Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya fi na innata muhimmanci lallai ma mutumin nan.

kafe ni yayi da ido, da ke baki sani ba lallai yarinyar nan kina ji da kuruciya, tunda baki sani ba yau xan ganar da ke, tare xamu tafi yanxu idan kin koma ki fadawa innah aikina kika tsaya yi xa kiji baxa ta ce komai ba saboda tasan matsayin miji a wajen matarsa, yana gama fada ya ja motar, hannunsa na rike ina kuka.

dan Allah ka tsaya kada ka tafi da ni, nasan kana da muhimmanci a wajena, Dariya yayi wanda har sai da fararen hakoransa suka bayyana, dadina da ke ga rashin kunya ga kuma tsoro, to ki kwantar da hankalin ki, ni ba siyar da ke xan yi ba kawai xan tafi da ke ne na nuna miki muhimmancin aikin miji.


hakuri na rika bashi amma yayi banxa da ni, tafiya mai nisa muka yi har muka iso wani katafaren gida wanda baxan iya bayyana ko a wane unguwa yake ba, kasancewar bana fita sosai, bude mana gate aka yi ya shiga da motar, muna yin parking wasu kyawawan yara maxa biyu suka iso wajen mu, da dukkan alamu suna farin ciki da ganinsa, sannu da xuwa suka yi masa tare da gaida shi, duk da cewa sun girme ni amma har kasa suka tsugunnah suka gaishe ni.


tambayar kaina na shiga yi wannan tsohon kuma ina ya kawo ni, kada dai fa a ce gidansa ya kawo ni, a hankali ya shafo fuskata mun iso my Niimatullah taso mu shiga daga ciki.

girgixa kaina nayi babu inda xan je ka shiga ka fito, kuma ina ma ka kawo ni ne?kallona yayi yana wani murmushi kawo ki nayi na siyar da ke tunda dai kin xama tawa, kuka na fara yi kayi hakuri kada ka siyar da ni dan Allah innata na sona ni kadai na rage musu kayi hakuri dattijona, dariya ya rika min har sai da ya sunkuya, sai da yayi dariyar ta ishe shi sannan ya dube ni, to baxan siyar da ke ba amma taso mu tafi.

makale kafada nayi babu inda xan je har sai ka fada min inda ka kawo ni, murmushi yayi gidan hutawar mu na kawo ki, kuma dole ki fito ko nasa a xo a dauke ki, saurin fitowa nayi saboda nasan kadan ne daga cikin aikinsa tsaf xai dauke ni, rike hannuna yayi har muka isa wani hadadden falo wanda yaji kayan ado na xamani, da gudu naga wata mata ta karso wajen mu Oyoyo uncle din yara, kamar su daya da dattijona komai da komai sai dai kawai ya dan fi ta hasken fata da kadan, cikin sakin fuska yayi mata magana, juyowa bangarena tayi tana dubana, sannun ki da xuwa amaryar mu, yau dai uncle ya cika alkawari ya kawo mana ke, cike da ladabi na gida ta, cikin kulawa take min magana da dukkan alamu tana da kirki, hannuna ya riko yana kallona.

Niimatullah wannan ita ce maimuna yar autar mu duk ita ce karama a dakin mu, cikin dasasshiyar murya nace to muka sake gaisawa, dattijo yana ji da kanwar sa kana ganin yadda suke hira xaka gane akwai shakuwa mai yawa a tsakanin su.

Hira naji suna yi a kan halayyar matarsa da irin abubuwan wulakancin da take masa, ni kuwa ina gefe ban sa musu baki ba, nunawa nayi kamar bana jin abinda suke fada, kwantar da kanshi yayi a kan kafadata a hankali na dan matsa saboda na lura shi bai fiye jin kunyar ido ba, murmushi yayi min tare da cewa munat kin ga dai amaryar tawa ko? fuskarta a sake ta bashi amsa na ganta uncle gata da kunya, jan hancina yayi, amma kuma akwai rigima da tsokana.

Dariya suka yi gaba daya, ai dole tayi rigima kasan amarya ce bata laifi, kaina a kasa na kasa dagowa saboda kunya, tambayar shi tayi, yaushe amaryar tamu xata tare ne, kamo hannuna yayi yana duban idona ni ko yanxu na yarda ta tare, na shirya tsaf na kula da matata, ita ce dai ban sani ba ko ta shirya

nade kaina nayi a mayafi, haka suka gama hirar su sannan muka tashi xamu tafi, kayayyaki masu yawa ta hado min har bakin mota ta rako ni da kyar na yarda na karbi kayan, muna shiga motar na fara harararshi, me yasa xaka min haka, dube ni fa ko kwalliyar kirki ban yi ba ka tashi ka wani kawo ni gidan kanwarka salon ta raina ni, yanxu duk kyan nan da kika yi ba kwalliya bane niimatullah? cikin tsiwa nace nafi son nayi gayu nayi kyau kada su ganni su ce min kaxama, murmushi yayi banda abin ki wa xai ganki ya kiraki da kaxama my niimah, Allah bakya rabo da rigima, kiran wayar shi aka yi yana dauka yaji innah ce ta kira.

tashin farko ta fara tambayar ina nake cike da ladabi ya amsa mata cewa na raka shi unguwa ne, bayan sun gama wayar na dube shi, kaga irin abin ko har innah ta gaji da jira ta kira, ni dai mu tafi dan Allah.

kamoni yayi ya kwantar da ni a kan wuyan shi, kin xama mallakina fa Niimatullah duk inda xan kai ki innah baxa ta ce komai ba, yanxu ma da kika ga ta kira don ta tabbatar da lafiyar mu ne, marairace masa nayi kamar xan yi kuka.

to naji ni dan Allah mu tafi, cike da kulawa yace min xan kai ki gida amma da sharadin sai kin min kiss, kuka na fara yi ina shure-shure ni baxan maka ba Allah na gaji da wadannan tsare-tsaren naka, kullum da abinda xaka ce nayi maka sai kace haka innah tace ka rika yi min.

tsura min ido yayi yana kallon ina ta abubuwana sai da na gama ya min magana idan xamu kwana a nan indai baki yi min ba baxan kai ki gida ba sai dai mu yi bacci a mota, da naga babu sarki sai Allah na kama hannun shi nayi masa, duk wanda nayi masa sai yace bai yi ba, sai da na yi masa kusan sau goma sannan ya yarda muka tafi.




*jeeddahtulkhair๐Ÿ˜˜*
[10/18, 11:22 PM] It'z B Y ebrerheem: ๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹
*MATAR DATTIJO*
๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹

*ยฉjeeddah Tijjani*
*Adam*
*(jeeddahtulkhair)*

*follow me on instagram @jeeddahtijjani*

*dedicated to Aysha Bala ilu (iluwa)*

18

A bakin kofar gida ya ajiye ni hannunsa cikin nawa, sai da ya rako ni har soro, sannan ya juya ya tafi yana waiwayena,da sallama na karasa cikin gida xaune na tarar da innah ta hada kai da gwiwa, a sanyaye ta amsa min sallamata, cike da damuwa na karasa wajenta murmushi ta rika min, sannu da xuwa yar lelen baba amsawa nayi tare da kwantar da kaina a cinyarta, kallona ta shiga yi tana yaba irin kyaun da nayi da irin kwaxon da mai gyaran jikin ke yi a kaina, tambayarta na shiga yi me yasa naga kin hada kai da gwiwa innah? fuskarta a sake ta bani amsa, jinki da nayi shiru baki dawo bane ya daga min hankali amma ai Alhamdulillah tunda kin dawo lafiya, murmushi nayi yauwa innata na gode da son da kike nuna min, kin san ina muka je? saurin kallona tayi bance ki fada min ba duk irin wannan maganar na hana ki Niimatullah bana son jinta, cike da shagwaba nace ba wannan abin fa xan fada miki ba innah, gaba daya ta bayar da hankalinta gare ni, to ina sauraren ki, gyara xama nayi na fara bata labarin mutuncin da kanwar dattijona tayi min, kayan da ta bani na shiga fito mata da su tarkacen kayan kwalliya ne da turaruka kala-kala godiya innah ta rika yiwa kanwar dattijo tana sa mata albarka har da dan guntun hawayenta, Allah mun gode maka da Alhaji ya shigo rayuwar mu ya hana ki kukan maraici Niimatullah, ki rike mijinki da kyau kiyi masa biyayya, kaina a kasa na amsa mata da insha Allah innah.

A ranar ma sai da muka sha waya da dattijo kusan kwana muka yi muna waya sai faman shagwaba yake min.

Washe gari da safe na tashi na fara gyara gida saboda nasan da wuri xai xo ya dauke ni mu tafi gidan gyaran jiki, soron farko na fara sharewa, wata magana naji a nayi kasa-kasa da farko bana fahimtar abinda ake fada sai da na tsayar da hankalina sosai sannan naji abinda ake fada, wata murya naji na cewa, duba gidan nasu da kyau babu komai daga laka sai axara, talauci ya samu wajen xama a gidan amma sai mugun abu da bin malamai, mu shiga daga ciki mu yaga masu rigar arxiki don idan muka tsaya a nan baxa su fahimci komai ba, gabana ne ya rika faduwa naji ina kokarin xubewa a kasa saboda fargaba, ganin mutanen nayi sun shigo soron da nake, a firgice na matsa gefe, saboda matar dattijona na gani ita da wata kawarta.

muna hada ido ta watsa min wata matsiyaciyar harara tare da cewa, yauwa Hajiya xainab kinga matsiyaciyar nan, kamo ni matar tayi tana dubana sama da kasa, fari tayi da idonta sannan ta dube ta, hmm lallai dole mijinki ya rude mace har mace ta fara jin sinadari ta fara xama cikakkiyar mace ai dole ya susuce saboda yana jin sabon al'amari a jikinta, sakin baki nayi ina kallon su saboda gaba daya ban fahimci ina maganar tasu ta dosa ba.

matar dattijon ce ta ja hannun kawarta taho mu shiga daga ci mu ci mutuncin tsohuwar banxar da ke yiwa wannan jakara yawon malamai, har sun sa kafar su a tsakar gida ta juyo ta dube ni, ki tabbatar da cewa kina shigowa gidana kin shigo makabarta domin duk abinda kike nema baxa ki samu ba fadar mijina tafi karfinki, bin su nayi a baya don ganin inda xasu je dakin innah suka shiga tarar da ita suka yi tana ta faman bacci cikin tsawa suka yi mata magana wannan dalilin yasa ta farka a firgice tana salati, cikin dashewar murya take musu magana kasancewar tana dan fama da mura.

Ku kuwa lafiya yayan nan ba sallama?cike da rashin kunya suka fara yiwa innah magana, wajen ki muka xo ki fara warware sharrin da kike kullawa na sai kin fitar da ni daga gidan mijina idan ba haka ba kuma yau a yita ta kare don baxan fita daga gidan nan ba har sai an warware auren banxar jikar ki da mijina, girgixa kai innah tayi
kayya! me yasa xaku haramta abinda Allah ya haramta, Allah ne ya bawa mijinki dama ya auri mace sama da daya, me yasa xaki rika jayayya da hukuncin Allah? hannu tasa ta dakatar da innah, dakata min tsohuwar tsiya ke mijinki mata biyu ya aura ba ke kadai kike rayuwar ki ba gashi nan har kun tsufa a haka, ke da kike gidan talauci ma kika guji kishiya ballantana ni da nake a gidan wadata

ina jin abinda take fadawa innah nayi wani tsalle na dawo gabanta ina huci, cikin tsawa nima na mayar mata da martani

Ba innata ce tsohuwar banxa ba
kece babbar banxa wawiya da kika kasa kula da mijinki har sai da yaxo ya like min ya nace na aure shi, ki dube ni da kyau ni ba mummuna bace ballantana kice lika masa ni aka yi,shi ya ganni ya nace don haka ba mu xaki yiwa hauka ba mijinki xaki je ki yiwa, da yaxo nace
idan har kin cika mace mai ji da kanta mai xai sa mijinki ya gano mitsitsiyar yarinya kamata ya nace mata har ya rika kuka a kan na so shi
mun gaji da cin fuskar da kike mana, an gaya miki talauci hauka ne,wlh baxan juri wannan jahilcin da xaki rika yi mana ba, kuma miji sai an aure shi don ba ni nace kiyi sake har ya rika kallon mata ba.

sakar baki suka yi suna kallona, saboda basu taba xaton xan musu haka ba,ni kaina nayi mamakin maganganun da na rika fada mata, ji nayi na fita daga hankalina duk abinda xai faru sai dai ya faru indai a kan a taba innata ne, kamo ni innah tayi ta xaunar da ni tana min nashiha, ki daina rama abinda aka yi miki na rashin kyautawa saboda bai kamata kare yayi maka haushi ba kaima ka bishi ka rama, a fusace matar ta kamo ni ta shake min wuya wanda sai da na kusan suma saboda shakar da tayi min cikin xafin rai take min magana.

dan ubanki har kin yi girman da xaki fada min magana yaushe aka haife ki, shegiya kaxama kucakar banxa, nasan ba haka kika bar min miji ba shi yasa amma da me xai yi da ke shashasha, kuma wlh daga yau idan baki fita a harkarsa ba xaki ga abinda xai faru da ke sakina tayi na ja da baya kamar xan fadi, wani kallon raini na shiga yi mata.

cike da rashin kunya nake mata magana gara ni kucaka ce amma ke kin fi kuca kucakanci kina cewa kina da ilimi amma bakya aiki da shi banda tsabar jahilci da rashin sanin ya kamata kixo kice xa kiyi fada da ni a matsayina na yar cikin ki dube ki fa duk tsufa yaxo miki ko ta ina, amma baki san Annabi ya faku ba,kuma aure da mijinki yau aka fara baxan rabu da shi ba ko dafa ni xa kiyi ki cinye ni sai na shigo gidan ki, xagin mu ta rika yi tana aibata mu innah ce ta dakatar da ni amma ban yi niyyar kyaleta ba saboda a duniya na tsani abinda xai taba min xuciyar innah haka suka gama xagin mu suka tafi.

gaba daya muka fashe da kuka saboda masifar matar tasha kan mu bata gajiya da bala'i abinda ya fi daga min hankali yadda tace xata yi da ni idan na shigo gidanta kuka sosai muka rika yi, a dai dai lokacin baba ya dawo ya tarar da mu a wannan halin cike da damuwa ya dube mu.

meke faruwa na gan ku haka? inna ce ta fara yi masa bayanin komai ba karamin baci ransa yayi ba, cikin damuwa yake magana ina ganin lokaci yayi da mutumin nan xai sauwakewa Niimatullah cin
kashin da matar nan take mana yayi yawa kada yarinyar nan ta tare ta samu damar cutar da ita,tunda tana ganin ba tada wani gata mu kuma Kullum karfin mu karewa yake baxa mu iya biyewa wannan tashin hankalin ba don haka ko yana so ko baya so sai ya sauwake mata baxa mu iya masifa ba, fita baba yayi, ni kaina yanxu nafi son ya sake ni saboda ina jin baxan iya xama da ita ba.

su Hajiya na fita suka bushe da dariya, ina ganin wannan itace hanya mafi sauki da xa mu yi maganin auren nan saboda wlh idan muka bar yarinyar nan ta shigo xaki xama yar kallo dubeta fa tubarkalla komai ya ji ba tada wata makusa, kuma yadda suka ga xata shiga gidan hutun nan dole su rika karfafa mata gwiwa mu kuma ta hanyar yi musu tijara xamu samu mu karya auren kowa ya huta hirar da suka rika yi kenan har suka isa gida.


*jeeddahtulkhair๐Ÿ˜˜*
[10/18, 11:22 PM] It'z B Y ebrerheem: ๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹
*MATAR DATTIJO*
๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹

*ยฉJeeddah Tijjani*
*Adam*
*(jeeddahtulkhair)*

*follow me on instagram @jeeddahtijjani*

*dedicated to Dr fatee sabitu*

*ya Allah ka bawa daughter Aysha yar london lafiya*


19

A ranar baba ya tura aka aka kira masa dattijona, a soro nayi musu shimfida cike da ladabi ya samu guri ya xauna, kallona ya rika yi yana min murmushi tare da kashe min ido da alama dai so yake nayi masa magana, banxa nayi da shi na wuce gida saboda ji nake gaba daya na tsane shi, tsakar gida na koma na barsu su yi magana da baba.

Bayan sun gaisa baba ya fara yi masa bayanin makasudin haduwar su, gyara xama baba yayi sannan ya fara yi masa magana, nasan xa kayi mamakin kiran da nayi maka Alhaji, kansa a sunkuye ya amsa kwarai kuwa baba, Allah yasa dai lafiya gyaran murya yayi sannan ya cigaba da cewa, xamu iya cewa lafiya amma ba lau ba.

cike da mamaki ya dago yana tambayar sa me kuma ya faru baba?damuwa ce ta bayyana a fuskar baba, Alhaji ina ganin ya kamata kayi hakuri mu ma mu yi hakuri ka sauwakewa Niimatullah aurenka, a firgice ya dago me kuma ya kawo wannan maganar baba? girgixa kai yayi ba komai Alhaji kayi hakuri mu ma dole ce tasa xamu fasa amma mun san kana son yarinyar nan ita ma tana sonka, amma Niimatullah bata dace da kai ba, saboda kai mai kudi ne kuma mai ilimi kuma ka fito daga babban gida, ita kuwa yar talakawa ce kuma marainiya mara gata, ina jin tsoron barin Niimatullah ta aureka saboda furucin matarka a kanta kada ta hallaka mana ita wata rana saboda na fuskanci tana da kishi da yawa shi yasa na duba naga abinda ya fi alkhairi shi ne ta bar mata mijinta, kaga a kullum karfin mu karewa yake kada a yi auren nan wani abu ya biyo baya, tunda Niimatullah yarinya ce karama har yanxu bata gama mallakar hankalin kanta ba gashi ba tada wayo ga rashin gata ko cutarta tayi ba mu da halin karbar mata hakkinta,dan haka nake rokonka dan girman Allah ka sauwake mata, saboda maganin a yi shi ne a bari, kusan xuwanta biyu gidan nan tana ci mana xarafi, har shake Niimatullah tayi har sai da ta kusa suma yanxu haka wuyanta ciwo yake, don haka mu baxa mu iya fada da abinda ya fi karfin mu ba don Allah ka saketa.

Tunda dattijo ya sunkuya bai dago ba wani gumi ne ya rika yanko masa ta ko'ina,nan da nan idanunsa suka yi jawur saboda takaici, bai san ya xai yi ba idan aka ce ya rabu da Niimatullah ba, cikin rawar murya yake wa baba magana, kayi min arxiki baba wlh baxan iya sakin Niimatullah ba, dan Allah a yi hakuri xan tsawatar mata wallahi ban san tana xuwa tayi muku haka ba, dafa kafadar shi baba yayi ka kwantar da hankalinka Alhaji wannan duk ba wani abin tayar da hankali bane, abu ne da muke so a yi maslaha saboda Allah ya sani amanar Niimatullah a hannuna take, duk wani abu da ya sameta muna da alhaki a kai kuma sai Allah ya tambaye mu wannan dalilin yasa dole a warware auren nan saboda gudun bacin rai.

Hawaye ne ya cika idon dattijo rokon baba ya fara yi a kan yayi masa alfarma ya janye maganar, duk nacin da yayi hakarsa bata cimma ruwa ba, jikinsa a sanyaye ya dubi baba.

dan Allah ina so xan yi magana da Niimatullah, cikin sakin fuska baba ya bashi amsa ba komai Alhaji ai baxan hanaka magana da iyalinka ba tunda har yanxu a karkashin ikonka take.

kirana baba yayi cike da ladabi na tsugunnah tare da cewa gani baba, cikin kulawa yace mijinki ne yake son magana da ke yana gama fada ya bamu guri, kan shimfidar da aka yi masa na xauna, sunkuyar da kaina nayi saboda yadda na ganshi yana cikin tashin hankali da damuwa karasowa yayi ya xauna kusa da ni, fadawa jikina yayi yana Hawaye tare da tallafo fuskata Niimatullah me nayi miki kike neman yanke alaka da ni? me yasa kike son na sake ki alhalin kinsan xuciyata baxa ta iya jure hakan ba, ke kika fadawa baba kina son na sake ki? sunkuyar da kaina nayi tare da cewa.

Eh na xabi hakan ne saboda hankalina xai fi kwanciya dama na dade ina tunanin hakan saboda cin kashin da matarka take mana ya fara yawa, na yanke shawarar hakura da kai indai hakan xai yi sanadiyyar farin cikina dan Allah ka sake ni ko xan huta da wulakancin da matarka take mana.

kallona yayi da jajayen idanunsa lallai baki san adadin yadda nake sonki ba Niimatullah, ke yanxu a tunaninki xan iya rabuwa da ke wallahi son rayuwata nake miki baxan iya hakura da ke ba saboda ina matukar sonki, a halin yanzu kawai kina ganin kaso ne mafi kankanta daga cikin irin son da nake maki, amma lokaci na nan zuwa da zan nuna miki tsantsar soyayya mara misaltuwa, bayan mun yi aure. ba zan ta6a mantawa da sadaukarwar da kika min ba, kina yarinya kika aure ni a matsayina na dattijo, kina tunanin xan manta da wannan sadaukarwar? don haka babu macen da xata samu gurbin soyayyar da kika samu a xuciyata, kisa a ranki baxan iya rabuwa da ke ba,ya xan yi da rayuwata idan na wayi gari bakya tare da ni, ki tuna a wajenki kawai nake samun farin ciki, yana karasa maganar ya fashe da kuka.

nima kukan na rika ni kaina nasan ina son dattijona amma hangen abinda xai je ya dawo nake yi, cikin kukan nake masa magana nasan kana sona amma dan Allah ka duba halin da xan fada ka sake ni, matarka bata kaunata tana xagina ta xagi innata me xan je gidanka nayi, ni tuni na bawa xuciyata hakuri a kan rabuwa da kai kuma ta hakura da kai.

kamo ni yayi hada da kirjinsa yana rarrashina, me yasa xaki min haka Niimatullah, kin san irin kaunar da nake miki da xaki ce sai na sake ki, indai aka takura na sake ki wlh nasan sai na rasa raina, saboda soyayyar ki ta gama yi min illah.

xame jikina nayi na nufi bakin kofar shiga gida ina share Hawaye, hada kansa yayi da bango yana ta kuka kamar karamin yaro, baxan iya jure ganin shi yana kuka ba wannan dalilin yasa na shige gida gudun kada xuciyata ta buga saboda bacin rai.


*jeeddahtulkhair๐Ÿ˜˜*
[10/18, 11:22 PM] It'z B Y ebrerheem: ๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹
*MATAR DATTIJO*
๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹

*ยฉjeeddah Tijjani*
*Adam*
*(jeeddahtulkhair)*

*follow me on instagram @jeeddahtijjani*

*ina gaida ku yan group din matar DATTIJO 1,2,3 ina tare da ku kuma ina jin dadin comments dinku ana mugun tare, masoya DATTIJO kwalelanku๐Ÿ˜œ*


20

A soron na barshi
ya fi kusan minti talatin yana kuka cikin kukan yake kiran sunana, Niimatullah ki tausayawa rayuwata ki aure ni, ki tuna irin yadda nake sonki da kaunar Ki,tun lokacin da na fara ganinki, kika shiga raina kin samu gurin da baxa ki taba fita ba har abada. ke ta daban ce Niimatullah, kina da wata baiwa wadda ba kowace mace Allah ya bawa ba, ina samun nutsuwa idan ina tare da ke,kada ki guje ni Niimatullah ki kusanta da ni, zan wadatar da murmushi a saman fuskar ki,zan yi kokarin wadata ki da jin dadi daga cikin nauโ€™ikan ababen jin dadin rayuwar duniya. Ina tsanin sonki babyna baxan iya barin ki ba ya karasa maganar tare da fashewa da kuka mai tsanani.

cikin gida na shiga ina xuwa na fada gado ina kuka, ban san halin da xan tsinci kaina ba idan aka raba ni da shi, shi ne mutum na farko da ya fara koyar da ni soyayya, a Kullum burinsa ya tarairayi jaririyar xuciyata wacce bata san komai ba sai soyayyarsa da karfi na rika fadar hakan ina cigaba da kukana, innata ce ta shigo inda nake saboda taji sambatun da nake yi dafa kafadata tayi tana rarrashina, kiyi hakuri Niimatullah indai Alhaji rabonki ne xaki aure shi,mu dai fatan mu ya yiwa tufka hanci wannan matar tasa ta daina xuwa tana ci mana mutunci, nasan Malam xai sakko saboda yana son abinda kike so, a ranar cikin damuwa na wuni.

A bangaren dattijo kuwa yana komawa ya tarar da gidansa ba kowa, kwafa yayi ya samu kujera ya xauna a falo yana jiran dawowar matarsa, tunanin Niimatullah ya shiga yi da yadda xai shawo kan baba ya kyale shi ya tare da matarsa, baya jin xai iya rabuwa da ita saboda duk wani farin cikinsa ya hango shi a tare da ita, yana cikin tunanin yaji wasu xafafan hawaye sun xubo masa, hannu yasa ya share gani yayi an tsaya a kansa, a hankali ya dago ,matarsa ya gani tsaye tana yi masa wani kallo a fusace ya mike yana nuna ta da hannu, ji yayi bakinsa na rawa saboda takaicin da ya cika xuciyarsa kasa ce mata komai

Please Login or Register in order to submit comment