Join Our WhatsApp Group

Subscribe for N1000/month for downloading access and an ad-free site. Contact WhatsApp +2348140419490 if you can't pay / subscribe. SUBSCRIBE

KARYA DA GASKIYA Complete Hausa Novel Document by KARYA DA GASKIYA


KARYA DA GASKIYA

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 24641



KARYA DA GASKIYA

Reading Time: 2 Hours

Added On: 28, Jun 2024

Author: Mansur Usman Sufi ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : 08137237071

Book License : Free

Category: Adventure novels

File Size: 131.84 kb

File Type: txt

Views: 394+

Download: 211+

Last download: 1 day ago

Description/Story: KARYA DA GASKIYA
Cigaban
TAFARKIN TSIRA
Rubuta Labari
MANSUR USMAN SUFI
Sarkin Marubutan Yaƙi










BABI NA ƊAYA






Al'amarin da firgita gaba ɗaya jama'ar dake fadar kenan suka sha jinin jikinsu, a lokaci guda Fitinatul-Amir ya turɓune fuska tamkar an aiko mashi da WASIƘAR MUTUWA, kawa sai ya dubi waɗansu ZARATAN DAKARU dake tsaye a gefen shi cikin matuƙar fushi ya buɗi baki ya ce "Ya ku dakaru ina so ku yi hanzari ku bi sahun dakarun dake ɗauke da haraji ku tabbatar da cewa ba a sanya dukiyar sarki Madsur a cikin Baitul-Mali ba, kuma ku tabbatar da cewa kun kawo mini Madsur da tawagarshi cikin ƙoshin lafiya domin na yanke masu hukunci dai-dai da abin da suka aikata mani,


Na rantse da girman halarar tsafi na idan ku ka yi kuskure a wannan aiki da na baku sai KAIFIN TAKOBI ya sha jininku,


Kafin sadauki Fitinatul-Amir ya gama rufe bakinshi dakarun su kimanin dubu sun zare makamansu sun ruga izuwa wajen fadar suka bazama cikin gari wasu bisa dawakai wasu a ƙasa, domin farautar sarki Madsur.


A she a ɗazu lokacin da Fitinatul-Amir ke tattaunawa da yaro Usaiba, kuma abin da Usaiban ya faɗa ya tabbata bayan Fitinatul-Amir ya gudanar da bincike 'yan majalisa sun ji da kunnuwansu, nan take suka raya a cikin cewa haƙiƙa wannan yaro yakasance ɗan baiwa taban mamaki, wai shin ma mene ne alaƙar dake tsakanin su,


Amsar tambayar da suka kasa bawa kansu kenan, kawai sai suka zuba idanu domin su ga sakamakon da dakaru za su dawo da shi.


Al'amarin sarki Madsur da tawagarshi kuwa, lokacin da suka fice daga fadar Fitinatul-Amir, sai Madsur ya karanta ɗalasiman tsafi suka ɓace ɓat! Tamkar ba su taɓa wanzuwa ba, ba su bayyana a ko ina ba sai a fadar Madsur dake cikin babban birnin Hairul-Maswat,


Fadar yakasance makekiya da aka ƙarara da nau'ikan ababen more jin daɗin rayuwar duniya, a wannan lokaci fadar ta cika maƙil da jama'a makaɗa, mawaƙa tare da dukkan wani mai faɗa a ji, lokacin da sarki ya zauna bisa kan karagar mulki sai waɗansu irin tsala-tsalan 'yan mata kuyangi suka shigo fadar ɗauke da nau'ikan kayan ciye-ciye da tanɗe-tanɗe suka shiga raba wa jama'a, nan al'umma suka fara kimtsa cikinsu cikin nishaɗi da annashiwa, makiɗa da makawa suka fara aikinsu na raye-raye da kiɗe-kiɗe domin ƙara wa al'umma nishaɗi, shi kan shi sarki Madsur tashi ya yi daga kan karagar mulki ya cire alƙyabbarshi ya zauna cikin 'yan majalissa suka shiga yin walimar suna shewa da tafi, da yawa daga cikin al'ummar dake fadar ba su dalilin da ya sanya aka shirya wannan walima ba, domin tsawon shekaru sarki Madsur yana buƙata daga sharrin Fitinatul-Amir amma bai taɓa farin ciki tamkar yau ba, ana tsaka da wannan walima ne sarki Madsur ya karɓi wani kofi mai ɗauke da barasa a hannun wani hadimin shi ya kai bakinshi da nufin ya ƙurɓe ruwan, amma sai kawai aka ga ya yi jifa da kofin ya faɗi ƙasa ya tarwatse sannan ya miƙe tsaye zumbur yana mai kwarara wawan ihu da ya firgita baki ɗaya jama'ar dake fadar kowa ya shiga taitayin shi, tsawon daƙiƙa talatin yana kururuwar sai tsuke bakinshi gami da murtuke fuska tamkar an aiko mashi da WASIƘAR MUTUWA, Kawai sai ya durfafi inda karagar mulki take ya juya ya fuskanci al'umma fuskarshi har gyatsine take yi saboda tsananin fushi sannan ya buɗi baki cikin kakkausar murya ya ce "Ya jama'ata ku yi sani cewa bakomai ya sanya ni wannan baƙin ciki ba face lalacewar dukkan wani shiri nawa da na yi na mallakar dukiyar Fitinatul-Amir shugaban 'yan fashin duniya, kuma ba wani ba ne ya watsa shirin nawa ba face wani hatsabibin yaro mai ɗauke da hatimin takobin SAIFUL-ZAYYAD, matsawar yaron yana tare da Fitinatul-Amir ba za mu taba yin nasara akan shi ba, sannan yaron zai zamo ANNOBAR SARAKAI da matsafa gami da bokayen duniya, sai dai kash! Ana dara ga dare ya yi shi kan shi Fitinatul-Amir bai sani ba cewa yaron annoba ne a gare shi domin abin da ya daɗe yana farauta dare da rana domin ya hallaka shi ko ya cika muradin shi ya samun magaji.


Saboda haka da nan zuwa kowanne lokaci zai iya kawo mana FARMAKIN BAZATO domin ɗaukar fansa, saboda haka wajibi ne a gare ni na gudanar da bincike mai zurfi domin tunkarar duk wani ƙalubale da zai iya biyo wa baya, sannan akwai buƙatar a daren yau a shirya tawagar dakarun kar-ta-kwana".


Lokacin da sarki Madsur ya zo nan a jawabin shi sai ya taka da ƙafafunshi ya durfafi ƙofar da za ta sada shi da gidan sarauta, cikin hanzari waɗansu ZARATAN DAKARU ma'abota baƙaƙen sulken yaƙi suka mara mashi baya har sai da suka ƙule izuwa cikin ƙofar sannan jama'a suka watse kowa ya kama gaban shi, zukatansu cike da matuƙar bargaba domin sun san cewa gwabzawa da Fitinatul-Amir tamkar mutum ya sayi ajalin shi ne kuɗinshi.


Wannan shi ne abin da ya faru da sarki Madsur a lokacin da ya bayyana a fadarshi, bayan ya miƙa haraji ga shugaban'yan fashin duniya sadauki Fitinatul-Amir.






Lokacin da dakarun sadauki Fitinatul-Amir suka fice daga fada sai suka kasu rukuni biyu, kaso na farko suka durfafi hanyar da zata sada su da Baitul-Mali, na biyun kuwa suka bi sawun tawagar sarki Madsur, rikuni na farko sun riski dakarun dake ɗauke da harajin sarki Madsur, sai suka garzaya baki ɗayan su suka dawo izuwa fada, bayan sun gurfana gaban sarki sun kwashi gaisuwa sai Fitinatul-Amir ya dubi shugaban dakarun fuskarshi a murtuke babu annuri tamkar an watsa mashi garwashin wuta a kan ta cikin kakkausar murya ya ce " Ya kai Huzlaif haƙiƙa da a ce wani acikin ku ya yi kuskure an sanya duniyar sarki Madsur a Baitul-Mali da ɗayanku ba zai tsira da rayuwar shi ba, bayan tafiyar ku na gudanar da bincike bisa halarar tsafi na na gani cewa sarki Madsur ya ɓace tare da tawagarshi yanzu haka yana birninshi, saboda ina so ka shirya dakarun yaƙi domin kai farmaki izuwa ga sarki Madsur kafin wayewar gari ina so a hallaka duk wata halitta koda kiyashin birnin ba na so a bar shi a raye"


Koda Fitinatul-Amir yazo dai-dai nan azancen shi sai ya mayar da duban shi ga wani garjejen ƙato ma'abocin kwarjini, ƙasumba da gemu baƙaƙe siɗik daga cikin jerin 'yan majalisar shi ya ce da shi "Ya kai dirkar birnina kai ne za ka jagoranci wannan kai FARMAKIN BAZATO ka tabbatar da an zartar da komai yadda ya dace"


Koda gama faɗin hakan sai sarki Fitinatul-Amir ya miƙe tsaye tsam! Daga kan karagar mulki ya durfafi ƙofar da zata sada shi da gidan sarauta cikin hanzari waɗansu ZARATAN DAKARU suka rufa mashi baya har sai da suka ƙule izuwa cikin cikin ƙofar sannan fadar ta watse kowa ya kama gaban shi, inda ace mutum zai ga yadda fadar ta yi watan! Sai ya rantse ya ce wata halitta bata taɓa wanzuwa a fadar ba.


Lokacin da aka garƙame da azababban yaƙi tsakanin Musulmi da kafurai sai yaƙin ya zamo abin tsoro ga kowa ne ɓangar, kabbarta musulmi haɗe da ihu da kururuwar kafurai gami da ƙarar karafniyar ƙarafa da haniniyar dawakai ta cika dodon kunne, rundunonin biyu suka wanzu suna kaiwa juna sara da suka cikin matuƙar zafin nama JURIYA DA BAJINTA, sassan jikkunan bil'adama suka dinga shawagi a sama suna zubowa ƙasa tamkar ana ruwan su ne daga saman, JINI DA ƘASA suka cakuɗe waje guda.


A ɓangaren manyan GWARAZAN JIYA kuwa sarki Rayyan da Lamsarul-Azlam sun wanzu suna kaiwa juna sara da suka cikin matuƙar zafin nama na gaban kwatance sai da sa'a ta shuɗe a cikin wannan hali ɗayansu bai samu nasarar lakutar jikin abokin gwamin shi ba,


Wohoho! Haƙiƙa masu iya magana sun yi gaskiya da suka ce kyan faɗa a kwana a na yi, kuma inda babu ƙasa nan ake gardmar kokawa, koda gwarazan biyu suka fahimci cewa sun kasa yin nasara ta hanyar amfani da makaman yaƙin su sai kawai suka yi jifa da makamansu suka ja da baya domin a gwada 'yar Kashi, suka ruga izuwa kan juna ya yin da ya rage saura taku goma tsakanin su sai suka dako wawan tsalle sama suka kaiwa juna huri suka naushi fuskokin juna, sannan suka diro ƙasa, koda kowanne su ya shafa hancinshi sai ya ji jini na zuba, kawai sai suka ruguntsume da sabon artabu, suka wanzu suna naushi da bugun juna hannu da ƙafa tamkar waɗansu ifritai.






Mu haɗu a babi na biyu domin jin cigaban wannan ƙayataccen labari


Daga mai ɗebe maku...


Read / Download KARYA DA GASKIYA

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album