Join Our WhatsApp Group

KIBIYA RATSA MAZA 1 to 5 Complete Hausa Novel Document by KIBIYA RATSA MAZA 1 to 5


KIBIYA RATSA MAZA 1 to 5

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 40235



KIBIYA RATSA MAZA 1 to 5

Reading Time: 3 Hours

Added On: 17, Sep 2023

Author: Abdulaziz Sani Madakin Gini ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Adventure novels

File Size: 226.84 kb

File Type: txt

Views: 1079+

Download: 636+

Last download: 7 hours ago

Description/Story: KIBIYA RATSA MAZA
Littafi na Daya(1)
Part A
Gudu takeyi iya karfinta domin ta
ceci rayuwarta
saboda bala'in daya biyo ta,
babu abinda za'a
kwatantashi dashi face ajali.
Babu abinda zai baka mamaki face
wannan budurwa dake wannan
azababben gudu,kyakkyawa ce
abar
kwatance,kuma
cikin shigar yaki take,ga takobi a
hannunta tsirara
ba'a ciki kufe ba.
Saboda karfin gudun da takeyi
tamkar tafin kafarta zai tabo
keyarta,amma duk da haka waige
waige takeyi a cikin alamun
tsoro,duk
da
cewa kana mata kallo daya zaka
gane cewa
jarumace ta kwarai mai kirar
sadaukai.
Kai bama ita
ba hatta aljanu da tsuntsaye dake
cikin wannan daji
da take gudu a cikinsa tsoron dajin
sukeyi da abinda ya biyota saboda
masifu da bala'in dake tare
dasu ballantana kuma bako irinta
wanda bai taba
shigowa dajin ba.
Ba wani abu bane yake bin
wannan
budurwar ba face wadansu irin
dodanni masu kirar
goggon biri.Kawunansu da
fuskokinsu irin na biri ne amma
kuma kirazansu cike yake da gashi
tamkar
zaki.Suna da tarin kwanji a
hannayensu tamkar na
bil'adama,amma banda a kirazansu
babu inda
mutum zai ga gashi koda kuwa a
kan
kawunansu.Saboda tsananin karfin
gudun
wadannan dodanni har tashi sama
suke tamkar tsuntsaye
saidai kaga suna tsallake mutum,
amma dukda haka
sun kasa cimma wannann
kyakkyawar jaruma
saboda karfin gudun nata ya ninka
nasu domin duk
sa'adda dodannin suka yi taku
biyar bisa turba to a
madadin nata taku guda yake.Ko
makaho ne yaji sautin gudun
wannan jaruma yasancewa gudun
nata
ya wuce na hankali da tunanin
kwakwalwar
bil'adama saidai a kirashi da gudun
sihiri.
Kokarin
wannan jaruma shine takaiga wani
katon tsauni
wanda ake kira da suna Lauhul-
Farras.
Su kuwa wadannan dodannin suke
gadin tsaunin sama da
shekara dari uku da arba'in da uku.
A tarihin
wannan
tsauni babu wani bil'adama daya
taba samun damar
hawansa.Hatta Aljanu da suka sami
hawansa ma
ba'a taba samun dayansu ya sauko
a raye ba,saidai aga an jeho
gawarsa daga kan tsaunin.
Shidai
tsaunin Lauhul-Farras duk wata
cuta ta duniya akwai
maganinta a kansa.
Duk abinda mutum yake so ya
samu a duniya indai ya hau kan
wannan tsaunin sai
ya sameshi,
to amma fa ba hawansa ba
saukar.Shi
kansa hawan ba karamin masifa
bace dole sai mutum yana da
gagarumar jarumtaka ta kwatance
gami da tsananin karfin sihirin tsafi.
Mafi akasarin
jaruman da sukayi kundumbala
suka siyar da
rayuwarsu suka durfafo wannan
tsauni da nufin su
haushi sun kasance 'ya'yan manyan
bokayen
duniya wanda suka yarda da
kansu.Lokacin da ya rage
saura baifi taku ashirin ba tsakanin
jarumar da bakin
tsaunin Lauhul-Farras,sannan kuma
tazarar dake
tsakaninta da wadannan dodanni
baifi taku ashirin
ba,sai ta tsaya cak ta waigo ta
fuskanci dodannin
tana mai bude hannayenta alamar
cewa a shirye take ayi duk abinda
za'ayi.
Ai kuwa suma dodannin
suka tsaya cak akayi cirko crko aka
fara kallon kallo
tsakaninsu da jarumar..
Ba komai bane yasa
dodannin suka tsaya suna kallonta
ba face itace
bil'adama ta farko data taba samun
damar shigowa
har cikin wannan daji tazo tafkin
wannan tsauni don haka basu san
iyakar shirinta da karfinta ba.
Baya ga
haka kuma komai yawan dakarun
aljanu gami da
karfin gudunsu walau a a sama ko
a kasa basa iya
tserawa wadannan dodanni face
sun karkashesu
sun
karar dasu,amma yau gashi mutum
daya jal kuma ma wai 'ya mace ta
gagare su kamawa bare su
kasheta har saida ma ta tsaya da
kanta.
Ita kuwa
wannan jaruma a tsorace take da
wadannan
dodanni
saboda itama duk irin tsananin
jarumtakarta da
karfin sihirinta bata taba haduwa
da masifaffun halittu ba irin
wadannan masu karfin gudu,bakin
naci,kwarjini da ban tsoro.
Kuma ba karamar
kundumbala tayi ba data tsaya ta
fuskanci wadannan
dodanni ba,sai saboda tasan cewa
idan ta basu baya
a lokacin da zata fara kokarin hawa
kan wannan
tsauni to tabbas komai zai iya
faruwa gareta.
Kodai suyi mata mugun raunin
dazai iya zama sanadin
ajalinta ko kuma su kasheta farat
daya.
Abinda ya
kara firgitata dangane da dodannin
shine a lokacin
data shigo farkon dajin ta kasa
tseren gudu
dasu.
Duk sa'adda ta waiga bayanta taga
yadda suke
bangaje duk abinda ke gabansu
suna tarwatsa shine
ya rugurguje,walau bishiya ko
dutse,shi yasa ta razana
ainun don tasan cewa ta gamu da
gamonta duk
kuwa da cewa itama tun tana da
shekara goma sha
daya a duniya mahaifinta boka
Saiham ya fara bata
horon yaki,horon gudu a cikin
duwatsu,kwazazzabai,­
rairayi har da cikin rabo.
Tasha bakar wahala wajen
koyan wadannan abubuwa ramkar
ranta zai fita har
mahaifiyarta ta rinka ganin kamar
cewa boka Saiham
bai damu da rayuwar 'yarsa ba duk
da cewa kuwa
ita kenan kadai gareshi.
Saida takai cewa kafin Jaruma
Safirat ta saba da wannan horo
kullum sai
tayi matsannanciyar rashin lafiya ta
zazzabi da
kumallo bayan sun dawo daga daji
ta karbo
horon.
Sannan a hankali bayan kwanaki
arba'ain da
daya jikinta ya saba da wannan
tsananin
wahala,yake iya jureta ya zamana
cewa ko ciwon kai baya sata.
A ranar da boka Saiham ya
kammala
baiwa Jaruma Safirat wannan horo
ne kuma ya
danka mata gaba daya sihirinsa na
tsafi.Ya dubeta a
lokacin da idanunsa suka ciko da
kwallahh har
hawaye ya subuto masa yace,yake
'yata yau kwana
arba'in da daya kenan ina baki
wannan horo mai tsananin wahala
tamkar zaki rasa rayuwarki.
To ki
sani cewa ba komai bane ya sani
nake baki wannan
horo ba face saboda tsananin SO DA
KAUNA,
kuma
saboda ina son nan gaba ki zama
sarauniyar
duniya.Wani babban matsayi nake
son ki samu
wanda ni bani da ikon samunsa
domin damar ta wuce.
Koda Boka Saiham yazo nan a
jawabinsa sai
Jaruma Safirat ta kamu da tsananin
mamaki ta
dubeshi cikin alamun rashin
fahimta tace,haba yakai
Abbana saboda me zaka dami
kanka kan cewa sai
na zamo sarauniyar duniya?
Ka tuna fa cewa ko
mutuwa kayi yanzu ni da
mahaifiyata kabar mana dukiya
mai tsananin yawan gaske da har
mu mutu
bamu isa mu iya karar da ita ba
koda kullum zamu
rinka dibarta muna rabar da ita ga
mabukata.
Ka
bani jarumtakar da komai
dandazon mayaka zan iya
kutsawa ta cikinsu na tsira da
rayuwata.Sannan
komai isar matsafi bazai iya cutata
da karfin sihirinsa ba.Koda jin
wannan batu sai Boka Saiham
yasa hannu ya share hawayensa
sannan ya rike
'yarsa Jaruma Safirat ya rungumeta
a kirjinsa
yace,haba yake 'yata shin kina son
na bata shekaru
talatin danayi a cikin kogon tsafina
a banza kenan?
Koda jin haka sai Jaruma Safirat ta
janye jikinta daga cikin na boka
saiham da sauri ta dubeshi cikin
kaduwa tace,yanzu dama duk
shekarun daka bata
cikin kogon tsafinka tun kafin a
haife ni wani
babban
al'amari ka kirkiro?
Boka Saiham yace kwarai
kuwa.Yake 'yata kiyi sani cewa ba
komai bana sana'anta ba face
KWARI DA BAKA wacce duk jarumi
ko sarko ko kuma matsafin daya
mallaketa zai iya
mallakar wannan duniya gaba
dayanta.
Amma inda
matsalar take na gano cewa ni
bazan iya sarrafa
wannan Kwari da baka ba saboda
shekaruna sun
haura ashirin da biyar.Kuma bisa
binciken danayi babu wani
bil'adama da zai iya sarrafata ko
kuma
aljani face wanda shekarunsa suka
haura ashirin da
biyar ko kuma suka gaza goma sha
takwas bai isa
ya iya sarrafa kwari da bakan
ba.Babban sihirin
wannan KWARI DA BAKA shine idan
har tana
hannun mutum tofa koda gaba
dayan mayakan duniyar nan
zasu taru a kansa ba zasu iya kaishi
kasa ba ko su
cishi da yaki.Kuma KAIFI KO TSINI ba
zai iya tasiri a
kansa ba.Idan kuma har ya harba
kibiya daya daga
cikin kibiyoyin dubu nata,kibiyar
zataje ta kashe
mutum biyar a cikin dakika biyar
kuma ta dawo ta koma cikin
kuttunta.
Kinga kenan a cikin kankanin
lokaci mai wannan kwari da baka
zai iya karar da
milyoyin abokan gaba.Saboda
ganin cewa bazan iya
sarrafa wannan kwari da baka bane
wacce na
sana'antata da hannuna,bayan na
gama tane na
fashe da kuka na bakin ciki amma
dana tuna cewa zaki iya mallakarta
sai na kwalkyale da dariyar farin
ciki.Abinda ya sanya kuwa kika ga
na baki wannan
horon yakin kuwa mai tsananin
wuya shine a
lokacin
da kika cika shekara sha takwas na
san
matsafa,jaruma da manyan
sarakunan duniya zasu kwallafa
ransu akan wannan kwari da
baka.Idan
baki
da wannan horon dana baki zasu
iya rabaki da ita
bayan kin sha wahala wajen
daukota a inda zan
boyeta.Koda jin wannan batu sai
mamaki ya sake
turnuke Jaruma Safirat a karo na
biyu tace,
Haba Abbana saboda me zaka
wahalar dani ka biye
wannan KWARI DA BAKA a inda
nima sai nasha
bakar wahalar daukota?
Koda jin wannan tambaya
sai
Boka Saiham ya numfasa cikin
alamun takaici a
lokacin da idanunsa suka sake
cikowa da kwallah yace,yake 'yata
kiyi sani cewa bana son ki sha
wahala daidai da dakika
biyar,amma idan na bar
wannan kwari da baka a gida ko a
kogon tsafina a
yanzu wasu takadaran matsafa ko
bokaye,jarumai
ko
sarakai zasu iya zuwa su saceta a
lokacin da bana raye kafin ki kai
munzalin da zaki iya mallakarta a
hannunki ki iya sarrafara.
Bisa wannan dalili ne na
yanke shawarar na raba kwari da
bakan na kaisu
wurare daban daban inda babu
wani mahaluki daya
isa yaje ya dauko su face ke.
Da farko zan dauki
Bakan na kai shi can dajin Sharjul
inda tsaunin Lauhul Farras yake na
dorata a kansa.
Ki sani cewa
babu wani bil'adama ko aljani daya
taba hawa kan
wannan tsauni ya sauko a
raye.Kuma duk abinda
mutum yake nema a cikin duniya
indai ya hau kan
tsaunin Lauhul Farras tabbas saiya
sameshi,amma fa
va zai sauko a raye ba.A matsayina
na sarkin Bokayen duniya a yanzu
na gano cewa da horon
dana baki yanzu gami da sihirin
tsafina dana
mallaka miki da kuma sa'arki zaki
iya hawa kan
tsaunin Lauhul Farras ki sauko
lafiya.Shi kuwa
kuttun kwarin zan dauke shine
nakai shi dajin Sarkif
na adana shi a kogon
mutuwa,kogon da ake adana
dukkan kayan yakin duniya tun
daga farko har
izuwa
na karshe.
A tarihin wannan kogo na mutuwa
duk
abinda ya shiga cikinsa tofa bazai
sake fitowa ba
saboda tsananin tsaron dake
cikinsa,
amma na gano
cewa ke zaki iya shiga cikinsa ki
dauko duk abinda kike bukata.
Bazan iya sanar dake komai ba
akan
wadannan wurare biyu ba,da kuma
irin bala'in dake
cikin dazuzzukansu ba.
Amma bayan na mutu zaki
karance komai a cikin litattafan
tarihin rayuwata da
zan bar miki wanda shine zai
jagorance ki a cikin
duk abinda zaki yi na rayuwarki.
Duk abinda ya shige
maki duhu zakiga mafitarsa a cikin
wannan kundi
dazan bar miki gado.
Kada kiyi wasa da wannan kundi
kuma kada ki kuskura ki bari yaje
hannun wani
mahaluki walau mutum ko
aljan,domin tamkar kin
bayar da dukkan sirrikan sihirin
tsafinki ne.
Sannan ki kasance tare da wannan
littafi a tare dake ko
yaushe.
Dare da rana ki kasance mai juriya
bisa duk
irin yanayin da kika tsinci kanki
domin ba'a zama
wane a banza ba.
Nima nan da kika ga na sami
wannan
matsayi na sarkin bokayen duniya
ban same shi a
banza ba saida na sha
gwagwarmaya da manyan mazaje
kuma na tara makiya marasa adadi.
Tsananin
sa'a da rabo ne suka sa na tsira da
rayuwata na
kawo a yanzu.
Tunanin wannan abu daya faru ne
yasa
jaruma Safirat take samun kwarin
gwiwa ta jure duk
irin wahalar data tsinci kanta a
ciki.Kafin Jaruma Safirat ta iso bakin
tsaunin saida tasha
gwagwarmaya da mugayen
bakaken
aljanu,muggan
dabbobin daji da mugayen
kwari.Tasha bakar
wahala
da taji kamar ta fasa zuwa tsaunin
Lauhul Farras ta koma da
baya,amma data tuno da wasiyar
da
mahaifinta ya bar mata cewar ba'a
zama wane a
banza kuma ta tuna cewa idan fa
bataje ta dauko
wannan kwari da baka ba ba babu
wanda zai iya
daukota kuma duk kokarin da
mahaifinta yayi ya
zama na banza kenan.
Sa'a daya kawai jaruma Safirat bata
sani rauni ko daya ba a jikinta
amma ta
jigata ainun.
Bayan anyi kallo kallon kallo
tsakanin
jaruma Safirat da wadannan
mugayen dodanni sai ta
sake zaro wata gajeriyar adda a
kuibin cinyarta ta
hagu ya zamana cewa makami
biyu ne a
hannunta,sannan ta gyara
tsayuwarta.Koda ganin haka sai
dodannin suka kama yin wani irin
mugun
gurnani mai ban tsoro da firgitarwa
suka rinka
dukan
kirazansu alamar cewa suma sun
yarda da kansu
kuma a shirye suke a fafata ba
gudu ba tsira.
A
wannan lokaci ne jaruma Safirat ta
lura da faratan hannayen dodannin
taga ashe zara zara ne masu
kaifin tsiya gami da tsini yadda duk
abinda suka
karta ko suka tsira take zai dare ko
yayi huda mai
zurfu.
Duk jarumtaka irin ta Jaruma
Safirat gami da
dakewar zuciyarta da kuma rashin
tsoro amma saida
taji gabanta ya fadi sosai domin taji
a jikinta cewa karo da wadannan
halitta ba wasa bane.
Amma data
tuna cewa bata da wani zabi
wanda yafi ta tunkare
su sai kawai ta daka tsalle sama
izuwa tsakiyarsu
tana mai kurma uban ihu mai
tsananin firgitarwa ta
dira tsakiyarsu ta hau su da sara da
suka.
Suma
suka wanzu suna masu maida
martani da gabas da yamma,kudu
da arewa.
Cikin kankanin lokaci sai
gashi tarwatsin wuta na tashi
sakamakon haduwar
makamanta da sassan jikinsu.
Ya zamana cewa KAIFI
DA TSINI baya tasiri a jikinsu.
Koda Jaruma Safirat
taga haka sai ta hada da kai naushi
da bugu.Ta
rinka karkadesu tana zubar dasu
kasa tana tarwatsa su.
Amma kuma sai taga duk irin
dukan da takeyi
musu suna iya shanyeshi su mike
tsaye zumbur su
cigaba da yakarta ba tare da sunji
jiki ba.
Haka suma
wadannan dodanni sunyi mutukar
mamaki irin
jarumtakar Safirat gami da
tsananin zafin namanta
gami da juriyarta.
Domin itace jaruma ta farko wacce
ta iya shefe sama da dakika goma
tana yakarsu a
tsawon shekarun da sukayi suna
tsaron wannan
tsibirin.Saida aka shafe rabin sa'a cif
ana yin
wannan bkin gumurzu tsakanin
wadannan dodanni
da jaruma Safirat.
Ita bata samu nasara ba
akansu,suma basu samu ba.
Koda ganin haka sai hankalin
jaruma Safira ya DUGUNZUMA ainun
saboda dalilai guda uku.
Dalili na farko shine tasan
cewa ita batada maganin kaifi da
tsini irin na
wadannan mugayen
dodanni,domin ga dukkan
alamu sun fita karfin sihiri.
Dalili na biyu shine ita
bil'adama ce mai kashi da jini da
tsoka mai saurin gajiyawa,don
haka idan aka ci gaba da wannan
fafatawa izuwa wani lokaci zata iya
sarewa,a sami
galaba a kanta.
Dalili na uku kuwa shine dole ne
tayi
iya kokarinta ta gano inda laggon
wadannan
dodanni
yake kafin ta gaji.
To amma ta yaya zata iya gano
hakan,alhalin babu inda bata soka
ba ko ta sara ba
a jikinsu,amma shiru babu wata
nasara.
Ai kuwa nan
cikin hakane wani dodo mafi naci
da jarumtaka daga
cikinsu ya shammaci Safira yayi
mata wani wawan
dundu a gadon bayanta.Take taji
kamar bayan nata
ya burma kasusuwan wajen sun
kakkarye.
Ta kife kasa da rub da ciki tama mai
yin aman gudan
jini.Koda ganin haka sai gana dayan
dodannin
sukayi caa izuwa kanta gaba
dayansu da nufi su
ciscisgeta filla filla kowa yaja
rabonsa.
Ba zato ba
tsammani sai suka ga Jaruma
Safirat ta wurkila
kafafunta tayi wata irin
katantannuwa a tsakiyar tasu
ta mammake kawunansu ta
tarwatsa su da karfin
tsiya.
A haka ta cigaba da yakarsu cikin
mutukar
karfin hali tama cigaba da kare
hare harensu ta hana
dayansu samun nasarar sake taba
jikinta da faratan
hannayensu.
Amma kuma sai suka rinka yin
tamola da ita a tsakiyarsu.Nan da
nan Jaruma Safirat ta fara
fita daga haiyacinta,ya zamana
cewa jini na yoyo ta
cikin hancinta da bakinta.
Take Jaruma Safirat ta
aiyana a cikin ranta cewa tata ta
kare,domin nanda
cikar yan dakiku kadan gaba dayan
karfin jikinta zai
kare a cita da yaki.
Domin a wannan lokaci jiri ya fara
dibarta ta fara ganin dishi dishi.Ana
cikin
hakane
taga wannan dodo mafi naci da
karfi ya dako tsalle
a sama tamkar an harbo shi daga
cikin baka,ya
bude hannayensa biyu da nufin ya
soke wuyanta da
tsinin dukkan faratan 'yan yatsun
hannayensa guda goma.
Koda Jaruma Safirat taga zata
hallaka
muraran bata san sa'adda ta
yunkura ba cikin bakin
zafin nama ta sunkuya kasa
hannayen dodon suka
caki iska.Kafin dodon yayi kasa ya
sake kawo mata
wani harin tuni ta doki kasa da
kafafunta tayi sama
tamakra itama daga cikin baka aka
harbota.Nan take ta soke idanun
dodon biyi da takobinta da kuma
addarta.Nan take ruwan idanun ya
fashe,jini ya
kama
tsiri daga cikinsu.
Alokacin da dodon ya kama ruri
da kuruwa sannan ya kama
birgima a kasa yana
kakarin mutuwa.Kafin cikar dakika
biyar komai na jikinsa ya sandare
ya zama gawa.Koda ganin haka
sai farin ciki ya lullube Jaruma
Safirat saboda ta
gano inda ruhin dodonnin yake.
Ai kuwa sai ta
cigaba da soke musu idanu cikin
tsananin jarumtaka
da zafin nama na ban al'ajabi ya
zamana cewa
karfinta ya dawo tamkar ma a
sannan ta fara gumurzun.Da bala'i
yakai bala'i sai gashi dodannin
sun fara ja da baya saboda ganin
yadda take
ragargazarsu suna zubewa kasa
matattu tamkar ana
sassabe a gona.Sai gashi duk
tsananin yawan nasu
ya zama na banza saboda ta zame
musu alakakai
sun rasa yadda zasuyi da ita.
Ita kanta Jaruma Safirat tayi
mamakin yadda ta cigaba da
wannan yaki
cikin kuzari da dacin rai.
To amma ba komai bane ya
bata wannan kwarin gwiwar ba
face gano lagon
dodannin.
Wohoho! idan kaji ana ga ki gudu
to lallai
sa gudu ne bai zo ba!!
Saida aka shafe sama da
sa'a uku Jaruma Safirat nata
karkashe wadannan dodanni
amma da kyar suka samu suka
yanketa sau
biyu.Yanka na farko akan damtsen
hannunta ne na
hagu,wajen ya dare jini ya
zuba.Yanka na biyu akan
cinyarta ne ta dama.
Duk da cewar a wani faffadan
kwalkwalin karfe akan cinyar tata
saida kaifin tsinin
farcen ya darashi ya yanke ta.Ta
kurma ihu saboda tsananin zafi da
zogin da taji.Amma a hakan dai ta
cigaba da yakarsu tana cigaba da
karkashe su.
Koda
dodannin suka ga jaruma Safirat ta
kashe kusan
kaso daya cikin kaso ukunsu,ga
gawarwakinsu nan
birjik a wajen tamkar yabanya sai
gaba dayansu
suka ja da baya suka daina yakarta.
Amma sai sukayi cirko cirko a
gaban tsaunin suna numfarfashi da
gurnani suna kallonta kawai.Koda
ganin haka saita
juya tana tangadi gami da jan kafa
a lokacin da jini
ke diga daga jikin raunikanta.Cikin
karfin hali ta
kama hawa kan tsaunin tana
waigen dodannin
saboda tasan cewa a koda yaushe
wani daga cikinsu
zai iya dako tsalle sama ya kawo
mata harin
bazata.
A haka dai cikin matukar karfin hali
ta cigaba
da hawa kan tsaunin a hankali da
kyar amma bata
isa saman tsaunin ba sai bayan sa'a
guda.Tana isa
kan tsaunin sai ta baje a kasa tana
kallon sararin samaniya tana
numfarfashi tamkar ranta zai fita
saboda tsananin gajiya da jigata.
Saida ta dan jima a
haka sannan ta mike zaune ta kalli
saman dutsen ta
hango inda aka ajiye bakan da tazo
dauka.Koda tayi
arba da bakan sai ta cika da
tsananin mamaki
domin bata taba ganin baka mai
kyansa ba wanda aka kawatashi
ainun.
An dora bakan ne akan wani
madauki na karfe mai siffar gwafa
wanda aka soka
shi cikin tsaunin.Kai da gani ka san
cewa dama anyi
wannan madauki ne musamman
saboda wannan
baka.
Cikin tsananin farin ciki Jaruma
Safirat ta mike
tsaye.Mikewarta keda wuya sai ta
hango...


Read / Download KIBIYA RATSA MAZA 1 to 5

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album