Join Our WhatsApp Group

BAKANDAMIYAR GUMURZU fita ta daya 1 Complete Hausa Novel Document by BAKANDAMIYAR GUMURZU fita ta daya 1


BAKANDAMIYAR GUMURZU fita ta daya 1

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 16054



BAKANDAMIYAR GUMURZU fita ta daya 1

Reading Time: 1 Hours

Added On: 17, Jul 2023

Author: Umar Abdulhadi Mati ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Adventure novels

File Size: 88.56 kb

File Type: txt

Views: 787+

Download: 218+

Last download: 3 days ago

Description/Story: BAKANDAMIYAR GUMURZU
Chapter 1: Kana tunkarar filin babu abin da zai fara maka maraba face karajin fusatar hatsabiban mutane da aljannu kai hada ma dodanni kururuwar mayakan asali ta yawaita, kasa ta rinka girgiza da raurawa kamar zata tsage duwatsu suka rinka farfashewa, itatuwa suka rinka kamawa da wuta, guguwar annoba ta tashi sama ta tokare hasken rana wananne ya ba filin yakin damar yin duhu, hatsabiban mutane da aljannu da dodanni suka rinka shawagi a sama suna fauce rayukan junansu tabbas wanan bakin gumurxun ya cika sunansa turnuku fadan ibilisai, daidai lokacin ne wata bakar gobara ta taso daga tekun bahar sufiyya inda makaman mazanjiya suke, saidai abin da zai baka mamaki idan aka ce maka duk wanan masifa da balain dake aukuwa bai sa bakaken rundunoniba suka dakata da yakar junansu ba saima kara himmatuwa da sukayi wajan yakar junansu da kaiwa juna sara da suka mutuwar yawa ta kara yawaita mayaka da dama sun afka tarkon mutuwa batare da sun ankara ba saidai lokaci daya wanan bakin gumurxu da ake ya tsaya shaidanun mutane da aljannu da dodanni da suke shawagi a sama suka silmiyo kasa domin tsira daga halaka duk wanan abu ya faru ne sanadiyyar bayyanar wani haske mai daukar ido yana saukowa daga sama a hankali hasken ya sauko kasa lokacin da ya gama saukowa sai hasken ya fara raguwa sai suka bayyana, bayyanarsu ce tasa kowani hatsabibi dake filin yakin ya shiga taitayinsa ga duk wanda ya karanta littafin mazan jiya farat daya zai shaida wadanan mutanen da suka bayyana"lallai kam to bari mubar wajanan tunda har manyan shaidanu sun fara bayyan me ya kawo su SARKI MAHRAZ DA SARKI DUJALU nan gurin bari kagani in bar gurin tun kafi ta ritsa dani'' cewar wani bakin katon mummunan aljani tsawar da yaji ce ta dakatar dashi daga tashi sama ba kowane ya kwantsama wanan tsawar ba face sarki dujalu sanan ya fara magana cikin murya mai amo yana cewa yaku mayakan birnin matsafa, jaruman birnin sadaukai duk dacewa kunsha tsimin dodo kiryanu, an saka ku a cikin ragayar tsafi tun kuna yara hakan ba zaisa ku taka matsayin murucin kan dutse ba mu mune muruccin kan dutse tsawar da sukaji itace ta tsaida sarki dujalu daga maganar da yake cikin zafin nama suka juya domin suga wani mai tsautsayine wanan juyawar su ita tayii dadai da karasowar wasu kibiyoyin tsafi wanda ake musu take da kibiya ratsa maza badan sarki mahraz yayi saurin dafa kafadar sarki dujalu sun bace ba da tuni kibiyoyin sun cake jikinsu sana suka bayyana a gefe cikin fushi suka daga kawunansu....
BAKANDAMIYAR GUMURZU
Chapter 2:
Yayinda su sarki mahraz da sarki dujalu suka daga kawunansu sama domin suga wani mai karar kwanane yayi musu wanan danyen aikin sai sukaga wani tsohon aljani mai kwarjini da cikar kamala zaune kan wata bakar kujerar tsafi tsaye kan iska hannun sa na rike da wani katon littafi a jikin littafin an rubuta da babban baki KUNDIN TSATSUBA da saukarsa kasa yayi daidai da sakin fitsarin wani katon bakin aljani saboda tsananin tsoro idan kayi duba zuwa ga tarin hatsabiban mutanen da aljannu da dodanni duk zakaga zabar tsorone da fargaba tab cike da fuskokinsu ” shin mi ya kawo SHAMHARU SHAHARARRE wajan gasar kwarzon kwaraza shida ya tsufa ko tafiya ma bashiyi" cewar sarki mahraz sarki dujalu yayi murmushi ya mayar masa da amsa ya kai aarki mahraz duk yanda kake tunanin wanan gasa ta wuce nan domin kaf sarakunan duniyar mutane da aljannu, dodanni zasu taru anan duk wani tsohon hatsabi zai nuna kansa don haka kada kayi mamaki dariyar shamharu ce ta katse musu firar tasu kafin bisani ya fara magana karyarku tasha karya duk da nasan ku ba kananun hatsabibaine ba kowani babba da babban sa don haka ni shamharu shahararre nine mamallakin kundin tsatsuba nine muruccin kandutse nine gagara badau kuma ni zan ci wanan gasar ta gwarzon kwaraza kamar walkiya ya bayyana cikin shiga ta tsaffin matsafa wanda suka amsa sunansu tsawarce da ya dakawa shamharu itace ta jawo hankalin manya-manyan hatsabiban saidai kafin a ankara dayawa daga cikin mayakan sun duke bisa gwiwoyinsu " lallai yau tamu ta kare tunda abin har ya kai ga bayyanar MARGANU" cewar wani tsohon mayaki wanda kana ganinsa kasan yaga jiya yaga yau anjima ana damawa dashi marganu ya fara magana da cewa ni MARGANU dan jaddadu jikan gundugurki magallabin maza nine zan cinye garsar gwarzo gwaraza... Zan cigaba

BAKANDAMIYAR GUMURZU.
Chapter 3:
MARGANU ya cigaba da magana dalilina kuwa na cewa ni zan cinye wanan gasa ta gwarzon gwaraza ku saboda ni na ziyarci yakin makashin maza da gallabar maza kuma ni naziyarci kogon zakun kogon da ya gagari mutum da aljan shiga nine mutuman da ake zaton ya mutu bayan shekaru aru-aru na dawo dan haka ni yafi can-canta in zama gwarzon gwaraza guguwar da ta karade filin ita ta tsaida marganu daga maganar sa nan take kowa ya daga kansa sama ba komai ne ya haddasa wanan guguwa ba face kadawar fukafukan wani kato aljani ba ajima ba aljanin ya sauko kasa wani kyakyawan dogon dattijo ya duro daga kan aljanin durowarsa ce ta haifar da wata kura yayin da kurar ta yaye sai gashi ya bayyana cikin shiga mwadda ta nuna murdadden jikinsa irinna manyan sadaukan da suka amsa sunansu duk da cewa ya fara tsufa amma hakan baisa ba kuzarinsa ya ragu yana nan yadda yake ga wanda suka sanshi cikin murya mai amo ya fara magana cikin takama da tsantsar nuna isa yana mai nuna shamharu da marganu yatsa kai tsaffin banza kusani ku baku isa ku kira kanku da gwarazan-gwaraza ba kai shamharu idan baka san ko ni wanene ba ka tambayi yayarka tsohu mundiga da danta kulkulu zasu baka labari na nin e SADAUKI makashin dodo kusumu da sarki jata nine mamallakin zoben sihiri dan haka nine yafi cancanta da in zama gwarzon gwaraza, karan takun dawakan azabar da sukajine yasa kowa juyowa wohoho nan take kallo ya koma sama abida suka gani shi yasa kowa shiga taitayin ba komaine suka gani ba face jarumi shaddadu hannunsa na rike da mashin galilul haraz bayansa kuwa ziya'ul hak ce ke take masa baya gefen damarsa kuwa sadauki hantarune hannunsa na rike da takobinsa saiful lujara hagunsa kuwa sadauki hulkas ne mai hular lamsara a gefensa kiwa yar uwarsa ce jaruma siyama suna zuwa tsakiyar filin suka ja birki kura ta tashi sama lallai idan har kayi karfin halin duban fuskokin taron hatsabiban dake wanan filin zakaga du kowa ya kara shiga taitayinsa domin miyagun makaman dake hannnun mazanjiya bayan shiru na dan wani lokaci sai aka karajin takun sawayen wasu dawakan azabar kallo ya kara komawa sama gani wasu kyawawan mutane mace da namiji sun tunkaro filin sunyi shiga irin ta mazajen fama duk dacewa macen tayi shiga irin ta kamala domin ta rufe duk jikinta idan ka dauke kyakyawar fuskarta suma sukazo suka ja turjiya bayan shiru na dan wani lokaci sai namijin ya fara magana cikin murya mai amoyana cewa ....

BAKANDAMIYAR GUMURZU
Chapter 4;
Kyakyawan saurayin ya fara magana cikin izza da takama nasan dayawa daga cikinku sun sanni musamman ma wadan da suka halarci wajan gasar GAGARA BADAU nine jarumi HASANUL BASARI makashin maza nine jarumin da ya zamewa sarki hamadu alakakai nine zakaran gwajin dafin da ya lashe gasar gagara badau wanan kuwa da kuka gani matatace jaruma safila uwar maza duk wanda ya halarci gasar gagara badau to yasan rawar da ta taka a tare da ita akwai rantsatsiyar takobin ta wanda ta gada daga wajan mahaifinta dirar wasu fararen dawakaine ya katse masa maganar sa hakika kowa na filin yayi mamakin ta yadda wadanan dawakai suka tsallake mutane da aljanun kai hadama dodanni suka dira a tsakiyar wanan filin nan da nan kowa ya zuba ido domin yaga wasu hatsabibanne wanan kuma da me suka zo yayinda matashiyar kurar da ta tashi sakamakon dirar dawakan ta yaye sai gasu sun bayyana cikin fararen tufafi dukkan jikinsu a rufe yake ba'a ganin komai sai idanuwansu dukkansu suna rataye da zabga-zabgan miyagun takubba duk ba wanan ya ja hankalin mutanen da ke filinba abinda aka rubuta a jikin takubban nasu shine yasa kowa dake filin ya kara shiga cikin taitayinsa idan ka cire jarumi basaru da matarsa safila wanda su maimakon firgici saima murmushi da sukayi na ganin "yan uwansu musulmai abinda aka rubuta a tkobin shine cikin manyan baki SAIFUL ISLAM nan take daya daga cikin jaruman ya yaye fuskarsa ga wanda ya karanta littafin saiful islam nan take zai shaidashi nan take ya fuskanci mazanjiya kafin ya fara magana cikin murya mai amo da yadda dakai yaku mazajen jiya ina mai baku shawara da ku bace mani da gani tun kafin a fara wanan gasar domin duk jarumin da ya sake mukayi arba dashi a wanan gasar har ya yadda makaminsa ya hadu da takobina ta saiful islam to hakika makaminsa zai narke domin kunfi kowa sanin takobina tana tarwatsa duk wani sihirin tsafi komin karfinsa saboda haka ina tausaya muku domin duk duniya babu wanda bai san irin bakar wahalar da kuka sha ba wajan mallakar wanan makamai ba na mazan jiya da irin rayukan da suka salwanta na masoyanku dama abokan gabarku dan haka ina mai shawartarku da kucire rai daga lashe gasar gwarzon gwaraza ....zan ci gaba.
JARUMAN GASA SUN GAMA HADUWA SAURA SARAKUNA

BAKANDAMIYAR GUMURZU.
Chapter 5:
Wanan maganar da jarumi HUZAIFA mai takobin saiful islam ba karamin batawa mazanjiya rai tayiba wanan ne dalilin da yasa ma sadauki HANTARU ya zare takobinsa dalilinda yasa haske mai daukar ido ya cika filin hade da wani yanayi na tsohon babban sihiri kafin ya afkawa sadauki huzaifa sai yaji an ruko rigarsa ta baya cikin fushi ya jiyo abinda ya gani shi yasa jikinsa yayi sanyi jarumi shaddadu ne ya rike masa riga yayi masa murmushi kafin ya fara magana me kake ci na baka na zuba ai inda ba kasa nan ake gardamar kokowa ka kyaleshi lokaci shine zai banbance, jarumi hantar yayi kwafa kafin yayi ajiyar zuciya sana ya meda takobinsa cikin kube dalilin da yasa yanayin wajan ya komo dai-dai hayaniyace ta mamaye wajan.
Abin zai baka mamaki idan nace maka duk wanan cakwakiya da take aukuwa tana faruwane a wani shimfidedan katon fili wanda duba daya zaka masa kasan cewa an tanadeshi ne kawai saboda rana irinta yanzu wato saboda gasar gwarzon gwaraza filin zagaye yake da kananu kujeru mararsa adadi iya ganin mutum sana bangaren sama kuma wani dansamaline wansa akayi shi da zinare samarsa shake take da manya -manyan kujeru na sarauta wanda akayisu da zallan zinare cikin katuwar shema wanda akayita da zare na alharini aka mata cin zanzana da ruwan zinare hakika wajan ya kawatu kallo daya zaka yiwa wajan kasan an tanadesane saboda hamshakan fitattun sarakuna wanda sunansu ya shahara wanan fili na musamman an ginashi ne a bayan birnin ruma shine babban birni a daular rumawa inda babban sarki nawwar ke mulki bairnin da duk duniya anyi ittifakin babu birnin da ya kaishi kyawu da tsari hade ma da kwanviyar hankali abinka da birni da yake gefen teku duk wani tattalin kasuwancinsu ya ta'alaka da wanan teku wanan ne dalilin da yasa idan har kayi duba zuwa ga gabar teku a yau zaka ganta cike take da manya-manyan jirage kowani jirgi da dakwai tambarin kasarsa a manne jikinsa sanan akwai hatsabiban dakaru da matsafa dake tsaronsa karan bude kofar birnin da ita kanta abin kalloce shi yasa dukkan hatsabiban mutane da aljannu da dodannin juyowa suna jiran suga wanene zai fito karan tambura,algaita da kakin sune suka fara wa mutane sallama sana suka hango wata tawaga tana fitowa daga birnin nan take kowa kallo ya koma sama idan kayi duba ga fuskokin mutanen dake wanan fili zaka ga tsantsar mamaki a tattare dasu ba komaine yasa su mamaki face wasu aljannu masu siffar batoyi da suka gani sun masa rumfa tabbas wanan inuwa ita akeyiwa kirari....


)
BAKANDAMIYAR GUMURZU
Chapter 6:
Tabbas wanan inuwar ita akewa kirari da inuwar mutuwa domin duk wanda ya tunkari wanan rumfa da nufin kawo wargi ga wanan hashakiyar tawagar sunan sa gawa yayin da suka iso filin nan take mafiyawa daga cikin aljannu da dodannin da hatsabiban mutanen dake filin vikinsu ya duri ruwa saboda duk wanda ya kwana ya yini a duniyar hatsabibanci to yasan wanan sarkin "kai sarki hamad mai turnuku fadan ibilisai, gagarabadau hamshakin sarki" cewar jarumi basari hakika bakaramar wahala da azaba ba muka sha a hannunsa yayin gasar gagara badau badan mun nemi taimakon ubangijin musulunci ba da tuni ya shafemu daga doron kasa jaruma safila ce tayi wanan maganar taku yake dai-dai cikin takama da nuna isa ta hamshakan sarakuna yana tafe ana shimfida masa wani tattausan kilishi wanda akayisa da jan alharini ya tunkari wata jibgegiyar katuwar kijera wadda akayita da zallan zinare ya zauna ya harde kafin ya ida gyara zamansa ne aka karajin wasu tamburan da algaitu, kakaki kowa ya kara juyowa domin ganin wanene zai kara bayyana wata tawagarce ta kara tunkaro filin kowa ya zuba ido domin ganin ko wani sarkine wanan domin tawagar ta nunka ta sarki hamard yawa da tsaro yayinda tawagar ta matso kusa abinda suka gani shi ya kusan girgiza kowa dake wanan filin sarakuna ne guda biyu tafe suke suna fira cikin annashuwa sunyi shiga irinta sarki harmad sak ga wanda ya karanta littafin mutum da aljan da littaffin mazanjiya farat daya zai gane wanan sarakun SARKI LAFFARU ne da SARKI ALKASIM tafe suke cikin tafiya ta hamshakan sarakuna wanda suka amsa sunansu a wajan jarumta, tsafi, girman kai, kai da ka gansu kasan basa shakkar duk wani mutum da aljan kai hadama dodanni suma suka samu kujeru irinna sarki harmad sak suka zauna suka kame.
Abinda ya ba kowa dake wanan filinamaki shine ganin har yanzu dakwao sauran kujeru har guda biyu wanda suka rage babu kowa a kansu nan take mutane suka zuba ido domin gani wasu issassun sarakuna ne zasu kara bayyan....

BAKANDAMIYAR GUMURZU.
Chapter 8.
Bayyanar labulayen da suka tokare da sama ce ta sa kowani hatsabibi dake cikin wanan fili kara shiga hankalinsa sanan kowanne daga cikinsu ya ware idanunsa yana mai kallon wanan abin mamaki labulen bakine sidik idan ka daga kanka sama zaka iya cewa ya tokare da sama domin iya ganinka shine zaka gani zukatan kowanne daga cikinsu na saƙa masa abubuwa da dama shin dama can wanan labule yana nan idan yana nan me yasa bamu ganshiba tun zuwanan mu lalle wanan aikine na tsafi kafin kowa ya dawo da nutsuwarsa ne sarki nawwar ya kara tafa hannunsa karo na biyu nan take wanan bakin labule ya fara nannade kansa yana yin sama abin da "yan kallo suka gani shine ya kara rudasu kuma tsabar mamaki ya kara gauraye fuskokinsu...


Read / Download BAKANDAMIYAR GUMURZU fita ta daya 1

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album