Join Our WhatsApp Group

TARKON MUTUWA BOOK 1 TO 9 Complete Hausa Novel Document by TARKON MUTUWA BOOK 1 TO 9


TARKON MUTUWA BOOK 1 TO 9

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 52856



TARKON MUTUWA BOOK 1 TO 9

Reading Time: 4 Hours

Added On: 27, Jun 2023

Author: Abdulaziz Sani Madakin Gini ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Adventure novels

File Size: 306.42 kb

File Type: txt

Views: 1669+

Download: 1004+

Last download: 9 hours ago

Description/Story: TARKON MUTUWA
Abdulaziz Sani madakin Gini
Typing:- prince auwal auzab
Post:- AA Misau
Littafi na daya 1
Part 1A
.
Awani zamani can baya mai tsawo daya shude
alokacin da akeyin mulkin kashin dankali wato
manya sune asama,kanana sune a kasa.
awannan lokaci zalunci ya yawaita sam babu
adalci,doka bata aiki sai akan talaka,mara
karfi,da makaskanci.
adaidai wannan zamanine akayi wata nahiya
wacce ta shahara a duniya aharkokin
kasuwanci,karfin mulki da yawan da yawan
al'umma.
kasar da tafi dukkanin kasashen dake nahiyar
daukaka itace bindal.
duk wani dan kasuwar dake mu'amala da birnin
indai yanason ya tsira da mutuncinsa da kuma
dukiyarsa to dole ya kasance ribar da zai samu
akullum ya rabata gida uku.kaso daya shine naka
kaso biyu kuma sai ya kaiwa sarki shamsal
sarki shamsal ya kasance gawurtaccen jarumi
mashahurin mayaki wanda babu kamarsa
anahiyar gaba daya domin atarihin jarumtakarsa
ba'a taba yi masa rauniba a yaki ko a gasar
jarumtaka.
yana iya shafe sa'a goma sha biyu yana yaki
batare daya gajiba yace
yana iya yin tafiyar
kwaba bakwai acikin gudu batare daya tsaya don
ya huta ba sai dai kawai ya daga battar ruwa
yasha yaci gaba da gudun.
kai idan sarki shamsal yayi wani abun na bajinta
ko jarumtaka sai kaga kamar ba mutum bane shi.
aljanine komai yawan mayaka yana iya tarwatsa
su ya kashe na kashewa,masu gudu su gudu don
tsira da rayuwarsu.
abangaren zalunci kuwa masu hasashe sun
tabbatar da cewa babu wani sarki anahiyar
wanda yafishi zalunci,domin shi yan uwansama
sarakai cin zalinsu yakeyi bare talaka.
idan ya kyallara ido yaga wani sarkin da
kyakkyawar mata saidai kawai ya aika masa da
ya kawo masa ita da kansa.
idan sarkin yaki kawota zai iya rasa ransa ko
mulkinsa don haka yana rawar jiki zai kaita.
batun haraji akan talakawa kuwa babu inda aka
tsananta shi sama da birnin bindal ko yaya
talaka yayi laifi yanzunnan zaisa azaneshi ko
kuma akai shi kurkuku ayanke masa hukuncin
shekara biyu ko fi.
atakaice dai inbanda sarki shamsal da
fadawansa,da kuma yan barandars babu mai
kwanciyar hankali acikin birnin bindal.
acan karshen birnin bindal abangaren kudu akwai
wani makeri wanda ake kira da suna satyan.
makeri datyan tsohone tukuf domin shekarunsa
sunkai dari da biyar kuma tun baifi shekara
taraba aduniya ya kware a harkar kira kuma ya
shahara domin gadon sana'ar yayi.
yana da shekara taran mahaifinsa ya rasu.
shikuma yaci gaba da aiwatar da aikin mahaifin
nasa.
hatta makaman yakin gidan sarautar sarki
shansal amakerar satyan ake kera su ba'ataba
samun wani sabani ba atsakaninsa da gidan sarki
shamsal ba.sarki shamsal bai taba ganin tsoho
satyan ba,haka shima bai taba ganin sarki
shamsal ba.
akar kashin tsoho satyan akwai yara ma'aikata
kimanin su saba'in da daya kuma duk suna
samun abin da suke rayuwarsu a karkashinsa.
albarkacin kayan yakin dayake kerawa
masarautane yasa ba'a tsananta masa haraji
ba,kuma tun azamanin mahaifin sarki shamsal
haka abin yake wakana.
tsoho satyan yana da matan aure guda daya
wacce itace girma ya kamata domin shekarunta
sunkai saba'in.
allah ya albarkacesu da yaya biyu kacal
aduniya,mace dana miji.
macen itace babba shekarunta sunkai ashirin da
biyar,ana kiranta da suna sadirat.
sadirat macece kyakkyawa daidai gwargawado
mai kyan siffa ta taso da farin jini sosai wajen
samari amma saboda itace kadai ke taimakon
mahaifiyarta a ayyukan gida bata son tayi aure
harsai kaninta hatyan yayi,saboda shi matarsa
zata zauna agidan ta dinga kula da mahaifiyarsu.
ita kuwa dauketa za'ayi akaita wani gidan.
tsakanin sadirat ban bancin shekara hudu ne
wato yanzu hatyan yana da shekara ashirin da
daya kacal aduniya,
allah daya gari banban ka kadan hatyan bai gaji
harkar kira ba.tun daya taso da kuruciyarsa babu
abinda ya keso sama da harkar farauta don haka
kusan kullun da koyaushe yana cikin daji.
tun safe idan yafita farauta baya dawowa sai
rana ta fadi.
wani ikon allah kuma sai ya zamana yana da
nasibi matuka a harkar domin baitana fita farauta
ya dawo babu wani abu ba.
sai an ganshi ya kamo babbar dabba ko babban
tsuntsu.
tun hatyan nada shekara tara aduiya aka gane
cewa sadauki ne domin tun asannan yake iya
gumyrzu da manyan dabbobin daji kuma ya
kashesu da hannunsa.
wannan baiwa da allah ya bashine ta sanya shi
kansa sarkin mafarauta na birnin ya jashi a
jikinsa kuma ya kaunaceshi ainun hakannenama
yasa ya rinka taimaka masa da yan sirrikan daji
dana tsafi domin samun tsari
Akullum abin da sarkin mafarautar ke nunawa
hatyan shine ya boye sadaukantakarsa
kada mutane su sani saboda al'adar sarki
shamsal itace.
duk sa'ad da yaji ance ga wani sadauki ya taso a
birninsa saiya tura a sirrance a kashe shi.
ba komaine ya jawo hakanba face bokayensa sun
gaya masa duk ranar da aka sami wani sadauki
mai irin baiwarsa ta jarumtaka dajuriyar yaki da
gudu to shine zai karbi mulkinsa bisa wannan
daliline
duk dabbbar da hatyan ya farauto da hannunsa a
daji sai ya boyeta acikin buhu ya kaita gidan
sarkin mafarauta
shine zai sayar masa da dabbar ya bashi ya
bashi kudinsa don kada a gane cewa shine ya
kashe dabbar.
duk sa'ad da hatyan ya shiga daji farauta baya
yarda wani ya ganshi alokacin da yake gumurzu
da manyan dabbobi.
aboye hatyan yake baiwa kansa horon gudu dana
sarrafa makami.
tun yana da shekara goma sha daya
idan ya kasa tsere da dabba komai karfin
gudunta saiya kure mata gudun ya rafketa.
hatyan na iya shafe kwana ashirin yana gudu a
daji batare da ya tsaya don hutawa ba ko cin
abinci ba sai dai kawai ya sha ruwa.
wato dai hatyan har yafi sarki shamsal juriya a
wajen gudu.
abinda sarki shamsal yafi hatyan kawai shine
karfin damtse da kwarewar yaki da sanin
makama.amma kuma hatyan yafishi zafin nama.
a duniya babu abinda hatyan keso da tsananin
kauna sama da yayarsa sadirat domin ko
kuda baya son yaga ya sauka ajikinta.da nufin ya
taba lafiyarta.
duk saurayi ko kuma wani dan iskan daya
kuskura ya taba sadirat da hannunsa to sai
hatyan ya batar da kamanninsa ya kai masa
ziyarar dare ya sare masa hannunsa ya mai
dashi musaki.
bisa wannan dalililine maza ke tsoron latsa
sadirat.
wayanda dama suke sonta da aure tsoron zuwa
wurinta suke.
lokacinda tsoho satyanyaga cewa kokadan dansa
baya sha'awar harkar kira sai farauta sai
hankalinsa ya dugunzuma ainun saboda tunanin
cewa duk ranar daya mutu babu wanda zai
gajeshi saidai yaransa shikenan sana'ar tabar
gidansu.
akan hakane ya rinka matsawa hatyan yana son
yayi masa dole akan yabar farauta.
koda ganin haka sai hatyan yaje ya sanar da
sarkin mafarauta abinda ake ciki.
dajin haka sai sarkin mafarauta ya taso dakansa
yazo gidan satyan dama can sun kasance
aminan juna sai dai shi sarkin mafarauta ne
shekarunsa basufi tamanin da biyar ba.
lokacin da sarkin mafarauta da satyan suka
kadaita acikin turaka kuma suka gaisa
saiya dubeshi yace
yakai abokina kayi sani cewa kowanne da yana
da irin baiwarsa.
danka Allah baiyishi makeriba,mafarauci ne
masu iya magana sunce ranar wanka ba'a boye
cibi
to yau zan sanar dakai wani babban sirri akan
danka wanda baka taba saninsa ba.
ahalin yanzu duk fadin garinnan inbanda sarki
babu wani jarumi wanda yafi hatyan
sadaukantaka,karfin gudu da juriyar wahala adaji.
kasani cewa tun yana da shekara tara yake iya
fada da manyan dabbobin daji ya kashe su
yakawo su gidana na sayar masa dasu ba tare da
kowa ya sani ba.
nine nake sayar da abubuwan daya farauto.
yanzu haka ya tara kudade masu dunbun yawan
da sun wuce dinare dubu dari biyar amm tsoro
yakeji yazo ya sanar dakai.
kasani nayi bincike acikin hallarar tsafina nagano
cewa
wannan yaro naka nangaba sai ya zama babban
mutum akasarnan don haka idan har sarki ya
sami labarin jarumtakarsa kasheshi zaiyi
babban abindayafi tayar mini da hankali shine
zafin zuciyar hatyan.
ina tsoron ranar da wani abu zai hada shi da
gidan sarauta.
indai aka tabashi bazai hakuraba tunda kana
ganin abinda yake yiwa samarin da suke yiwa 'yar
uwarsa sadirat wargi.
a yanzu haka ya janyo kowa tsoronta yakeji
awannan garin.
ka tuna cewa sarki shamsal yana da azzalumin
da wanda shima shekarunsa basufi na hatyanba
yana da muguwar al'ada tayiwa mata fyade.
a garin nan yarima zainur yayiwa yan mata sama
da yam mata guda dari fyade.
kuma ko magana iyayen 'yan matan sukayi sai a
kashesu.
mahaifinsane ya daure masa gindin yayi duk
abinda yaga dama saboda yana sonsa fiye da
komai aduniya.
ina tsoron ranar da yarima zainur zai yi arba da
sadirat,
na tabbatar da cewa bazai kyaletaba idan kuwa
ya taba ta sai hatyan yayi masa mummunan
hukunci.
sa'adda sarkin mafarauta yazo nan a jawabinsa
sai tsoho yaji hankalinsa ya dugunzuma ainun
fiye da koyaushe.
daga can saiya dago kai ya dubi sarkin
mafarauta yace
yakai abokina kayi sani cewa
dangane da batun sadirat bani da wata fargaba
saboda kullum sadirat na gida bata zuwa ko ina
saboda ko yaushe itace takeyin ayyukan gida.
kaga kenan babu yadda za'ayi ta hadu da zainur
tunda babu abinda zai kawoshi nan
ko batun kayan yakin gidan sarauta akwai wakilin
kayan wanda shi yake zuwa ya karba.
ni yanzu kawai damuwata akan hatyan ce.
me zai hana ka dauke mini shi daga garinnan
gaba daya ka turashi can wani garin.
wajen abokan sana'rka yayi rayuwarsa a
can,tunda ni na tsufa tawa ta kare,
mahaifiyarsu ma girma ya soma kamata.
abinda muke buri kawai shine muga auren
'ya'yan mu kafin ajalin mu
gashi su biyun sun shaku da junansu ainun basa
son rabuwa idan har za'a dauke hatyan daga
garin nan lallai a hada su tare.
ni ina gane wannan ne kadai hanyar da zamubi
mu tserar da rayuwar hatyan data yar uwarsa
daga sharrin sarki da dansa.
saboda haka a yau dinnan idan hatyan ya dawo
daga farauta ka taho dashi mu zauna gaba daya
tare da mahaifiyarsu mu sanar dasu hukuncin da
muka yanke.
yan kudin da hatyan ya tara
sun ishesu su gudanar da sabuwar rayuwa a
wani gurin amma babbar shawarata
itace subar wannan nahiyar gaba daya.
lokacin da tsoho satyan yazo nan a jawabinsa sai
sarkin mafarauta yakamu da tsananin tausyinsa
har kwalla ta zubo masa
ya sunkui da kansa kasa yace
inda matsalar take shine
tayaya kake tsammanin hatyan da yar uwarsa
sadirat zasu iya barinku
kai da mahaifiyarsu su tafi can wata nahiyar su
zauna alhalin kuna raye baku mutu ba?
koda wannan tambaya sai hankalin satyan ya
dugunzuma ainun.
nantake hawaye me yawa yazubo masa yace
rabuwarmu dasu a wannan lokaci itace tafi alheri
atsakaninmu
idan kuma sukaki su tafi to anan gaba zasu yi
tafiyar dole ayayin da babu mudin
cikin rashin fahimta sarkin mafarauta yace
nifa bangane me kake nufiba
satyan yace banaso ka fahimta din amma dai
lallai ka tilasta
hatyan ya dauke yar uwarsa su bar nahiyar gaba
daya kuma su manta damu.
idan darabon zamu sake ganawa
zamu gana nan gaba
ni da mahaifiyar tasu zamuyi jiranku idan hatyan
ya dawo daga farauta
koda gama fadin haka sai satyan ya mike tsaye
ya kama hannayen sarkin mafarauta ya tashe shi
tsaye
suka kurawa juna ido
sannan yace nagode abokina
nagode da wannan shawara daka zo mini da ita
da kuma wannan sirri na dana daka baiyana mini.
tabbas kai masoyine na kwarai bazan taba
mantawa dakai ba
Allah yabar wannan zumuncin namu wanda tun
iyaye da kakanni yake
gidan makera da gidan mafarauta mun zama
tamkar jini daya.
kayi sani cewa inaji ajikin bazan dadeba
ajalina zai riskeni.
ajalina yana kusa donhaka nabar maka amanar
iyalina.
kayi iya kokarinka wajen karesu da basu shawara
ta gari
lokacin da makeri satyan yazo nan azancensa sai
hawaye ya zubowa sarkin mafarauta ya
rungumoshi yana mai cewa.
na rantse da girman iyayena zan rike wannan
amana taka hannu biyu har izuwa karshen
rayuwata.
sai da suka jima suna zubar da hawaye sannan
sarkin makera ya yi masa sallama ya tafi.
a can gidan sarauta kuwa da farkon yammaci
sarki shamsal ma zaune acikin dakin shakatawa
tare da matarsa suna shakatawa sai ta dubeshi
tace
yakai mijina kayi sani cewa duk sa'ad dana
kalleka sai naji farinciki ya turnikeni
saboda nice nake auren sadaukin jarumin da
babu kamarsa awannan nahiya.
kuma nice nake da sarkin da babu kamarsa a
daukaka da arziki.
nice ke auren zakaran da ya lashe gasar
jarumtaka sau ashirin da daya awannan nahiya
gaba daya.
har yanzu kaike rike da kambun wannan gasa
koda sharifa matar sarki tazo nan a zancenta sai
farin ciki ya turnukeshi ya bushe da dariyar
murna sannan ya dubeta yace
hakika duk abinda kika fada gaskiyane barima ki
gani
sarki shamsal ya mike tsaye ya shiga cikin
turakarsa ya bude wata katuwar akwatu wacce
rabonsa da budeta shekara guda kenan tun da
nadawo daga gasar jarumtaka wacce akayi
abirnin rum
yana bude akwatin saiga wani kambu amma na
hular sarautane
wanda akayishi da zallan farin lu'u lu'u.
wannan kambun jarumtakar ya ciwo a shekarar
data wuce sarki shamsal ya dauko wannan
kambu ya tawo dashi falo domin ya nunawa
sharifat.
adai dai wannan lokacine yarima zainur ya shigo
falon da gudu cikin murna yanakwallawa sarki
kira.
bisa tsautsayi kuwa sai sukayi karo da juna
wannan kambu ya subuce daga hannunsa yafadi
kasa.
take kambun ya tsage kuma ya rabe gida biyu.
al'amarin daya yi saurin fusata sarki kenan
baisan sanda yasa hannu zai zabgawa yarima
zainur mariba amma sai ya kasa.
koda ganin haka
sai hawaye ya zubowa zainur ya durkusa bisa
gwiwoyinsa agaban sarki yana neman afuwarsa
yana cewa
abbana kayi mini gafara.
tabbas wannan kambu yanada matukar daraja a
wajenka domin tunda kuruciyata kawo izuwa
girmana
baka taba yi mini fada ba bare kayi yunkurin
zagina amma yau har kayi yunkurin dukana.
idan har ka yafe mini to ka bani dama na kai
wannan kambu inda za'a gyara shi da kaina.
koda yarima zainur yazonan azancensa sai jikin
sarki shamsal yayi sanyi don haka sai yakama
kafadun yarima zainur ya tasheshi tsaye cikin
murmushi yace........
.mukasance daku gobe idan Allah ya kaimu
TARKON MUTUWA
Abdulaziz Sani madakin Gini
Typing:- prince auwal auzab
Post:- AA Misau
Littafi na daya 1
Part 1B
.
Shikenan dana na yafe maka amma ka sani cewa
duk fadin kasarnan babu wanda zai iya gyara
wannan kambu ya dawo inda yake face makeri
satyan.
ka nemi zamhas mai kula da makaman yaki ka
bashi wannan kambun yaje ya kai masa.
zainur yace
A'a ai hannun daya bata wannan kambu shi zai
aishi gyara don haka sai dai na nemi zamhas ya
rakani gidan makeri satyan saboda ban taba
zuwa ba.
dajin haka sai sarki shamsal yayi murmushi yace
amma kayi ladabi ga tsoho satyan kada kayi wani
abu mara kyau agareshi domin makusancine ga
mahaifina kuma amintaccensa shiyasa nima nake
daraja shi.
zainur yayi murmushi yace
lallai zan zamo mai kyauta tawa a gareshi.
nan take yarima zamnur ya juya ya fice daga
cikin falon rike da kambun jarumta tsagagge.
zainur bai zame ko'ina ba sai gidan s
zamhas
yana zuwa ya nuna masa matsalar da aka samu.
kuma ya bukaci ya rakashi gidan makeri satyan.
babu yadda zanhas baiyiba akan yarima zainur ya
hakura da zuwa shi ya bashi yakai ya gyaro
amma sai yaki
ya nace saidai suje tare.
nantake aka kawowa yarima zainur da zamhas
dawakai suka hau sannan dakaru guda ashirin
suka take musu baya suka fice daga ciikin gidab
sarautar.
daga gudan sarautar zuwa gidan makeri satyan
tafiyace ta sa'a guda don haka sai da yarina
zainur suka iso gidan inda suka iske makeri
satyan a zaune akofar makerarsa yana hutawa
yaransa nata faman aiki.
koda satyan ya hango zanhas tare da yarima da
kuma dakarun sarki sun dufafo kofar gidansa sai
hankalinsa ya dugunzuma ainun,
tsoro ya baibayeshi,jikinsa ya kama kyarma
nantake abubuwa biyu suka fado masa arai
abu na farko da yayi zargi shine duk yadda akayi
anyi wani kuskure babba akayan da aka kerawa
sarki shine ransa ya baci ya turo akamashi
abu na biyu kuma dayazo masa arai shine anya
kuwa ba bokayene suka gayawa sarki cewa
hatyan ne yaron da zai karbe karagar mulkinsa
cikin matukar karfin hali satyan ya mike tsaye
yana dogara sandarsa da kyar ya taryesu yana
marhaban
cikin girmamawa yarima zainur ya sauko daga
kan dokinsa ya rissina akaron farko a rayuwarsa
yagaida satyan.
bakomaine yasa yagaida satyan ba sai saboda
dalilai guda biyu.
dalili na farko shine yaji mahaifinsa ya fadi
darajarsa awajensa
abu na biyu shine kuma shine yana da son yaga
ya gyara masa wannan kambu jarumta yayi kyau
sosai tamkar bai taba tsagewa ba
yadda dan sarki ya gani zaiyi matukar farin ciki.
batare da bata lokaciba yarima zainur ya dauko
wannan kambu ya yi masa bayanin abida ke tafe
dasu.
koda jin haka sai farinciki ya kama tsoho satyan
domin ya fahimci cewar duk abubuwan da yake
zargi basu bane.
satyan ya karba ya duba shi dakyau sannan yayi
murmushi yace
ai acikin rabin sa'a kachal za'a gama gyara
wannan kambu kamar yadda yake da babu wnda
zai iya gane cewa ya taba karyewa.
kodajin haka sai yarima zainur ya kamu da
frinciki
nantake satyan ya jasu izuwa makerarsa
yasavaka hura wuta
inda sukuma suka koma gefe daya suka zauna
akan kujeru suka zuba ido suga yadda za'a gyara
wannan kmbu cikin rabin sa'a.
kafin cikar rabin sa'a tsoho satyan ya gama
gyara wanan kambu
sai gashi kambun ya koma daidai yadda
yakevkuma ya kara kyau sai sheki da walwali
yake.
nan dai...


Read / Download TARKON MUTUWA BOOK 1 TO 9

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album