Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

min magana, saboda karbar da kika min hannu biyu yasa na baki wannan tukwicin, ki duba ki gani gumbar mata ce tana kara niima sosai yadda angon nan naki yake xumudi a kan ki idan kika sha har kyautar mota xai baki, wata mata ce take kawo mana tallanta office, ina siya sosai kuma naji dadinta, shi yasa kema na siyo miki, kada kiyi wasa kisha yana da kyau.

Karba nayi tare da yin godiya sannan muka yi sallama.

*follow me on wattpad @jeeddahtulkheer Tijj*


*jeeddahtulkhair💋💋💋💋💋
*MATAR DATTIJO*
💋💋💋💋💋

*©jeeddah Tijjani*
*Adam*
*(jeeddahtulkhair)*

*Duk masoyin wannan littafi na Matar dattijo ya taimaka ya saka dan uwana a cikin addu'a Allah yaji kansa ya gafarta masa,Allah yasa aljannah ta xama makoma a gare shi😭*

40

Jujjuya kayan na shiga yi xuciyata cike da mamakin wannan kyautar da ta yi min, tambayar kaina na shiga yi ya aka yi tasan ina bukatar wannan abin da har xata kawo min tace nasha ko dai dattijo ne ya fada mata baya jin dadin tarayya da ni shi yasa ta kawo min? Irin tambayoyin da na rika yiwa kaina kenan,xuciyata bata amince na sha abin ba saboda ni ban gama amincewa da ita ba,sannan ni gaba daya shaye-shayen maganin mata baya burge ni, wurgi nayi da shi gefe daya na koma kan kujera na cigaba da kallona.

A bangaren Hajiya maryam kuwa, samun kanta tayi cikin farin ciki saboda ta fara samun hadin kan Niimatullah domin ta fara amincewa da ita, don ta haka ne xata samu ta cika burinta, waya ta dauka ta kira kawarta ta shaida mata yadda suka yi da Niimatullah nan ma dai wata shawarar ta sake bata a kan kulle-kullen da xa a yi a barar da cikin Niimatullah.

Da misalin karfe hudu na tashi nayi sallar la'asar bayan na idar nayi addua na roki Allah a kan ya kare ni daga dukkan sharrin da xata kullo min, kai tsaye kitchen na shiga na fara kokarin dora girki sallama naji don haka da sauri na fita don ganin mai sallamar, maman munir dai na sake gani cikin sakin fuska ta fara tambayata.

Da fatan dai Kin sha abin nan Niimatullah, yanzu muka yi waya da kawata ta kara jaddada min bayani a kan ingancin maganin shi yasa na sake dawowa nayi miki tuni, murmushi nayi tare da bata amsa nasha tun daxu Aunty yanzu haka na fara jin canji a jikina alamun maganin mai kyau ne.

Rausayar da kai tayi tana murmushi,baxa ki gane kyansa ba ma sai dare yayi,rufe fuska nayi kamar ina jin kunya bata san gwalo nake mata ba a xuciyata nace ta Allah ba taki ba.

Har xata tashi ta tafi ta dube ni au na manta ban fada miki ba,ko da kin ji cikinki da mararki na ciwo kada ki damu kice xaki sha wani abu ki bari xaki dawo normal saboda dama haka dabi'ar maganin take.

Girgixa kaina nayi tare da cewa na gane, ina godiya da abin arxiki Allah ya bar xumunci, lumshe ido tayi ba komai ai mun xama daya kanwata

Kitchen na koma na cigaba da aikina bayan na gama na yi wanka don tarbar dattijona, tun daga nesa naji yana ta kwala min kira da hanxari na fita ina ganinsa ya sakar min wani kayataccen murmushi tare da bude min hannayensa na fada jikinsa na rungume shi, daukana yayi cak ya kaini daki cike da shagwaba nake masa magana

Ka tafi office ka kyale ni ina ta missing dinka babynmu sai kuka yake bai ganka ba,murmushi yayi tare da bude cikin yana shafa shi hakuri ya rika bawa babyn kamar yana ganinsa sannan ya dawo gare ni ya sumbaci goshina cikin salon soyayya yake min magana.

Yau kawai xaman hakuri nayi da ban dawo gida na ganki ba niimatuna,ina fatan dai kin kula min da kanki kwantar da kaina nayi a jikinsa na gyada kaina alamar eh.

Cikin shagwaba na dube shi, babyna bari na tashi na kawo maka abinci, kallona yayi ya dan bata rai yanzu duk maganar da nayi miki a kan kada kiyi girki sai da kika yi, ni nayi fushi ma na daina kula ki.

Juyar da kansa gefe yayi yana kumbure-kumbure, cikin salon jan hankali na kewaya na fara bashi hakuri, a cikin kankanin lokaci na shawo kansa ya hakura.

Mayar da kaina jikinsa nayi ina masa kallon nayi kewarsa, cike da soyayya na dube shi wallahi kullum kara kyau kake yi dattijona komawa kake yi kamar saurayi dan shekara ashirin da biyar musamman idan kayi kwalliya.

Murmushi ya hau yi da dukkan alamu yaji dadin maganar da na fada masa, shafa fuskata yayi lallai Niimatullah yau xuga ni kawai kike yi, murmushi nayi Allah gaskiya na fada dattijona kana Kara kyau musamman ma idan kana bacci, murmushi yayi na gode niimata Allah ya bar mu tare amsawa nayi da ameen, sake mayar da kallona nayi gare shi.

Yauwa na tuno wani albishir da nake son yi maka, gyara xama yayi tare da cewa wane albishir ne amaryar dattijo, murmushi nayi kafin na fada maka sai ka bani goron albishir tukunnah, lumshe idanunsa yayi ki fada min ko nawa ne nayi alkawari xan biya.

Gyara murya nayi yau uwar gidanka taxo mun yi sulhu ta nemi na yafe mata a kan dukkan abinda tayi min a baya tace kuskure ne, tsare ni yayi da ido yana saurarona maimakon naga fara'a a fuskarsa sai naga ya bata fuska, lura da yanayinsa nayi don haka na tsayar da maganar na shiga tambayarsa, ya naga ka bata rai dattijona? Dole raina ya baci haka kawai sai da taga bana nan xata xo tace ku yi sulhu me yasa tun ina nan bata xo da maganar ba ni sam ban yarda da wannan abin ba bana son na rika ganin kafarta a cikin gidan nan.

Cigaba da tambayata yayi bayan wannan abin sai kuma me ya faru? Murmushi nayi ya naga duk hankalinka ya tashi dattijona babu fa wani abu da tayi min.

bata fuska yayi na sani amma ki fada min komai rausayar da kai nayi, hira muka yi sannan ta bani wani magani tace na sha don na rikitaka yau da daddare.
A xabure ya dube ni magani kuma? maganin menene fada mata kika yi kina bukata,cikin xafin rai ya mike ina maganin da ta baki, Allah yasa dai baki sha ba, cike da xaulaya na bashi amsa da nasha.

A firgice ya kalleni kinsha fa kika ce shikenan kin kasheni Niimatullah,wannanmatar da bata kaunar mu ita ce xata baki abu ki sha Allah yasa dai ba wani sharrin ta xubo ba, wallahi dole na takawa matar nan burki a kan shigowarta wajen nan naga alama idan ban yi da gaske ba cutata xa tayi.

Sai da na bari ya gama fadan sannan na fada masa cewa ban sha ba tsokanarsa nake yi, dukan bayana yayi amma kin shigar da ni da yawa nima xan rama.

Maganin na dakko masa ya duba sannan ya ajiye a gefe, cikin nutsuwa yake min magana ko nan gaba idan ta baki abu kada ki fara ci saboda ba tada kyakkyawar niyya a kan mu.

Mikewa yayi yanzu xan je wajenta na kafa mata dokar kada na sake ganinta a wajen nan idan ba haka ba xata yi a bakin aurenta, riko kafarsa nayi ina masa magiya, kayi hakuri dattijona ka kyaleta tunda dai nasan xaman da xan yi da ita.

Baxai yiwu na kyaleta ta cuce mu ba kokarin janye kafarsa ya rika yi.



*Follow me on wattpad @Jeeddahtulkhaeer Tijj*

*jeeddahtulkhair😘*💋💋💋💋💋
*MATAR DATTIJO*
💋💋💋💋💋

*©jeeddah Tijjani*
*Adam*
*(jeeddahtulkhair)*

*follow me on instagram @jeeddahtijjani*


41

Da karfi na rike kafar shi ina masa magiya,dan Allah ka dawo dattijona kayi hakuri ka kyaleta kada kaje kayi masa magana har da dan guntun hawayena, xaunawa yayi yana mayar da numfashi cike da nutsuwa ya dube ni, ina ji a raina baxan samu nutsuwa ba har sai na samu matar nan na ja mata kunne ta fita a harkar cikin nan tun kafin igiyar aurenta tayi rawa, cikin marairaicewa nake masa magana, kayi hakuri dattijona ka kyale ta yanzu idan kaje ka fada mata xata canja wata hanyar ne kuma ta haka ne xata samu damar cutar da mu, girgixa kai yayi haka ne Niimatullah na fahimce ki.

Tun daga wannan ranar yasa mata ido baya bari ya fita ya barni ni kadai, ita ma tunda taga haka sai ta daina shigo min gaba daya sai dai idan ya dan fita ta saci jiki ta leko mu gaisa, wannan dalilin yasa na kara gane tana da wani mugun nufin a kaina tunda gashi bata shigowa a lokacin da dattijo yake nan,sai ta tabbatar da baya nan take xuwa.
Yau da safe bayan dattijona ya fita nima na fita don yiwa mai gadi magana a kan wani sako da aka bar min, ta saman bene ta hango ni da sauri ta sakko wajena da fara'arta ta karaso inada nake cike da ladabi na gaida ita, cikin sakin fuska ta dafa kafadata, murmushi tayi sannan ta fara yi min magana kin yi amfani da abin nan kuwa Niimatullah? kaina a sunkuye na amsa mata da eh nayi Aunty yana da kyau sosai Allah ya bar xumunci.

murmushi tayi tare da cewa ba komai kanwata kin fi haka a wajena, kokarin ja na da hira tayi tana bugun cikina a kan xamana da dattijo ni kuwa kin hirar nayi na hanxarta na koma bangarena.

Rayuwa nake cikin farin ciki ni da mijina babu wata matsala da nake fuskanta daga gare shi, cikina kuma na cikin koshin lafiya don laulayin da nake yi duk na fara samun sauki, yau kusan sati uku kenan da bani wannan maganin a tunaninta xan samu wata matsala amma shiru babu labari.

Don haka ta sake dawowa, yau ranta a bace na ganta don kana kallonta xaka gane cewa bata cikin walwala, sallama tayi min cikin sakin fuska na amsa mata tare da bata wajen xama ta xauna, tabe baki tayi tare da cewa ba xama ne ya kawo ni ba,cike da mamaki na dubeta ki xauna mana Aunty ya naga duk ranki a bace ko wani abin ne ya faru?

Yatsina fuska tayi ko ban fada miki ba kin san da abinda ya faru,don haka kawai baxa ki ganni a wajenki ba,sakin baki nayi ina ganin yadda take jujjuya idanu kamar xata dake ni..

Cigaba da magana tayi, nayi asarar kudina na baki magani amma baki yi amfani da shi ba ko gani kike xan cuce ki ne?cikin marairaicewa nace ai nasan baxa ki cuce ni ba, nayi amfani da shi tun a ranar da kika bani, dakatar da ni tayi kada ki raina min hankali ki mayar da ni karamar yarinya mana, idan har kin yi amfani da shi wlh xan sani kuma yanzu ma nasan baki yi amfani da shi ba kawai kin fada ne,don haka yi sauri ki bani abuna kafin na yi miki rashin mutunci.

Tsareta nayi da ido ina kallonta jira kawai nake naga kalar rashin mutuncin da take cewa xa ta yi min. Sake daka min tsawa tayi ke nake jira ki dakko min kayana kafin na saba miki kamanni na illata ki yanxun nan.

Cike da mamaki na dubeta wai me kike fada ne haka da har kike cewa xaki illata ni,dole ne don kin bani abu sai kin san nayi amfani da shi ko ban yi ba?nace da ke ina bukatar wani abu ne da xaki kawo min ko an fada miki ni irinki ce salam ba test? Wani duka ta kawo min Allah ya bani sa'a na kauce, cikin xafin rai take min magana.

Wallahi yau babu mai raba ni da ke a gidan nan sai kin gane ba ki da wayo,ranki sai ya baci yau sai na xubar da cikin nan sai dai duk abinda xai faru ya faru, kokawa muka fara yi ta buga ni jikin bango Allah ya bani sa'a nima na turmusheta tana dukana ina ramawa, babban burinta kawai ta daki cikina Allah bai sa ta cimma burinta ba kokawa muke yi sosai ni da ita,kwantar da ni tayi tana bugun cikina, kokarin kwatar kaina na rika yi.

Ban Ankara ba naji ta saki wani ihu ashe dattijo ne ya dawo ya kai mata duka,kokarin raba mu ya rika yi amma taki sakina sai dukana take yi Shi ma dukanta ya rika yi ba sasautawa har sai da ta sake ni, cikin fushi yake mata magana dama ba ki da hankali maryam me yasa xaki xo wajen karamar yarinya ki hau kokawa da ita kuma alhalin kin san tana da karamin ciki.

Da karfi ta danki wuyan rigarb shi na gaji da bakin cikin da kake cusa min a cikin gidan nan wallahi yau ko ni ko kai a gidan nan,sai inda karfina ya kare don a yau sai na barar da cikin nan kowa yayi asarar sa, yana jin ta ambaci barar da ciki yayi wurgi da ita ya kulle kofa ya kyaleta a waje tana masifa.

Wajena ya dawo yana duba jikina sannu Niimatullahi, shi yasa tun tuni naso naje na yiwa tumfar hanci amma kika hana ni gashi nan taxo tana neman cutar mu.

Kwantar da kaina nayi a jikinsa duk jikina ciwo yake yi, rarrashina ya shiga yi yana cigaba da duba cikina, wani kara yaji na saki cikin tashin hankali ya karaso wajena yana tambayata,lafiya Niimatullah me kuma ya faru? nuna masa cikina nayi jini ya gani yana xuba daga jikina cike da tashin hankali ya fara jijjiga ni ki taimake ni Niimatullah kada cikin nan ya cube dan Allah.

Daukana yayi cikin rashin hankali ya fita da ni ya saka ni a mota.


*Follow me on wattpad @Jeeddahtulkhaeer Tijj*

*jeeddahtulkhair[11/5, 11:10 AM] It'z B Y ebrerheem: 💋💋💋💋💋
*MATAR DATTIJO*
💋💋💋💋💋

*©jeeddah Tijjani*
*Adam*
*(jeeddahtulkhair)*

*Kamar yadda kike ta daban,sunanki na daban haka ma halin ki na daban ne, komai naki ya banbanta da nasu, kina da hakuri da kirki da son mutane Allah ya Kara miki daukaka, ya kare ki daga sharrin makiya, na sadaukar da shafin nan gaba daya gare ki AISHATUL HUMAIRA,ina yin ki irin totally din nan*

42

Gaba daya a rude yake sai gumi yake sharewa,ya kasa driving din gaba daya sai jujjuya ni yake yana hawaye, kiran abokinsa yayi yaxo ya ja motar kasancewar ba shi da nutsuwar da xai iya jan motar, rungume nake a jikinsa hawaye na sauka a kan fuskarsa, ban san halin da xan shiga ba idan na rasa cikin nan, dan Allah ki taimake ni kada ya xube Niimatullah, idona a rufe yake saboda bana fahimtar komai banda ciwo babu abinda cikina ke yi, hakuri abokinsa yake bashi yana kwantar masa da hankali.

muna isa asibitin aka fara bani taimakon gaggawa cikin rudewa dattijo ya tambayi likitan, doctor ya lafiyar cikin da fatan yana nan bai xube ba?Cike da kulawa ya bashi amsa yana nan amma daf yake da barewa, dafa kanshi yayi cike da damuwa yake magana, dan Allah duk taimakon da ya kamata a bayar a yi don kada ya xube, cikin nutsuwa ya bashi amsa insha Allah xa mu yi kokari Alhaji.

Cigaba da bani taimako aka yi har aka samo kaina na daina bleeding din da nake yi, a ranar a asibitin muka kwana don ko su innah bai fada musu ba don kada hankalin su ya tashi, haka muka kasance a asibitin yana kulawa da ni yana min dukkan abinda nake bukata.
Washe gari aka sallame mu, kafin a bamu sallama sai da ya fada masa cewa dole ne na daina aiki mai yawa saboda kada cikin ya xube, kuma ya fada masa cewa a daina bata min rai idan ba haka ba cikin xai iya xubewa a kowane lokaci, wannan dalilin yasa ya wuce da ni gidan innah don na samu Hutu.

Da sallama muka shiga gidan hannun shi janye da akwatina, innah na ganin mu ta mike tana tambayar mu lafiya, cike da ladabi dattijona ya gaida ta sannan ya fara yi mata bayani

Dama daga asibiti muke innah, cike da kulawa ta tambaye shi wane kuma ba lafiya? Kansa a sunkuye ya amsa da Niimatullah ce innah, kwana biyu tana yawan rashin lafiya ne shi ne muka je asibiti aka ce tana bukatar hutu shi yasa na kawota don ta huta.

Cike da kulawa innah ta kamo ni ta kwantar da ni a kirjinta sannu Niimatullah ki rika kula mai yaron ciki ba a so ta rika aiki mai yawa kin ji autar baba, narkewa nayi a jikinta sannan na amsa mata da to innah.

Hira suka fara yi ita da dattijo bai tafi ba sai wajen karfe biyar na yamma, kallona yake yana wani kashe min idanu innah na ganin abinda yake yi ta tashi ta bar mana wajen saboda kada a yi abin kunya a gabanta.
Matsowa yayi daf da ni ya kwantar da kaina a wuyansa yana shafa fuskata, cikin salon soyayya yake min magana wallahi bana so na tafi na bar ki amma hali ya kama dole na tafi na bar ki.

Xan kasance cikin kunci da bakin ciki a cikin wannan daren,musamman idan dare ya tsala bakya kusa da ni, fatana dai ki kula min da kanki duk abinda doctor ya hana ki daina yi mana don tabbatar da lafiyar jaririn mu,rungume ni yayi kamar baxai sake ni yana sumbatata ta ko ina, cikin shagwaba na bashi amsa xan kula maka dattijona, rike hannuna yayi ya tsura min ido kamar xai yi kuka bana gajiya da kallon kyakkyawar fuskar ki Niimatullah, ba don kada su innah su ga kamar nayi rashin kunya ba da a nan xan rika kwana.

Murmushi nayi tare da lumshe ido yanzu ma xaka iya dawowa ai dama ba kunya ne da kai ba,jan hancina yayi xaki ga ba nida kunya idan na tattaro kayana na dawo nan, harararshi nayi dawo din mana, bayana ya koma ya sakalo hannunsa ta wuyana, cikin rada yake min magana.

Yau xan yi irin baccin da na dade ban yi irinsa ba Allah ya sani bana so na tafi na bar ki,kina samun sauki xan xo gobe na tafi da ke don baxan iya wannan xaman hakurin ba.
Marairaice masa nayi kamar xan yi kuka dan Allah kayi hakuri ka barni dattijona kaga a nan innah xata kula da ni kuma baxan rika shiga damuwa ba. Tsare ni yayi da ido yana kallona idan kince haka Niimatullah ni kuma ya xan yi da soyayyarki na riga nayi sabo da ke baxan iya zama babu ke ba,kawai xan xo gobe na tafi da ke yau dai na hakura ki huta.

Duk nacin da nayi masa a kan ya barni na xauna har na haihu amma yaki, sallama muka yi sannan ya xaro kudi ya bani.

Bayan ya tafi innah ta shigo cike da tsokana take min magana, har kun gama rashin kunyar ko Niimatullah, wato har kin goge kin san dadin miji yanzu ba a kawo min karar laifin da yayi,hannu biyu nasa na rufe fuskata Allah ba haka bane innah hira kawai muka yi.

Murmushi tayi dama nima ai ba wani abu nace ba, mayar da kallona nayi gareta, kafin na fara magana har idanuna sun fara hawaye, cikin rawar murya nace innah wallahi ina cikin matsala dalilin hakan ne ma yasa kika ga na dawo gida.

Cike da fargaba ta fara tambayata saboda bata san irin matsalar da naxo mata da ita ba, cikin kulawa take magana, matsalar Menene Niimatullah?har xuciyata ta shiga fargaba wlh bana so naji an ambaci matsala.

Goge hawayen da ya fara sakko min a idanuna nayi sannan na fara yi mata bayani, wallahi innah matar dattijon nan ta takura min da xagi da cin mutunci, baro bangarenta take yi ta taho wajena kawai don ta tayar min da hankali,kwanaki ta kawo min wani magani tace na sha da naki sha shi ne jiya taxo ta hau xagina ta kama ni da kokawa har da cewa sai ta xubar da cikina, ni dai wallahi innah na hakura da auren nan baxan koma ba, ya nemi wata matar ya aura.

Tunda innah ta sunkuyar da kai bata dago ba saboda abin ya daure mata kai, cike da damuwa ta dube ni, kiyi hakuri Niimatullah kowace rayuwa da kike gani akwai jarrabawa a ciki baxai yiwu a ce kina xaman aure kuma kina samun abinda kike so dari bisa dari ba,dole sai kin yi hakuri da matsalolin da xaki fuskanta, ke ki godewa Allah ma da ba mijinki ne yake wulakanta ki ba kishiya ce, don haka ki cire damuwarta a ranki ki fuskanci abinda ke gabanki ki farantawa mijinki, kuma kada na sake jin kin ambaci Kalmar saki a bakinki.

Kwantar da kaina nayi a jikinta ina kuka, dan Allah innah ki taimake ni ki raba ni da auren nan wallahi ni nasan irin axabar da nake sha a hannun matar nan, indai ba so ku ke bakin cikinta ya kashe ni ba to ku raba ni da mijinta.

Rarrashina innah ta rika yi tana kwantar min da hankali.

*****

A bangaren Hajiya Maryam kuwa kwanan farin ciki tayi domin duk a tunaninta cikin Niimatullah ya xube sai kiran kawayenta take yi a waya tana fada musu, fitowa tayi tana kewaye gida tare da leka kanta bangaren Niimatullah samun kofar tayi a kulle, wani dadi taji ya ratsa xuciyarta, tasan cewa Niimatullahi na asibiti tana cikin wani hali.

Motar dattijo ta hango na kokarin shigowa cikin gida da sauri ta koma wajenta ta xauna a parlour, yana ajiye motar ya shiga wajenta, kawai ganinshi tayi a kanta yana huci kamar xai dake ta ya fara yi mata magana.

Burin ki na son hallaka abinda na dade ina burin mallaka a rayuwata bai cika ba kuma baxai cika ba har abada, domin wannan cikin ya fi karfinki sai dai ki kalle shi kiyi kuka,kuma wallahi ki nutsu tun wuri ki kama mutuncin ki idan ba haka ba kuma xaki ga hukuncin da xan xartar a kanki...

Fita yayi ya bar mata dakin, wani tsallen dadi tayi har a ranta tana jin ta fara samun nasara, girgixa kai tayi tana magana, kawai nasan fada yake yi amma wannan dukan da nayi mata dole yasa cikin nan ya tashi daga aiki,masifa kuma yanzu aka fara ta har sai ta gudu don kanta.

Dattijo na shiga bangaren Niimatullah yaji gidan ba dadi, komawa parlour yayi ya kwanta tare da daga kansa sama, gaba daya gidan yayi masa xafi ji yake kamar ya dau mota ya tafi ya dakko matarsa, juye-juye ya rika yi don a yanzu babu abinda yafi bukatar gani a kusa da shi fiye da Niimatullah.

*follow me on wattpp@jeeddahtulkhair Tijj*


*jeeddahtulkhair😘*
[11/5, 11:10 AM] It'z B Y ebrerheem: 💋💋💋💋💋
*MATAR DATTIJO*
💋💋💋💋💋

*®jeeddah Tijjani*
*Adam*
*(jeeddahtulkhair)*

*dedicated to Queen maryam maman surayya*

43

A ranar da kyar yayi bacci banda juye-juye babu abinda yake yi yana neman Niimatullah dinsa, kosawa yayi gari ya waye yaje ya ganta, domin duk rufe idon da yayi ita yake gani a cikin baccinsa.

Washe gari da sassafe ya nufi gidan su niimatullah,da sallama ya shiga gidan bai tarar da kowa a tsakar gida ba don haka kai tsaye dakinta ya nufa, tarar da ita yayi tana bacci karasawa wajenta yayi ya xauna sumbatar ta ya shiga yi saboda wani kyau take yi masa idan tana bacci, musamman ma yanzu da cikinta ya fara fitowa ta kara kyau da haske fatarta har wani sheki take,kwantar da kansa yayi a jikin cikin yana jin yadda take sauke numfashi, wani da dadi yaji yana ratsa xuciyarsa saboda yaji babynsa na lafiya yana numfashi yadda ya kamata.

A daidai lokacin innah ta shigo hannunta rike da abincin karin kumallo,bai yi xaton shigowarta a wannan lokacin ba, da sauri ya dago yana sosa keya duk kunya ta kama shi cike da ladabi ya gaida ta, fuskarta a sake ta amsa masa tashi tayi ta fita saboda taga duk a kunyace yake.

Komawa kusa da niimatullah yayi ya cigaba da aikin shafa cikinta kamar yadda ya saba a hankali na bude idona, muna hada ido ya sakar min wani kyakkyawan murmushi tare da cewa barka da tashi maman Baby, a hankali na amsa tare da yunkurin tashi xaune taimaka min yayi ya xaunar da ni.

cike da shagwaba na fara yi masa magana, haba dattijona yanxu da sassafe ka taho baxa ka bari kayi bacci da yawa ba jiya fa ka gaji

Please Login or Register in order to submit comment