Join Our WhatsApp Group

MAZAN JIYA Book 2 Mujalladi na daya 1 Complete Hausa Novel Document by MAZAN JIYA Book 2 Mujalladi na daya 1


MAZAN JIYA Book 2 Mujalladi na daya 1

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 23246



MAZAN JIYA Book 2 Mujalladi na daya 1

Reading Time: 1 Hours

Added On: 07, Dec 2023

Author: Abdulaziz Sani Madakin Gini ,

Ebook Compiler : Shuraihu Usman

Author Group : Unknown group

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Adventure novels

File Size: 123.34 kb

File Type: txt

Views: 1366+

Download: 446+

Last download: 22 hours ago

Description/Story: MAZAN JIYA
BOOK 2 - Abdulaziz Sani Madakin Gini
Typing by Shuraih Usman 99%
Post and Published at Taskarnovels - 2023

KASHE GARI da sassafe rundunar su Sarki Dujalu suka mike suka ci gaba da tafiya, bayan kowa ya kimtsa cikinsa. Tun da aka fara tafiyar sai sarki Dujalu ya lura da cewa 'yar uwarsa Hursiya bata da sukuni.

A duk sa'adda ya dubeta sai ya ga alamomin damuwa cike a fuskarta kawai sai ya yi murmushi domin shi kadai ne ya san abin da ke damunta.

Abin da ya bashi mamaki shi ne, mene ne ya hanata ta baiyana masa abin da ke damunta, ba wani abu bane ya ke damun Hursiya ba face tsananin son jin ci gaban labarin sadauki Hantaru.

Haka dai aka ci gaba da wannan tafiya har tsawon kwana uku, Duk sa'adda aka yada zango sai Hursiyya ta lallaba sarki Dujalu domin ya ci gaba da bata labarin.

Da zarar ya fuskanci abin da take so, sai ya kama gyan-gyadin karya, bisa dole Hursiya ta hakura itama ta kwanta har barci ya saceta bata sani ba.

Da yammacin kwana na uku ne wannan runduna ta su sarki Dujalu ta iso wani katon daji mai ban tsoro wanda ake yiwa lakabi da Sauratul Auzur.

Duk da tsananin yawan wannan runduna ta aljanu da mutane da kuma gagarumin shirinsu sai da kowa yaji tsoro ya shigeshi, bisa tsintar kansu a cikin dajin Sauratul Auzur, sarki Dujalu ne kadai bai girgiza ba.

Shi dai dajin Sauratul Auzur babu komai a cikinsa face manya-manyan bishiyoyi da manyan duwatsu masu ban mamaki.

Babu inda mutum zai je a duniya ya ga irinsu, sannan siffofin bishiyoyin da duwatsun ma ababan tsoro ne. Sau tari sai mutum ya ga suna motsi da rangaji tamkar za su haifar da girgizar kasa a dajin gaba daya.

Daga dajin Sauratul Auzur zuwa tekun bahar Sufiya tafiya ce ta wata hudu kacal, kuma a cikin dajin Sauratul Auzur mutum zai yi ta tafiya ta tsawon wata hudu.

Da isowar su sarki Dujalu farkon dajin Sauratul Auzur, sai sarki Dujalu ya bada umarnin a tsaya.

Nan take kuwa na kan dawakai suka dakatar da dawakansu, aljanun da ke tafiya a sararin sama kuwa suka saki fuka-fukansu suka sauko kasa.

Nan fa kowa yai ladaf aka yi tsit tamkar babu mai numfashi a wajen. Sarki Dujalu yai gyaran murya sannan ya ce,

"Ya ku jama'ata kuyi sani cewa mun iso dajin Sauratul Auzur. Daga nan zuwa tekun bahar Sufiya inda takobin Saiful Lujara take tafiyar wata hudu ce kacal. Ku yi sani cewa masifu da bala'in da ke cikin wannan daji sun wuce tunani don baka sai kowa ya gyara damararsa, domin komai zai iya faruwa.
Ko shakka bana yi da yawa daga cikinmu za su iya rasa rayuwarsu acikin wannan daji. Wadanda duk suka kai izuwa karshen wannan daji araye a cikin koshin lafiya sun cika mazajan kwarai ababan yabo da jinjina." ai Koda gama fadin haka sai sarki Dujalu ya dubi Hursiyq ya ce,

"Komai wuya da tsanani ki tabbatar da cewa a ko yaushe kina tare da ni. Hursiya ta gyada kai tana mai nuna nun cewa lallai za ta kiyaye. A Nan take sarki Dujalu ya zunguri cikin aljanin da ke dauke da su shi da Hursiy, suka fara wucewa kan gaba, sannan kowa ya bi bayansu a cikin yanayin tsoro da dari-dari. Sai da aka shafe sa'a guda ana tafiya a cikin dajin ba a hadu da komai ba kuma ba a ga wani mugun abu ba.

Al'amarin da ya jefa kowa cikin tsananin mamaki ke nan domin in banda kukan kananan tantsaye da kwari babu wani sauti da ke ratsa kunnuwa. Kwatsam! Ba zato ba tsammani sai kawai aka hango wata jibgegiyar halitta a can gaba ta cika hanya tun daga sama har kasa tamkar za ta tokare da hadari.

Babu ta inda za a bi a wuce face ta cikin halittar. Ita dai wannan halitta tana kama da bil'adama, aljan da kuma dodo, Kuma gaba dayan jikinna ta ne yake da siffofi ukun. Ma'ana fuskarta da gangar jikinta da hannayenta.

Koda aka yi arba da wannan halitta sai gaba dayan dakarun sarki dujalu suka firgice suka tsaya cak A waje dqya Aljanin da ke dauke da dauke da sarki Dujalu wanda ake kira Rauzuf sai ya fara kaɗa fuka-fukansa a hankali alamar shima ya tsorata amma bai fasa tunkarar haittar ba saboda gudun fishin sarki Dujalu, ammna gaba dayan jiinsa karkarwa yake tamkar wanda ya kamu da Zazza6i mai zafi."

Koda sari Dujalu ya fahimci halin da aljani Rauzuf ke cilki sai ya daka masa tsawa ya ce, "Ya kai Rauzuf a kul ka kuskura ka ja da baya ko kuma ka tsaya ga ci gaba da tafiya idan kuwa ka tsaya ni da kaina zan zare maka ruhin numfashi". Koda jin wannan batu sai aljani Rauzuf ya kara karfin tafiyarsa ya tunkari wannan katuwar halitta kai tsaye.

Sai da suka iso daf da halittar ya ZAmana cewa tazarar da ke tsakaninsu ba ta wuce kamu uku ba sai haittar ta wangame katon bakinta mai kama da kofar gari ya buso wata irin iska mai karfin gaske tamkAr guguwa. Take aljani Rauzuf ya fado kasa tim! Sarki Dujalu da Hursiya suka tuntsuro kasa daga kansa suka baje a kas. Hatta sauran dakarun da ke bayansu sai da iskar ta tarwatsasu, na sama suka rikito kasa na kasa kuwa suka baje.

Daga can sai katuwar halittar ta bushe da mahauknciyar dariya mai tsananin ban tsoro wacce ta sa kowa da kowa ya sume face sarki Dujalu Gaba dayan dajin ya hautsine ya kama rangaji. wuta ta kama bishiyoyi. Babu abun da ya rage a tsaye bisa duga-digansa face sarki Dujalu.

A wannan lokaci ne shirgegiyar halittar ta bude idanuwanta kwala-kwala masu kama da girman rana ta dubi Dujalu cikin tsananin mamaki. Fiye da shekaru dubu da doriya wannar halitta ke tsare wannan hanya, duk abin da ya zo gabantan in dai tayi wannan dariya sai abin ya fadi Kasa sumamme amma yau ga wani takadarin bil'adama guda daya a tsaye cak a gabanta ko girgiza bai yi ba.

Cikin wata irin kakkausar murya halittar ta dubi aljani Dujalu ta daka masa tsawa Duk da cewa sarki Dujalu gwarzon namiji ne wanda bai san tsoro ba sai da hantar cikinsa ta kada shi kuwa aljani RauZuf take ya kara sumewa a karo na biyu.

Halittar ta dubi Dujalu cilkin nutsuwa ta ce, ya kai wannan hatsabibin bil'adama wane ne kal kuma wane tsautsayi ne ya shigo da ku cikin Wannan daji na Sauratul Auzur alhali kun sani cewa ba a taba ratsowa ta cikinsa ba?" Sa'adda sarki Dujalu yaji wannan tambaya sai ya bushe da dariya sannan ya murtuke fuskarsa kamar wanda aka aikowa da sakon mnutuwa ya ce, "Ni ne sarki Dujalu mai mulkar kasar Hawarul din.

Ya kai wannan babbar halitta ka sani cewWa na yarda da kaina domin ni ne DODON MAZA a wannan ZAmani, magajin MAZAN JIYA. Duk bala'in da ke cikin wanann daji na san da shi kuma sai na ketare ta cikinsa domin na isa tekun bahar Sufiya don na dauko takobin Saiful Lujara."

Koda sarki Dujalu yazo nan a zancensa sai katuwar halittar ta sake bushewa da dariya a karo na biyu sannan ta ce, "Sama da mutum dubu dari ire-irenku wato masu irin wannan buri naka sun hallaka bisa wannan tafarki wadanda duk abin da kake takama da shi sun fika. Babu wanda ya taba haye bala'in bare har ya shafe sauran tafiyar da ke cikin dannan daji na Sauratul Auzur ya ketare sauran masifun da ke cikinsa ya isa bakin tekun Bahar Sufiya.

Ina mai shawartarka da ka juya da baya kai da jama'arka domin kada ka janyo asarar miliyoyin rayuka a banza." Sariki Dujalu ya yi murmushi mai nuna yarda da kai, sannan ya ce, "Ko mutum daya daga cikin jama'ata ba zai rasa rayuwarsa ba. Ni kadai zan samar mana da hanya mu wuce gaba saboda haka ina mai shawartarka da ka kauce daga kan hanyarmu idan har kana son ka tsira da rayuwarka don ban ga abin da ya isa ya hanani ratsawa ta cikin wannan daji ba." Kafin sarki Dujalu ya gama rufe bakinsa tuni katuwar halittar ta mike tsaye. Alamarin da ya sa gaba daya dajin ya yi lumshi tamkar rana ta faɗi ashe da can a zAune take ba a tsaye ba. A sannan ne sarki Dujalu ya daga kansa sama ya dubi halittar Nan take halittar ta sake buso iska ga sarki Dujalu,


Wannan karon sai iskar ta dagashi sama ta fara gwarashi a jikin manyan bishiyoyin dake dajin. A dai-dai wannan lokacin ne Hursiya da sauran Dakarun gaba daya suka farfado daga dogon suman da suka yi suka ga abin da ke faruwa.

Koda suka ga sarki Dujalu a sama ana gwarashi a jikin bishiyoyi har ya fara galabaita sai bankalinsu ya dugunzuma ainun suka karaya lta kuwa Hursiya sai ta fashe da kuka domin ta tabbatar da cewa shi ke nan ta rasa dan uwanta. Gaba dayan dakarun dai sai suka cika da mamaki saboda a yadda suka san sadaukantakar sarkinsu da karfin sihirinsa amma sai gashi duk sun zamo banza ya kasa ceton kansa ma bare suma ya cecesu.


Nan fa wasu daga cilkinsu suka fara tunanin su ja da baya don kada Wannan halitta ta gama da sarki dujalu sannan ta dawo kansu . Kafin su yanke hukunci ne wani abin mamaki ya faru, kawai sai gani suka yi shima sarki Dujalu ya yi nuni da hannunsa izuwa ga wannan iska mai karfi da take wujijigashi take wata irin iska ta fito daga cikin haAnnun nasa ta kama đaya iskar mai wahalar da shi suka kamna gumurzu, Nan fa kallo ya koma kan iskokin biyu suka rinka tsiri a sama suna fitar da wata irin tsawa da kugi mai razanarwa.


Wani lokacin idan iskokin suka yi sama sai ka ji sun fado kasa fat! Tamkar giwa ta fadi. Katuwar halittar da sarki Dujalu sai sulka zuba idanu kawai suna kallon gumurzun da iskokin ke yi. Nan fa dajin ya kara ruguntsumewa domin a duk sa'adda iskokin suka hada jiki sai ka ga wuta na feshi da tartsatsi. Al'amarin da ya sa gaba dayan dakarun suka dimauce ke nan suka kama guje-guje a cikin dajin suna neman ma6oya. Kafin a jima filin wajen ya dade babu kowa face sariki Dujalu sai aljaninsa Rauzuf da kuma Hursiya wadda jikinsu ke makyarkyata saboda tsananin tsoro, shi aljani Rauzuf ma bai san sa'adda ya fara sakin fitsari ba, amma bisa mamaki sai ya ga wannan feshin wuta da tartsatsin basa zuwa inda suke shi da Hursiya sai dai su zuba a gefensa.


A duk sa'adda iskokin biyu suka fađo kasa kuwa, sai gaba dayan dajin ya kama tambal tamkar jirgin ruwa akan kogi sa'adda ruwa ta kada. Haka dai aka ci gaba da wannan dauki ba dadi har tsawon sa'a guda.

Daga karshe ne iskokin biyu suka kankame juna suka kama da wuta sulka kone kurmus suka zama toka. Koda faruwar hakan sai aka fara kallon-kallo tsakanin sarki Dujalu da katuwar halittar a ya yin da ta sauko da dogon kanta kasa tamkar zal6e ya leko da wuyansa waje daga cikin tagar daki.

Koda sarki Dujalu ya yi arba da mummunar fuskar halitar sai yaji zuciyarsa ta buga da karfin gaske. Wannan shi ne karo ne farko da sarki Dujalu yaji tsoro ya shigeshi a rayuwarsa. Bisa dole Dujalu ya ja da baya taku uku, amma saboda yana da dakakkiyar zuciya sai ya ki gudu ya tsaya ya zare takobi, kuma ya gyara tsayuwa akan aljani Rauzuf.

Ya yin da babbar halittar ta ga abin da Dujalu ya yi sai ta bude hannayenta biyu ta dagasu sama kai kace Lagwayen tsaunikane ke yawo a samaniya sannan Sai ta wangame katon bakinta ta kwarara uban ihu wanda ya zamo sanadin sake ruguntsumewar dajın fiye da ko yaushe. Shi kansa Dujalu bai san sa'adda ya kara ja da baya ba. Ita kuwa Hursiya sai ta kankame Dujalu ta baya ta fashe da kuka.

Cikin kwarin zuciya Dujalu ya 6an6areta daga jikinsa ya zaunar da ita kasa bisa kan aljani Rauzuf sannan sai ya tashi sama kamar tsuntsu ya juyo ya dubi aljani Rauzuf ya ce, "Ku dan ja da baya kadan ku zuba ido ku ga abin da zai faru. Idan na sami nasarar hallaka wannan halitta sai mu ci gaba da tafiya idan kuma ta hallakani ku koma da baya ku nemi sauran abokan tafiya domin ku koma can birnin Hawarul din, gimbiya Hursiya ta gaji karagata".

Koda gama fadin haka sai sarki Dujahu ya yunkura da dukkan karfinsa ya tasarmma katuwar halittar ya kai ma ta wawan sara a hannunta na hagu." Koda takobin Dujalu ta sari hannun sai tartsatsin wuta ya tashi gami da wata irin kara tamkar karfe da karfe. Halittar ta yi girgiza tamkar susa aka yi ma ta. Dujalu yaja da baya kadan, koda ya dubi kaifin takobinsa sai ya ga ta dakushe. Al'amarin da ya matukar girgizZa hankalinsa kenan ya gamsu cewa lallai yau ya gamu da gamonsa.

Dujalu ya kurawa halittar idanu yana tunanin irin dabarar da ya kamata ya yi don ganin ya kawar da ita. Abu na farko dai shi ne, ya tabbatar da cewa in dai batun karfin damtse ne ba zai iya da ita ba, don ko ba a gwadaba linzami yafi karfin bakin kaZa. Haka kuma idan batun karfin Sihiri ne nan ma ya san babu nasara tun da an gwada an yi RAGAS. To wai shin mene ne zai kwaceshi a hannun wannan halitta? Ai babu mafita face sa'a, Kafin sarki Dujalu ya gama aiyana wannan furuci a bakinsa sai halittar ta yi masa wawan mangari da hannunta guda a fuska saboda karfin dukan sai da sarki Dujalu ya ga taurarin wahala a idanunsa numfashinsa ya sarke a lokacin da yi sama tamkar an janyeshi da kugiya Dujalu ya gwaru da bishiya har keyarsa ta tsage ya fado kasa a cilkin wani irin mugun hali mai kama da rabin suma.

Koda jibgegiyar halittar ta ga ta sami wannan nasara sai ta bushe da mahaukaciyar dariya. Koda gama fadin haka sai Hursiya ta kwarara uban ihu ta fashe da kuka, domin zuciyarta ta gama karaya ta sallama cewa dan uwanta ya gama halaka, Shi kuwa aljani Rauzuf sai ya yunkura da nufin ya bude fuka-fukanssa ya gudu.

Ai kuwa shima sai ji ya yi an fyadeshi ya baje a kas, sai ga jini na zuba ta cikin hancinsa da bakinsa, ko motsi bai yi ba tamkar gawa. A dai-dai wannan lokaci ne katuwar halittar ta fara tako kafafunta ta nufo inda sarki Dujalu ke kwance da kafuta, da nufin ta mitsttsikeshi...


Read / Download MAZAN JIYA Book 2 Mujalladi na daya 1

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album