Join Our WhatsApp Group

COLONEL UBAIDULLAH Complete Hausa Novel Document by COLONEL UBAIDULLAH


COLONEL UBAIDULLAH

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 79005



COLONEL UBAIDULLAH

Reading Time: 6 Hours

Added On: 27, Nov 2023

Author: Zahra Abdul ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : 08165550116

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 434.19 kb

File Type: txt

Views: 781+

Download: 894+

Last download: 8 hours ago

Description/Story: [8/19, 10:54 AM] Zarahh: 👮🏻 *COLONEL UBAIDULLAH*👮🏻
( _the story about a young gentle man_)



*ᏚᎢᎾᎡY ᏔᎡᏆᎢᎢᎬN ᏴY*✍🏻


*Z͢A͢H͢R͢A͢ A͢B͢D͢U͢L͢* (ᴹᴼᴹᵞᴺ ᴬᴴᴸᴬᴺ)


( *y̾a̾r̾ s̾a̾r̾a̾r̾i̾n̾ k̾a̾i̾n̾u̾w̾a̾*)
👸🏻 *SAHIBAR KAINUWA*👸🏻

_dedicated to my brother_

*U̶B̶A̶I̶D̶U̶L̶L̶A̶H̶I̶*

_my wattpab_@Fateemah0

_QAUNAR KU DABAN YAKE_
*ANTY HAUWA MMN USWAD*
*&*
*ANTY FAUZAN YAR AMANAR KAINUWA*
_ALLAH YA RAYA ZURIA MY ANTY'S_💘
____________________
_Alhamdulillah ina qara godewa Allah a ko da yaushe salati da daukaka da tsira da aminci su qara tabbata ga shugabanmu Annabi muhammad S,A,W da iyalan gidansa da sahabban sa da ma goya baya har izuwa ranar sakamako_🤲🏻
__________________
Ya Allah kabani ikon farawa lpy na kuma gama lpy🤲🏻

*بسم الله الرحمن الرحيم*
*____________________________________*


*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*____________________________________*

*page°°°1&2*



*9JA,BARRACKS ABUJA*

Tsaye yake daga shi sai 3quarter mai ratsin tambarin sojoji a jiki, sai farar T-shart and p-cap shi ma na sojoji.

Dogo ne amma baza kace masa dogo sosai ba ,yana da ɗan fadin fuska daidai wa daida ,sannan baza kace masa fari ba, za dai ka iya saka shi a layin chocolate color
Yana da gashin baki wanda ya kewaye masa baki wanda hakan ba ƙaramin kyau ya qara masa ba, duk da idonsa sanye yake da black shadow,but yana da ƙananan ido kmr na yan'chinese , yana da faɗaɗɗan ƙirji irin na gwarazan maza jarumai saɗaukai.

Duk ya zuba hannayen sa a aljihu, yana tsaye fuskar sa babu alamun fara'a domin shi ko da smiling ne bai cika yiba infact baya ma yi balle kuma dariya bcox baya daukar raini a *barracks*, bama iyakar barracks ba ,a koma ina ne baya daukar raini, duk da sojoji ne amma da yawan ana shakkar sa.

Iska ne ke ƙadawa awajan domin a garden din barracks din yake tsaye.

Bakin sa ne ke moving ahankali saika Lura da kyau kafin ka fahimce ashe waya yakeyi but da airpieces a kunnan sa.

Bisa alama kuma da mahaifiyarsa yake wayar domin yadda yake wayar cike da natsuwa.

Mama tace.

"*UBAIDULLAH* ina fatan dai komai lafiya?"

Sai da ya numfasa ya hura iska kafin ya ce

" eh mama lafiya lau fatan kuma kuna nan lafiya? Ina su sister's ?"

Mama tace.

" lafiyarmu lau hafiza ta je gidan yayarku ummu,na aiketa ,ita kuma na'ila wai taje karban aron littafi agidan su kawarta."

"Mtsww!!! wlh mama na'ila bata jin magana at oll,na hanata zuwa yawo amma bataji, wani irin littafi da rana haka?"

Mama tace.

" indai na'ila ce sai dai mu dinga taya ta da adduah Allah ubangiji ya shiryeta."

Ya amsa da ameen
Hira suke dan tabawa na tsakanin uwa da ɗanta.

mama tace.

"Ubaidullah yaushe zaka zo ka gan mu ne kam munyi, kewarka sosai wlh."

" Karki damu mama zanzo a next week weekend In sha Allah."

mama tace.

" Allah ya kaimu" suka ci gaba da hira,
Ji yayi anyi hugging dinsa ta baya azafafe ya juyo domin yaji kamshin turarenta
Kashe wayar yayi yana cewa I will call u back mama luv you!!

Sa ke fuskantar ta yayi yana tamke fuska , ita kuma tana murmushi sanye take da kakin sojoji itama sai murmushi take masa, tasa hannu zata shafi fuskarsa ya buge hannun, sannan ahankali ya bude mouth dinsa lyk mai koyan mgn yace.

"waike *RUMAISA* how many times zan fada miki ki dai na haɗa jikin ki da nawa?"

Smiling tayi tace.

" first lieutenant Ubaidullah I will never tried to say I love u duk fadin barracks din nan oll ladies din DA suke rububin suna sonka karya su keyi! ni ce masoyiyar ka Wanda nake maka true love, plss I beg u Ubaidullah ka so ni ko da kaɗan ne "

ta ƙarasa tana so ta shige jikinsa ya bankaɗe ta ya wuce yana jan dogon tsaki ,rumaisa kuma tayi kwafa ta juya domin indai wannan wulaƙancin Ubaidullah din nan ta saba shan sa.

Ahanya kafin ya isa dakinsa ya hadu da close friend dinsa infact garinsu daya tare suka taso burinsu ɗaya arean su ma ɗaya.

*ZAIDU* yace.

" Ubaidullah tun dazu nake neman ka ban ganka ba ina ka shiga?"

A kasalance yace.

" ina garden barrack ne menene?.

" No dama stall sergeant David ne yazo neman ka akan mgnr meeting din da za a gudanar anjima a babbar filin taro na *murtala barracks* shine lieutenant general yace. A fada maka kai da commander Ku shirya domin taron ma yana da nasaba da mu dan gsky naji ƙishin ƙishin akan cewa zabe za ayi domin tura jama'ai izuwa bordern Niger domin kama yan'ta'adda."

"To kai Zaidu a bakin wa kaji ?"

"Na dai fara ji a bakin sergeant first class A,M kasan halinsa maybe shima ji yayi."

Ubaidullah yace .

"ok amma K,B yasan da mgnr ?.

Zaidu yace.

" eh dazu ma mun hadu dashi na fada masa kaine kawai baka sani ba."

Ba tare yayi mgn ba ya jinjina kai kawai.

Duk inda ya gitta sai an kallesa amma ya tsare gida dan Ubaidullahi akwai tsare gida, su na tafiya suna dan taba hira har suka isa part dinsu.

Suna shiga parlour suka sa mu Raihana kwance a 3seter sanye take da wandon sojoji da black T-shart kanta ko p-cap din ma babu, balle kuma dan kwalli ko veil"

Ubaidullah yayi tsaki yace.

" ke kuma fa? oya tashi ki fita kafin raina yabaci ya fada yana mata nuni da kofar waje."

ahankali Raihana ta miƙe tana taku harta zo daf dashi domin numfashin su har yana sarkewa waje daya tace.

" i will,but ina so kasani wlh wlh bazan taba barin ka ba Ubaidullah, ta juya ta fice."

Zaidu ya kwashe da dry yace.

" wlh ladies din yanzu duk sun gama kwarkwancewa kalli fa yadda suke rushing akan ka?"

Tsaki Ubaidullah yayi ya shige bathroom domin yayi fresh'up.


Bayan ya fito ya shirya, ya ɗauki doguwar jallabiyya ya saka,
yadan kwanta.

Ya lumshe ido yana tuno rayuwar baya , haƙiƙa yanzu komai yana so ya zamo masa tarihi,sai kuma babban burin sa, na gaba.

Bacci ma yake ji amma bazai iyaba dan haka ya tashi zaune.

Kallon sa.

" Zaidu yayi,lafiya kuwa Ubaidullah?.

"Mtsww wlh Zaidu ina yawan tuno baya ne."

"Bai kamata ka dinga tuna baya ba Ubaidullah,ka fuskanci gaba kawai,a rayuwar ka komai ya wuce, tunda a karshe Allah ya cika maka burin ka na zama jami'in soja, wanda kuma ake alfahari dashi."

Numfasawa yayi.

" Zaidu kasan ina da buri sosai a rayuwa ta, but bana so na dawo dasu mama barracks din nan,cox ka kalli abinda ladies ke min mama ba za ta ji dadi ba, ba ma zata jure ba."

"Haka ne kuma ,to amma ya zakayi?"

"Abinda nima ban gama yanke shawara ba kenan."

Tattaunawa suka cigaba dayi.

K,B ne yayi sallama ya shigo da sauri har yana tuntube,
Zaidu yace lafiya kuwa K,B?

"Ina kuwa lafiya, ga Raihana da Zeey can su na dambe wlh ina tausayawa Raihana dan babu abun da zata ɗauka, a jikin Zeey, yarinyar da ko wasu mazan tsoronta sukeyi, balle kuma Raihana."

Dryn mugunta Zaidu ya hauyi, yace.

"Ubaidullah tashi muje mu gani,kai Zeey bata da hakuri,am sure Raihana ce bata da gaskiya, cewar Zaidu."

Duba agogon sa Ubaidullah yayi,yaga har to 4, yace.

" i don't have time for this stupid ladies, Ku shirya mu tafi meeting."

Shiryawa sukayi cikin kakin su na sojoji ,suka fito su na taku a hankali, wanda na Ubaidullah ya sha banban da nasu.

Commander suka sa mu sannan suka ɗun guma *murtala barracks*.


•••••••••••••••••••


Duk inda ka wulla idon ka baza ka iya banbance waye da waye awajan ba.

Sojoji ne birjik ta ko ina da ina.

Nan aka nemi da a buɗe, taro da adduah ,major usman shine wanda ya buɗewa musulmai nasu,sai major jonh shine ya buɗewa christian nasu,
Kafin, aka fara gabatar da meeting.

yayin da major general yake jawabi cikin harshen turanci, akan jaruman da barracks ke ji dasu za a tura ,amma kafin nan za,ayi ƙarin girma ga wa'inda suka je yaƙin maiduguri,
Lieutenant general ne ya karbi jawabin daga hannun major general ya ɗora,da nasa akai.

Mutum na farko daya lashe takwabin girma mai tambari shine...!!ehem ehem! *first lieutenant Ubaidullah* wanda a yanzu zai karbi matsayin, *CAPTAIN UBAIDULLAH*,nan jami'ai, aka hau tafa masa ji kake rab! rab! bayan anyi wa Ubaidullah ƙarin girma, shima Zaidu matsayin captain aka bashi, K,B kuma a tym din aka basa ,matsayin first lieutenant ,daga nan aka cigaba da rabon muƙamai.

Ba a watse ba kuwa, sai da aka kira sallar magriba tukunna musulmai sukayi masallaci sai da suka idar, yan'9ja barracks suka koma.

A gajiye suka shiga part dinsu.

" Zaidu yace oh Allah ƙarin girma babu gayyata sai dai kawai gayyar sojoji? ai da an bari iyayen mu da yan uwanmu sunzo kafin ayi mana ko dan bamu da mata ne? Ko kuma,mu bamu kawo iyalan mu barracks ba?"

K,B ya kwashe da dry yace "Zaidu kenan yanzu kai a tunanin ka, ka kai aure ?"
" ai abun ne yazo ba shiri shiyasa kuma kaga nan da wata daya ne zamu tafi border gashi naji major general yace gobe zamu fara sabon training,amma kusan Allah commander victor bai so wannan ƙarin girma da a kayi ba, daka kalli kwayar idonsa zaka hango baƙin ciki da hassada ƙarara."

"Wlh K,B ka kiyaye ni! Cewar Zaidu, ni zaka kalla kace ban isa aure ba?" Wani dry Ubaidullah ya kwashe dashi,sai da suka dan tsorata su na kallon sa.

"Ubaidullah wannan dry haka?" cewar Zaidu.

K,B yace "ina kuwa lafiya mutum sai kace mai iskokai."

"No wlh hirar taku ce ta ban dry ,kunsan ai ni dry bata cikin manner dina "

Zaidu yace "dama kai kam dryr ka ,sai dai kana gida,ko kuma kana tare damu."

"But nifa wlh hassadar commander victor bai dame ni ba,tunda hassada a barracks ba yau farau ba,and bazai zama karshe ba, so just 4get about this matter,mu fuskanci yin gaban kanmu dan yanzu mun sake zama manya, captain ai ba wasa ba,muna tafiya yaran mu su na bin mu a baya."


Ubaidullah yace "b4 mu tafi i need to go home,I want to see my momma and my lovely sister's."

Zaidu yace " ok when are u going?"
A takaice Ubaidullah yace, "next week In'sha Allah."

"When did u come back?"
Sai da ya ɗauki som minute kafin yace "5days."

Zaidu yace " zan bika mu tafi tare sai mu dawo, but kasan fa, sai mun samu permission daga wajan, *GENERAL OF THE ARMY*."


Ubaidullah yace

"eh nasani."

K,B ne yace.

" kenan ni kadai zaku barni?"

"Hahaha my guy kaima ka shirya kawai kaje ganin gida,amma seriously da mun dawo aure nake so wlh."

Girgiza kai Ubaidullah yayi, yace mayan aure kawai,ku tashi muje sallah, tashi sukayi suka fito atare,sukayi hanyar ma sallaci



*WANENE UBAIDULLAH*?
×××××××××××××



Sharhin ku ne zai sa mu cigaba ko mu dakata......!!!! Domin fahimtar littafin ya muku ko bai muku ba



COMMENTS
&
SHARE


BY MOMYN AHLAN✍🏻
[8/19, 10:56 AM] Zarahh: *COLONEL UBAIDULLAH*
( _the story about a young gentle man_)



*ᏚᎢᎾᎡY ᏔᎡᏆᎢᎢᎬN ᏴY*✍🏻


*Z͢A͢H͢R͢A͢ A͢B͢D͢U͢L͢* (ᴹᴼᴹᵞᴺ ᴬᴴᴸᴬᴺ)


( *y̾a̾r̾ s̾a̾r̾a̾r̾i̾n̾ k̾a̾i̾n̾u̾w̾a̾*)
👸🏻 *SAHIBAR KAINUWA*👸🏻

_dedicated to my brother_

*U̶B̶A̶I̶D̶U̶L̶L̶A̶H̶I̶*

_my wattpab_@Fateemah0

_QAUNAR KU DABAN YAKE_
*ANTY HAUWA MMN USWAD*
*&*
*ANTY FAUZAN YAR AMANAR KAINUWA*
_ALLAH YA RAYA ZURIA MY ANTY'S_💘
____________________
_Alhamdulillah! ina qara godewa Allah a ko da yaushe, salati da daukaka da tsira da aminci su qara tabbata ga shugabanmu Annabi muhammad S,A,W, da iyalan gidansa da sahabban sa, da ma goya baya har izuwa ranar sakamako._🤲🏻
__________________
Ya Allah kabani ikon gamawa lpy.🤲🏻

*بسم الله الرحمن الرحيم*
*____________________________________*


*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*____________________________________*

*page°°°°3&4*


*UBAIDULLAH ABDULLAHI GALADIMA.*
Shine asalin cikakken sunansa, haifaffen garin Bauchi ne, ya kasance maraya Mahaifinsa tsohon Soja ne."

Ubaidullah tun yana yaro yake sha'awan aikin soja, sakamakon ganin yanda mahaifinsa yake ɗebi ba ɗaɗi da yan ta'adda.


Su hudu ne rak awajan Mama mahaifiyarsu, Ubaidullah shi ka
ɗai ne namiji, shi ne na biyu, Anty Ummu ita ce babba, sai ,Ubaidullah,Hafiza,Na'ila.

"Tun Ubaidullah yana da shekara goma a duniya Allah yayiwa mahaifinsu rasuwa, a wani yaƙin garin jos da a kayi, aka kashe mahaifinsu, sunyi kukan rashi a lokacin da aka shigo musu da gawar Baba, wanda a lokacin yake riƙe da matsayin commander na sojoji, Baba ya taka muƙamai da dama a aikin soja, bayan rasuwar Baba komai ya dagule musu, domin a lokacin sun ga jarabawan rayuwa.


Abinci ma gagararsu yake yi, Mama tayi kuka harta godewa Allah, a lokacin kuma su hafiza su na yara, dan Hafiza shekararta biyar Na'ila kuma tana da shekara hudu, Ummu kuma tana da shekara goma sha takwas. Dan tsakanin Ubaidullah da Ummu ratan shekara takwas ne, Ubaidullah kuma yana bawa Hafiza shekara biyar harda rabi,
tsakanin Hafiza da Na'ila kuma ratan shekara daya ne, shiyasa suka taso kansu daya.


Sun sha matukar wahala kafin Mama data ga zaman ba zai yuwu ba, ta koma toya kosai a bakin kofar gida, domin a cikin dangin Ubansu Ubaidullah babu mai taimaka musu, a lokacin da Baba yake raye kuma kullum zaka gansu sunzo suna bin su, su na jan su a jiki kamar da gaske, amma tun da ƙasa ya rufewa baba ido shikenan suka ɗauke kafarsu, babu wanda ya sake tako kafarsa izuwa cikin gidan balle ya kawo musu ko da ƙwayar marasa ce.


Mama tasha wuya ba ka ɗan ba wajan kula da yaranta, Ubaidullah ganin burinsa bazai cika bane ya sa shi zuwa wajan ƙanin mahaifinsa domin ya taimaka masa, amma abun mamaki sai ya koreshi, Ubaidullah yana da matuƙar zuciya tun a lokacin yaci Alwashi akan burinsa, sannan ko zasu mutu bazai sake taka kafarsa ba izuwa wajan dangin mahaifinsa ba.


Da wannan Alwashin Ubaidullah ya ba zama neman aiki, yana ɗan shekara goma a lokacin amma ba labari, dan haka ya fara aikin cire yashi sai ya siyar, da haka ya koma makaranta, a wajen ne kuma suka hadu da amininsa Zaidu.


Ya na da shekara goma shabiyu ya koma aikin karfi wato buga block, tun Ubaidullah yana ƙarami amma ɗamtsensa duk sun fito sakamakon aikin karfin da yake yi.


Rayuwa kenan har Ubaidullah ya zo ya hana Mama toya Kosai, har ya fara biyawa ƙannansa kudin makaranta, ya biya nasa ya biya nasu.


A lokacin da aka tashi bikin Anty Ummu, Mama tayi kuka kamar ranta zai fita, saboda ba kudin da zata yiwa 'yarta kayan ɗaki, inda a karshe Mama taci bashin kudi har dubu ishirin awajan wata mata, ashe kudin nan zai zama tashin hankali.


Bayan biki mata ta dinga rashin kirki wa Mama tana gaya mata baƙaƙen maganganu, ran Ubaidullah ya baci dan ya tsani abun da zai batawa mahaifiyarsa rai, dan tun bayan rayuwar Baba Mama ta kamu da cutar hawan jini.


Kudinsa daya tara zai biya kudin makaranta ya ɗauka ya bayar,dan bazai jure ganin hakan ba.


"Ubaidullah yana da shekara sha biyar a lokacin kuma yana ɗan zuwa training jikinsa duk ya murɗe, wata ranar laraba suka buga ma wani babban mutum block sannan suka masa aiki, nan ya mai dasu kamar yaransa, sosai...


Read / Download COLONEL UBAIDULLAH

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

1 Comments On COLONEL UBAIDULLAH
avatar
zainab-hassan

4 months ago

Reply

????

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album