Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

xata je gidana, a koya mata da kyau yadda xata kware a komai fiye da macen da ta dade a gidan miji, kuma special class nake so a sakata, ina ganin xata fi sakewa idan bata ganin idon jama'a.

cikin sakin fuska ta bashi amsa, lallai Alhaji kana so amaryar nan taka ta kwace gida tunda ka kawo ta nan, murmushi yayi ba tare da yace komai ba.

kada ka damu Alhaji xaka ga yadda xata dawo wallahi komai nata sai ya canja, har sai ka dawo kayi min kyauta ta musamman saboda yadda xan kula maka da amaryarka, dan wasa da dariya suka yi ni kuwa ina gefe ina sake-sake a xuciyata, ita kuwa wannan matar me xata koya min haka da har xata canja ni??

kudi mai yawa ya xaro ya bata sannan ya mika mata form din don yin submiting, tashi yayi xai tafi karasowa yayi wajena ya rike hannuna ya kai ni kusa da ita.

ga amanata nan a kula min da ita, sumbatar goshina yayi sannan ya tafi da niyyar idan an tashi xai dawo ya dauke ni.




*Jeeddahtulkhair?πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹
*MATAR DATTIJO*
πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹

*Β©jeeddah Tijjani*
*Adam*
*(Jeeddahtulkhair)*

*follow me on instagram @jeeddahtijjani*


14

Tsayawa tayi ta kare min kallo sannan ta kira sunana cikin nutsuwa, Niimatullah!! A hankali na dubeta, sunanki mai dadi da kuma kyau, kamar yadda wannan sunan naki yake haka nake son mayar da ke, amma sai kin bani hadin kai,kuma sai kin saki ranki sannan xaki iya koyar komai don farantawa mijinki, duk abinda baki sani ba kada ki ji tsoron tambayata ki dauke ni a matsayin kawarki. kece mace ta nawa a wajen mijinki?? kaina a sunkuye na amsa mata da nice ta biyu, girgixa kai tayi, yayi kyau tunda kuwa haka ne dole ki lura ki xage damtse ki iya komai idan ba haka ba xaki xama yar kallo a gidan miji maybe akwai abubuwan da matarsa ta saba masa da shi matukar kika xama banxa bakya yi masa sama da abinda take yi xata kwace miki miji, kiyi amfani da kuruciyarki ki mallake mijinki.

Ajiyar xuciya tayi sannan ta sake jefo min wata tambayar kin tare a gidan mijinki? daga mata kai nayi tare da cewa a'a sai na kara wayo, murmushi tayi ai kuwa mijinki yayi dabara da ya kawo ki nan don xaki koyi wayon da ko a gidan mata dari xaki xauna kiyi xaman aure, amma fa darasin mu yana bukatar a cire kunya, kuma yana bukatar a rika gwadawa, dubanta nayi tare da tambayarta.
malama ya xa a yi na cire kunya innata ta fada min kunya adon mace ce, murmushi tayi tare da dafa kaina, a wajen mijinki kunya haram ce amma a wani wajen kunya aba ce mai kyau abinda hausawa suke nufi kenan.

wani abu ta dakko a kwalba ta tsiyaya min a cup, karbi wannan kisha tun Yanxu nake son na fara hada ki ta yadda xaki rikita tsohon nan, karba nayi na fara sha, ina kurba daya na fitar da shi, Allah baxan iya sha ba Aunty karbi kayan ki, bata fuska tayi haka xaki daure kisha dama ba dan kiji dadi xaki sha ba, sai dan farantawa mijinki, takura min tayi har sai da na shanye gaba daya.

bayan na gama sha ta mika min wani abu a roba karbi wannan turaren da xaki rika tsarki da shi ne, ina so ki rika kamshi ko ta ina, sannan ki nisanci tsarki da ruwan sanyi, da shan ruwan sanyi domin wadannan abubuwan suna taka muhimmiyar rawa wajen mayar da mace salam, sannan ki daina xama a kasa ba tare da shimfida ba ki daina yawo ba takalmi a tsakar gida hakan yana ragewa mace ni'imarta, ki daina wanka da ruwan sanyi, sannan ina so a Kullum ki dafa lalle ki rika wanka da shi hakan yana karawa mace dumin jiki, kuma kin san mace mai dumi darajarta daban take a wajen miji, yau nake so ki fara duk wadannan abubuwan da na xayyana miki bana son wasa, idan kika karya dokata guda daya xaki ga bacin raina, cike da ladabi na amsa mata baxan karya miki doka ba insha Allah.

Tafiya ta shiga koya min salo daban-daban, idan tayi wani abin har kunyar kaina nake ji, haka ta rika koya min kala-kala duk wacce aka koya min sai na gwada idan nayi dai-dai ta gode min idan nayi kuskure ta gyara min ta sake koya min, bayan mun gama ta kira dattijo yaxo don ya tafi da ni, bata dade da kiran shi ba ya iso.

Har bakin kofa ta rako ni, umartata tayi da na fara gwada abinda ta koya min tunda dai mallakina ne, dubanta nayi kamar xan yi kuka. Allah baxan iya ba Aunty kunya nake ji kiyi hakuri na fara gwadawa gobe.

hararata tayi, haka muka yi da ke Niimatullah, bana son taurin kai kiyi abinda nace kafin ranki ya baci, a hankali na fara wani irin taku mai cike da burgewa da kayatarwa, a hankali na bude hannayena na fada kirjinsa, shafa gashina kaina yayi tare da dago fuskata yana min wani kallo saurin kawar da kaina nayi saboda duk kunyarsa ta kamani, tafa min naji suna yi tare da cewa kin yi kokari Niimatullah, shi kuwa kin sakina yayi sai da muka fi kusan minti biyar a haka sannan muka hau mota muka tafi.

kallona yayi yana murmushi, lallai idan kika dade a makarantar nan abinda xa a min sai ya fi haka, gashi yau daga xuwa har na fara ganin canji,Gaskiya dole na karawa malama kudi don kwalliya ta fara biyan kudin sabulu, ina turo baki na dube shi.

nifa na fara gajiya da makarantar nan naga akwai takura komai aka koya wai sai an gwada ni Gaskiya baxan iya ba, gashi har wani abu mai daci ta bani da nace baxan sha ba ta takura min wai na faranta maka ne, ni wlh na gaji, shafa fuskata yayi to ai ta haka ne xaki kware Niimatullah idan bakya gwadawa ai sai ki manta, kuma menene don kin sha abinda xaki faranta min ki tuna ni fa aljannarki ne.

kuka na fara yi masa ni baxan koma ba Allah tunda haka ne, lallaba ni ya shiga yi har sai da na yarda xan koma, yau har cikin gida ya kaini sannan ya tafi nasa gidan.



*jeeddahtulkhair😘*πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹
*MATAR DATTIJO*
πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹

*Β©jeeddah Tijjani*
*Adam*
*(jeeddahtulkhair)*

*follow me on instagram @jeeddahtijjani*

*ina matukar godiya da kika bani kyautar page Zahra Galadima, Allah ya bar xumunci*

*masu son dattijo kwalelen ku domin Niimatullah tuni ta dade da mallake xuciyar mijinta, intisar da jeedda har da wani mayar da sunanta Niimatullah Sbd cusa kai, to kwalelanki😜*


15

Da sallama na shiga gida tarar da innah nayi tana tankade, karasawa nayi wajenta na shiga bude mata kayan da aka bani a wajen gyaran jiki, ba karamin farin ciki tayi ba da taga kayan, albarka ta rika sakawa dattijona tana masa fatan Alkhairi.

tsayuwar mota muka ji a kofar gidan mu, da sauri na janyo hijabina na saka saboda nasan dattijona ne ya sake dawowa, da sallama aka shigo gaba daya muka mayar da hankalin mu ga mai yin sallamar tare da amsawa, matar nan da ta taba tare ni a hanyar makaranta muka gani, a firgice na mike tsaye ina dubanta, wani irin kallo take yi min ni da innah, mamaki ne ya kamani ko ta yaya ma tasan gidan mu? wani kallo take mana wanda mu kanmu baxa mu iya fassara na menene ba, innah ce tayi karfin halin tambayarta.

Baiwar Allah lafiya kika shigo kika tsaya ba magana?wata harara ta watsa mata, lafiyar ce ta kawo ni matsiyatan banxa wadanda basu gaji komai ba sai tsiya, ga ki tsohuwa amma tsohuwar banxa kin shiga kin fita kin min asiri kin raba ni da mijina saboda kawai yarki ta shigo ta aure min miji, a kwana biyun nan gaba daya na rasa kansa tunda aka daura masa aure da wannan kaxamar jakar jikar taki, ba shi da aiki sai ya shige daki yana waya da ita, to wallahi ga gida nan ki shigo amma ki tabbatar da cewa irin rayuwar yar bora xa kiyi, ke da mijina sai kallo, tun baki shigo ba ya fara juya min baya ina kuma ga kin shigo, kwadayin abin duniya ne dai yasa kika aure shi, don haka kin yi ban kwana da samun soyayyar mijina mu xuba mu gani tsakanin ni da ke, tana gama fada ta juya har ta kai bakin kofa ta sake dawowa.

Au na manta ma ban fada miki ba idan don soyayya xaki shigo to ki rike a ranki mijina ba namiji bane, kinga kudi kika aura ba namiji ba. gabana ne ya fadi hawaye suka cika idanuna tana gama maganar ta fita ta bar mu cikin jimami. kan innah na fada ina kuka ni wallahi innah baxan iya da matar nan ba, kina ganin dai irin abinda take fada a kan mu tana cewa kwadayi ne yasa na aure shi ni dai wallahi sai an fasa, gashi har tana cewa ba namiji bane, me take nufi da hakan innah? cike da damuwa innah ta dube ni, ki kwantar da hankalin ki Niimatullah duk wannan abin da take yi kishi ne, amma batun tace mijinki ba namiji bane karya take, idan ba namiji bane ya aka yi suka haifi wadannan yayan da take takama da su, kawai dai tana so ne ta karya miki gwiwar shiga gidan mijinki, ki kwantar da hankalin ki babu abinda ta isa tayi miki sai abinda Allah ya kaddara miki.

Haka innah ta rika kwantar min da hankali amma duk da haka ban samu nutsuwa ba, saboda duk abinda xai tayar min da hankali bana son shi, bayan tafiyar matar da kadan yaxo, kirana yayi a waya yace naje na same shi a waje, cikin shagwaba na fada masa baxan iya xuwa ba sai dai shi yaxo da kansa.

A tsakar gida ya same mu gaisawa yayi da innah sannan ya koma gefe ya tsaya, ganin mu yayi duk a cikin damuwa tambayar innah ya shiga yi, cikin nutsuwa innah tace masa ba komai, duk nacin da yayi a kan ta fada masa amma taki fada, juyowa yayi ya dube ni Niimatullah ina so xa mu yi magana, turo baki nayi ka fada a nan kowa ya ji, inna ce ta dube ni tashi kije mana Niimatullah.

daki muka shiga, ina shiga innah ta kira ni, saura ki fada masa abinda ya faru bana son ki hada ma'aurata fitina ki kyaleta duk abinda tayi ita da Allah, amsa mata nayi da to sannan na koma, wani jarababben kallo yake bina da shi, cikin nutsuwa na taka har na isa wajen da xan xauna, gefe na samu na rakube, cikin karamar muryarsa ya kira sunana my Niimatullah, a hankali na amsa masa.

kallo yake min mai cike da alamomin tambaya, me yasa na ganku a cikin damuwa ke da innah, hankalina ya tashi da naga yanayin da ku ke ciki, ki fada min damuwar ku dan Allah. hannu nasa a fuskata na fara murxa idona xan yi kuka, rarrashina ya shiga yi kiyi hakuri ki fada min kada kiyi kuka.
cike da shagwaba nace innah tace kada na fada maka saboda kada na hada ka fada da matarka, yana jin abinda na fada yasan inda maganar ta dosa, Ajiyar xuciya yayi tare da girgixa kai

kuka na fara yi, ka sake ni dan Allah ka daina xuwa gidan mu, na fasa auren nan naji tace kai ba namiji bane, dan Allah ka fada min Gaskiya da gaske ne kai din ba namiji bane? murmushi yayi to idan ni ba namiji bane menene babyna? turo baki nayi nima ban sani ba.
kallona yayi yana murmushi, to ni namiji ne Niimatullah ko baki yarda ba? gyada kai nayi gaskiya ban yarda ba saboda ance akwai mata maxa, dariya na bashi sosai ina sonki my Niimatullah, ni namiji ne gwarxon namiji ma kuwa, ko kina so kiga xahiri, da sauri na amsa masa da eh, hannu yasa xai kamo ni da hanxari na kauce ina ihu.

Dariya ya rika min, tunda kina tunanin ni ba namiji shi yasa xan fara nuna miki yanxu, dago idanu nayi ina duban shi, to ai nasan kai namijin ne tunda kaya ma irin na maxa kake sakawa amma matarka.......har xan karasa na tuno da abinda innah ta fada min, tsare ni yayi da ido amma me? kaina a kasa nace ba komai.

matsowa yayi daf da ni, ki fada min ko kuma nayi miki kuka, sunkuyar da kaina nayi innah tace kada na fada maka, lallaba ni ya shiga yi, fada min yar matata babu wanda xai ji abinda muka tattauna.

matsawa nayi sannan na bashi amsa, matarka ce tace kai ba namiji bane amma dan Allah kada ka fadawa innah, murmushi yayi baxan fada mata ba my niima, amma xan miki wasu yan tambayo yi.

kin taba ganin mata maxa yayi aure?girgixa kai nayi alamar a'a, to ki kwantar da hankalin ki namiji xaki aura kuma gwarxo a cikin maxaje, ta fada miki haka ne don kiji tsoro ki fasa, ni kuwa bata san cewa baxan iya rabuwa da yar kyakkyawar matata ba, turo baki nayi ni fa masifar matar nan taka ma ta fara isata, tsoro nake ji kada wata rana ta xane ni, murmushi yayi tare da dago fuskata, ki kwantar da hankalinki indai kina tare da ni babu abinda xata yi miki kin ji ko, to nace masa kwantar da ni yayi a kafadarsa yana shafa gashin kaina, sai da ya gama kwantar min da hankali sannan ya tafi.




*jeeddahtulkhair😘*πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹
*MATAR DATTIJO*
πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹

*Β©jeeddah Tijjani*
*Adam*
*(jeeddahtulkhair)*

*follow me on instagram @jeeddahtijjani*

*dedicated to Amina Nasir*

*godiya ta musamman gare ki yar uwa,Suhaima M Bello ban san da irin bakin da xan gode miki ba sai dai nace Allah ya bar xumunci*

16

kirana innah tayi da hanxari na karasa wajenta, ledar kayan da aka bani a wajen gyaran jiki na gani a gabanta, fito da maganin ta shiga yi fara tsiyaya min tayi a cup,ungo karbi ki sha, tunda kika xo da kayan nan baki taba amfani da su ba saboda shiririta, turo baki nayi xan fara kuka ni wallahi innah baxan sha wannan dacin ba, menene amfanin na rika shan abinda babu dadi ni Allah ki kirata ma taxo ta dauki kayanta,ajiye mata cup din nayi na koma gefe na cigaba da buntsure-buntsure na.

lallaba ni ta shiga yi, kisha Niimatullah dama magani ai ba dan dadi ake sha ba, sai don a samu fa'ida kuma nasan xaki ga amfaninsa nan gaba, don xaki samu soyayyar mijinki dari bisa dari.
kallonta nayi ina dan hawayena ni dai baxan sha ba innah, ko ban sha ba xai so ni, yanxu ma fa yana fada min yana sona sosai, ni na bar miki ma ki shanye gaba daya innah tunda yana da amfani.
tsayawa tayi tana kallona, wai yaushe xaki daina wannan taurin kan naki Niimatullah?Kullum sai an yi fama da ke a kan shan magani, xan karbi lambar malamar taku duk ranar da baki sha ba sai na kirata na fada mata, tunda ni bakya jin maganata. kuka na fara yi kiyi hakuri innata wallahi idan kika fada mata wanda xata bani sai ya fi wannan daci.

kiran wayar innah aka yi hannu tasa ta dauka, kirana tayi, xo ki duba ki ga wane ne ya kira, a sanyaye na karaso na karba wayar ina dubawa naga sunan dattijona, bata fuska nayi nace mata shi ne ya kira innah, dubana tayi wanene shi Niimatullah? wannan tsohon mana innah ko kin manta shi, hararata ta yi, bakya jin magana mijin naki kike kira da tsoho, ko ma dai menene ai da shi xa kiyi rayuwa, ki kira shi da abinda ya fi tsoho ma ni ba ruwana.

turo baki nayi to innah ba Gaskiya na fada ba, ke fa kika fada min duk abinda xan fada na rika fadar gaskiya, shiru innah tayi sai kawai girgixa kai da take yi, numfasawa tayi sannan tace xo ki dauki wayar don nasan da ke xai yi magana.

dukan kasa na fara yi da kafata ni Allah baxan dauka ba innah, ina dauka xai fara yi min irin maganar da baba ya hana ya rika yi min, rarrashina ta fara yi nace duk magana iri wannan ki rika shiru da bakin ki bana so ki rika fada saboda sirrin mijinki ne. duk rarrashin da tayi min a kan na dauki wayar amma naki dauka, sai da ta gaji da ringing ta katse.

sake kiran wayar yayi sai innah ce ta dauka, bayan sun gaisa yake tambayarta ina nake, murmushi innah tayi yau amaryar taka daru take ji, abu kadan sai ta hau kuka wayar ma tace baxa ta dauka ba, kuma taki shan maganin gyaran jikin da aka bata, murmushi yayi ai Niimatullahina akwai rigima, Allah dai ya bani ikon riketa amana, amsawa tayi da ameen, rokon innah ya fara yi dan Allah ki lallaba min ita innah ina so xa mu yi magana da sauri ta kara min wayar a kunnena, cikin kasalalliyar murya ya fara min magana,

Haba matata ta kaina me yasa xaki ce baxa kiyi magana da marayan mijinki ba, ki min magana ko xan samu saukin radadin da ke damuna, maganar ki ita take sawa naji saukin jarabar da ke taso min idan bana tare da ke, lumshe idanuna nayi muryata a kasa nace in wuni, cike da tausasawa ya amsa min da lafiya lau, kiran sunana yayi my Ni'imah!! A hankali na amsa masa, cike da shagwaba ya fara yi min magana.

ki taimaki dan mijinki ki rika amfani da duk abinda aka baki, ko bakya son ki rikita dan dattijonki ne? shiru nayi ba tare da na bashi amsar maganarsa ba, kin yi shiru my Niimatullah a sanyaye na bashi amsa.

Ni fa a kan na rika shan kayan dacin nan gara na hakura da gyaran jikin gaba daya, dama ai babu abinda take koya min idan ba iskanci ba, duk abinda innata ta hana ni shi take sawa nayi, daga yau ma baxan sake xuwa ba, na karasa maganar ina son yin kuka.

murmushi yayi wanda har sai da naji sautinsa a kunnena, yanxu kula da miji da tarairayarsa ne iskanci, lallai da sauranki yarinyar nan, kowace mace da kike gani haka take yiwa mijinta.

kuka na fara yi masa Allah ba haka masu aure suke yi ba, ga innah da baba nan ai su ma masu auren ne amma ban taba ganin baba yace xai taba hannun innah ba, toshe baki yayi subhanallah ki daina bada misali da baba kinga iyayen mu ne kin ji ko? gyada kai nayi nace to, nasiha ya cigaba da yi min, ki daure ki rika bin duk abinda malama ta sa ki, xa kiga amfaninsa a gaba, ina so muna fara amarci ki rika saka ni kukan dadi, ware idanu nayi dama dattijo yana kuka?

Dariya ya rika yi, sosai ma kuwa xa kiga yadda xan rika kuka idan na fara karbar kulawa daga wajen ki yar yarinyata, nasan idan na same ki na samu aljannar duniya Kullum ina jikin ki ina hutawa ta, bata fuska nayi, yanxu duk girman nan naka sai ka xauna a jikina tabdi idan na karye fa?

murmushi yayi baxan karya ki ba amanata, idan ma na karya ni xan dora abata.

kukan shagwaba na fara yi ka kashe wayarka bacci nake ji, bacci yanxu Niimatullah? da ina kusa xuwa xan yi mu yi tare don nasan xaki fi jin dadi ga ki ga mijinki.

da sauri nace a'a kayi xamanka, murmushi yayi okay korata ma kike yi ko, to gani nan xuwa yau a hotel xamu kwana sai ki kore ni da hujja, hakuri na shiga bashi don nasan xai iya xuwa ya tafi da ni, bayan mun gama magana ya fada min gobe xai xo da wuri mu je wajen gyaran jiki.

Washe gari da wuri yaxo ya dauke ni muka tafi,yau ma har ciki ya raka ni bayan ta koya min kula da kaina sannan ta fara shafa-shafa min wasu abubuwa wai na gyaran jiki ne, kowane lungu da sako na jikina sai da aka shafa, tana min ina kuka har aka gama, yau ma dai sai da muka yi fada da ita sannan na sha maganin, wasu ta kara bani tace lallai na sha a gida, da misalin karfe biyu na rana yaxo daukana, har bakin motar shi ta raka ni, bayan sun gaisa take xaulayarsa.

Alhaji anya amaryar nan taka tana so ta rikita ka kuwa, Kullum sai na sha fama take shan magani, kunnena ta ja wannan yar tawa ta fiye taurin kai wlh.

da wani shu'umin kallo ya bini yana sakar min wani hadadden murmushi, saboda gyran jikin da aka yi min ni kaina nasan nayi kyau, gaba daya fatata ta canja sai kyalli take, ga wani kamshi da nake yi na musamma. lumshe idanu yayi sannan ya bata amsa.

Hajiya a cigaba dai da hakuri a kula min da babyn tawa haka nake fama da rigimarta kullum, murmushi tayi ai Niimatullah hukuma ce sai rarrashi Alhaji murmushi suka yi gaba dayan su.


hannu ya bude min alamar na shigo kirjinsa noke kafada nayi ....... murmushi yayi tunda baxa ki xo ba to shiga mota mu tafi, sallama tayi mana ta wuce xuwa Office dinta.

Har yanxu bai daina damuna da jarababben kallon shi ba, hannuna ya rike da sauri na kwace na mayar da shi cikin hijab, murmushi yayi yana dubana Niimatullah fadan ki yayi yawa amma xan yi maganin ki, shiru nayi masa ya rika maganganunsa ba tare da na bashi amsa ba.



*jeeddahtulkhair😘*
*[10/18, 11:22 PM] It'z B Y ebrerheem: πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹
*MATAR DATTIJO*
πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹

*Β©jeeddah Tijjani*
*Adam*
*(jeeddahtulkhair)*

*follow me on instagram @jeeddahtijjani*

*godiyata da tukwici na baxai yanke ba a gare ku sai dai kawai nace Allah ya bar xumunci*

*Et'z Yusuf*
*Abdurrahman ibrahim*
*it'z b y Ibrahim*
*na gode Allah ya bar xumunci*

17

Kai tsaye gida ya kaini, muna isa na bude kofar motar xan fita, ba tare da na kalle shi ba nace sai anjima, har nasa kafata a waje ya riko ni ya dawo dani hada fuskata yayi da tasa yana kallona, cikin siririyar muryarsa yake min magana, haka ake yiwa miji sallama Niimatullah? turo baki nayi to ai haka kowa yake yi, kokarin kwace hannuna nayi xan fita, dawo da ni jikinsa yayi tare da jan kumatuna yana murmushi, ke ba kowa bace da xaki rika yin abinda kowa ke yi, ke ta daban ce haka ma mijinki na musamman ne don haka yake bukatar komai na musamman daga wajen ki, domin son da yake miki ma na musamman ne, juyo ki kalle ni my Niimatullah nasan xaki tabbatar da hakan a idona.

ina kallonsa nayi saurin kawar da fuskata saboda yadda idanunsa suka canja, ni kaina baxan iya fassara irin kallon da yake min ba, murmushi yayi min tare da kwantar da ni a kirjinsa, me yasa har yanxu kike jin kunyata Niimatullah? ina ganin lokaci yayi da ya kamata ki daina jin kunyata, juyo ki dube ni, makale kafada nayi tare da cewa a'a, tallafo fuskata yayi tunda kunyata kike ji ina ganin yau xan tafi da ke na cire miki wannan kunyar saboda idan muka cigaba da kasancewa a haka xata cutar da ni, saurin dagowa nayi na dube shi, ka daina fadar irin wannan maganar Allah xan daina kula ka, shafa fuskata yayi ko kin daina kulani, ni sai na kula ki my Niima, dan turo baki nayi dama ba kada xuciya dattijon nan dariya yayi indai a kanki ne ba nida xuciya na yarda a kira ni da kowane irin suna.

rufe kofar motar yayi cike da mamaki na tambaye shi, a gida fa muke amma ka sake kulle mota, kallona yayi yana kashe idanu, ina bukatar ganin matata a kusa da ni shi yasa na kulle, yanxu ma tafiya xan yi da ke na shakata da abar alfaharina.

hawaye naji suna kokarin fito min a hankali na dube shi, kayi hakuri ka bani hanya na wuce gida kaga rana tayi kuma akwai aikin innah da ban karasa ba, jan kumatuna yayi yana min wani kallo, aikin mijinki ya fi muhimmanci fiye da wanda xaki je kiyi, dan yamutsa fuska nayi, aikin naka ne

Please Login or Register in order to submit comment