Join Our WhatsApp Group

RUDANI Complete Hausa Novel Document by RUDANI


RUDANI

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 11391



RUDANI

Reading Time: 0 Hours

Added On: 26, Apr 2024

Author: Fatima Dahiru Funtua Bintu ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : 09162526909

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 77.11 kb

File Type: txt

Views: 176+

Download: 73+

Last download: 20 hours ago

Description/Story: Fatima Dahiru Funtuwa: RUDANI 1






Sunana Fatima Dahiru funtuwa Binta
Anhaifeni a cikin garin funtuwa jihar katsina,ashera Alif dari Tara da cisain da bakwai (1997)
Nayi primary school dina a nan funtuwa, (model 'kur an primary school funtuwa)
Haka kuma nayi secondary school dina nan cikin garin funtuwa (Government girls day secondary school funtuwa)
Bayannan sainayi aure a zariya,
Wannan dai shine takaitaccen tarihina













Fatima Dahiru Funtuwa: RUDANI 1
page 1

NA

FATIMA DAHIRU FUNTUWA BINTA
09162526909

Godiya tatabbata ga Allah mai kowa mai komai daya sake hadamu cikin wani sabon littafin, tsira da amincin Allah sukara tabbata ga shugabammu annabi Muhammad S A W da sahabbansa da iyalan gidansa baki d'aya
Wannan littafin 'kagaggen labarine bawai abune Wanda yafaru da gaskeba,don haka idan kaga yazo daidai da irin naka rayuwar to bakaidin bane don wata kilamani bansan ka/ki ba,shirin labarinne kawai yazo dahaka.

GARGADI !!!!!

Ban yadda ajuyamin wannan littafin tawata sigarba,kokuma a Dora shi a YouTube bada izininaba,akiyaye.
Godiya agareka Yusuf Ibrahim mai Sallah funtuwa, Allah yatsareka yakareka,yabaka abinda kake nema duniya da lahira,yadaukakeka.

RU'DANI 1 fateema Dahiru funtuwa

Misalin karfe biyar nayamma,lokacin da iska mai dad'i take kadawa,daidai lokacin Alhaji mansur yayi parking din motarsa,adaidai wani gida,dagani gidanna talaka wane,inbandadai da ake gyaransa yanzun,taredayimai kwaskwarima,yafito cikin motar yana kara kallon masu fantin gidan,suka nufoshi cikin sauri suna gaisheshi,shikuma yana amsa masu cike da kulawa tareda yaba yanayin aikinnasu.
Bayan ya'kara duba gidan sosai,saiyakoma cikin motarsa,yadauki wayarsa ya lalubi number dayake so yakira,ba'ajimaba tadaga wayar.
Yace ranki shidade inanan kofar gida inajiranki.
Ta amsa Mashi sannan yakashe kiran.
Mintina biyar saigata tafito,cikin shigarta mai kyau,tabude gaban motar tazauna,tareda gaisheshi.
Shikuma yabude baki yana kallonta sosai,yace gaskiya amaryata kinyi kyau,kamar dai yau ake kamu!
Tasa tafukan hannayenta guda biyu tarufe fuskarta tana dariya.
Yace aah!aigaskiya nafada.
Tace nagode tana dariya.
Yace toya shirye-shiryen komai lafiya ko?
Tad'anyi farrr! da idanunta sannan tace iee toh!!lafiya lau,maganar tata cike dayanga Wanda dama abinda yafi daukar hankalinsa kenan.
Tace sai dai abinda ba'arasaba,haka 'kanana wad'anda dole saimun bukaci kud'i,kasan hidimar aure bawasa bace.
Yace to shikenan bamatsala indon wannan ne zanturo maki,don banaso asamu matsala kwata-kwata.
Tace insha Allahu aiko mai yana tafiya dakyau,kaga shima gyaran gidan ankusa kammalawa.
Yace e nagani gaskiya yayi kyau sosai.
Suna cikin fira saitaga yakauda kansa gefe guda yayi wani murmushi Wanda takasa gane manufarsa,hardai tace Alhaji mekakeyima dariya?
Yayi saurin maido hankalinsa akanta cikin razana cikin rawar murya tareda yin wata dariya ta rashin gaskiya, yace inadariyane idannatuna dacewa yau saura sati daya burina yacika,kizama amaryata,don a yanzun jinake tamkar bantaba aureba akankine zanfara.
Nan take farin ciki yamamaye zuciyarta,tace shiyasa wani lokacin idan inataredakai sai inji tamkar bada tsofo nake tareba,hakan shiyasa nake karajin sonka.
Yace kai!kai!!kaih!!!baricewa tsofo!don yanzun jinake tamkar Dan shekara talatin.
Sukayi dariya sosai,sukayi firarsu cikinnishad'i,anan yake sanar da ita cewa gobe zaikoma Kano,bazai dawoba sai ana igobe d'aurin auren, don haka duk abinda take bukata tayi magana donya kammala da wannan 'bangaren.
Nantasanar dashi duk abinda suke bukata ,yace zaituro mata ta account, dama matsalar dai batawuce takudi,sukayi sallama yatafi.
Bazana cemaku Alhaji mansur tsofo bane kamar yadda bazankirashi da yaroba,domin dai ahaife ya haifi Mariya, saidai kyakyawan mutumne sosai,Wanda kuma yakeji dakudi!
Yanemi auren mariyane dukda take 'yartalaka,saidai kuma komai nadawainiyar bikin yazamana akansa,mafiyawa daga cikin hidimar shikeyi.
Anan garin zai zauna da ita,dukda bagida gareshi ananba,amma dayake yaso abin saiya kama hayar gida mai kyau.
Idannacemaka duk dukiyar da akazuba acikin dakin Mariya shine yazubata kada kayi mamaki,don koda Dana su aciki kadanne,hatta gyaran gidan iyayen Mariya da akeyi shine yadauki dawainiyar abin.
Dukda dama ita mariyar marainiyace ,tun tana karama mahaifinta yarasu,to saidai mahaifiyarta mai mugun son abin duniya,donda karfin gwiwarta Mariya keson Alhaji mansur, don da mariyar tafara zillewa akan batason Alhaji mansur din, don ita yayimata manyantaka dayawa,kuma gasaurayinta Wanda takeso.
Amma inah!!!mahaifiyar ta tayi tsalle tace ita samm!batasan wannan ba,indai ba bakin ciki zatayimataba,tana ganin ga inda zata huta itama tahuta,zatace ta'kishi,shi saurayinnata meyakedashi?
Don haka Mariya idan zaki kwantar da hankalinki muci arziki mubarsa to kibi abinda nakeso ,indai dakud'i wake duban wani tsufa?
Ahankali dai ta lallashi 'yarta harta amince da Alhaji mansur din,duk dadama shima yariga yasakarmasu bakin aljihunsa sosai,yawanyimata kyauta day akeyi daga ita har mahaifiyar tata,yasa itama takamu da sonsa,duk dadai soyayyar badon Allah bace, kudinsa kawai akeso.
Shikuwa tsofon saurayin ta Wanda yadad'e yanasonta,kusan uwaka ubaka akarabu dashi badon dad'iba,don kuwa kudi sunriga sunrufe masu ido,domin kuwa suna wankar Alhaji mansur.

HASHIMU kuwa tsofon saurayin ta ba'arabu dashi tadad'iba,donya nuna ranshi ya 'baci sosai,da tsakaninsa da mariyarne kawai suke hayaniyar,yana nunamata bata kyauta maiba abinda tayimasa.
Nandanan saitafarayimai rashin kunya,tanad'an gaygayamasa magana haka,har mahaifiyar ta JUMMAI tajiyosu,saita kirasu gaba d'aya harcikin d'akinta,yashiga ya gaishe ta cikin girmamawa,sai tace:
Mariya yanakejin kamar kuma hayaniya azaure?
Tace mamammu hashimu ne wai akan maganar aurennan nawa,yace shifa bayyaddaba,domin shiyafara nema,ya aza'azo daga baya ace ankasashi?
Mama jummai takalleshi sosai tace:abinda nakeso ingayamaka shine,shifa aure nufin Allah ne,bar ganin kadad'e kana nemanta,idan Allah bai hukunta Kaine zaka auretaba dole kahakura kabarta, kuma kada kace ba'ayimaka adalciba, nice idannabaka 'yata banyima kaina adalciba!domin bawanda zaiga arziki irinna Alhaji mansur yazo Neman auren 'yarsa,sannan yahana yaba talaka kamarka!toma inbanda abinka Hashimu INA kaga abinda zaka auri Mariya?
Yabude baki zayyi magana tadagamai hannu,taredafadin dakata hashimu!! Nasan abinda kake bukata,iyakadai kace abaka abinda kakashemata,wato kudin ka,wannan dukme saukine awurinmu ,kaje kayo lis,tundaga ranar daka fara kashe mata kudi harzuwa yanzun konawane za'abiyaka!
Yagirgiza kansa hawaye nazuba a idanunsa,yace bahaka baneba mama,inason Mariya, bazan iya rabuwa da itaba,duk Wanda yace zairabani da ita yacuceni.............
Tadakamai tsawa,taredafadin da Allah ya isheka! rufemana baki!!tunda aiyazama dole karabu da ita!!tare kukaxo duniyar?kaje nika lissafo duk abinda kakashe mata abiyabaka!!!!
Yace mama bana bukatar kudinku,ita kawai nakeso.
Tace to aidama bacewanayi kudimmuba!!kudin ka mukace kalissafa,Mariya ta kuma tafi karfinka!gadai mai halidai bazamu dauka muba talaka ba!kaji nagayamaka!!kanannade guntun talaucinka kafita!!!!
Wannan magana tabata masarai,yadago kai yakalleta,yace to shikenan, Allah yabimin hakkina, INDAI KUDINE GAKU GASUNAN!!!sai kunga sakayya!mutum bazayyi Abu don Allah ba,saidon abin duniya!!
Sannan yakalli Mariya yace balaifinki bane,nasan kinasona ,kudine suka rufe maki ido,da kuma shawarar mahaifiyar ki,don haka indai baku sauyaba ZAKUGA WULAKANCI!!Auren kudi auren wulakancine da kaskanci,indai badon Allah Akaginasaba,kuma kusani Alhakinama bazai barkuba,don banyafeba!!KUMA ZAKUGANI!!!!
Cikin sauri mama jummai tamike tsaye,taredafadin,babu abinda zamu bani sai Alkairi!!kuma aniyarka tabika!kuma duk abinda yasamu 'yata agidan aurenta Kaine!!kaibama abinda zai sameta,mezaka iyayi?dommu munfi karfinka!!!!
Haryafita tana masifa,sannan tajuya takalli Mariya,tace kekuma tsayuwar mekikeyimani anan?yaunaga yaran zamani!toko kinasonshi bazaki aure shiba!!!
Donbakiyimin wannan bakin cikin wallahi!!a ah!!hakanan ga inda zamusamu arziki sai azauna ayimana wata sagegeduwa!!!to duk nasan maganinku.
Sannan daga baya takara komawa talallashi 'yarta dacewa:
Kinga yanzun Mariya ba'a auren soyayya ,auren soyayya yanzun auren wahalane,daga zaran anyi auren wannan soyayyar takare,dakinje gidansa bashida ko sisi,akan kudin cefane isashshema saiku fara kai ruwa ranadashi,
Inko kika auri mai kudi babu ruwanki da wannan matsalar, muyanzun ba gashi munfara futawaba,hatta kudin auren ki duk a jikinsa zamusamesu,kinhad'a da wannan sullutun! Don haka kikwantar da hankalinki ,kije kishiga cikin arziki da daula,harnima danake agefe insamu.
To wannan shine yadda mama jummai takatse soyayyar Mariya da hashimu, taba Alhaji mansur, duk dayake shi Alhaji mansur din dattijone,amma tunda yanada kudi aiba matsala aganinta.
Haka akatsaida biki da Alhaji mansur, kamar yadda tafada kuwa kayan dakin Mariya duk a jikinsa suka samu kudin nan,banda wadanda suke amsama hakanan, WANNAN KENAN.
Alhaji mansur kuwa baibaro kano ba sai ranar juma'a ana yagobe za'adauka aurensa da Mariya.
Nan gidan su mariyar kuwa shagali ake sosaiba, tunda duk 'yan uwansu sun hadu wurin bikin,sai ranar akakawo lefensa,shima yayi kyau sosai,abokinsane kawai yakawo lefen.
To abin yaso yadaurema mutane kai,tayaya za'ace kawo lefe mutum d'aya? Saikace dai yanayin abin amunafince,sai mata akarika Dan 'kana nan maganganu,saikace angon bashida kowa!
Mama jummai ko sai washe baki take,don ita wannan bai dametaba,tundadai ankawoma 'yarta kaya masu yawa,koma shiyakawo dakansa INA ruwanta!saita fara yada bakakan maganganu.
Ai indai bakin cikin akeyimana asamun arziki!to kamar munsamune,talaucidai banakai 'yata inda zata sha wahala,shikuma wancan din (HASHIMU) da ake cewa yana kwance yanzun bashida lafiya,toyagajima yawarke.
Tadafa kafadar yayarta,tace kiganemin nan lariya!aa sai in dauki 'yata inkaita ga talauci,gadai arziki ina kallo,wai tsofon saurayinta shine akazo ake sanar dani bashida lafiya,to aiyama gaji yatashi,don gobe iwar haka mariyama tana dakin mujinta,kuma duk matsalar data samu auren 'yata bazan yaddaba!!!
Lariya tace haba jummai yakike irin wannan maganar kamar wata karamar yarinya,abinda yawuce aiya wuce,tundadai baki bashi 'yarkiba bashikenanba,saikibishi da Addu'ar samun sauki,bakiyimai mummunan zatoba.
Mama jummai tace yaya lariya idanba tsaye-tsaye nayiba abinnan saiya gagareni,abinda matasan samarinnan suka ganeyi yanzun kenan,saisu hana yarinya zaman aure,saboda anyi biyu anan makwabtammu nagani,gayarannan suna zawarci,saisu hana yara zaman lafiya agidan mazajensu.
Aida kikaga inata wannan kumfar bakin inafada,ba'abanza nakeyiba!inayine don intauna tsakuwa aya taji tsoro!don duk abinda yasamu yarinyata agidan muji tayadda zanyi ba!! Kinsanni sarai yaya lariya!
Lariya tace to Allah madai shikiyaye,kiyi shiru hakanan kada idanun mutane yadawo kammu.
Washe gari ranar asabar aketa shirye- shiryen auren Mariya da Alhaji mansur.

Hashimu kuwa NA zaune bisa gadonsa,sai abokansa guda biyu da suke zaune kusa dashi,suna bashi hakuri,taredayimai nasihohi,akan duk abinda kaga baisamu mutum ba dama Allah bairubuta zai samesaba,kuma rabonka baya ta'ba ku'bucemaka,munsan abinda akayi maka daciwo,amma idankadaure watarana abin zaizama kamar ba'ayiba,ka kwantar da hankalinka hashimu,karika cin abinci.
Hashimu yace nagode, tareda kallon agogon dayake manne ajikin bangon dakin,yace karfe sha d'aya da rabi za'adaura aurennanko?
Daidainan kuka yakwacemai tareda sarkakken tari,dagyar suka samu suka shawo kansa,har bacci yadan daukesa.
Baccin dabai wuce na mintuna gomaba,daidai sanda yafarka,sayya fara tuna abinda yafaru tsakaninsa da Mariya tuntana karama,dayadda yake dawainiya da ita.

***** ****** ******** *******

Baba kabiru shine mahaifin Mariya,dattijon kirkine,baita kadaice yahaifaba,tanada yayye maza da mata,amma itace karama.
Tsakanin gidansu danasu Hashimu babu nisa, tunsuna kanana basusan menene soba suka shaku da junansu,tare suka tafiya makaranta,tare da 'yan uwanta,shine yake taremata fad'a dayake bataji,har suka fara dagawa,yanabata kula sosai.
Har mama jummai watarana dai wata rana tace:Hashimu kikanaso inbaka autarnan ta wane?
Yadayyi dariya,tareda ajiye takalman Mariya daya dauko mata daga waje,tabatosu saboda tsabar rigima.
Mama jummai tace kazo kazauna asamaku tuwo tunda kuntaso makarantar.
Dayake yayi wayau,sayyace nakoshi nabarma Mariya taci yahada danawa,alokacin shi zaikai shekara goma sha Hudu,itakuwa bata wuce shekara takwas ba.
Bayan kwana biyu kuwa,suna zaune atsakar gida harda malam kabiru,kamar dawasa saisukaji Hashimu yace,mama rannan kince zaki bani Mariya, to idan mungirma nidai inasonta.
Akasa dariya gaba d'aya, sunadauka shirman yarintane,sai malam kabiru yace to Allah yanunamana girmannaku,indai kanaso aisai inbaka,mama jummai tayi dariya tace kaji shiriritar yarinta,kaih!!Allah dai yashiryamana.

BAYAN SHEKARU HU'DU
Lokacin Mariya Nada shekara goma sha biyu, rashin lafiya tasamu mahaifinta baba kabiru,ananan yayi jinya sosai,donduk saida 'yankadarorinsu suka 'kare wurinneman magani,suka zama basuda cinyau basuda nagobe.
Hashimu shike zuwa yayo buga-bugarsa abinda yasamo yakawo masu,duk dalilin son dayake yima Mariya,kuma daga gidansu hashimunma ana taimaka masu sosai, dakayan abinci,alokacin Hashimu din baiwuce shekara goma sha takwas ba.
Abin mamaki kuma mama jummai tanada 'ya'ya sanari,har wadanda suka girmi Hashimumma,amma dayake mashiriritane,basa ta'buka komai,tayi fad'an -tayi fad'an harta gaji,saiyazamana Hashim din yafiyemata su,don hatta aikace-aikacen gida basasonyi,kamar irinsu AIKE- 'DEBO RUWA-DA KAI NI'KA,wani lokacin tafiso taba Mariya tayimata.
To dalilin...


Read / Download RUDANI

START READING

OR

DOWNLOAD TXT NOW
Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album