Join Our WhatsApp Group

AUNTYN YARA Complete Hausa Novel Document by AUNTYN YARA


AUNTYN YARA

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 76932



AUNTYN YARA

Reading Time: 6 Hours

Added On: 01, Sep 2023

Author: Sad Nass ,Hamagee Muhd ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 436.03 kb

File Type: txt

Views: 831+

Download: 468+

Last download: 14 hours ago

Description/Story: ANTYN YARA
Sad nas & hamagee muhammad
Made:- Shuraih Usman

Domin samun wasu kayatattun hausa ebooks na soyayya dana yaki sai ku ziyarci
shafinmu na yanar gizo gizo akan wannan adireshi http://shuraih.waphall.com

Kuna iya ziyartarmu a shafinmu na facebook ta hanyar wannan adireshi
www.fb.com/hausaebooks

[7:07am, 4/2/2017] Sadiya Taheer: BISMILLAHIR RAHMANUR RAHEEM...

🍭🎈AUNTY'N YARA🍧🎁AUNTY'N YARA🍧🎁

Written by Sad-Nas
&
Hama gee muh'd

1-2 Had'ad'd'un motocine guda uku ne suke wucewa 406 ne a gaba,se prado a
tsakiya, sannan benz a karshe suna tfy a titin GIREI local government.
Daga nesa kuwa wani tsohone kwance akan titi yanata birgima,sega wata budurwa
tana rik'e da kwanon abinci da kuma ruwa mai sanyi tana tfy a gefen titi se
idonta yakai gun wannan tsohon daya fad'in.
"Da sauri ta ajiye abinci tayi gun wannan tsohon da bisimillah sannan ta
d'agoshi tana cewa sannu baba lfy? Meke damunka? Ita kanta tasan bazata samu
amsar tambayanta daga gareshiba gashi babu yadda zatayi seta hango motocinnan
suna zuwa. Kwantar da tsohon tayi ta mik'e tare da tsayawa akan titi tanata
k'ok'arin tsaida motocin amma sam basu da niyan tsayawa. Ganin halin da tsohon
yake cikine setak'i matsawa akan titin dole dai 406 d'innan ya tsaya ganin
budurwan tak'i kaucewa. Da saurinta ta k'araso gun motan tanata buga glass,
d'aya daga ciki ya sauke glass d'in gaba yace ke wace irin...bata bari ya
k'arasaba tace dan Allah malam fito ka taimakamin wancan tsohon ya fad'i bansan
meke damunshiba. Suka kalli junansu sukace bazamu iyaba, mamaki ya cikata seta
rabu dasu taje gun pradon tanata buga glass d'in gaba dana baya. Glass d'in baya

aka sauke nidai SAD-NAS idanu na bud'e da kyau dan ganin wani had'ad'd'en
saurayi a ciki yana sanye da suit fari tas k'amshine kawai yake tashi. Budurwan
ta had'iyi yawu sannan tace bawan Allah pls ka taimaka min wancan tsohon yana
neman taimako sannan ni kad'ai bazan iya d'agashi daga kan titiba shiyasa na
tsai daku. Cikin mamaki seya cire glas d'in idonshi ya ajiye a gefensa sannan ya
bud'e mota ya fito batare daya ce mata komai seyayi mata nuni da hannunshi
alaman muje. Da sauri ta wuce gaba yana biye da ita har suka k'arasa gun
tsohon,budurwan tace toya ka tsaya kuma d'agashi ka maidashi gefe mana, saurayin
yana kallonta har cikin ido yayi magana a hankali yace to ai ke nake jira mu
d'agashi tare. Mamaki ya kamata tace yanzu kai a matsayinka NAMIJI bazaka iya
d'agashiba harse na taimaka maka? Kai kawai ya d'aga mata alamar EH. Ba musu ta
kama tsohon suka d'agashi zuwa gefen titi, saurayin ya lura da cewa farfad'iyace
take damun wannan tsoho, dan haka ya koma gun 406 ya karb'i inhela sannan ya
dawo ya taimakawa tsohon cikin ikon Allah tsohon ya dawo hayyacinsa sannan
saurayin yace sannu baba Allah ya baka lfy sannan ya juya ya koma motarshi.
Budurwan tace sannu baba ina zuwa kaji, sannan ta mik'e taje gun pradon ta sake
buga glass d'in a hankali lokacin motar tana k'ok'arin tashi. Saurayin ya sake
sauke glass tare da cewa me kuma? Budurwan tana murmushi tace nagode da
taimakonka. Saurayin yace me alakarki dashi? Tace MUSULUNCI bayan wannan
bakomai, saurayin yace dama "you don even know him? Budurwan tace yeah na
taimaka mishine saboda yana buk'atan taimakon dan haka nagode Allah ya kiyaye
hanya, harta juya ta fara tfy seyace 'yan mata. Na'am tace dashi tare da dawowa
gun ta tsaya, yasa glass d'inshi yace nima nagode da kikasa na samu wannan
ladan. Budurwan tace karkamin godiya bawan Allah amaimakon godiyan da zaka min,
inaso idan ka sami dama toka taimaki mutum UKU kuma suma kace musu su taimaki
mutane UKU inaga K'ASARMU zataci gaba tayin hakan se'anjima sannan ta tafi.
Kalaman yarinyar sun burgeshi sosai yace da driver'n shi "lets go" nan driver
yayi hon se 406 d'in tayi gaba sannan suma suka wuce saurayin yanata bin
budurwan da kallo se karkad'ewa tsohon jiki takeyi sannan ta rik'e hannunshi ya
mik'e yana cewa nagode sosai yarinya Allah ya miki albarka. Budurwan tace ameen
baba, amma banason godiyan nafiso idan ka samu dama a rayuwarka toka taimaki
mutum UKU kuma suma kace musu su taimakawa mutane UKU. Tsohon yace to shikena
yarinya ya sunanki? Tace sunana MARYAM amma amfi sanina da AUNTY'N YARA,seta
d'auki abincinta ta tafi yanata binta da kallo.

Shi kuwa wannan saurayin kalaman MARYAM kawai yaketa mishi yawo a kwakwalwanshi.
Suna cikin tfyane seya hango wasu mutane UKU suna bin wata yarinya a guje se
kuka takeyi. Yace da driver tsaya, bayan driver ya tsayane seya cire farin suit
nashi da glass d'insa ya fita da sauri ya fara bin bayan mutanennan da gudu
harya cafko biyu. Jin hakan yasa yarinyar tsayawa tana cewa bawan Allah ka
taimakamin wai fyad'e zasumin. Duka ya fara musu kamar ba gobe suna bashi
hakuri, yace baku da tausayi sam,yanzu ku zakuso ayiwa k'anwarku fyad'e? Sukace
a'a kayi hakuri bazamu sakeba, yace ina fata zaku gyara halinku inba hakaba
wataran se anyiwa k'annenku koma 'ya'yan cikinku. Jikinsu yayi sanyi sukace kayi
hakuri kema kiyi hakuri daga yau mun dena kuma mungode. Saurayin yace karkumin
godiya,amaimakon godiyar da zakumin inaso arayuwa idan kun samu dama toku
taimaki mutane UKU2 suma kuma kucemusu su taimakawa wasu mutane UKUN ya juya ya
kalli yarinyar yace harda kema sannan ya tafi sunata binshi da kallo sukacewa
yarinyar muje zamu rakaki har gida, dad'i taji sannan suka tafi.

Shi kuwa ya koma mota yasha ruwan FARO mai sanyi sannan ya goge takalminshi tare
dasa suit da glass nashi sannan driver yaja mota se gida.
Suna isa saurayin ya fito ya shiga ciki. Wata kyakkyawar budurwace ta fito
daga d'aki tana sanye da wandon jeans fari da kuma black top mai hannu d'aya
kanta ba d'ankwali ta baza gashinta tana danna TAP ahannunta daga ganinta kasan
k'anwar wannan saurayinne dan kamannin harya b'aci. Murmushi takeyi tare da cewa
"The Prince! "The Captain!! "And d Bro MANOSH!!! Daga ina ka fito hakane dukka
dawo a gajiye bro MANOSH? Suit d'inshi yake cirewa yanacewa "pls not now MIHER"

Bari na watsa ruwa se inzo kinji? Alright tace dashi sannan ya wuce side
d'inshi ita kuwa MIHER ta zauna tanata buga game d'inta. Sallama taji, ta masa
batare data kalli kosu wayeba, tap d'in hannunta taji an karb'e seta d'ago kai
da murna sosai tace "The 6 Emms" (M) yaushe kuka shigo k'asar without alartn me?
dariya sukayi mata amma banda d'aya daga cikinsu, MIHER tace bro MARWAN
miskilancin ya tashi kenan? Marwan yace ke ina MANOSH, tace yana ciki,duk suka
wuce sukabar MAJID yana rik'e da TAP d'in yace bana hanaki irirn wannan
shigarba? Tace am sorry luv aidan ina gidane kuma bansan kun dawoba wlh amma
promise daga yau bazan sakeba tana murmushi. Shima murmushin yayi yace to
shikenan kije kisa himar ina jiranki a side d'in PRICE, ok luv ina zuwa me za'a
kawo muku? Karki damu a k'oshe muke ruwa kawai muke buk'ata kuma zamu samu agun
bro naki dan haka ki huta my luv yana mata murmushi sannan ya bata TAP d'in ya
wuce itama ta shige ciki dansa hima...
[7:07am, 4/2/2017] Sadiya Taheer: 🍭🎈AUNTY'N YARA🍧🎁AUNTY'N YARA🍧🎁

Written by Sad-Nas
&
Hama gee muh'd

3-4 Palon manosh suka wuce kai tsaye suka baje akan kujerunsa masu kyau ga
laushi. Muhammad ya kunna musu TV tare da d'ansa volume ta yadda manosh zaisan
akwai mutane a palon,ball suke kallo suna hira. Manosh ya fito sanye da shets
fara da kuma bak'in jeans,mamakine ya kamashi su kiwa dariya sukasa tare da cewa
the prince captain manosh. Karasawa yayi ya zauna kusada muhsin da marwan yace
gaskya bakuda kirki wlh,ashe kuna hanya shine har marwan kana cemin wayankane ba
charg,marwan yai mirmushi yace muhsin ne yace karmu gaya maka,muhsin yace haba
dude haka zakamin kuma,dariya sukasa dukkansu manosh yace to ina tsarabana
naganku empty hand. Majid yace babu ya ibada ya hanya kawai se tambayan
tsaraba,gaskya bakada kirki,manosh yace wannan tambayan ai mata kad'ai akeyiwa
dan sune sakaltattu amma kana namiji dan kaje UMRAH harse anyi maka wani
sannu,muhammad yace sosai kuwa ai haka ya dace,manosh yace toku rik'e tsarabanku
indai hakane nasan marwan zai bani. Marwan yace ni ibada kawai naje ba sayan
tsaraba ba my friend,muhsin ya mik'e ya d'auko ruwan sanyi yasha sannan yace to
nidai zanje hira,kuda bakuda kowa sekuyita hiranku da kallon ball,harzai wuce
manosh ya janyoshi yace wlh baka isaba nima na samu matar aure had'add'iya kuwa
tamafi MIHER d'inka dan haka ka dena wani cika baki,ba majid kad'aiba dukkansu
suka juya suna mishi kallon mamaki,domin duk cikinsu manosh ne kawai tun
tashinsu bai tab'a ganin wata 'ya mace yace yana soba koda wasa. Muhsin yace
"wow dude" gaskya zanso inga mai wannan SA'AN yau kaine da budurwa kodai wasa
kakeyi? Manosh ya bisu da kallo dan dukkansu idonsu a kanshi yake suna jiran jin
mezaice,yace wlh yauna had'u da wata yarinya bafulatana nitsatsiya gata tason
taimakon wanda bata saniba sedai k'aramace,amma wlh ta burgeni sosai kuma kunsan
wani abu dayasa na damu da ita "we luk alike dudes" zanso ku ganta she's so
sweet. Majid yace harka tab'ata kenan,bugun wasa yakaiwa majid yace kai d'an
iskanefa a hakanma wai k'anwata kake so shine kake min wannan maganan,majid yace
to ai naji kace she's so sweet ne shine ban kane ba,manosh yace eh ina nufin
voice nata yadda kasan mutum in yana mura kasan muryanshi yana canjawa,to amma
nata yayi dad'i sosai kuma ba muran takeyiba natural voice nata kenan,bari dai
in tak'aice muku kunsan dai muryan RANI dabanyake a cikin sauran matan indians
da suke FILM,to haka dai itama yarinyan amma nata yafi na RANI dad'i idan tana
magana bazakaso ta gamaba wlh nd.....marwan yace enoght me sunanta? Manosh yace
nidai bansan sunantaba but zan dinga kiranta da MY APPLE. Ajiyar zuciya suka
sauk'e muhammad yace gaskya zanso in ganta ko zan samu k'awarta nima,manosh yace
ai wannan ne nakeso in samamishi k'awarta dan naga ya kusa ya tsufa baiti
aureba,marwan yayi murmushi yace kai baka tsufaba seni,muhsin yace gara dai kam

ka taimakawa marwan dan tunda FADILA ta rasu ta barshi gabad'aya bana gane
mishi. Majid yace kuka sani kozai bitane ku kyaleshi kawai,duka marwan zaikawa
majid se yayi sauri wucewa gun k'ofa yana cewa to ai gaskyane nidai na tafi gun
luv d'ina prince ina tayaka murna dolene muje nemo soyayyar APPLE namu,manosh
yace gaskya na baka k'anwata koba'ayi tambayana nariga dana baka ita. Dariya
suka sa sannan majid ya tifa gun MIHER,su kuwa sukaita hira nada'an wani lokaci
sannan suka fito kowanne ya shiga motarsa ya tafi.
Miher tace bro manosh k'awata tana sonyin magana da kai amma kuma idan kun had'u
seta kasa saboda kunya. Manosh yace wata k'awarkin kenan,tace LUBNA nama bro
kaima kasan banida da k'awar data kaita duk duniya,manosh yace to to ai bata
cika maceba kenan tunda tana tsoron na miji,miher tace bafa tsoro takejiba
kunyane da kuma tunanin disgin da zaka mata,manosh yayi murmushi tare dajan
hancin miher yace wani irin disgi kuma luvlyn sis,tace bro SONKA fa takeyi wlh
amma takasa gaya maka nace ta bari in sanar dakai amma tak'i tace wai ita zata
sanar dakai kuma wlh bazata iyaba pls bro ka amin....shiii sis karki k'arasa pls
kedai ki bari tunda bata sakiba harse lokacin dataga ya dace seta sanar dani
kinji,miher tace hakan ya nuna kaima kana sonta kenan? Manosh yace nop ina dai
sonta a matsayin k'anwan abokina kin gane yana mata murmushi,miher tace dat why
nake so ku fahimci juna tunda k'anwar marwan ne. Manosh yace zomuje palo mu
zauna,bayan sun shiga sun zaunane yace miher akwai abinda baki saniba inaso ki
nutsu ki saurareni kuma bance ki gayawa kowa,miher tace haba bro kasan akwai
sirri mai karfi a tsakaninmu kuma babu wanda yake sani se mutum d'aya,manosh
yace wa kenan? Tace zuciyana mana tana dariya wanda yake kara mata kyau,shima
dariyan yayi yace to kina jina

Ita dai LUBNA ba k'anwar marwan na jini bane, iyayen marwan suna son bby girl
tun farkon aurensu tunma ba'a haifemuba,se Allah ya basu d'a namiji marwan
kenan,sunyi farin ciki sosai kuma ke kanki kinsan yadda suke sonshi,amma ita
mahaifiyarshi tanata so ta haifi mace gashi kuma bata sake haihuwaba shine
sukaje gidanmarayu suka d'auko lubna tun tana jaririya suka riketa tamkar 'yar
cikinsu. Mamaki sosai mihertayi dajin wannan lbrn da bro manosh ya bata,tace bro
da gaske kake?murmushi yayi yace na tab'a miki karyane,tace wlh abun yaban
mamaki amma to itama lubnan batasan da hakaba ko? Manosh yace bata saniba amma
duk iyayenmu sun sani damuma,shiyasa banaso kiyinunakin sani kema. Miher tace to
amma shine dalilin da yasa baka sonta kenan,manosh yace bahakabane sis yana
jnkumatunta yace ai lubna yarinyar kirkice gata kyakkyawa duk namijin daya ganta
zai sota amma kuma nid'in ban shirya neman mace bane yanzu shiyasa,ya kare
maganar yana murmushi tare da barin palon ya d'auko key'n motansa ya fito yana
cewa me,zan sayo miki sis,binshi kawai take da kallo tace bro ina zakaje
kuma,yace gurin OGA na zanje yana nemana daga nan kuma zanje a rage min gashin
kaina dan yana damuna sosai,miher tace pls kar'a rage dewa domin gashin yana
maka kyau ai adai gyara maka shi,to luvlyn sis byee,itama hannun ta d'aga mishi
guards d'insa sun mik'e da sauri yace no ni kad'ai zanfita karku damu,ok sukace
dashi sannan mai gadi ya bud'e gate ya fita.

Auntyn yara har an gama abincinne,eh baba an gama ya rana ya kasuwan?
Alhamdulillah yau na samu ciniki sosai se hamdala,murmushi tayi tace to madallah
baba kaci abincin idan anzo saya se in sayar,to 'yar baba nagode ya maman
naki,lfyanta k'alau tace in gaidaka,yace to ina amsawa yau kind'an dad'e yar
baba,tace wlh baba wlh mutum ne farfad'iya ta kamasa akan titi ya fad'i shiyasa
kaga na dad'e, yace Allah sarki 'yar baba Allah ya rayamin ke Allah ya miki
albarka,Allah yasa kiyi kyakkyawan karshe a rayuwarki. Tace ameen baba harda kai
da mama da dukkan 'yan'uwa musulmai. Tun daga nesa ta fara jin muryan yaran
makaranta sunata cewa oyoyo auntyn yara2,da sauri ta fito daga cikin gidan
FLOWER tana murmushi tare da tafa hannun tana cewa oyoyo kannen aunty suka
rungumeta dukkansu yaran amma banda d'aya, seda suka gama oyoyon sannan d'aya
yaron yace sannu auntyn yara,tace sannun Abdallah nah ya makarantan,yace
alhamdulillah sannan ya gaida baban auntyn nasu,yaran sukace aunty mutafi gida
to, tace to baba ka gamane? Babanta yace na gama kuje yana murmushi,suka mishi

sallama tare da addu'an Allah ya kawo kasu mai albarka suka tafi.
Dad'i yakeji a ransada samun 'ya kamar maryam gashi tana da marrin jini kowa
yana sonta manya da yara...
[7:07am, 4/2/2017] Sadiya Taheer: 🍭🎈AUNTY'N YARA🍧🎁AUNTY'N YARA🍧🎁

Written by Sad-Nas
&
Hama gee muh'd

5-6 Maryam ko kuma ince auntyn yara suna tfy suna hira da yara se bata lbrn
makaranta sukeyi ita kuwa tanata dariya dayake ita d'in akwai fara'a ga kowa.
Abdallah yace auntyn yara wai yaushe uncle ibrahim zai dawone,tace yadai kusa
akwai wani abune,yace kawai dai naga nauyin ya miki yawane,tayi murmushi ta e
aiba komai koda ya dawoma ai aiki zai kama tunda bautar k'asa ya tafi,abdallah
yace har inaso in girma da wuri kodon indinga taimakawa kamar ke,dariya tayi
tace insha Allah burinka zai cika abdallah. Haka dai suketa hira da yaran
unguwansu suna tafiya jama'an dake wucewa sunata d'agawa auntyn yara hannu tare
da gaisuwa maza da mata kowa ya santa a garin girei.

Maryam ita kad'aice agun iyayenta suna sonta sosai fiye da ransu gashi sunyi
sa'an yarinya tunda ta taso da son mutane take musamman yara k'anana kowa nata
duk gireim ana alfahari da ita tun tana primary ita take zuwa na d'aya har
secondary kuma ko'a islamiyama haka gata da murya mai dad'i musamman idan tana
karatun Qur'an kyaututtuka sosai garin girei ta samu dukta dalilin maryam har
gasan Alqur'ani mai girma tana zuwa state state kuma ita take zuwa na d'aya kona
biyu ta hakanne takai iyayenta makka da kyautar kujeran da take samu agun
MUSABAK'A,dayake ta samu kujeran sau dewa dan...


Read / Download AUNTYN YARA

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album