Join Our WhatsApp Group

GWARZON SADAUKI Book 1 Complete Hausa Novel Document by GWARZON SADAUKI Book 1


GWARZON SADAUKI Book 1

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 16296GWARZON SADAUKI Book 1

Reading Time: 1 Hours

Added On: 25, Feb 2024

Author: Abdulaziz Sani Madakin Gini ,

Ebook Compiler : Abubakar Saleh AlQuyraemey, Shuraihu Usman

Author Group : Unknown group

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Adventure novels

File Size: 83.24 kb

File Type: txt

Views: 943+

Download: 429+

Last download: 6 hours ago

Description/Story: GWARZON SADAUKI
Littafi Na Daya (1)
Part A
Marubuci: Abdulaziz Sani M/Gini
Typing: Abubakar Saleh AlQuyraemey
Kurkuku ne wanda aka gina dakunsa da katangarsa da zallan duwatsun wuta. Kofofin gidan gabadaya da tagoginsu an yi su ne da bakin mummulallen karfe mai kaurin kamu guda. Tsayin katangar wannan kurkuku kamu sittin ne don haka duk wani fursuna da ke cikinsa bai taba tunanin haurewa ba. Akalla akwai zaratan dakaru guda dubu daya da đari biyu. masu gadin wannan kurkuku wadanda su kansu ababen tsoro ne saboda kwarjininsu gami da surarsu ta manyan sadaukai domin ido ba mudu ba ne amma ya san kima.
A daidai wannan lokacin fursunoni na tsaitsaye a tsakiyar wannan kurkuku suna yar hada- hadarsu kamar yadda suka saba. Wasu suna wasan motsa jini wasu hira suke yi!wasu kuma suna kai kawo. Dama kullum an ware musu irin wannan lokaci domin samun nutsuwa. Kwatsam! Sai suka ji motsin bude katuwar kofar gidan wacce tsawonta da fadinta kamu sittin-sittin ne. Karar bude kofar ta cika dajin gabadaya da amsa kuwwa kai ka ce wani katon dutse ne ya mirgino da gudu. Ita dai wannan kofa ana budeta ne da wata irin na'ura mai dauke da kaca da kuma hakoran mawanin karfe mai juyawa. Dakaru ashirin ne ke iya juya mawanin sannan kofar ta bude a tsawon dakika dari uku da sittin.
Kofar na gama budewa sai fursunoni suka ga dakaru kimanin guda arba'in sun tuso keyar wani mai laifi wanda aka daure hannayensa da kafafunsa da manyan sasari kai ka ce giwa a ka janyo.
Shi dai wannan mai laifi ya kasance matashin saurayi wanda shekarunsa baza su haura ashirin da shida ba. Ya kasance kyakkyawa ne mai kirar sadaukai. Fuskarsa cike take da murmushi kawai sai kalle-kalle yake yi yana duban tsawon katangar gidan da kuma tsarin kofofin da tagogi.
Bayan an shigo da wannan saurayi tsakiyar kurkukun a lokacin da aka rufe kofar shigowa sai aka tsayar da shi cak aka fara kallon kallo tsakaninsa da Sauran fursunonin gidan. Kowa sai ya tsaya ya daina abin da yake yi. Su dai fursunonin gidan mamaki suke yi kuma suna tambayar junansu suna cewa wannan kuma wane takadari ne haka har da za a daure shi cikin manyan sarkoki. A saninsu duk wani gawurtaccen ma laifi a duniya idan aka kawo shi wannan kurkuku nanbirnin Kisra risina yake ya kama kuka da nadama to amma shi wannan gashi da murmushinsa ya shigo ko kuwa bai san Irin masifar dake ciki ba ne.
Wata irin muguwar rayuwa ake yi cikin wannan kurkuku wacce mai karfi ne kadai yake tsira. Ba a raba abinci a cikin nutsuwa sai masu Karfi sun fara dibar nasu sannan in ya yi ragowa marasa karfi su diba. Idan mutum ba samu ba sai dai ya kwana da yunwarsa. A kullum akan dauki gawa guda biyu ko uku a cikin wannan kurkuku saboda bakin zaluncin da ke faruwa a tsakanin fursunonin.
Idan fursunoni za su kwana suna yaki a tsakaninsu ko kallonsu dakaru ba za su y ba. amma a da zarar fursuna ya karya doka guda daya take dakaru za su ufe shi da luguden duka sai sun ga ya suma sannan za su kyale shi kuma a dauke shi a kai shi wani kuntataccen daki wanda ko kwanciya zai yi ba zai iya mike kafafunsa ba kuma daki ne cike da shara, tsutsa ga doyi sauro da kudaje ma sun ishi mutum masifa.
Ana cikin wannan kallon kallo tsakanin bakon fursuna da sauran fursunonin gidan kenan sai wata kofa daga can wani bangare ta bude, shugaban dakarun gidan ya fito tare da wasu tsirarun dakarunsa masu ake masa baya suka durfafo inda bakon fursuna yake.
Shi dai Shugaban dakarun wannan kurkuku ya kasance wani garjajen kato mai sura irin ta mutanen farko Kallo daya za ka yi masa ka san cewa sadauki ne kuma jarumin gaske mai fasa taro. Shigarsa ta fita dabam da ta sauran dakarun gidan domin rigarsa, takalmansa da doguwar safar hannu duk na karfe ne Takubba biyu ne rataye a bayansa.
Duk jikinsa a murde yake cike da kwanji ga jijiyoyi burdin-burdin. Sai da suka iso daf da bakon fursunan yadda tazararsu ba ta wuce taku biyu ba sannan suka tsaya cak shugaban dakaru da bakon fursuna aka yi kallon kallo na tsawon dakiku biyar sannan Shugaban dakarun ya yi dan guntun murmushi ya dubi bakon fursunan ya ce.
"Sunana Gadaraz ni ne shugaba a wannan kurkuku Ya kai bawa Insam na yi maka barka da zuwa gidan mutuwa. Labari ya iske ni cewa sau biyu kana samun nasarar guduwa daga can kurkukun cikin gari ana kamoka da kyar to ka sani nan ba a iya guduwa. Duk fursunan da aka shigo da shi nan sai dai a fitar da gawarsa amma bai įsa ya fita a raye ba. Yau tsawon shekaru goma sha hudu kenan da kafa wannan kurkuku ni da jama'ata muna gadinsa babu wani fursuna da ya taba karya wannan tarihi. Ka sani muna da dokoki guda tara a gidan nan. Dokoki biyar daga ciki idar ka aikata su za a yi maka hukuncin
dukan kawo wuka gami da horo nai tsanani Ragowar dokoki guda hudu kuwa hukuncin kisa ne a kan su. Ina mai yi maka gargadi da ka kiyaye wadannan dokoki wadanda za a sanar da kai su yanzu take idan kana son ka tsira da lafiyarka da rayuwarka."
Koda gama fadin hakan sai shugaban dakaru Gadaraz ya dubi wani Badakare ya ba shi umarmi.
Badakaren ya bude baki ya ce.
"Doka ta farko a gidan nan ita ce. "
Caraf sai bawa Insam ya tari numfashin Badakaren ya ce. "Dakata ba na bukatar jin dokokinku lna son na karya kowace doka daya bayan daya har guda taran yadda za a iya hukunta ni. Daga yau ina mai tabbatar maku da cewa babu wata doka da zata yi aiki a kaina sai dai akan sauran fursunoni.
Ko da jin wannan batu sai dakarun dake kewaye da Gadaraz suka daga kulakensu za su afkawa Bawa Insam amma sai Gadaraz ya daka musu tsawa ya ce, "Ku dakata ka da ku tabashi.
Da jin haka sai dakarun suka ja da baya suka tsaitsaya. Gadaraz ya dubi Insam ya bushe da dariyar mugunta. Lokaci guda kuma ya murtuke fuskarsa ya ce "Da kyau haka nak s ha ga jarumi mai dakakkiyar zuciya da karfin hali irin ka. Ai ka rage mana wahala tun da ka zabi hanyar da ta fi sauki a garemu. Mu dama amfaninmu a gidan nan horo tsaro da hukunci! Burinmu kawai a aikata laifil Ga fili ga mai doki! kai ku kwance masa duk sarkokin dake jikinsa kuma a nuna masa dakinsa na kwana amma da zarar ya karya doka daya a zartar da hukunci a kansa."
Ko da jin wannan batu sai mataimakin Gadaraz cikin alamun fargabaya ce "A'a ya shugabana Sarkiya gaya min cewa wannan yaron yana da matukar hadari don haka bai kamata a kwance masa sarkokin nan ba.
Gadaraz ya daka wa Bartus tsawa ya ce 'Ai so nake na ga iyakar hadarin nasa. Maza ku kwance masa sarkokin na ce."
Da jin haka sai wasu dakaru biyu suka zaro mukullai suka kwankwance sarkokin dake jikin hannayensa da kafafuwansa. Saboda dadewar daurin duk shatar karfe ta fito a kan hannayen da kafafun. Ko da Insam ya ga an kwance shi sai ya yi mika gami da murnushin murna domin ji ya yi kamar ya samu yanci ne daga matsayin bawa, shi kuwa Gadaraz sai ya juya da baya ya nufi kofar da ya fito dakarun dake tare da shil suka bi shi a baya. Wani Badakare daban ya dubi nsam ya ce ka biyo ni.
Ba tare da wata gardama ba kowa sai Insam ya bi Badakaren a baya suka nausa wani 6angaren daban na gidan. Duk wannan abu dake faruwa sauran fursunonin gidan suna ta kallon bakon bawa insam. Ko da aka nufi cikin gidan da shi sai ya ga gabadayan fursunonin gidan sun biyo su a baya. Hakan ne ya sa Insam ya fahimci cewar lallai akwai wani abin da ke shirin faruwa don haka sai ya yi shirin tarar ko mene ne a ransa.
Lokacin da aka iso wajen da rukunin dakunan barcin fursunonin yake sai Insam ya hango wani babban daki guda đaya wanda ya bambanta da sauran dakunan. Zaune a kofar dakin bisa wata kujera wani narkeken kato ne bakar fata, kansa ya sha askin kwallon molo, ga katon yari guda biyu a kunnuwansa. Yana da saje gami da murtukaken gashin baki. Wannan bakin mutum ya kasance mummuna kuma dogo ne sosai domin gabadaya gidan babu mai tsawonsa da kira ta sadaukai face sadauki Gadaraz.
Fursunoni ashirin ne a zagaye da kujerar ta wannan bakın mutum ke zaune suna fadanci. Kai da gani ka san shi ne shugaban fursunonin wannan gida. Duk fursunan da ya zo wucewa ta gabansa sai ya zube kasa bisa guiwoyinsa biyu ya yi gaisuwa sannan zai wuce. A cikin fursunonin dake kewaye da shi akwai masu yi masa fifita, akwai mai yi masa tausa sannan akwai masu dauke da faratan ya'yan itatuwa da abinci da ababen sha kala-kala.
Shi dai wannan bakin bawa ana kiransa da suna Barsad A iya rayuwa Barsad bisa binciken da aka yi ba a taba ganin ya yi murmushi ba sai daí dariyar mugunta. Kullum da koyaushe fuskarsa a murtuke take babu annuri. Zuciyarsa cike take da zunzurutun rashin tausayi da zalunci. Shi kansa bai san iyakar adadın mutanen da ya kashe ba a rayuwarsa.
Yanzu ne dubunsa ta cika aka kamo shi da kyar aka kawo shi wannan kurkuku sakamakon laifin haura gidan Sarkin Kisra da nufin yin sata shi da yaransa mutum arba'in aka yanke musu hukuncin daurin rai da tai.
Lokacin da Bawa Insam ya zo zai wuce ta gaban Barsad sai ya kau da kai ya yi kamar bai ganshi ba ya wuce gaba yana biye da Badakaren dake masa jagora. Kawai sai ya ga Badakaren ya ratse g fe guda ya tsaya cak ya juyo baya wasu fursunoni kimanin su ashirin suka taho da gudu suka yi wa Insam kawanya. Daya daga cikin su ya dube shi a fusace ya ce.
"Kai wannad bckon fursuna ka yi ganganci da ka ki sauraron dokokın gidan nan guda tara dazu. To ka sani wancan na zaune shi ne Sarki a gidan nan, hatta dakaru ma shakkarsa suke bare kai fursuna. Dole ne ka rinka gaishe shi sau uku kullum kana durkuso bisa guiwoyinka a gabansa, wannan yana daga cikin dokokin gidan nan guda tara.
Sa'adda Insara ya ji wannan batu sai ya kyalkyale da dariya sannan ya dubi fursunan da ya yi maganar ya ce, "Yau an sami Sarki na biyu a gidan nan, ni ma sai dai a rinka gaisheni kamar yadda ake gaishe shi."
Kafin Insam ya gama gama rufe bakinsa tuni fursunonin da suka kewaye da shi sun lullube shi da duka, Sun durkusar da shi kasa. Kawai sai aka ga ya yunkuro sama ya watsar da su duka wasunsu suka yi sama tamkar da majajjawa aka janye su suka gwaru a jikin gini suka zubo kasa. Fursunonin suka sake tasowa da sauri suka ugo kansu aka ruguntsurne da fada.
Duk fursunan da nsam ya nausa sa ga ya baje a kasa ya kasa mikewa idan kuwa kafarsa ya doka ko hannunsa sai dai a ji ya kurma ihu sakamakon karyewar kashinsa.
Kafin cikar dakika dari da ashirin ya bazar da fursunonin ashirin a kasa an rasa dayansu da ya iya mikewa tsaye.
Ko da ganin haka sai sauran fursunonin da ke wajen gabadayansu suka yunkura za su afkawa Insam amma sai Barsad ya daka musu tawa suka tsaya cak! Barsad ya mike tsaye daga kan kujerar da yake zaune ya tako da kafafunsa tamkar wani toron giwa ya zo daf da Insam ya tsaya kai ka ce zaki ne a gaban kyanwa saboda bambancin girmansu. Barsad ya sunkuyar da fuskarsa daidai kan ta Insam ya ce.
"Kai yaro ai ba a sarki biyu a birni guda. Shekarata bakwai a gidan nan ba taba samun tsageran da ya yi mini rashin kunya ba sai kai!
Tabbas kwarin zuciyarka ya burgeni sai dai ka yi a banza domin yanzu zan kared maka ruhin numfashinka."
Sa'adda Insam ya ji wannan batu sai ya yi murmushi kuma ya juyawa Barsad baya cikin jin izza gami da yarda da kai ya ce "'Ba za ka iya kashe ni ba face kwanakina sun kare ka ja mutuncinka da kimarka in ba haka ba kuwa za ka ji kunyar da ba ka taba ba.
Kafin Insam ya gama rufe bakinsa, tuni Barsad ya kawo masa Wawan mangari a wuya. Cikin zafin nama Insam ya sunkuya hannun Barsad ya doki iska.
Nan fa suka kacame da masifaffen fada, ya zamana cewa Barsad na kai wa Insam naushi da bugu hannu da kafa yana karewa da hannu da kafa. Duk sa'ad da suka hada jiki sai ka ji kamar duwatsu ne suka hadu! Nan fa mamaki ya kama gabadayan fursunonin da dakarun dake wajen Sai da Insam da Barsad suka shafe kusan dakika dari uku da arba'in suna gwamarzuwa amma dayansu bai sami nasarar nausar wani ba.
Ko da suka ga wannan naushi da bugun da suke wa juna babu nasara sai suka ja da baya suka yi cirko-cirko suna kallon juna kamar zakaru.
Kowannensu tunani da mamaki yake a cikin ransa bisa ganin yadda karfinsu ke neman zuwa daya.
Nan fa suka fara tunanin dabarar da ya kamata su vi don sam nasara. Kawai sai Barsad ya daga hannunsa guda take wani daga cikin yaransa yajefo masa takobi ya cafe.
Ko da ganin haka sai Insam ya daka tsalle sama daga inda yake tamkar daga cikin baka aka harba kibiya ya yi wata irin alkafira a sama ya fizgo wadansu kulaken guda biyu daga hannayen dakarun tsaron gidan yarin, sannan ya dira kasa bisa kafafuwansa yana mai gyara tsayuwa.
Gabadaya dakaru da fursunonin dake wajen ba su san saadda suka kama yi wa Insam tafi ba saboda ganin irin wannan gagarumar bajinta da ya yi. Dole ne Insam ye burge duk wanda ya ga yadda ya iya wulkita jikinsa a sama tamkar mazari.
Nima dai Abubakar Saleh inkiya Mijin soja dake yi maku typing sai da na tafa wa Imsam ganin irin namijin kokari da yayi kuma nake cewa mu hadu a wani lokaci dan jin cigaban wannan labari.
Domin samun Complete dinsa dama wasu littattafan zaku iya tuntubata 08138873799
GWARZON SADAUKI
Littafi Na Daya (1)
Part B
Marubuci: Abdulaziz Sani M/Gini
Typing: Abubakar Saleh AlQuyraemey
Cikin fushi Barsad ya dubi dakarun da fursunonin yana mai daka musu harara. Nan take kowa ya yi sauri ya sunkuyar da kansa kasa. Faruwar hakan ke da wuya sai Barsad ya rugo izuwa kan Insam yana mai kwarara uban ihu mai matukar firgitarwa. Karar taku sawun kafafunsa suka cika dodon kunne, ihun nasa kuwa ya firgita kowa dake wajen amma shi Insam ko gezau bai yi ba. Kawai sai ya kara gyara...


Read / Download GWARZON SADAUKI Book 1

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

4 Comments On GWARZON SADAUKI Book 1
avatar
maimunatu-7

3 months ago

Reply

Inasan litafin nan pls

avatar
maimunatu-7

3 months ago

Reply

Inasan litafin nan pls

avatar
daiy

3 months ago

Reply

Replying to maimunatu-7

Ki downloading ki karanta ko ki karanta shi anan shafinmu amma ki sani kafin ki iya downloading dole sai kinyi subscribtion na shafinmu wanda mafi karanci shinw 1k Naira

avatar
atiku

1 month ago

Reply

Zansamu complete littafan nan a pfd kuwa

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album