Join Our WhatsApp Group

RUHIN JARUMTAKA Mujalladi na ɗaya 1 Complete Hausa Novel Document by RUHIN JARUMTAKA Mujalladi na ɗaya 1


RUHIN JARUMTAKA Mujalladi na ɗaya 1

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 163233



RUHIN JARUMTAKA Mujalladi na ɗaya 1

Reading Time: 13 Hours

Added On: 21, Feb 2024

Author: Umar Muhammad Sangaru ,

Ebook Compiler : Shuraihu usman

Author Group : Unknown group

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Adventure novels

File Size: 893.88 kb

File Type: txt

Views: 614+

Download: 1031+

Last download: 5 hours ago

Description/Story: RUHIN JARUMTAKA!
*
Babi na 1: *Aymanul Faris*
*
Wannan littafin sadaukarwa ne ga ZAHRA A. ADAMU ba zan manta dake ba.
***
Shimfiɗa: Barka da wannan lokaci jama'a, mun dawo bakin aiki. Allah yasa yadda muka fara rubuta littafin nan, mu gama shi lafiya. Fatan zaku bamu haɗin kai, ta hanƴar yin sharhi, likes kai har ma sharing.
***
Marubucin littafi: ✍️Umar Sangaru✍️
****
*Ƙauyen Gazwar na ɗaya daga cikin kauyukan dake cikin jahar Mauzil ta birnin Damashkar. Gaba ɗaya mutanen dake cikin wannan ƙauye 'yan wata ƙabila ce da ake kira banu Kuyuru. Allah ya horewa kabilar Babu Kuyuru gawurtattun sadaukai majiya karfi, da kuma zaratan jarumai masu dakakkiyar zuciya, baiwar iya yaki da sarrafa takubba. Adadin mutanen wannan ƙabila ba zai wuce dubu uku ba, kuma Allah yayi su masu tsananin kyawu ne mazansu da matansu.
Ƙauyen Gazwar na bisa wani ɗan karamin tsibiri ne wanda teku da manyan duwatsu suka kewaye, basu da wata sana'a da ta wuce noma da kiwo saboda albarkar ƙasar da suke da. Kuma wani iko na Allah a shekara suna iya noma abinda mutanen birnin Damashkar zasu ci gaba dayansu har tsahon wata shekarar, bisa wannan dalili ne ƙabilar Banu Kuyuru suke samun kudin shiga kwarai da gaske. Shugaban kabilar ya kasance wani sadaukin mutum mai tsananin adalci da ake kira Hasanul Jalwar bn Kusuful Jalwar.
Shugaba Hasanul Jalwar ya kasance sadaukin sadaukai kuma jarumin jarumai, don kaf cikin kabilar Banu Kuyuru babu wani sadauki mai karfin damtse kamar sa. Haka kuma ya kasance adali mai son al'ummarsa suma kuma suna tsananin kaunarsa saboda yadda yake kishinsu da son ci gabansu. Hasanul Jalwar yana da matar aure guda daya jal, wata kyakkyawar mace wacce ake kira da suna Hajriya. Sai da suka yi aure da shekaru bakwai sannan Allah ya albarkace su da samun haihuwa, suka haifo wani kyakkyawan jariri wanda suka kira shi da suna, AYMANUL FARISI.
Aymanul Faris kyakkyawan saurayi ne ɗan kimanin shekaru goma sha tara. Yana da murɗaɗɗen jiki da tarin ƙwanji. Fatar jikinsa fara ce tas, irin farin da ba kowanne farin mutum keda kalarsa ba, fari mai bayar da haske. Gashin kansa baƙi ne wuluk, kai kace rina shi akayi. Idanuwansa ma farare ne tamkar farar madara, da wani ɗigon baƙi tamkar an ɗiga tawada a cikinsu. Tun Aymanul Faris yana ɗan shekara bakwai shugaba Hasanul Jalwar ya ke bashi horon yaki, tun yana kuka saboda tsananin wahalar da yake sha, har ya saba. Lokacin da ya kai shekara goma sha tara sai ya zamo ɗaya daga cikin manyan zaratan dakarun wannan ƙabila, saboda tsananin jarumtakarsa da juriyarsa. Sau uku Aymanul Faris yana yin gagarumar jarumtaka wacce take girgiza dukkan wani mahaluƙin da ke zaune a ƙauyen Gazwar.
A karon farko da ya fara nuna jarumtakarsa shine, lokacin da waɗansu dakarun sumame suka kawo mamayar bazato izuwa tsibirin Gazwar bisa jiragen ruwa. Da sassafe ne kafin rana ta fito, kafin kowa ya tashi daga bacci kawai sai aka jiwo kururuwar mazaje daga can bayan gari, nan fa kowa ya farka a firgice aka fara iface-iface da guje-guje saboda tsananin razana. Jarumai suka fara ɗaura ɗamarar yaki suna tunkarar bayan gari inda suke jiwo wannar kururuwa, mata da kananun yara kuma suka fara kulle ƙofofin gidaje suna buya. Saboda wannan shine karo na farko da aka taɓa kawowa ƙauyen Gazwar mamayar bazato.
Aymanul Faris na kwance a cikin ɗakinsa bisa gado yana ta sharar bacci kawai sai yaji iface-ifacen jama'a ya soma cika garin, cikin hanzari ya farka a firgice sannan ya sauƙo daga kan gado, ya zaro takobinsa dake jikin bango, ya ruga da gudu ya nufi kofar gida. In banda takalminsa da dogon wandon dake jikinsa babu komai a jikinsa.
Tabbas Aymanul Faris ya kasance jarumi mai murɗaɗɗen jiki da tarin kwanji, gashi dai yaro ne dan shekara goma sha tara, amma jikinsa ya mummurɗe tamkar wani tsohon sadauki.
Lokacin da Aymanul Faris da sauran mayaƙan ƙabilar banu Kuyuru suka iso gaɓar teku sai suka hango wadansu girɗa-girɗan sadaukai tsaitsaye a cikin manƴa-manƴan jiragen ruwa, dauke da muggan makaman yaki suna ta ihu da kururuwa tamkar zasu ci babu. Kallo daya mutum zai yiwa sadaukan ya razana saboda tsananin girmansu, faɗinsu da kuma kaurinsu. Idan kuwa mutum yayi arba da waɗannan zabga-zabgan makaman dake hannunsu sai ya saki fitsari a wando saboda tsananin razana. Adadin 'yan fashin zai kai dubu biyar kuma gaba dayansu sanƴe suke da baƙaƙen tufafi, sun rufe fuskokinsu da wani irin ƙyalle mai launin kore, wani garjejen ƙaton mutum ne mai ƙirar mutanen farko tsaye a gabansu kai da gani kasan shine shugabansu.
Koda waɗannan 'yan fashi suka ga dakarun su Aymanul Faris 'yan tsiraru sai suka fara bushewa da dariyar mugunta, domin sun tabbatar da cewa sai sun sami nasara akan su. Ba tare da ɓata lokaci ba aka tuko waɗannan jiragen ruwa na ƴan fashin suka zo bakin gaba, 'yan fashi suka sassauka suka yi jeru laya-layi suna masu jiran umarni.
Garjejen mutumin nan ya ratso ta tsakiyarsu sannan yazo ya tsaya a gabansu, ya kurawa Aymanul Faris idanu tamkar mai yin nazarin wani abu. Daga bisani kuma ya kyalkyale da dariya ya dubi Aymanul Faris ya ce, "Tabbas ku kanku kun san cewa sai munyi nasara akanku, mene ne dalilin da yasa zaku wahalar da kanku, ku fito domin gwabza yaki damu alhalin kun san cewa baza kuyi nasara ba?" Aymanul Faris ya daka masa tsawa ya ce, “Kai katon banza! Mene ne dalilinka na zuwa har kauyenmu kana son ka farmake mu, shin kai ɓarawo ne ko kuma dan fashin kan teku?” Katoton mutumin yayi shuru yana mai kurawa Aymanul Faris idanu.
Tsahon dan lokaci sannan ya bushe da wata mahaukaciyar dariya ya ce, “Tabbas ba zan yi mamaki ba, idan aka ce babu wanda ya sanni akan wannan tsibiri naku. Saboda nasan bakwa yawo, babu inda kuke zuwa kullum kuna kan wannan tsibiri naku. Suna na RASHBIR ɗan KAIRUFA, gogaggen ɗan fashin kan ruwa wanda ya gallabi gaba dayan tekun birnin Damashkar. Na jima ina fakon wannan ƙauye naku, kuma na jima ina tura 'yan leken asiri domin ganin ribar da kuke samu. Tabbas a yau sai na hallaka kowa dake wannan tsibiri sannan na kwashi komai dake kan wajen wanda ya shafi dukiya ko allura bazan bar muku ba.” Lokacin da dan fashi Rashbir yazo nan a zancensa, sai ran Aymanul Faris ya ɓaci ya sake daka masa tsawa a karo na biyu, ya ce, “Na rantse da girman iyayena, ko allura guda ɗaya baku isa ku ɗauka a wannan ƙauye namu ba, kuma na rantse da darajar iyayena ni kaɗai ɗinnan sai na tarwatsa wannan baƙar runduna taka ba tare da na nemi taimako daga ɗaya daga cikin dakaruna ba.” Yana gama faɗin haka ya juyo ya dubi mayaƙan ƙabilar banu Kuyuru dake tsaitsaye a bayansa, ya ce, "Bana buƙatar taimakon ɗaya daga cikinku, ku barni dasu ni kaɗai tabbas yau zan basu mamaki. Aymanul Faris na gama fadin haka ya ɗaga takobinsa sama ya falfala da gudu cikin 'yan fashin nan, sauran mayakansa suka tsaitsaya a inda suke cikin jimami da tsoro, saboda basu taɓa ganin jarumtakar Aymanul Faris a zahiri ba, amma da suka tuno cewa ƊAN GIWA, GIWA NE, sai hankalinsu ya kwanta don sun san jarumtakar Hasanul Jalwar. Kai hasalima a cikin zuri'ar su Hasanul Jalwar ba'a taɓa samun rago ba, a kullum sadaukai da jarumai ake haifowa.
Koda su sadauki Rashbir suka ga haka sai suka ce dawa aka hadamu? Nan fa aka ruguntsume da mugun azababben yaki, aka fara ragargazar mazaje. Duk inda Aymanul Faris ya kai sara sai dai kaga kawunan bil'adama ko kafadunsu yana tashi sama, jini yana tsartuwa. Ihu kuma ya cika kunnen duk wata halitta dake wannan waje. Ya wanzu a tsakiyarsu tamkar shaiɗani, yana kai SARA DA SUKA cikin baƙin zafin nama da bajinta. Sadauki Rashbir na zaune bisa dokinsa yana ganin yadda wannan gumurzu ke wakana cikin nishadi tamkar ba dakarunsa ake kashewa ba, sai murmushi yake.
A duk lokacin da wadannan dakaru suka lullube Aymanul Faris sai ya yi kururuwa ya tarwatsa su da karfin saran takobinsa, kai sai da ta kai cewa Aymanul Faris ya rine da jinin wadannan dakaru. Koda aka shafe sa'a ɗaya da rabi ana wannan gumurzu sai dakarun sadauki Rashbir suka fara gajiya suna sarewa, shi kuma Aymanul Faris tamkar ma a lokacin ya fara wannan gumurzu. Nan fa ya ci gaba kashe dakarun sadauki Rashbir, kisa mai muni domin mutum ɗaya sai yayi masa aƙalla sara biyar ko bakwai. Kan kace me wannan tuni ya kashe kaso biyu cikin ukun dakarun sadauki Rashbir, ba tare anyi masa rauni ko guda ɗaya ba. Nan fa waɗanda suka rage ɗin suka rude suka fara guduwa suna faɗawa cikin teku, sadauki Rashbir ya daka musu tsawa, ya ce, “Su tsaya, komai rintsi komai wuya su tabbatar da cewa sun sare kan Aymanul Faris.” Koda Aymanul Faris yaji umarnin da Rashbir ya basu sai ya sake falfalawa da gudu ya shiga tsakiyar dakarun nan, ya yi ta ragargazar su. Sai dai a wannan lokaci Aymanul Faris a matukar fusace yake, yaƙi yake da dukkanin karfinsa da juriyarsa. Nan fa ya zamewa wadannan dakaru guguwar bala'i yayi ta saransu da sukarsu aka rasa mutum daya jal, da zai sami nasarar koda lakutar jikinsa. Koda mayaƙansa suka ga irin barnar da yake yi sai suka cika da tsananin mamaki, basu taɓa tsammanin jarumtakarsa ta kai haka ba. Kafin kace me wannan tuni Aymanul Faris ya gama kashe 'yan fashin nan gaba ɗayansu ko ɗaya bai tsira ba. Wani abun mamaki shi ne har yanzu Rashbir na zaune bisa dokinsa bai ko motsa ba, kawai ya kurawa Aymanul Faris idanu. Koda yaga Aymanul Faris ya gama kashe dakarunsa sai ya sauƙo daga kan dokin, ya tsaya a daidai inda Aymanul Faris ke tsaye. Ya fiddo wani abu mai kama da madubin tsafi ya nuna Aymanul Faris da shi, wani farin haske ya fito daga cikin madubin tsafin ya haska Aymanul Faris sannan ya ɓace ɓat.
Ɗan fashi Rashbir ya bushe da dariya ya nuna Aymanul Faris da ɗan yatsansa guda ya ce, “Tabbas ka cika jarumi kuma ka burgeni, amma ba zan fafata da kai ba, domin kuwa na sami abinda ya kawo ni.” Yana gama faɗin haka ya juya falfala da azababben gudu yana mai kyalkyala dariya, ya shiga cikin ɗaya jiragen ruwan nan ya gudu. Nan take dukkanin dakarunsa ma da Aymanul Faris ya kashe suka bace bat! Tamkar basu taba wanzuwa a wajen ba.
Koda Aymanul Faris yaga faruwar wannan al'amari sai yaji gabansa ya faɗi, zuciyarsa ta buga da ƙarfi, ya tabbatar da cewa lallai wannan ɗan fashi turo shi akayi, domin yazo yaga tsananin jarumtakarsa. Aymanul Faris ya tambayi kansa to wane ne zai turo shi? Amsar da ya gagara baiwa kansa kenan. Har yunƙura da niyyar ya bi bayan sadauki Rashbir, yaga ai tuni ya ɓace a cikin duhun hazon dake bisa tekun. Kawai sai ya juya ya nufi hanyar da zata mayar da shi cikin ƙauyen Gazwar.
Abinda Aymanul Faris bai sani ba shine ko kadan ba fashi bane, ya kawo su Rashbir wannan tsibiri. Kawai wani uban gidansu ne ya turo su, domin suyi masa farautar wani jarumi da yake nema, wanda zai taimaka masa sosai a waɗansu gawurtattun sata da zaiyi.
***
Aymanul Faris yana komawa gida ya baiwa mahaifinsa labarin duk abinda ya faru, koda Hasanul Jalwar yaji wannan labari sai ya cika da tsananin mamaki, domin kuwa a duk faɗin kauyen Gazwar shi kaɗai ne yasan waye Rashbir. Amma sai ya dubi Aymanul Faris ya ce, kada ya fadawa wani wannan batu.
Wata rana da yammaci jama'a na gona suna ta aiki, kwatsam! Ba zato ba tsammani sai aka ga ruwan teku ya soma hautsinewa, wani irin huci ya soma fesowa izuwa cikin Ƙauyen, ruwa ya soma fantsama da feshi. Kasancewar ƙauyen Gazwar a bakin teku yake basu da zafi, kullum sanƴin hunturu ne keta kaɗawa. Fiye da shekaru ɗari babu wata muguwar halittar da suka taɓa gani ta fito daga cikin tekun ta shigo ƙauyen Gazwar, saboda tsarin da kakan Hasanul Jalwar yayi.
Wata irin zabgegiyar macijiya ta faso wannan ruwa ta afka cikin gari, tsahonta ya kai kamu sittin kuma tana da wani katon baki wanda take hadiye giwa dashi komai girmanta. Nan fa wannan macijiya ta fara lankwame jama'a wadanda ke gudun ceton ransu, kan kace me, ta lamushe mutum talatin. Nan fa ta tashi hankalin wannan ƙauye, jama'a suka tarwatse kowa yana ta kansa. Kawai sai gani aka yi Aymanul Faris ya tunkari inda wannan macijiya take da gudu tamkar zai tashi sama, babu komai a hannunsa face wani zabgegen gatari mai tsananin kaifi, a wannan karon ma ko riga babu a jikinsa.
Lokacin da yayi arba da wannan ƙatuwar macijiya sai kirjinsa ya buga da ƙarfi, don tun da yake bai taba yin arba da wata halitta mai tsananin girma da muni kamar wannan macijiya ba. Tana da dogin hakora masu tsananin tsini, a yayin da wani jan dafi keta zirya a tsakaninsu, idanuwanta jajawur ne tamkar wuta ke ruri a cikinsu. Komai dakewar zuciyar mutum indai yayi arba da wannan macijiya sai ya razana, musamman ma idan mutum yaga doguwar jelarta wacce akalla zata kai gammo nadi arba'in.
Aymanul Faris na tsaye kawai yaga wannan macijiya ta kawo masa duka da jelarta, nan fa ya daka wani wawan tsalle izuwa gefe guda. Jelar ta sami wani katon dutse dake bakin teku, take dutsen ya tarwatse tamkar an nika shi. Koda ganin haka sai hankalin Aymanul Faris ya dugunzuma domin kuwa ya tabbatar cewa lallai yau ya gamu da gamonsa. Kawai sai shima ya daga gatarinsa sama ya falfala da gudu suka ruguntsume da yaki da wannan macijiya, ya zamana cewa yana kai mata sara da duka ita kuma tana zane shi da jelarta kuma tana kawo masa hadiya da bakinta. Sai da suka shafe rabin sa'a a haka ba tare da sun tabuka komai ba, amma Aymanul Faris ya soma gajiya saboda tsananin zafin namar wannan macijiya....


Read / Download RUHIN JARUMTAKA Mujalladi na ɗaya 1

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album