Join Our WhatsApp Group

ZAKI GANE KURANKI Complete Hausa Novel Document by ZAKI GANE KURANKI


ZAKI GANE KURANKI

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 38708ZAKI GANE KURANKI

Reading Time: 3 Hours

Added On: 15, May 2024

Author: Fadeela Lamido ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : 07014197556

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 207.33 kb

File Type: txt

Views: 302+

Download: 298+

Last download: 8 hours ago

Description/Story: [6:34PM, 11/6/2016] ‪+234 701 419 7556‬: 💞💞 ZAKI GANE KURANKI 💞💞
1
✍MMN YAZEED
07014197556

Santalelan saurayi ne mai kimanin shekara 35 yafaka mutarsa a kofar gidan su ya ziro kafafuwan shi farare tas kamar ka taba jini ya futo,
yafara taku d'aid'ai ya doshi hanyar da zata sadashi da d'an d'ashe shen gidan nasu, yana taku dai dai irin na manyan sojoji yayi sallama abakin falon,
can daga cikin falon aka amsa mai, sallama dattijo ne mai kimani shekara 60 yana zaune tare da matansa guda uku duk suka waigo da murmushi akan fuskan su sabanin guda 1 data had'a rai daga cikin matan, ya karaso cinkin murmushi ya zauna yace sannunku da hutawa. duk suka amsa yace Abba ina wuni yace lfy lau, babana daga ina ka futo yace naje gidan babane. ka kyauta yaka same su. lfy lau, sunce agaishe ku yace muna amsawa wani kyakyawan yaro ne, ya rugo da gudu ya fada jikinsa yana fadin abba faruk kaga momy zata zaneni ko, ya rungumo shi yana fadi mekayi mata, yace waitace na dameta da surutu. Faruk ya fara fada bawa da bakinsa za'a hana shi magana ne. hjy safyya tace to masu da ai wannan mijin namu bayajin mgn hjy aisha wadda suke kira da momy tace rabo da shi dan allah aishi banzai gane ba in banda yawon bin kasashe me ya sani. shedai faruk ko sauraron su beyiba yanacen ya duka satin yaron yana cemai my son ka kwantar da hkln ka baxan bari ta dakekaba, zo muje dakina bama zaka koma dakin ba bare tace ka dameta.
yaron yace abba faruk idan dady ya dawo be ganiba zaimin bulala. Waye dadyn naka, ya taba ka yagani saina zane shi .yaron ya zaro ido ya ce zaka iya zane shine faruk yace sosai makuwa yaron ya kalkale da dariya yace idan ya dakeni saina kiraka ko. yauwa may son ashe ka gane, toh tashi muje.
nan suka mike yadauke shi suka nufe dakin faruk suko su hjy safyya da Anty amarya suna ta tattaunawa akan shakuwar faruk da yaron itako hjy Aisha wato momy banda hararar faruk ba Abun da take har alhaji ya lora da haka yace Aisha lfy kuwa. lfy lau alhaji meka gani. yace a,a Amman dai ni abinda nakeson kigane kirage nunawa yaron nan halin ko in kola, kirinka janshi ajikin ki. mikiwa tayi tare da fadin alhaji kenan saikace wani dan karami yaro, toh goyashi zanyi ne koko mezan mai, sa annin shifah daga mai yaya 3 sai mai 4.
tayi daki tabar alhaji yana fadi Allah ya shiryeki Aisha sudai su hajiya suna ta darawa.

TUSHEN LABARI


Malam faruku matawale babban malami ne kuma sananne agarin kano yana da matarsa 1 Wanda suke kira da inna sun haifi yara uku dukka ninsu maza ne Ahmad shine babba, sai mai binshi yusuf sai karamin su wato usman kasan cewan malam faruku bai samo karatun boko mai zurfe ba saiya ci alwashin in Allah ya yarda yayan shi zasuyi, dan haka ya jajirce da taimakon mahaifiyar su wacce suke kira inna kuma Allah yacika masu burin su wada dukkan ninsu suna aikin gwamnati yusuf wadda kasance da na 2 acin yayan malam faruku sai ya kasance ya fesu daukaka da tarin dokiya kasan cewan malam faruku malami ne da yasan abinda yake bai nunawa yayan shi ban banciba suka taso da matukar San junan su ayanzun haka alhj ahmad yanada mata 2 da yara 7 shikuma alhj yusuf matan shi 3 yara 6 alhj yusuf shine mahaifin faruk wadda yaci sunan mahaifin su wato malam faruku sai karamin su alhj usman yana da mata 1 da yara 3

gidan alhj yusuf gidane da ya ginu akan tarbiya, yara da manya kowa na girmama kowa hjy safyya itace uwargidan alhj yusuf tana da yara 2 Sulaiman shine babba yana da mata 1 da yara 2 sai hafsat itama tayi aure yaranta 3

hjy aisha itace ta 2 yaran ta 3 faruk shine babba maibin shi aminu shi aminu yayi aure da dan shi 1wannan dalilin yasa mahaifiyar su hjy aisha take matukar jin haushin faruk sabuda yaki yin aure acewarshi shi har yanzon baiga wacce tamai ba duk da yawace yawacen kasashe da yayi adalilin karatun shi ayanzun haka dai ya kammala karatun shi ya zama cikakken soja Aminu kuwa yana zaune da matarsa anan cikin gida mahaifin su haka kuma akwai shakuwa tsakanin faruk da abdallah yaron kaninshi aminu sai karamar su mena yanzu tana shekara17 .

anty amarya ita takasace amaryar alhj yusuf data 1 aliyu tundaga shi bata kara haihuwa ba yana shekara10

faruk tunda ya dauki abdallah suka shiga daki basu suka futo ba saida aka kira sallahn mangariba sannan suka futo lokacin falon bakowa sai meena zaune tana kallo. ke mekike har yanzon kinanan, tashi kije kiyi sallah dan ubanki. afurgece tamike ta nufi daki dan balakin tsoron shi sukeji saboda masifan faruk ko aminu dake binshi be bariba. faruk narike da hannun abdallah suka doshi kofar fita domin zuwa masallaci, nan sukaci karo da aminu yafuto shima zashi masallahci. a'a yaya dama yaron nan yana wajenka ne. eh menene a'a bakomai nadauka yana wajen su momy ne.
ka hanashi zuwa gun sun ne . yaya naga ida yaje saiya wuni yana sasu surutu dama shiyasa nace yana maganar yana sosa keya. dakata aminu kaga daga yau karku sake dukan shi akan surutu, lfy ce da beda lfy da be yiba, kuma kace ma maman shi, nace karta kara dokan shi. yace angama ranka ya dade. da haka suka isa masallaci saida akayi ishai su kadawo bayan sunci abinci sunkare yace toh my son tashi kaje ka kwanta kaga gobe akwai makaranta ko. ni banajin banci fah abba a'a maza katashi karka makara . nandai ya tashi bada sanran shiba yanufi dakin maman shi shiko faruk daga nan falo alhj yawoce haka al adan gidan alhj yusuf take da daddare suna zama hira da iyalan shi yatarar da sunata hirar su suna dariya ya nemi wori ya zauna akasa bayan sun sha hirarsu sai alhj ya waigo gun faruk babana waikai baka sha,awan kayi aure ne? maganar tazowa faruk abazata dan haka ya dirirece yarasa mema zaicewa Abba ne .a da idan zaimai magana makaman cigar wannan baya mai acikin mutane kamar haka.
waibada kai nake magana bane, ko Baka jine? inaji alhj ya hausan kanaji amma kiyimin shiru. furuk ya dukar dakai zanyi ne abba, ka kwantar da hankalin ka . kamar yaya nakwatar da hankalina karka bari fah raina yabaci, nagaji da ganinka ahaka indai Baka da lfy ne kafada anemar ma magani, amma ninafara gajiya da ganinka haka. hjy aisha ce tasa baki ai alhj asamu ko wacece ahada shi da ita .hjy babba tace a'a baza ayi haka ba adai karamai lokaci.
tun yaushe nake samai lokaci, alhj ne yake fadin haka cinkin fada harcewa nayi yaje gidan yaya ahmad yazaba acikin yaran gidan amman ko kala baice minba.tokai faruk meyasa baka jeba? alhj yace ba magana ake maka bane, karka maidamu en iska. yace abbba aibasai najeba nariga ai nasansu. yace au toh waceka zaba acikin su ukun?
ban zaba ba abba. baka zaba ba? alhj ne yayi tambayan ciki bacin rai toh meye dalili ? faruk ya dada dukar dakai yace abba ai sun tsofa. duk falon suka kwashe da dariya banda hjy aisha faruk ya dada kulewa yana ganin ansa shi atsakiyar kannan shi suna mai dariya faruk yace kai kutashi kubar nan. alhj yace baza su tashiba, idan kayi zuciya kayi aure .zuciyar faruk kamar ta faso ta fito dan bakin ciki 🏇🏻
[6:34PM, 11/6/2016] ‪+234 701 419 7556‬: 💞💞ZAKI GANE KURANKI💞💞
2
✍MMN YAZEED
07014197556

Alhj yace toh yanzun me kake nufe, kana nufin sunma tsofa kenan?
yace kuma dai ai da kunsani kunyimusu aure tuntuni, yanzun xfah duk sun wani yamushe.
suka kara kwashewa da dariya bandan aminu da ya wjuyar da kai yana dariya babu sauti dan gudun kar yaya faruk yagan shi meena kuwa tasa kanta acikin hijjabi tana dariya
hjy aisha ce tace kuje ikon Allah wai talle keyiwa audi gori.alhj yace tunda kadawo ai sai ka aurar da dasu.
kai faruk kaji tson Allah yanzo dan wulakanci su Hafsat dinne suka tsofa kana ganin yan mata masu ji da kansu.anty amarya ce ke fadi haka tare da murmushi akan fuskarta.
dan Allah abba kabar maganar su zan nemi wata nan bada dadewa ba kansa aduke.

nagaji da sama lokaci gidan babanku usman ma ai akwai yan mata, kaje cen ka duba .
abba ai duk kalansu daya. toh shike nan amma inason kasini tun ina kebeka yau har nayi maka maganar cikin yan uwanka ka kiyayi ranar da zanma mai gaba daya.
in Allah ya yarda ma haka bazai faruba inji hjy babba.
da haka hirar tasu ta tashi.


bayan kwana biyu faruk tafe cikin shirin shi na zuwa warin aiki yayi sallama dakin momy daga ciki aka amsa yashiga ya zauna ya gaisheta ta amsa ba yabo ba fallasa momy zatafi. adawo lfy tace atakai ce.
momy waike saiki rinka cemin adawo lfy bazakiyi min ardu,a ba.
ai ita nama .
wlh wannan ba ardu,a bane.
toh me kake son nace maka .
cewa zakiyi Allah yatsare ya kuma bada sa,a.
toh Allah ya tsare ya bada sa,a.
ameen ameen,yau bazan dawo da wuriba zan wuce gidan baba.
au ka canza shawara kenan da kuma kace sun tsofa.
a,a niba gunsu zanjeba wajen nura zani. kaidai kasani.

ya juya yatafi yana tunani azuciyar shi waisu dasuka dage sainayi aure saikace natare masu wani abun hard a momy ita da ada ko gaishe ta nayi dakar take amsawa saboda wai kuya ta yayan fari amma ayanzun ta ware har tana min maganar aure, Allah ya hadani da irin matar da ke mafarkin samu na huta da surutu.

wuraran karfe biyar faruk ya baro wurin aiki ya doshi gidan wan mahaifin shi yashiga gidan sai ga hafsat anata karairaya ansa matsatson kaya da dan gyale azuciyar shi yace ji wadda ake tunanin ni zan aure ta Allah ya kyauta
ke zo nan.
takara so atsora ce dan baza ta mance yaya faruk ba,
dan ba imani gareshi ba
ina zaki haka?
zanje bikin kawata ne.
kice zaki fatty.
a,a yaya wlh ba faty zani ba.
ya kai mata duka ni kike karyatawa wuce gida ki canza kaya.
ta wuce tana kuka yabi bayanta

alhaji ahmad yana zaune a falo saiga hafsat tana kuka ke lfy kuwa.
yaya faruk ne ya dakeni wai daga yaganni zanfita yace wai zani faty
bata rufe baki ba saiga faruk yashigo tare da sallama alhj ya amsa masa tare da murmushi maraba da babanmu faruk ya zauna tare da gaishe shi ya amsa ya mutanen gidan naku. lfy lau, baba wadannan yaran baza ayi musu aure bane alhj yayi murmushi yace babana kenan kadai gaji me sunan naka sosai shima jiya da naje harna tashi maganar shi kenan xkuma kaga sunada tsayayyu can ma gidan babanku duk xsuturo mana yaran da suke son aure kuma mungama binkece amma na dakatar da maganan ne dan yusuf yazo min dawata magana, ban saniba ko ya sanar maka? a,a baba wacce magana ce?
wai da yana tunanin ko zayi yar gida.
eh yafada min .
toh wani shawara ka yanke, nasan dai ba kunyata kakeji ba dan bamu fara haka dakaiba kuma banason mufara.
baba yaran ne duk kunbar su sun girma agida. alhj yayi dariya sosai yace inna fahimta kana nufin sunma tsofa,
yayi murmushi irin nasu na manya yace babana kaima fah ka tsofa. furuk yayi dariya yace baba aini namiji ne . toh kodai yar secondary zamu samo maka? dai dai nan nura ya futo yana fadin kai dan rainin wayo ne tundazon nake jiranka. nura yaron alhj ahmad ne shine na 3 yayyin shi guda buyu mata ne suyi aure sai sai mai binshi salisu da kannan su mata su uku shima nura yayi aure yaran shi 2 yana zaune agidan mahaifin shi kafin ya karasa ginin shi ya tare furuk da nura tare suka taso kowa yasan sirri kowa basa boyewa juna komai. alhj yace yauwa nura zo ka zauna.bayan nura ya zauna. dama akwai tam bayan da zanma.
toh baba yafada tare da gyara zama. wai wace irin mata zaku aure ne ?
nura ya fahimci inda alhj yasa gaba.

yayi dariya ya dukar da kai yana dan sosa keya abba wai da muna neman wadda zamu karashe rainon ta ne, ko yar secondary ce.
toh toh na fahimta kuma kana da gaskiya babana,amma abinda nake so dakai karku ja mana lokaci kaga su hafsat suna da tsayayyu baza asa lokaci mai tsowo ba kuma baza atabayi baka ba rana daya za ayi, dan na fahimci kasa wasa a al amarin ka.
nura ne yayi magana baba insha Allahu wannan karo ba wasa. toh ai muna son haka, baba yanzun ina zaku, faruk ne ya dago kanshi domin tunda nura ya fara wa alhj magana faruk ya dukar da kanshi . dama cen gida zamu .
toh adawa lfy
suna fita faruk yafara hararar nura suka nufi motar faruk bayan sun hau titi nura ya waigo yaga faruk sai shan kamshi yake yace gafara malam dan kasamu na rufa ma asiri kake fushi.
ai da nagaya maka ra,ayi na bance kagaya ma baba.
aida kasani ka kar yata ni kawai agaban shi kace karya nakeyi, kaga sai subaka wacce suka ga dama komai tsofan ta.
faruk ya waigo ya kalle nura fuskar shi da murmushi toh saime, ina ruwanka,
kaini nama samu matar da zan aura.
karya kake wlh,kai zaka iya tunkaran budurwa kace kana so.
lallai nura ka raina min wayau, ko nakaika kaganta? eh kakaini makaryacin banza kawai .
toh shikenan bari mujuya,zanga waye makaryaci ni ko kai nan faruk ya dauke hanya nura dai nabinshi da ido.
yaga ya shiga layin gidan kakannin su.
anan kasamu matar ? eh yace atakaice ya faka motar akofar gidan malam faruku suka futo.
nura ya waiga ya kalli faru dake raraba ido yana neman dan aike.yayi murmueshi yace idan baka da number ta aikeni nakira maka ita mana.
a,a yace tare da kiran wani almajir
shiga nan gidan gidan kace ana sallama da inna. nura yayi dariya yace wlh faruk kai dan iskane🏇🏻
[6:34PM, 11/6/2016] ‪+234 701 419 7556‬: 💞💞ZAKI GANE KURANKI💞💞
3
✍MMN YAZEED

Lokacin da yaron yashiga gidan inna na zaune atsakar gida akan kujera yar tsugune .alhj usman da yazo kawo ma iyayen shi ziyara yana zaune akan tabarma suna ta hirar su saiga yaro yayi sallama inna ta amsa .yaron yace...


Read / Download ZAKI GANE KURANKI

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album