Join Our WhatsApp Group

MATSATSUBI BOOK 3 Complete Hausa Novel Document by MATSATSUBI BOOK 3


MATSATSUBI BOOK 3

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 25997MATSATSUBI BOOK 3

Reading Time: 2 Hours

Added On: 19, Feb 2024

Author: Abdulaziz Sani Madakin Gini ,

Ebook Compiler : Shuraihu usman, Habibullah Muhammad Kabara, Najibullah Muhammad

Author Group : Unknown group

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Adventure novels

File Size: 153.06 kb

File Type: txt

Views: 936+

Download: 599+

Last download: 1 day ago

Description/Story: DOCUMENT COMPILED BY SHURAIHU USMAN
TYPING HABIBULLAH MUHAMMAD KABARA
POSTED BY NAJIBULLAH MUHAMMAD
**MATSATSUBI**💥💥
LITTAFI NA UKU✍️✍️
PART A ❤️❤️
NA: ABDUL'AZIZ SANI MADAKIN GINI 🤴
POSTING: NAJIBULLAH MUHAMMAD ☝️☝️
TYPING: Habibullah Muhd Kabara ✍️✍️
Tom mun dawo bakin aiki...
Ina mana barka da JUMA'A fatan Allah ya maimaita mana❤️✍️🙏
Marubucin littafin ya ci gaba da cewa....
Lokacinda su jafar suka tsinci kansu a cikin wata
sabuwar duniya a samaniya sai suka kidime
suka cika da tsananin mamaki
domin kuwa komai akan iska yake yawo hatta
gidaje d dabbobin garin kuwa ba atsaye suke ba
awaje guda
su kuwa mutanen garin sun kasance masu wata
irin halitta tamkar dodanni kuma jikinsu kwari
gareshi kamar dutse
kaurin jikinsu da tsayinsu duk iri dayane babu
wanda yafi wani
gaba daya jikinsu lullube yak da gashi
kowannensu na da kaho guda biyu akansa
sunada manyan kunnuwa kamar n jaki kuma
idanuwansu da bakunansu irin na mutane ne
sosai amma hannunsu 'yan kanana ne kamar
dosana su akayi suna tafiya ne acikin iska
kamar ana cilla kibiya duk da cewa basu da
fukafukai
su kuwa su jafar idan suka daga kafafunsu da
nufin suyi tafiya sai suga ana juyasu acikin iska
kamar katantanwa bisa dole suka tsaya waje
guda suka cure su biyar din
gaba daya mutanen garin babu wanda ya kalle
su bare yace
ci kanku, kuma duk wanda sukayi kokarin yiwa
magana baya sauraronsu
haka dai sukaci gaba da tsayuwa awaje daya her
tsawon wani lokaci
kwatsam ba zato ba tsammani sai sukaga
gungun mayaka sanye da kayan karafa
kimanin su dari sun taho garesu cikin
matsiyacin gudu acikin iska
wadannan mayaka suma irin mutanen garin ne
kowannensu na dauke da wani irin lafcecen
makami irin wanda su jafar basu taba ganiba
da zuwan mayakan sai suka yiwa su jafar
kawanya ya zamana babu 'yar kafa wadda zasu
iyabi su wuce
daya daga cikin mayakan ya fiddo wani abu
acikin rigar karfensu mai kama da madubin
karfe ya shafe shi
saiga hoton fuskar sarkinsu ta bayyana akai
sarkin ya kasance mai rafkeken kai wanda yafi
na kowa girma agarin kuma shi kaho dayane
akansa hakama idon sa da kunnensa duk dai
dai ne
wanda ke rike da madubin ya dubi sarki yace
ya shugabana gamu nan tare da bakin me
kakeso ayi musu?
kodajin wannan tambayar say sarkin ya
kyalkyale da dariya cikin wata Irin murya mai
kama da karar karafa yace
yauwa kuyi maza ku kawosu fadata hakika burin
mu na daf da cika domin abin da muka dade
muna nemane bamu samuba to yau sune
sukazo suka kawo kansu
yana gama fadin hakan ne dakarun suka cafke
su jafar sukayi sama dasu suka cilla aguje cikin
iska nanfa sukayi ta gifta garuruwa da birane da
kauyuka iri iri har suka iso wata babbar alkarya
wadda tun akofar birnin sukaga an rubuta
BARKA DA ZUWA BIRNIN HARJULUL MULK
birnin harjulul mulk ya banbanta da sauran
biranen dake wannan duniya, domin gidajensa
da komai nasa akan turba suke waje guda,
ma'ana babu wani abu dake yawo asama cikin
iska,
koda aka shigar dasu cikin birnin sai suka ga an
sauko kasa ancigaba da tafiya akasa bisa turba,
abindaya basu mamaki shine gaba daya biranen
birnin anyi sune da zallan karfen zinare
kuma an kawatasu da kayan alatu fiye da
tunanin kwakwalwa
haka kuma mutanen garin da mutane masu irin
halittar su jafar wato b dodanni bane dukkansu
al'amarin daya jefa su jafar cikin matukar
mamaki kenan
koda ganin su jafar ahannun dakarun tsaro sai
jama'ar suka kura musu idanu suna mamakin
ganin su
babu wanda yace dasu kala har akayi tafiyar
kusan rabin sa'a sannan aka iso wani babban
gida mai tsananin fadi da tsawo
wanda idan mutum ya daga kansa bai isa ya
hango rufinsa ba
har yanzu dakarun suna rukunkume dasu jafar
ko kyakkyawaan motsi basa iyayi
da kofar gidan sarki sai wata kofà mai siffar
kwai ta bude kanta ,kai tsaye dakarun suka
shige dasu jafar ciki sannan kofar ta rufe kanta
da shigarsu sai suka ga wasu ma'aikata
azazzaune kan kujeru da tebura
akan kowanne tebur wani farin allon tsafine
gaba dayan ma'aikatan kowa na rike da wata
siririyar sandar tsafi
ajikin kowanne allon tsafi ana ganin abinda yake
faruwa awata duniyar daban
akalla za'a iya samun allon tsafi guda miliyan
dubu daya awannan tamgamemiyar fada
hakama adadin mutanen dake sarrafa madubin
yake
daga can karshen fadar kuwa bisa wani gini mai
tudu sukayi arba da wani katon allon tsafi
wanda yafi gaba daya sauran girma,
zaune agaban allon sarki arbir ne zaune
yakurawa su jafar idanu yana murmushi
abindayà daurewa su jafar kai kenan cikin
tsananin mamaki jafar ya dubesu alokacinda
dakarun nan suka watsar dasu agabansa
tamkar an watsar da tsummokara jafar yace
yakai sarki azbir ya akai kazo nan alhalin mun
rabu dakai tun acan duniyarka abakin rijiyar nan
data zukemu
sarki azbir ya mike tsaye yazo gabansu jafar
wadanda ke zaune dirshan akasa ya tattashesu
tsaye
sannan ya rike hannun jafar yace
ka kwantar da hankalinka yaka jafar ku sani
cewa yau kun fado hannun sarki azmul gallar
mai mulkin birnin harjulul mulk
birnin da shine mafi girma da daukaka acikin
wannan nahiya ta duniyoyin sama
inason ka sani cewa sarki azmul gallar ya tsani
sauran duniyoyin dake can kasa
wato kamar irin duniyarku kuma bashi da wani
buri wanda yafi ya shafesu gaba daya daga
doron kasa
yayi binik ya gano cewa idan yana son ya
hallakar da duniyoyin dake doron kasa dolene ya
kera wani sundukin tsafi mai tsananin haske ya
aikashi izuwa can duniyoyin kasa
hasken wannan sundukine zai narkar da
wannan duniyoyin gaba daya
yanzu haka angama kera wannan sunduki
amma an kasa aikashi saboda so ake asamu
mutane irinku acikin wannan sundukin guda
uku ko sama da haka
sannan sundukin zai iya tafiya
haka kuma sundukin babu wanda zai iya sarrafa
sundukin face ni kadài
shiyasa sarki azmul gallar ya kamoni ya kawoni
nan
kuyi duba izuwa can kuga abin mamaki
cikin sauri jafar, jelisa, gulzum, da mazalish
suka juya suka dubi inda sarki azbir yayi musu
nuni
kawai sai. sukayi arba da ita
ba kowa bace face katuwar macijiyar nan mai
kawuna barkatai wadda ta had! yesu
cikin tsananin tsoro suka ja da baya gaba
dayansu
adaidai wannan lokacin ne macijiyar ta sauko da
kanta guda daya kasa ta wangame shi kamar
zata hadiye komai dake wajen
bisa mamaki sai suka ga sarki azmul gallar ya
fito ta cikin bakin macijiyar yana kyalkyla dariyar
mugunta yana fita daga bakin macijiyar ya dafa
kanta yace
jeki abinki uwar macizai na sallame ki
kamar walkiya macijiyar ta bace bat sarki azmul
gallar ya dubi su jafar daya bayan daya ya jinjina
kai sannan ya sake bushewa da dariya wacce
tayi dai dai da irin ta mutane ba dodanni ba
kamarsa
azmul gallar ya dubi su jafar yace
gaisheka takadirin yaro kaine wanda ya zamewa
boka shamharu alakakai
kuma kaine mai shirin zama alakakai agareni
amma bazan baka damar yin hakanba
ka sani cewa ahalin yanzu ka bankado sirrin
boka shamharu domin kaine sanadin bude
KUNDUN TSATSUBA
tabbas gaba daya sirrikan tsafin boka shamharu
na nan cikin littafin KUNDUN TSATSUBA na
farko
nikuma nawa suna nan acikin sabon KUNDUN
TSATSUBA na biyu wanda yanzu haka
mahaifinka ruziyal yana kam aikin ruvutashi
acan duniyarku tareda aljni rafkamagu da boka
hajarul makarus wadanda ke taimaka masa
wajen ziyaràr sarakunan duniya suna basu
labaran abubuwan al'ajabi
ya zama dole agareni na tsaida wannan aiki
nasu ta hanyar ta hanyar kulle sabon KUNDUN
TSATSUBA da kubar MUFTAHUL ZARBIL
yanzu haka kubar MIFTAHUL ZARBIL na nan
ajikin kundun na farko
wanda kuka fara karantawa kubar ba zata
zaruba daga jikinsaba ta kowanne hali harsai
kun gama karanta littafin
gama karanta littafin kuwa zaikai tsawon
shekara goma sha tara da "yan watanni kuma
lokacin zaizo daidai da lokacinda za'a gama
karanta sabon KUNDUN TSATSUBA zai zo dai
da lokacin da za'a hattama rubuta kundi na b!yu
idan na bari aka kai wannan lokacin za'a san
sirrina
ya zama wajibi agareni na kera sabuwar kubar
MIFTAHUL ZARBIL
wannan kubar kuwa bazata keruba face na
narkar da duniyarku gaba daya
da narkakkiyar kasar duniyar kune zan iya kera
kubar MIFTAHUL ZARBIL
yanzu sai ku shirya don zan sauya muku halitta
ne yadda zan iya c!ka burina
koda sarki azmul gallar yazo nan azancensa sai
hankalinsu jafar ya dugunzuma
yeli$a,mashrila, da sarki azbir suka kama kuka
saboda sunji ance za"a sauya musu halitta
kuma koba komai sunsan ba karamar wahala
zasu sha ba akan wannan aiki wata kilama su
iya rasa rayuwarsu
jafar, mazalish, da gulzum kuwa kokadan basu
razanaba dajin wannan batu na sarki azmul
gallar
cikin rashin tsoro da gadara jafar ya dubi sarki
azmul gallar yace
yakai wannan sarki inason ka wayar mini dakai
akan matsayin boka shamharu awajenka
domin na fuskanci cewar kusan burinku daya
shin yanason ya mallaki komai da kowane dake
duniyar kasa, kai kuma kanaso ka hallaka komai
da kowane dake duniyar kasa,
kodajin haka sai azmul gallar ya bushe da dariya
yace
yaro baka fahimta sosaiba ai tsakanina da
shamharu babu komai face matsananciyar gaba
kamar yadda na fada muku cewar bazan iya
kera kubar MIFTAHUL ZARBIL ba saina narkar
da duniyarku haka shima shamharu bazai iya
tsaidaku daga karatun KUNDUN TSATSUBA na
farko ba harsai ya narkar da wannan duniyar
tamu
kusan kuwa abune da bazai taba yiwuwaba
agareshi.
Mu hadu a part B don Jin cigaban wannan KAYATACCE KUMA KASAITACCEN LABARI ✍️
**MATSATSUBI**💥💥
LITTAFI NA UKU ✍️✍️
PART B ❤️❤️
NA: ABDUL'AZIZ SANI MADAKIN GINI 🤴
POSTING: NAJIBULLAH MUHAMMAD ☝️☝️
TYPING: Habibullah Muhd Kabara ✍️✍️
MARUBUCIN YACI GABA DA CEWA..
Kafin wani daga cikin su jafar ya kara cewa
komai sai sarki azmul gallar ya dubi dakarun
nan da suka zo dasu jafar take suka kama su
suka hada da sarki azbir suka nufi wni bangare
daban dasu
sai da akayi wata 'yar doguwar tafiya dasu
sannan aka shigo wani katon daki
babu komai acikin dakin face tarin wasu manya
manyan tukwane na gilashi
acikin tukwanen ruwan zafine launi launi yanata
zabal bala
wani ruwan sai kaga ja ne, wani kuma shudi,
wani kore kai atakaice dai babu irin kalar d
babu
ba tareda bata wani lokaciba dakarun nan suka
daure su jafar d wata sarkar tsafi
wadda da zarar su jafar sunyi yunkurin kubuta
zasuji kamar ana tsotsar jinin jikinsu
bisa dole suka rungumi kaddara ,wani abin
mamaki shine aljani gulzum yafi wadannan
dakarun girma da kwarjini
amma sarrafa shi suke kamar dan mitsitsin
yaro da babba
koda su jafar suka ga anyi musu mummunan
dauri haka sai hankalinsu ya dugunzuma suka
rasa abinda yake musu dadi tsoro ya baibaye
zuciyar su ta fara bugawa da sauri
nantake dakarun nan suka kama sarki azbir da
karfin tsiya suka nufi wata kwalba mai dauke da
shudin ruwan zafi
nan take sarki azbir ya kama ihu da koke koke
yana rokon su kyaleshi
al'amarin daya kara dugunzuma hankalinsu
jafar kenan
don basu san dalilin dayasa sarki azbir ya
firgice haka ba her yake kukaba
adaidai wannan lokaci ne sarki azmul gallar ya
shigo cikin dakin yana kyalkyla dariyar farinciki
kawai sai ya dakawa dakarun nasa tsawa yace
me kuke jirane dashi?
maza ku jefasho cikin kwalbar mana
kafin azmul gallar ya gama rufe bakinsa tuni
daya daga cikin dakarun yasa hannu biyu ya
bude murfin kwalbar mai kma da katon faranti
aikuwa yana budewa aka jefa sarki azbir a ciki
aka rufe ,tamkar an sanya alli acikin ruwa haka
jikin sarki azbir ya dinga zagwanyewa
tun yana ihu ana jin muryarsa har muryar ta
dishe
ahankali gaba daya jikin nasa ya narke ya
cakude da ruwan cikin tukunyar ya dinga
hautsinewa yana bori kamar kwalbar zata fashe
jim kadan kuma sai aka g ainihin siffar sarki
azbir ta dawo
kuma ya dinga rikida ya zama abubuwa iri iri
kamar kyanwa, maciji, kunama, da sauransu
saidaya zama abu dari da daya
acikin darin ne ya zama wani irin mummunan
gwaggon biri ya zana zama hakan sai kwalbar
ta fashe da kanta
gwaggon biri ya tako da kafafunsa yaje gaban
sarki azmul gallar yana mai sujjada
alamun yin biyayya,
cikin tsananin farinciki azmul gallar ya bishe da
dariyar mugunta
duk wannan abu dake faruwa au jafar n gani
kuma tuni sun fara kuka da bakin ciki
jafar ya dubi gulzum yace
amma dai kaji kunya tunda karfinka da
girmanka ya zama na banza bazaka iya ceton
mu ba
gulzum yayi tsaki yace
amma dai kai banzane waya gaya maka cewa
karfi da girma zaiyi tasiri anan?
ina tabbatar maka da cewa ko boka shamharu
ne ya kuskura y fado nan ya zama nama sai
yadda akayi dashi
bare ni daban zama komai a ilimin tsafiba
ita kuwa yeli$a saita dubi mazalish tace
yake ma'abociyar hikima, ina rokonki daki
hanzarta tunanin kubutar damu
inba haka b yanzun nan za'a mai damu irin
ahinda aka maida sarki azbir
kodajin wannan batu sai hawaye ya zubowa
mazalish tace
yake kawata kiyi sani cewa. hikima ko karfi ko
sihiri ba zasuyi aiki anan ba
domin sunzo gidan kakanninsu
inda kunsan ma abindana sani da kun
gwammace mutuwa gaba daya yanzu take
ina bakin cikin sanar daku cewa idan har sarki
azmul gallar ya mai damu burarrika to har abada
babu wanda zai iya dawo damu ainihin siffar
mu face shi kadai
ku sani cewa idan aka samu acikin sundukin
haske aka tura mu duniyar mu to mun tafi
kenan ba zamu sake dawowaba
bare ya dawo damu ainihin siffofin mu
ku sani cewa alokacinda sundukin hasken zai
narkar da duniyarmu to tareda mu zata narke
kunga shikenan tamu ta kare
mazalish na gama fadin hakan kenan
sarki azmul gallar ya tsaya da dariyarsa
sannan ya dubi su jafar yace
to idan akwai wanda yakeda wasiyya ga
danginsa ko 'yan uwansa saiya fada kafin n
jefaku acikin kwalbar tsafi tabbas zan taimaka
nakai wasiyyar
mazalish ta share hawayenta tace
inada wasiyya amma ga masoyina JARUMI
HUBAIRU abokin gaba LU'UMANU
inason ka bashi labarina ka fada masa cewa na
baro kasata saboda shi, na kashe mahaifina
saboda shi kuma na rabu da mahaiyata
sabodashi don kawai y zama abokin rayuwata
wannan shinè kadai burina lallai banaso na.
mutu ba tareda hubairu yasanni ba a duniya
kodajin wannan batu sai sarki azmul gallar yayi
yace
ai wannan mai saukine nayi alkawarin zan idar
da wannan wasiyya,
waye kuma zai sake bayarda wata wasiyyar
daga cikinku? azmul gallar ya tamb@ya
jafar ya dubeshi yatsine cikin raini yanzu kai
nan nufinka shine zakayi amfani damu wajen
biyan bukatrka mu kuma mu hallaka?
to kasani cewa buktarka bazata biyqba kuma
zamu dawo nan mu yakeka mu tarwatsa
dukkanin irinka
kodajin wannan batu sai sarki azmul gallar ya
tuntsure da dariya ya karewa jafar kallo sama
da kasa sannan yace yakai jafar kai kuwa mene
takamarka?
ka sani cewa nafiku karfi, sihiri da komai tayaya
zaku iya yakata harku sami nasara akaina?
jafar yace bana takama da komai face sa'a
ka sani cewa babu wanda yayi tsammani cewa
zamu iya dauko kundun tsatsuba bare har mu
iya samo kubar miftahul zarbil mu budeshi
gashi yanzu harmunyi nisa acikin karatunsa
muna kan shafi na ashirin da daya
bana mamakin cewa zamu iya kubuta daga
hannunka harmuje wata duniyar inda zamu
hadu da wani takadirin wanda yafika shaidanci
azmul gallar yayi murmushi yace ai yaro kayi
kuskure babu wani mahaluki kmata tsakanin
duniyarku ta kasa da sauran duniyoyin dake
nan sama
da wannan kalami nake muku sallamar karshe
ina maiyi muku fatan riskar ajalinku @saukake
cikin "yan dakiku kadan
yana gama fadin hakan ne dakarun nan suka
kama jafar, yeli$a, gulzum, da mazalish suka
tsomasu acikin kwalaben nan masu ruwan zafi
nan take jikinsu y fara narkewa tun sunayin ihu
har suka kasa
ahaka dai har siffofin su suka juye izuwa na
burarrrika kamar yadda aka maida sarki azbir
koda aka fito dasu daga cikin kwalaben wato
bayan kwalaben sun farfashe da kansu
sai suka jeru su hudun suka zube gaban sarki
azmul gallar suna masuyi sujjada agareshi
cikin tsananin farinciki azmul gallar ya kece da
dariya sannan ya dubi dakarunsa yace
ku tafi dasu izuwa dakin sundukin 'aske
cikìn biyayya dakarun suka iza keyar burarrikan
shida sukai gaba saida sukayi tafiyar rabin sa'a
cif sannan suka iso wani tangamemen daki
babu komai acikin dakin face wani mulmulallen
karfe mara nauyi asamansa ankifa wani
zagayayyen gilashi mai siffar kwai
wanda ta cikinsa na iya hango wasu kujeru
guda shida dake cikin sa
kujera ta farko nadaga gaba sauran kujerun
kuwa guda biyar suna bayanta ajere reras
agaban kujera ta farko kuwa wadansu yan
kananan ramukane guda huda ja, fari da ruwan
dorawa
kowanne rami arufe yake da gilashi amma
akwai siririn tsinken tsafi ajikinsa
da shigowa cikin wannan daki saisu jafar
sukayì arba da wannan gabjejen sunduki na
farin karfen gurar ruwa
nanfa suka wangame baki suna kallon surar
dukda sun kasance acikin siffar burrai kasan
cewa mamaki sukeyi
batareda bata lokaciba sarki azmulgallar ya
nuna su jafar da danyatsa
kawai sai suka bace bat basu bayyanaba sai
acikin sundukin karfen
sarki azbir ne agaba,
jafar yelisa ,gulzum, mazalisha
na daga kujerun baya koda suka tsinci kansu
cikin wannan sunduki sai suka mimmike tsaye
sunata dukan gilashin daya rufesu don su sami
damar fita amma abanza kamar suna dukan
dutse
koda sarki azmul gallar ya ga haka sai ya sake
nunasu da hannunsa na hagu
t@ke suka koma suka zauna, zamansu keda
wuya sai sarki azbir ya...


Read / Download MATSATSUBI BOOK 3

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

1 Comments On MATSATSUBI BOOK 3
avatar
abasu-kala

3 months ago

Reply

Good really enjoy the book waiting for Miftahul Zarbil

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album