan abinda yake nema, wannan nasihar da na tuna ita ta kwantar min da hankali, nayi bacci mai dadi.

gari na wayewa na xuba ido ko xan ga dattijona ya shigo amma shiru bai leko ni ba, don haka na shiga hada kayana ina cigaba da kuka, duk na hargitsa dakin, a dai-dai lokacin naji an turo kofar dakin da nake. muna hada ido nayi gefe da kaina,
cike da nutsuwa ya karaso wajena tambayata ya fara yi, lafiya Niimatullah ina xaki je kike hada kaya?cikin kuka nake masa magana baka sona dattijona gida xan tafi,Allah kuma sai ka sake ni a kan wannan tsohuwar matar taka ka tafi ka barni na kwana ni kadai, Allah sai na koma gidan innata.

rarrashina ya fara yi, kiyi hakuri my Niimatullah wlh ina sonki, kuma aurena da ke mutu ka raba, idan kinga kin fita daga gidan nan sai dai idan ni ne na mutu ko ke kika mutu, amma a auren mu babu saki na riga da na yiwa kaina wannan alkawarin. kuma ban tafi na barki don na wulakanta ki ba sai dan na bata hakkinta kuma na tsayar da adalci a tsakanin ku, kuma jiya ma kin min laifi, me yasa kika cewa matata don bata kula da ni na auro ki, shin yanxu baxan iya yin sirri da ke ba xabina, kina so ki rika tona sirrina ba a wajen innah kawai ba har a wajen mutane, ki sani ina daraja matata saboda uwar yayana ce, baxan bari wulakanci ya shiga tsakanin ku ba, yanxu kina ganin akwai wadda xan bari taxo ta wulakanta ki? ba auren ki kadai ne abinda nayi ba Niimatullah har tarbiyyar ki a hannuna take, baxan bari ki dore a haka ba Niimatullah saboda xan iya mutuwa na barki ko kuma wani abin daban, kuma ina so na hada kan ku ne ku xama tsintsiya madaurin ki daya. gaskiya guda daya ce baxan iya bari ki rika yin abinda bai kamata ba.

jikina ne yayi sanyi da maganganun da dattijona ya fada min, cikin kuka nace baka ga ita taxo ta fara yi min wulakanci ba har dakina kuma ta mare ni.

na sani Niimatullah amma duk inda babba yake babba ne ya kamata ki girmamata ko don yayan da ta haifa, kuma maganar mari duk nayi mata fada a kan haka kema kuma ki rika girmamata kin ji amaryar dattijo.

gyada kaina nayi alamar eh, cike da xaulaya ya fara min magana kin san ma wani abu ne, ni fa xuwa nayi ki bani kulawa don jiyan nan nayi missing din ki sosai, dago ido nayi ina hararasa Allah baka isa ba sai dai ka koma wajenta ai ba kwana na bane, da sauri ya mika hannu ya damko ni, kokawa muka shiga yi banda aikin kuka babu abinda nake yi har sai da yayi abinda ransa ke so sannan ya kyale ni.


*follow me on wattpad @jeeddahtulkheer Tijj*


*jeeddahtulkhair??*??????????
*MATAR DATTIJO*
??????????

*©jeeddah Tijjani*
*Adam*
*(jeeddahtulkhair)*

*follow me on instagram @jeeddahtijjani*

*wannan shafin gaba daya sadaukar wa ne gare ku masoyana*

1-Maearyerm malakso
2-Meela
3-Maryam Bello
4-Jamila d.Gada (Ummu Yasmin)
5-Maman khaleesat
6-Rukayya Sufyan
7-Maman hanan
8-Ummu Islamm
9-Aysha Abdullahi
10-Habiba maman abulkhaeri
11-Aysha Musa
12-Maryam Aminu
13-Aminatu Aliyu
14-Huraera
15-Ummey
16-Sa'adatun hydar
17-Nafisa muhammad
18-Rahma
19-Amina Sunusi
20-Maman Fatyma
21-Khadija Abubakar
22-Ashphat Omar
23-Dija Misku
24-Shamsiyya Faruk
25-Maman mubeenah
26-Ummu hamxa
27-Maman Ummi
28-Aisha Ibrahim
29-Maryam Bello yar pot
30-Maman Amatullah
31-Maman Anas
32-Laelah
33- Sakinatu Umar
34- samira bishir
35-Respectable
36-Zee M
37-fulanee
38-Aisha b nuhu
39-Hajara lawan
40-Maman Aysha
41-Hajjo
42-Aminatou boulkassoum
43-Maryam Auwal
44-Hauwa'u hafizu alkali
45-Hauwa'u T usman
46-Amsopy
47-Ummu hanan
48-Maman Seeyam
49-Maman Amatullah
50-Rasheeda
51-Maman Ra'iz
52-Aisa yer meduguri
53-Belau sokoto
54-ummyn al-ameen
55-Salma Nura
56-Ummu hanif
57-Ummu Ameera
58-Mom khairat
59-Queen feedy
60-Mymmyn farhan
61-Ubiyyat A Tahir
62-khadijah ummi
63-Aysha Sulaiman Ahmad
64-Beeboh

33

Bai wani dade a dakina sosai ba ta rika kiransa a waya ya dawo gareta, fuskarsa cike da damuwa ya dube ni, xan koma wajen momyn munir tana kirana, bata fuska nayi tare da yin gefe da kaina, ba tare da na bashi amsa ba na cigaba da tunanina.

matsowa yayi daf da ni tare da dago fuskata kiyi hakuri nima ba a son raina xan tafi na bar ki ba, daga yau saura kwana daya na dawo gare ki da fatan xaki shirya min tarba mai kyau, don kin san ke din ta daban ce komai naki na musamman ne, fuskata a kasa na amsa masa da to.

A sanyaye ya tashi ya fita, bin sa nayi da kallo ina tunanin irin matsalar da xan shiga idan baya kusa da ni, ji nayi kamar nasa masa kuka ya dawo dakina, xafi xuciyata ta rika yi, wani kishi ne ya taso min ji nayi kamar na rusa ihu da sauri na rika karanto innalillahi wa inna ilaihi raji'un ban taba tsammanin haka xafin kishi yake ba, kwantar da kaina nayi tare da lumshe idanuna ina tunanin mijina, na saba kwana a kan kirjinsa da jin harbawar numfashinsa yau kuma da pillow xan yi matashi, hawaye naji na shirin xubo min, a ranar cikin damuwa na wuni tun daga xuwan da yayi min da safe bata kara barinsa ya leko wajena ba.

Da misalin karfe tara nayi wanka na fara shirin kwanciya bacci, sallama naji an yi min a falo cikin hanxari na fito don ganin mai sallamar, daya daga cikin yayan dattijona na gani, cike da ladabi ya gaida ni tare da cewa dadynsa na kirana,cikin sakin fuska na amsa masa da ina xuwa.

Hijabi na saka har kasa, kasancewar kayan bacci ne a jikina, kulle kofa ta nayi sannan na nufi wajen dattijona, a bakin motarsa na tarar da shi yanayin sa kawai na kalla nasan yana cikin damuwa.

cike da nutsuwa na karasa wajensa, a hankali ya dago ido yana kallona tare da cewa ai na xaci baxa ki xo ba Amaryar dattijo, murmushi nayi me xai hana ni amsa kiran mijina sai dai idan ko ba ni da lafiya ne.

Daga min hannu yayi tare da cewa matso nan xa mu yi wata magana, A hankali naja jikina na karasa gare shi tare da kwantar da kaina a wuyan shi, farin gashin da ke kewaye a fuskar shi na shafa kasancewar nayi missing din shi, cike da soyayya ya fara min magana.

Ina cikin wani yanayi Niimatullah,matar nan ta kasa kulawa da ni kuma ta hana ki kula da ni na rasa yadda xan yi da rayuwata, shi ne nace ki taimaka kixo ki taya ni hira a nan ko xan samu sauki da sauraren muryar ki.

cike da shagwaba na bashi amsa, ni dai baxan iya ba tunda ba lokacina bane dakina xan koma nayi baccina, ka koma wajenta ka lallabata nasan xa tayi maka duk abinda kake so.

ina kammala fada masa na kama hanyar komawa bangarena, jawo ni yayi ya hada fuskata da tasa da alama yana cikin yanayi, kamar xai yi kuka yake min magana.

Baxa ki tallafi mijinki ki tsamo shi daga fadawa halaka ba ko, da kika ce na koma wajenta yanxu haka kofar dakinta a kulle yake ina kike so naje naji dadin rayuwata,ke da kike sona kuma xaki juya min baya Niimatullah wane yanayi kike tunanin xan fada idan kika bar ni, na dade da fada miki kice nutsuwata kece farin cikina.

kaina a sunkuye na bashi amsa, kayi hakuri dattijona baxan iya danne hakkin wata ba,tunda lokacinta ne kaje ka sameta idan bata baka kulawa ba, ka dawo xan kula da kai.

fuskarsa cike da fara'a ya dube ni da gaske kike amaryar dattijo? cikin kulawa nace masa eh, rungume ni yayi yana kissing dina, na gode Allah yayi miki albarka Niimatullah, dole ta rika bakin ciki da ke kin fita biyyaya kin fita komai, na gode amaryata, cikin rada nake masa magana kaje yanxu ina jiranka a cikin gida.

cikin rawar jiki ya tashi ya nufi bangaren Hajiya maryam, sallama ya yi amma shiru ba a amsa masa ba, dudduba dakin ya shiga yi ko xai ganta, a bakin brander ya hangota tsaye, jikinsa a sanyaye ya karaso wajenta.

fuskar sa cike da murmushi ya bude baki xai mata magana, hannu ta daga masa, kai malam dakata tsohon munafuki duk abinda kake yi a kan idona, ka koma wajen kaxamar matarka tayi maka duk abinda

Please Login or Register in order to submit comment