Join Our WhatsApp Group

ZUCIYATACE Complete Hausa Novel Document by ZUCIYATACE


ZUCIYATACE

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 46679ZUCIYATACE

Reading Time: 3 Hours

Added On: 21, May 2023

Author: Amina Umar Farouq ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 298.36 kb

File Type: txt

Views: 1079+

Download: 771+

Last download: 2 days ago

Description/Story: COMPILED N COPY BY
ESHAAT SMILER HOM OF HAUSA NOVLES DOCUMNTS
WASAPP 08066360176 FOR MORE馃挊馃洭馃洭馃洭馃挊
馃挊馃洭 馃洭 馃挊
馃挊馃洭馃挊
馃挊
馃挊 ZUCIYATA CE馃挊

_Besad on true life story_

馃挊
馃挊馃洭馃挊
馃挊馃洭馃洭馃挊
馃挊馃洭馃洭馃洭馃挊

(Labarin Sarkakkiyar Soyayya)


1鈨�


WRITTEN BY

馃挊AMEENAT馃挊 UMAR FARUQ馃挊
OR 馃挊(MEENAT)馃挊*GODIYA*

*Godiya ta tabbata ga Allah ubangijin Halitta daya bani ikon rubuta wannan littafi tsirada Amincin Allah su tabbata ga Shugaban mu* *Annabi Muhammad (S.A.W) da iyalan gidansa da Sahabbansa da* *wayanda sukabashi*
*Gaskiya harzuwa Ranan Alkiyama Amin*


*SADAUKARWA*

*Nasadaukar Da wannan page ga Aunty Na Adama* *datarigamu gidan gaskiya Ina rokon Allah yajikanta da Rahma yasa* *Aljannar Fiddausi ne makomarta tareda yan'uwan musulmai gaba daya Amin*.


*DOMIN KU*

*Iyayena Abun Alfahari Na Addu'a ta agareku bazata taba karewa ba har sai Ranan Dana bar numfashi fata Allah yasa kucikada* *IMANI AMEEN YA RABBI.**SHIMFIDA*

*Wannan littafin kagaggen labairne bawai yafaru da gaskiya bane nayisane don* *fadakarwa dakuma nishadan tarwa saidai labarine dayake dauke da abubuwan dake* *faruwa a wannan zamanin namu soyayya, cin Amana, San zuciya, yaudara da kuma ha'inci* *kudai kubiyoni kusha Labari acikin ZUCIYA TACE!!!!*


*Wannan littafin bawai nayisa bane don cin zarafin wani kowata Ko kuma wasu duk Wanda yaga suna ko hali yazo dai dai danasa toh bada shi ake ba*.


*Banyarda A yachanza min labarina tawata siga batareda izibi naba yin haka babban kuskure ne sai a kula*.


-----------------------------------------
*庐PEN WRITERS ASSOCIATION*

*PEN: THE STRONGEST WEAPON*
-----------------------------------------


*only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers*鉁嶐煆�


_*Bissimillahirra hamanirrahim*_


Keh! Keh!! Ke!!! Waiba zakufito kutafiba sai kun makara ko? daga can bangaren naji ance na'am "inna gamu nan fitowa,

Wata yar matashiyar budurwar ce
Tafito yar kimani shekara goma shabiyar,wani yaro na biye da ita dan kimani shekara goma jikinta sanye da rigada wando masu ruwan anta hannun ta dauke da qur'ani mai girma tareda wasu littafai da kuma hijab shima mai ruwan anta ga dukkan alamu makarantan islamiyya zasu tafi,

Sai dai kallo daya zakaima uniform din kagane yasha jikin (wato yatsufa) saboda yanda yafara barin asalin kalarsa Na dark marrow yafara komawa light marrow saboda tsabar tsufan dayai, saidai kasan cewar yana hannun mai tsafta toh" akoda yaushe awanke yake kuma agoge, toh" ko" yanzuma uniform din wankanke ne tas yaci Karin guga sai walkiya yake,

Tsaye tayi abakin kofar dakin tana gunguni fadin cewa wai haka kawai baza akira mutum da sunan saba sai aitakiran Mutum wai keh! keh!! sai kace keke tadanyi kwaf, tana kokarin tasaka hijab din amma kuma sai tafasa sakama kom dariyar da wannan yaron yakeyi mata da alama kaninta ne domin kuwa kamarsu guda dashi shima yana sanye da uniform din irin Nata Riga da wondo da hula,

Harara ta watsa masa tace Sajeed Allah zan'mareka Ina wasa dakai ne wai?

Yace sorry Aunty *SAJEEDAH* Na bari,

Tadanyi tsaki mtsww tareda da kokarin saka hijab din,

Nikam
ganin haka yasa naisauri nakare mata kallo itadai bafara bace kuma ba baka ba saida kalarta irin kalar nan ce mai tsada wacce acikin mutane Dari dakyar kasamu daya wato chocolate colour,

itadai ba kyakkyawa bace saidai kuma baza'a kirata mummuna ba, tanada hancinta Dan dai dai Shiba dogo ba kuma bagajere ba, dan bakinta Dan karami idonta fari kalkal kamar Na chaina amma bamai can ciki din nanba, tanada tsawo kadan, san nan kuma tanada tarin sumam Kai mai yawa Wanda bata masa shanpoo haka nan jikinta duk gargasan sumane Wanda yake kwance luf-luf ajikinta gaskiya *SAJEEDAH* tanada tsari mai ban sha'awa kasan cewar ta kirar coca colar,

Tanada hips sosai da boobs hmmm saidai ace tubara kalla Masha'Allah, adai dai lokacin da tasaka hijab din *SAJEEDAH* kenan,

Diya ga "Malam "Abubakar da "Inna saratu su biyu ne a gurin iyayansu itada kaninta Sajeed Dan shekara goma saboda akwai tazar shekara biyar tsakani *SAJEEDAH* da Sajeed, asali Malam "Abubakar mutumin Nijarne kuma marayane gaba dabaya ma'ana ba uwa ba ubah iyayansa duk sun rasu sai yan'uba dasuka sashi gaba saboda haka sai ya barmasu kasaar yadawo Minna dazama,

Yana dan buga-bugan sana'arsa ahaka Allah ya hadasa da saratu ya aure ta Allah ya azirtasu da yara biyu Sajeedah DA Sajeed agaskiya iyayan *SAJEEDAH* talakawa ne futuk zaka fahimci hakane daga yanayin tufafinsu dakuma mahallin dasuke zaune,

"Su *SAJEEDAH* suna zaune ne A
Wani kango gida da aka zagaye sa da fallan kwano yana dauke da dakuna biyu da'akayi gininsu da bulon kasa babu fulaster ballan tana fanti kofar dakunan duk basuda marfi sai bayi wato (toilet)guda daya Wanda yake shima anzagaye sane da fallan kwano Wanda idan kashiga ka mike tsaye toh" tabbas wanda yake waje zaya ganka,

Suna zaune ne a unguwar tunga dake garin Minna *"SAJEEDAH* datai makon Allah dana sana'arda mahaifinta yake nasaida kayan miya anan yar kasuwar maje, ada amma yanzu yabari saboda rashin ciniki da baya samu yanzu haka Dan tebur ya'aje akofar gida yana saidai kayan tireda, tayi primary school dinta dake nan Cikin tunga takuma yi junior (waec) dinta yanzu haka tana zaune agida bataje gababa wato bataje S.S one ba saboda rashin kudi,
kuma burinta shine taje school of Nursing ne saidai rashin kudi zai mata chikas,

A Kulum Addu'an Malam "Abubakar mahaifin ta shine Allah yabashi ikon cikama *"SAJEEDAH* burinta nason zama Malamar asibiti,

Saboda haka islamiyya kawai take zuwa yanzu Wanda dama tadade da sauke Al'Qur'ani mai girma yanzu kuma tanayin hadda ne saboda *SAJEEDAH* akwai brain
Kota'ina tana kawo wuta sos脿i Arabic da Boko,
Shima Sajeed yanada kokari yanzu haka yana primary five a islamiyya kuma izifinsa ashirin, *SAJEEDAH* da Sajeed akwai shakuwa tsakanin su saboda haka nema suke matukar kaunar junansu,

*SAJEEDAH* takasace natsartsir yarinya ga Ladabi DA biyayya tanada matukar kunya da kamun Kai tanada son ibada(da'alama taci sunan ta),gatada shuru-shuru sannan tanada sanyi murya kuma akwaita da hakuri sosai kamar damo take saboda hakuri saidai kam idan tai fushi Hmmm batajin lallashi wasan dadi toh"dama ance mai hakuri bai'iya fushi ba, Sajeed kusan halinsu guda da kaninta Sajeedah guri kandan ne sukasha ban-ban,kasan cewar shi yanada surutu gakuma Neman tsokana,

*SAJEEDAH* tanajin Haushin Keh! din da innar su ke kiran ta dashi, don haka sai tai ta gunguni shikuma Sajeed sai yaita mata dariya,

(Nima dai kam cewa nai toh" Sajeedah ai saikiyi hakuri tunda kin kasan ce yar Fari kuma da alama lnna Saratu tana cikin mutanan Dan Lol)

"Malam Abubakar yanada wani Mako'ci bafillace mai suna "Alhaji Siddi mugun mai kudi saidai kuma mugun zumbuli ne(wato kakan marowa ta) bayason talaka ko" kadan kudi garesa kamarsu kashesa Amma baya tai makon talakawa, hattada mako'cinsa baya tai maka masa (Abu guda yazama masa dole wato zakka ko shima Da kyar yake badawa) yanada mata biyu suma dukkansu Fulani ne yanada yara biyar mata hudu namiji daya,

Uwargidansa mai suna "Hajiya Harira (suna kiranta Mama) takasan ce mace mai hakuri kuma bata kyamar talaka tanada yara biyu duka mata "Maryam da "Balkisu,

Sai "Amarya Hajiya Hajara ita kam halinta irin Na mijinta ne wato rowa Da kyamar talaka tanada yara uku mata biyu namiji daya Sadeeqah ce babban adakin ("Momi kamar yanda suke kiranta ) sannan "Suwaiba sai namiji mai suna Maniru Amma sai suna kirasa Kiroh,

Aunty Maryam da Aunty Balkisu Dukkansu suna karatune a nan C.O.E Minna

Ita kuma *SADEEQAH* tana S.S one Suwaiba kuma tana J.S.S two shikuma Kiroh yana J.S.S one dukkansu awata tsadaddiyar private school suke karatun mai suna Nuhu Raizin tundaga primary har yanzu dasuke secondary din saidai ita Sadeeqah datayi junior (weac) sai aka maida ita wata body school dake Abuja yanzu hakama tana can school din,

Gidan Alhaji Siddi kam babu tarbiyya ko kadan toh" dama dama ma dakin Hajiya Harira Amma dakin "Momi kam sai a slow, wannan kenan,

*SAJEEDAH*
Kawarta guda tak! wato Sadeeqah toh" dama sa'anin junane jininsu ya hadu sosai da *SADEEQAH* suna matukar kaunar junansu kawance nasu tunsuna kanana Wanda Anyi Anyi *SADEEQAH* tarabuda "Sajeedah anyi fada Amma ina taki rabuwa da ita,
*SADEEQAH* tasha dauko abincita daga gidansu takawo gidansu sajeedah suci idan kuma aka bata kudin makaranta sai tadiba taba *SAJEEDAH*
Ansha dukanta akan labari Amma bata Bari ba.

Wanda *SAJEEDAH* tasan da haka tunda itama anshayi mata gargadi,Momi tasha murderwa *SAJEEDAH* kunne akan tarabu mata DA yarta Amma Ina hakan baiyuyuba Toh" kaunace daga Allah,

Shiyasa *SAJEEDAH* takema *SADEEQAH* wani irin So Naban mamaki badan komai ba saidai Kaunar da tanuna mata bata kyamace taba kasan cewar ta yar talakawa futuk, don haka take kaunar ta tsakani Da Allah wani lokaci ma sai kaga kamar *SAJEEDAH* tana tsoron Sadeeqah, saidai abun bahaka bane yanayita ne kawai Na shuru shuru.

Wani abun mamaki kuma shine duk wannan kawance da kaunar juna dasuke halinsu badaya ba,
*SADEEQAH* takance mara kamun kai gata batada kunya gata yar wankan swaga don harda fati take zuwa tanada wasu kawaye daban yayan masu kudi ga yangan tsiya kodan taga tanada kyaune oho?

Lallai kam "itadin kyakkyawa ce ta bugawa ajarida farace sosai saidai kam batada tsari ko kadan domin kuwa ta tafine kamar one, gakuma son karya (nikam nace toh" aiba matsala tunda sunada abun karyan wato kudi) ga wani halida takeda shi Wanda sam *SAJEEDAH* batasan tanada shiba Wato bin maza(wa' iyazubiIlah)

Abunda *SAJEEDAH* ma bata saniba shine Sadeeqah tun tana J.s.s two akazu barmata da Cikin yanzu ma dataje school Abuja idonta yakara budewa (Ayya toh" Allah ya shiryamu shirin Addini Islam Amin )
Wannan kenan.

Cikin hade fuska *SAJEEDAH* ta kalli Sajeed tace Toh" ai sai mutafi ko?
Yai fuskar tausayi tareda kallon "lnna datake juya koko abokitin fanti karami, ya hadiye yawu yace don Allah Aunty *JEEDAH* mu tsaya musha kinji? ( haka yake kiranta wani lokaci ko yace Aunty Sajeeh ita kuma tace masa Junior Jeed )

Ta harare shi tace toh" sannu acici salon mu makara koh?

Inna tace makara ta yaushe kuma? Ai tunda nariga nadama kawai Ku tsaya kusha, kinsan shi ba'irinki bane dakike zama dayinwa tana magana ne tana zuba masu koko.

A hankali take shan kunun kamar bataso Inna tana kula "da'ita shikam Sajeed sai sha yake ba abinda yada mesa, haushi duk ya kashe Inna saboda haka sai ta tabe baki tace "ke kam Allah ya yaye maki wannan rashin son cin abinci,

Murmushi *SADEEJAH*tayi wanda yasa na zaro ido saboda hango beauty point agefen kumatun ta daya (nace hamm Ashe dai *SAJEEDAH* nan ta Tara abubuwa masu kayatar wane a jikinta) sunkuyar dakai kasa tai batare datake komai ba,
Banya sun gama shan kunun sannan suka tafi islamiyya.

**************
Yau asabar kuma a yaune akesa ran saukar alhazan Niger zasu sauka saboda haka
Filin jirgin saman dake Karin Minna yacika makil da jama'a kowa ka kalli fuskasa cike da farin Cikin yau zaiga dan'uwansa,
Toh" already dama anfada masu jirgi ya kusan sauka saboda haka kowa ya zama cikic shirin tarban dan'uwansa,

Fadar haka baifi da 30 mints ba Cikin kudirar Ubangiji saiga jirgin yasauka Lafiya, jirgi ya kusa kai 30 mints sannan A hankali Alhazai suke fitowa daga Cikin jirgin sunatako steps din Cikin nutsuwa suna saukowa, fuskokimsu cike DA annashuwa
Cikin abinda baifi 30 mints ba suka gama fitowa.

Wani Zankadeden saurayin dan kimanin shekara 30 Na hango yafito daga wata kofa shida wani dan kakkawar "mutumi Dan kimani shekara 45 bakine yanada tsayi kadan ga dukkan alama sune matukan jirgin, domin kuwa sanye suke da uniform Riga white wando navy blue, da hulla hannun farin saurayi rikeda suweiter itama navy blue da kuma wayoyin sa manya guda uku a hankali yasa hannun yacire hular, aikam suman kansa tabaiyyana Wadda take achukurkude sai walkiya take famanyi saboda tasha gyara,

Farine guy din kyakkyawa dashi ajin farko gashi dogo yanada kirar masu karfi yanada fadin kirji, fuskarsa" zagaye take da wani lafiyayyen saje da dogon Hanci idonsa kamar mai jin bacci bakinsa Dan karami pink colour,gaskiya guy din yahadu iyakar haduwa kallon daya zakai masa kagane yahada jini Da larabawa,

cikin nutsuwa yake tafiya wani office naga sun,nufa shida wannan "mutumin baifi 15 mints ba sai wannan guy din yafito sannan yanufi wata dankareriyar mota wadda akaima rubutu da manyan baki kamar haka *PILOT S. A SARDAUNA,*
Drive yadan risinna kadan yace U are welcome Sir! cikin zazzakar muryarsa mai dadin yace thanks Peter hw far ? yace fine Sir yace is gud, sanna yabude masa gidan baya yashiga ya zauna sannan yarufe kofar shima yazaga yazauna amazauni sa Na driving yaja suka tafi.

Wani kayatattacen gida suka shiga wanda yatsaru iyakar yatsaruwa kyansa baya musaltuwa infert dai ya hadu matuka, direct gurin ajiye mota peter drive yanufa yai fakin motocine birjek sunkai kimanin guda goma tsadaddune ko wacce ta amsa sunanta mota,

Da sauri Peter yafito yabude masa kofa
A hankali yazuro santala-santalan kafafunsa kasa hannun sa rike da tarkacen sa Cikin nutsuwa yake tafiya kamar baya son taka kasan,

Wata kyakkyawar budurwa gajera fara tanada kumatu sosai saida batada hanci yar kimani shekara ashirin ce naga ta nufoshi da gudu har kumatun ta yana rawa Da alama hug dinsa take sanyi,

Akam take agurin yadaka mata wani uban tsawa dayasa ta tsaye chak!
Saboda tsananin razanar datayi.

gaskiya nima kam na razana dajin wannan tsawa saboda haka ne ma harsaida alkalamin rubutu na yafadi kasa,

Cikin matsananci takaici Da daga murya naji yace.....?Kubiyoni

A

馃挊ZUCIYATA CE馃挊Tareda Alkamin

鉁嶐煆�

馃挊LUFHAT CE馃挊
[8:25AM, 2/20/2018] 鈥�+234 902 288 0912鈥�: 馃挊馃洬馃挊馃洬馃挊
馃挊馃洬馃挊馃洬馃挊
馃挊馃洬馃挊
馃挊

馃挊 ZUCIYATA CE馃挊

Based on true life story
馃挊馃洬馃挊馃洬馃挊
馃挊馃洬馃挊馃洬馃挊
馃挊馃洬馃挊
...


Read / Download ZUCIYATACE

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album