Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kaina cikin rashin son nisa da innah da baba.
innah ce ta shigo dakin da nake rarrashina ta fara yi gami da kwantar min da hankali, kiyi hakuri niimatullah duk ya mace yar gidan wani ce, mu ma duk haka aka rabo mu da gidajen iyayen mu tun ban kai kamarki ba gashi nan yanxu har abin ya xame mana jiki, kiyi hakuri ibada xaki tafi Allah xai baki kada, cikin kuka nake magana ni na fasa samun ladan innah a barni a wajen Ki na cigaba da xaman, ko kuma ki biyo ni gidan da xan xauna.

Cike da kulawa ta dube ni,imar ai ba a haka Niimatullah yadda na Saba kema haka zaki saba a hankali, kukana na rika yi har da majina.

A dai-dai lokacin ne malamar da ke min gyaran jiki ta iso, gaisawa suka yi da innah cike da kulawa take min magana.
"niimatullah me ya same ki kike kuka haka har da su majina" idanuna cike da hawaye na dubeta, malama dama idan xa a yiwa mutum aure dole ne sai ya bar gida? Dan Allah ki roki dattijo ya kyale ni a wajen innata.

Dariya ta rika yi sosai lallai niimallah da sauran ki, a ina kika taba ganin an yiwa mace aure ta xauna a gidan su, ko a garin gaba-gaba ba a taba yi ba ballanta a wajen masu hankali, dole sai kin bar gidan innah ta haka ne xaki fi samun ladan da kowace matar aure take samua gidan mijinta, idan aka barki a nan me aka yi kenan ai anyi ba ai ba.

Kuka na cigaba da yi ina shura kafata ni a lallai baxan tare a gidan dattijo ba,kiran wayar innah aka yi da sauri ta mika hannu ta dauka, dattijona ne ya kirata yake fada mata cewa ya iso tare da wadanda zasu jera min kayan dakina baya so ya ka isu gidan kai tsaye ba tare da an samu wani wakili daga bangarena ba, saboda gudun gorin matarsa, godiya innah ta rika yi masa har da dan kukanta tana sa masa albarka.

Yan uwan mamana daga bichi duk sun iso don haka aka samu wasu suka tafi jera min dakina

dakin innah muka shiga inda aka fara gyara ni, bayan ta gama shafa min wasu abubuwa ne ta bani wani abu a kwalba wanda take fada min cewa tsumi ne da ke karawa mace ni'imar jiki, har sai da ta koya min hadinsa, inda ta fada min cewa xan samu sassaken baure da kanumfari da citta kadan da mazarkwaila da minannas da kuma, xan fara dafa sassaken bauren ne idan ya dahu na tsame shi na xuba kayan hadin da ta lissafa min a baya, idan ya dahu na sauke ta koya min ne kasancewar tana so na dauwama ina yin shi. godiya nayi mata duk da cewa ban gane abinda take nufi ba game da amfanin abinda ta fada min.

Bayan na kammala shan wannan tsumin da ta bani lalle ta dakko ta matsa lemon tsami ta xuba gishiri da kuma man zaitun kadan murje min jiki ta shiga yi sannan ta fada min amfaninsa don gyaran jiki ne, kuma ta fada min larabawa da mutanen sudan sukan yi amfani da wannan hadin don gyaran jikin su. tayi min amfani da turaruka masu kyau da kamshi duk wata gaba ta jikina sai da aka shafa mata turare.

Daga karshe ta dakko min wani hadi na musamman wanda ta fada min cewa na gyaran breast ne kuma muddin mace ta juri amfani dashi breasts dinta baxa su taba faduwa ba, shi ma ta fada min cewa larabawa ke amfani da shi, amma bata koya min hadin ba saboda tace sirrin sana'arta ne.

bata kammala gyara ni ba sai wajen sallar Magariba nayi kyau na fita, kana matsowa wajena xaka ji ina tashin kamshi na musamman, daga karshe taja kunnena a kan daina amfani da ruwan sanyi wajen tsarki ta koyar da ni dafa ganyen magarya da lalle, tace na rika amfani da su a lokuta da dama saboda rigakafi ne na kamuwa daga cutar infection.

Ba karamar godiya nayi mata ba, innah kuwa sai sa mata albarka take yi saboda malama tana iyakar kokarinta wajen ganin na xama sarauniya a wajen dattijona.

bayan nayi sallar isha'i na koma daki na kwanta saboda ba karamar gajiya nayi ba, ga tunanin barin gida da ya sanya jikina yin sanyi, ji nayi kamar xaxxabi ke shirin kama ni, innah na gani ta shigo kiran sunana tayi niimatullah tashi kije soro mijinki yazo yana son magana da ke.

Bata fuska nayi haba innah bacci fa nake yi kice masa kawai bana nan, kallona innah tayi tare da hararata bana son gaddamar nan fa niimatullah tashi kije kika sani ko abu mai muhimmanci xai fada miki, raina a bace na tashi na nufi soron, a tsugunne na same shi da alama ya gaji da tsayuwa ne shi yasa ya xauna.

karasawa wajen shi nayi tare da dan taba kansa a hankali ya dago ya dube ni yana murmushi sai an ja min aji xa a xo ko niimatullah?

Cike da shagwaba nake masa magana, ba kai bane ka tashe ni ina baccina mai dadi, tashi tsaye yayi yana dubana tare da yin murmushi

ke da kin kusa xama tawa wata rana ma baccin xan hana ki yi gaba daya, cike da mamaki nake kallonsa Allah baka isa ka hanani baccina ba tabdi jam kayi kadan yaro.

Murmushi yayi tare da lakace min hancina, xaki ga nayi kadan yarinya saura dai kwana uku Ki shigo hannuna don haka ki daina tsiwa da cika baki, kallon shi nayi kamar xan kuka, Allah tunda haka kace sai na fasa auren tunda xaluntata xaka rika yi.

Hannuna ya riko yana min murmushi ina matukar sonki baxan iya xaluntarki ba babyna, kuma da nace zan hana ki bacci ai ba wani abu bane duk soyayya ce xata sa hakan, amma fa kema a lokuta da dama kina hana ni bacci, da sauri na dube shi yaushe na hana ka bacci banda sharri fa.

dariya ya rika yi min wallahi kina hana ni niimatullah ko baki sani ba? da sauri na amsa masa da eh fada min lokaci da ranar da na hana ka.

cikin salon soyayya yake min magana, idan dare ya tsala na juya ban ganki a gefena ba sai tunanin ki da shaukin ki su hana ni runtsawa, ko yau din nan ban yi bacci ba saboda begen ki.
Turo baki nayi Allah ba kada kunya dattijon nan, murmushi yayi tare da kai hannu xai kamo ni, da sauri na kauce, zaki ga ba nida kunya yanxu baki fara ganin komai ba my ni,ima sai kin shigo fadata.

hakuri na shiga bashi, kayi hakuri to kana da kunya mantawa nayi na fada, murmushi yayi tare da riko hannuna ina sonki niimatullah ga tsiwa ga tsoro.

cike da shagwaba na fara yi masa magana ka fada min abinda ya kawo ka kaga sauro har ya fara cizona, dan murmushi yayi gami da shafa farin gemunsa wanda ya sha gyara, yi hakuri mai niimatullah nima ba a son raina na kira ki yanxu ba don nasan kin gaji da yawa, dama xuwa nayi mu yi magana a kan abubuwan da xa a yi a lokacin bikin mu.
langwabar da kaina nayi ni babu abinda xan yi kawai innah ce xata gayyato kawayenta, ni kaga ko kawayen ma ba nida su.

Murmushi yayi to ni dai sai an yi ko baki da su sai kin nemo su duk inda suke, bata fuska nayi xan yi kuka
A'a ni dai ka bar kudinka tausayinka nake ji kaga ka kashe min kudi masu yawa, yau ma ka siya min kayan daki ka bar hidimar haka kada kudinka ya kare mutane su ce wayo nake maka.
Dariya na bashi sosai kina burge ni da yawa idan kika xaro wani zancen, waye xai ce xaki min wayo kin ganki fa yar karama, harar shi nayi ka daina kallona haka idan na tashi girma sai na fika kiba

xaulayata ya rika yi, duk nacin da yayi a kan ya hada min dinner naki yarda, da xa mu yi sallama ya kirgo kudade masu yawa ya bani wadanda baxan iya fadar adadinsu ba kasancewar ban tsaya na lissafa ba sallama yayi min ya wuce gida.

Innah na dankawa kudin ko komawa ta kansu ban yi ba,saboda babu wani abu da zan yi da su, komai innata tana iya bakin kokarinta wajen ganin ta faranta min.


*jeeddahtulkhair😘*
[10/18, 11:22 PM] It'z B Y ebrerheem: 💋💋💋💋💋
*MATAR DATTIJO*
💋💋💋💋💋

*©jeeddah Tijjani*
*Adam*
*(jeeddahtulkhair)*

*follow me on instagram @jeeddahtijjani*

*dedicated to Zainab Zubairu (Mrs Mustapha Ali Busuguma)*


26

Ban fito ba sai da naji ana kiran sallar asubah, leko da kaina na rika yi ko xan ganshi tsaye yana jirana, A hankali na bude key na fito tarar dakin nayi ba kowa don haka hankalina kwance na koma na xauna, ban kwanta ba sai da nayi sallar asubah, bacci mai nauyi ne ya dauke ni kasancewar jiya ban samu na rintsa ba.

shi kuwa dattijo dakinsa ya koma ya kwanta yana tunanin yadda xai bullowa al'amarin Niimatullah, wani irin kwadayinta da tausayinta yake ji banda haka babu abinda xai hana shi karbar hakkin shi a wajenta, tashi yayi ya nufi bandaki ya yi wanka sannan ya fita masallaci don yin sallar asubah yana idarwa ya nufi dakinta, kwance ya tarar da ita tana ta sharar bacci, a hankali ya taka har ya isa wajen da take, wani kyau take yi masa idan tana bacci, matsawa yayi ya xauna a gefenta yana shafar gashin kanta xuwa bayanta duk abin nan da yake yi bata san a duniyar da take ba saboda baccin da yayi awon gaba da ita, murmushi yayi gami da lumshe ido a xahiri yace ina sonki Niimatullah.

wannan maganar da yayi ita ta farkar da ni daga baccin da nake yi,da sauri na tashi jikina na rawa abinda ya fara fitowa daga bakina shi ne kayi hakuri dattijona, murmushi yayi hannun shi rungume a kirjinsa, menene kika wani xabura kin san dadewar da nayi a nan kina bacci?da sauri na amsa masa da a'a, shafa bayana yayi ki daina jin tsoron babu abinda xan miki da nayi niyyar yin wani abu da ke da tun daxu labari ya sha banban.

kwantar da kaina nayi a kirjinsa ina shafa fuskarsa, na gode dattijona yaushe xaka kaini gida naga innata, tsare ni yayi da ido tunda baki bani abinda nake so ba yaushe xan kai ki gida wani ya ganki ya xaci har yanxu budurwa ce, ki bani dama na xamar da ke matar aure a ranar da kika xama xan kai ki gida.

dan turo baki nayi, yanxun ma ai matar auren ce ni Allah baxan yarda da wannan dokar taka ba, daga kafada yayi tunda baki yarda ba shikenan haka xaki yi ta xama a gidan nan, ko xaki shekara dari baxa ki je ko ina ba muna tare a nan.

kuka na fara yi, dan Allah ka bar ni naje naga innata, dago fuskata yayi wai baki ji abinda nace miki bane Niimatullah?cikin kukan nace naji amma dokar taka ce tayi min tsauri dan Allah kayi min afuwa, murmushi yayi xan miki babyna ai ina sonki amma yanxu dai ki bani dama na nuna miki irin son da nake miki, shafa jikina ya fara yi tare da kokarin cire min kayana da karfi na kwala ihu Allah ka bari na hakura da xuwa gidan, nan da nan naga yanayinsa ya fara sauyawa kokawa muka shiga yi da shi sosai da kyar da magiya na samu kaina, sauka yayi daga gadon yana kallona ina sha'awar ki Niimatullah amma kina ja min rai, duk ranar da kika shigo hannuna xa kiyi baya ni dallah-dallah.

turo baki nayi xan fara kuka me kake nufi da wannan sha'awar ne ni wlh bana so kake fada min, kan gadon ya dawo yana kallona tare da rike hannuna, ina sha'awar hannunki Niimatullah mikewa nayi ina dukan kasa Allah bana so dattijona, murmushi yayi wannan tsallen da kike min ma sha'awa yake bani, cigaba da buga kafata nayi sake dago fuskata yayi komai na jikin ki sha'awa yake bani, kuka na rika ina cewa bana so.

mayafina naja na dauki akwati nace masa sai na tafi gida, ina isa bakin kofar na ji ta a kulle, cike da tsokana yake min magana ki tashi ki tafi ki gayawa innah yadda muka yi da ke,ita ma fada xata yi miki idan da duka ma sai ta hada miki da shi, dawowa nayi na fara yi masa magiya a kan ya daina fada min irin wadannan maganganun, lallashina ya shiga yi daga nan ya fara shafa ni gami da aika min da wasu sakonni, matse ni yayi jikin bango yana mayar da numfahi duk ihun da nayi akan ya sake ni amma yaki sai da ya gama jagwalgwala ni sannan ya kyale ni.

Bayan mun yi breakfast, ya ja hannuna muka tafi bangaren kishiyata a xaune muka sameta ta dora kafa daya kan daya wani irin kallo take bina da shi,ni kuwa ina manne jikin dattijona na dora hannuna a kan kafadar shi saboda bana son na rika hada idanu da ita, waje muka samu muka xauna cike da kulawa yace na gaidata, ban yi masa musu ba na gaida ita, a yatsine ta amsa min gyaran murya yayi sannan ya fara magana.

Alhamdulillah an yi biki lafiya an gama lafiya ga amarya an kawo dakinta don haka hajiya ina kira a gareki ki rike ta amana ki dauketa a matsayin yar da kika haifa kada ki rika yi mata abubuwan da bai kamata ba, kuma idan kika ga xata karkace ki rika yi mata fada, domin diya ce a wajenki, ke kuma niimatullah ki riketa a matsayin mahaifiyarki duk abinda xa kiyi ki rika neman shawarar ta ina addu'ar Allah ya hada kanku ya baku xaman lafiya Allah ya bani ikon yin adalci a tsakanin ku, wani kallo ta dago tayi masa, daga murya tayi ta fara yi masa magana.

kai saurara kaji baxan karbi amanar wannan yarinyar mai kama da karuwai ba dubi fa wai amarya ce amma kalli yadda ta wani rukunkumeka, wannan karuwar xaka bani amana sam baxan karba ba wlh xaman aure taxo yi kowa yaji da kansa, tashi tayi ta bar mana dakin, fuskarsa cike da damuwa ya dube ni kiyi hakuri niimatullah kiyi mata biyayya kinga ta haifeka. gyada kaina nayi alamar eh har ya tashi xamu tafi na saka masa kuka cike da kulawa ya dube ni me yake damunki Niimatullah cikin shagawba nace ni sai ka goya ni baxan tafi da kafata ba, sunkuyawa yayi ya dauke ni a bayan sa ya fito dani ta cikin window ta hango ya dauke ni, ji nayi tana xagina tana aibata mu, shi kuwa ko ta kanta ma bai bi ba, kai tsaye dakina muka wuce muna shiga ya dire ni a kan gado.

kallona ya shiga yi kinga irin halin da nake ciki a gidan nan niimatullah don haka fa na auroki ki share min hawayena ki cigaba da bani hakkina na aure, amma gashi nan kema kina guduna, shafa gashin da ke kewaye a fuskarsa nayi,ba gudunka nake yi ba dattijona dan Allah kayi hakuri ni bana son abin ne gaba daya, rarrashina ya shiga yi yana fada min muhimmancin hakan ga rayuwar ma'aurata da kuma irin halin da xai shiga a duk lokacin da na hana shi kaina, hirar mu muka rika yi cikin farin ciki da annashuwa.


*follow me wattpad @jeeddahtulkhaeer Tijj*


*jeeddahtulkhair😘*
[10/18, 11:22 PM] It'z B Y ebrerheem: 💋💋💋💋💋
*MATAR DATTIJO*
💋💋💋💋💋

*©jeeddah Tijjani*
*Adam*
*(jeeddahtulkhair)*

*follow me on instagram @jeeddahtijjani*

*dedicated to Aysha sammani Alatu (maman kauthar) ina miki murnar samun baby Allah ya raya shi*

*ya Allah ka bawa diyata Aysha yar London lafiya*

25


Dattijo ne ya turo kofar dakin ya shigo sanye yake da farar shadda wadda tasha aiki da farin xare, takalmin dake kafarsa ma fari ya sanya, hularsa ma fara ce, xan iya cewa duk abinda ya sanya a jikinsa fari ne, sanye yake da farin glass a fuskarsa, hannu shi kuwa dauke yake da ledoji wanda baxan iya bayyana abinda ke cikin su ba. kasancewar ta cikin mayafi nake hango shi.

yana murmushi ya karaso wajena, sallama yayi gami da ce min amarya kin sha kamshi, ledojin da je hannun shi ya ajiye a kan side drower sanan ya hau kan gadon da nake, kusa dani ya xauna tare da bude lillibin da ke rufe a fuskata, ni kuwa banda aikin kuka babu abinda nake yi, cikin kulawa yake min magana my niimatullahi meye na kuka, bayan kina tare da mijinki, godiya xamu yiwa Allah da ya cika mana burin mu na xama ma'aurata, kiyi hakuri ki daina kuka haka kowace mace take samun kanta,a kawota gidanta har ta girma ta haifi yaya ita ma ta zama uwa, hada ni yayi da jikinsa tare da cire min mayafin dake sanye a jikina rarrashina ya shiga yi gami da shafa kaina tamkar jaririya, cikin salon soyayya yake kallona, wow!! amaryata kin yi kyau sosai, don ma kukan nan da kika
ya bata min kwalliyata dubi fa har idonki ya fara kumbura.

turo baki nayi to ba innah ce taki biyo ni ba, dariya yayi gami da cewa kiyi hakuri, a cikin daren nan zan kai ki har gidan innah amma ki share hawayenki ki daina kuka tukunna.

handkercheif yasa ya fara goge min hawayen da ya cika fuskata, cike da nutsuwa ya sake kallona tashi mu yi alwala mu yi sallah mu godewa Allah a bisa niimar samun juna da yayi mana.
Hannuna ya kama xai mikar da ni tsaye amma na makale naki tashi, cike da shagwaba nake masa magana baxan tashi ba har sai ka min alkawarin xaka mayar da ni wajen innah yanxu, murmushi yayi tare da kwantar da ni a kirjinsa, xan kai ki babyna tashi mu fara gabatar da sallah sai mu yi magana, alwala muka dauro inda muka yi nafila sannan muka yi addu'a muka shafa.
ledar da ya shigo mana da ita ya dakko, inda ya fara fito min da kayan da ke ciki, kayan kwalliya ne da kayan shafe shafe da kuma sleeping drees na haduwa, daya ledar kuma kaxa ce da kuma fresh milk, cikin nutsuwa ya dakko min kaxar karbi kici babyna nasan kina jin yunwa, gefe nayi da kaina bana ci, dago fuskata yayi me yasa baxa ki ci ba Niimatullah, cikin shagwaba nace masa ance maganin bacci kuke sakawa a ciki, dariya yayi tare da cewa wannan tunanin ki daina yinsa karya aka fada miki, lallaba ni ya fara yi a kan naci kaxar amma naki, tashi yayi ya shiga kitchen ya dakko cup, fresh milk din ya tsiyaya min a cup karbi ki fara sha kinji babyna kurba nayi na ajiy shi a gefe, matsowa yayi daf dani tare da dafa kaina so nake yi ki shanye gaba daya tunda kin ki cin naman na riga na karbi amanar ki a wajen baba hakkina ne na kula da ke my niimatullah, karba nayi na fara sha, kadan na sha na ture hannun shi, bayan mun gama sha ne ya dauki kayan ya tattara ya kai kitchen.

komawa nayi gefe na jingina kaina jikin pillow wani fargaba da tsoronsa ne ya xiyarci xuciyata, tashi yayi ya shiga bathroom jin shi nayi yana wanka daga bisani ya fito daure da towel, ina kallon shi sau daya na sunkuyar da kaina wani kwarjini ya kara min a idona ban taba xaton haka dattijona yake ba. fita yayi sanyo jallabiya fara sannan ya dawo ya xauna.

cike da kulawa yake min magana Niimatullah tashi kema kije ki watsa ruwa, cikin dasasshiyar muryata na amsa masa da nayi wanka tun a gidan innah, cike da xaulaya ya dube ni ki tashi kije kiyi ko na kai ki nayi miki kinga yau dai mu biyu ne babu innah ballantana kiyi min tonon silili.

da sauri na tashi saboda yanxu ina tsoron wasan sa yanxu xai mayar da abin gaske, shiga bandakin nayi na fara watsa ruwa sai da na saka kayana complete sannan na fito, kallona yayi yana murmushi da wannan kayan xaki kwanta Niimatullah cike da tsiwa nace mashi dam da wanne xan kwanta, ni da su na saba kwana a gidan mu, jan kumatuna yayi tare da cewa nan ai ba gidan ku bane nan gidanki ne kuma gidan mijinki abinda nake so shi xa a yi, tashi yayi ya jawo ledar da ya shigo da ita, wata fitinanniyar mitsitsiyar riga ya dakko min tare da cewa, da wannan nake so kiyi bacci daga yau na hana ki bacci da atamfa.

cikin shagwaba na mayar masa da amsa ni Allah baxan saka wannan kayan kafiran ba, matsowa yayi ya rungume ni yana sumbatar goshina, shi nake so ki saka min Allah ko kuma yau din nan mu yi yaki ni da ke.


kokarin xame jikina na shiga yi amma na kasa cikin kuka nace masa, ka sake ni xan saka maka,a hankali ya cika ni na koma gefe ina mayar da numfashi,lumshe idanu yayi yana sake kallona, ki saka min kin ji my Niimatullah idan baki saka min ba waye xai saka min? cikin tsiwa nace ga matarka can ita xata saka maka, tasowa yayi ya matso kusa da ni da sauri na matsa tare da kwala ihu xaunawa yayi yana min murmushi ki daina tsorona ni ba abinda xan miki, da yaga dai ba nida niyyar saka kayan ne ya kyale ni komawa kasa nayi na xauna.

takowa yayi har inda nake ya tsaya daga baya yana min magana ya kamata mu kwanta Niimatullah nasan kin gaji nima na gaji sosai tashi kixo ki kwanta, gyara min gado ya shiga yi, tashi ki kwanta kin ji babyna, makale kafada nayi tare da tambayarsa kai a ina xaka kwana.

shafa gashin kansa yayi a kusa da ke mana, kuka na fara yi Allah baxan kwana tare da kai ba, dariya yayi min tare da cewa kiyi kwanciyar ki da wasa nake yi nima dakina xani na kwanta, kashe min fitilar dakin yayi sannan ya fita ban san ina xai je ya kwana ba.

kwantawa nayi na dade ina mutsu-mutsu kafin bacci ya dauke ni saboda tunanin innata,cikin dare naji tashin numfashi a bayana a xabure na juya don ganin wane ne dattijona na gani kwance ya manna bayana da kirjinsa, muna hada ido ya sakar min murmushi tare da juyo da fuskata sake manna ni da kirjinsa yayi tare da kissing dina, cikin kuka nake tambayarsa meye haka dattijona kai da kace xaka yi bacci me yasa ka dawo xaka hana ni nawa baccin? cike da soyayya yace matukar ban hada jikina da naki ba baxan iya bacci ba niimatullah ki taimaki mijinki ki barni naji dumin ki.

kuka na fara yi masa, kokawa muka shiga yi da shi, cikin shagwaba yake min magana

kiyi hakuri my niimatullah na raya mana wannan daren da muka dade muna jiransa baxan iya hakuri da ke a halin yanxu ba ihu na shiga yi ina kiran innah da kyar na kwace na fada bandaki na mayar da kofa na kulle ina mayar da numfashi.

buga kofar bandakin ya fara yi yana rokona na bude na fito har da dan kukan shi amma naki bude masa, nima cikin kukan na ke bashi amsa Allah baxan fito ba tunda haka abinka yake, kuma gobe da safe xan tafi gida duk abinda kayi min sai na fadawa innata kuma baxan sake kwana a gidanka ba,lallabani ya shiga yi ki fito Niimatullah indai kika fito yanxu xan dauke ki na mayar da ke gida na miki alkawari, kin fitowa nayi duk nacin da yayi min haka na kyale shi tsaye yana ta faman bugun kofa.

*follow me on wattpad @jeeddahtulkhaeer Tijj*

*jeeddahtulkhair😘*
[10/18, 11:22 PM] It'z B Y ebrerheem: 💋💋💋💋💋
*MATAR DATTIJO*
💋💋💋💋💋

*©jeeddah Tijjani*
*Adam*
*(jeeddahtulkhair)*

*follow me on instagram @jeeddahtijjani*

*dedicated to Aysha sammani Alatu (maman kauthar) ina miki murnar samun baby Allah ya raya shi*

*ya Allah ka bawa diyata Aysha yar London lafiya*

25


Dattijo ne ya turo

Please Login or Register in order to submit comment