Join Our WhatsApp Group

YESMEEN Complete Hausa Novel Document by YESMEEN


YESMEEN

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 14803



YESMEEN

Reading Time: 1 Hours

Added On: 18, Oct 2023

Author: Ummyn Yusra ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 95.84 kb

File Type: txt

Views: 579+

Download: 190+

Last download: 1 day ago

Description/Story: ๏ปฟ[02/05, 6:02 a.m.] Zeee Bello: ๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž
๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž
๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž
๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž
๐Ÿ’ž


*YESMEEN*

๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž


*WRITEN BY:*
*UMMYN YSRH*



*ยฎPURE MOMENT OF LIFE WRITER'S*
*(P.M.L)*




_MASOYA NA KWARAI HAR ILAYAU BAKI BAZAI IYA FURTA KALAMAN GODIYA DA ADDU'A AGAREKUBA DA BAZARKU NAKE RAWA๐Ÿ’ƒ๐Ÿป_

*MERMUE* *(MRS JABO)*

*YESMEEN TAFEESU*

*QUEEN MIEEMIE*

*RASH KARDAM*

_Fatan alkhairi agareku_
_Allah k'ara d'aukaka_
_Allah k'ara nisan kwana da tsawon rai mai amfani_
_Ina godiya Allah yabar zumunci_

_DASUNAN ALLAH MAI RAHMA MAIJIN K'AI TSIRA DA AMINCI SU TABBATA GA FIYAYYEN HALITTA ANNABI MUHAMMADU (S.A.W)_


*1~5*

Babbar motoce d'auke da d'alibai,kowacce kaganta cikin farin ciki take na murnar kammala makarantarsu ta secondary,motar d'auke da tambarin Gov't Girls College Bauchi (G.G.C.B).

D'alibaine da yawa wanda suka fito daga garuruwa da yawa ko wacce za'a kaita har garinsu.

Garin Jos suka dosa,duk d'aliban garin basu wuce mutum bakwai ba,kowa murnar komawa gida yake,daga gefe na wango wata y'ar budurwa zaune duk wake_waken da d'aliban suke bata sauraransu tunda suka d'auko hanyar garin nasu taji duk jikinta yayi sanyi ga kuma fad'uwar gaba da takeji,sun kuyarda kanta tayi jikin seat d'in moton.

Tunda suka shigo garin ba wani hayaniyar mutane wasu guraren ga k'onannun motoci,kwata_kwata ba wani alamar mutane sosai agarin sai d'aid'aikun mutane dakuma jami'an tsaro,tasha aka sauk'esu motar ta k'ara lulawa gaba don kai sauran d'aliban garu_ruwansu.


Sunfi awa guda suna zaman jiran abun hawa don kaisu gidajensu amma ba kowa duk shagunan kasuwar arufe suke ba mutane masu d'oki da wak'ok'i duk jiki yayi sanyi.
Gajiya sukayi da jira kowacce ta d'aura d'amarar da'bawa ak'ar don tafiya gida.

Haka suka rabu daga wajen *Yesmeen* datun amoto batada wani kuzari haka ta kwashi kayanta tayi gaba itama,ahanya tahad'u da wani take tambayarshi meke faruwa agarin nan yake shaida mata fad'ane ya kaure kwana uku dasukawuce,cikin dare aka rink'a bankama gidajen musulmai wuta musamman unguwar rogo anyi ta'adi sosai,jin an ambaci unguwarsu yasa tad'au hanya bataredata tsayajin k'arshen zancenba.


Sauri take batamasan inda take jefa k'afartaba, burinta kawai Allah kaita gida lafiya.

Abunda tagani ya mugun firgitata,gaba d'aya gidansu ya k'one ba alamar wani abun amfani ko rai mai motsi awaje duk da gidan nasu tamkar unguwace guda don duk danginsu na cikin gidan sai k'alilan da suke wani garin,don mafi yawansu auren dangi suke kuma duk wanda zaiyi aure cikin gidan yake zama.

Salallami kawai takena

_INNALILLAHIWA'INNA'ILAIHIRRAJU'UN_

nima dake gefe tayata nake had'e da kwalla๐Ÿ˜ฅ




~UMMYN YSRH~
[02/05, 6:02 a.m.] Zeee Bello: ๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž
๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž
๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž
๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž
๐Ÿ’ž

*YESMEEN*
๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž

*WRITEN BY:*
*UMMYN YSRH*


*ยฎPURE MOMENT OF LIFE WRITER'S*
*(P.M.L)*


*6~10*


Salati kawai take tare da tafiya da baya da baya,ji tayi tayi karo da wani abu juyawar da zatayi taga k'onannen motar mahaifinta,ga mashind'in yayan babanta shima yasha wuta duk ya k'one,wani sabon hawaye takumaji ya kuma gangaromata,kamar wacce aka tsikara ta zura aguje tayi cikin gidan ba komai ciki sai gayyar toka da k'onannun k'asusuwar mutane da kuma gawayi.


Sassa kusan gomane cikin gidan amma duk angama dasu,wasu sassanda wuta bai kamasuba jinine kwance awajen tamkar kwata mayankar dabbobi,da gudu tajuya tabar wajen gefensu tashiga ba wani abu cukinshi komai ya k'one wajen ajiye Qur'anansu ta nufa mamakune ya kamata ganin duk wani abu dake cikin lokar ya k'one amma wuta bai tab'a Qur'ananba sai d'an gefe_gefe wajen daba rubutu tace "ALLAHU AKBAR."
saikuma tasake rushewa da kuka,wajen ta d'urk'ushe rungumeda Qur'anan.

Jitake kawai inama azo asake cinnama gidan wuta ko itama suyi gunduwa_gunduwa da ita kozata huta,don ayanzu bataga amfanin cigaba da rayuwartaba.

"Wai yaushe garinsu zai sami zaman lafiya?"

"yaushe za'a daina irin wannan kashe_kashen?"

"yaushe za'adaina maida mata zaurawa?"

"yaushe za'a daina maida yara marayu?"

"marasa yanci,galihu,bamai kuladasu,saidai ad'ebesu akaisu gidan marayu a jibgesu bamai kuma waiwayensu,bamai basu wadataccen ci,sha,sutura,uwa uba Ilmi."

"Wai ina masu kud'inmu shuwagabanninmu?"


"Yaushe garinmu zata sami tsaro adainawannan tashin hakula?"
Maganganu kawai take ita kad'anta tare da tambayoyon dabasuda wani amfani balle amsa.


Lokaci maitsawo ta d'auka durk'ushe awajen,tana tunanin wani irin rayuwa zatayi ayanzun idan tace Bauchi zata koma wajen k'anwar babanta wazai bata kud'in moto?,ina zata sami moton ta shiga? don daga dukkan alamu garin bashiga ba fitane,yanzu ya zatayi?kodai tazaunanan ko cikin dare itama zatasami masu k'arasata.

Zamatayi tareda dura kanta cikin cinyoyinta,tacigabada kukanta,chan nesa takejin maganganun mutane,ji take kamar cikin gidan suke shigowa yadda takejin tafiyar manyan takalma tasan masu k'arasatane duk jikinta ya k'ara d'aukar sanyi,ko yatsar hannunta bata fatan ya motsa balle har tajega d'aga kanta taga yanayin halittar makasanta, chan taji wani daga cikinsu yana "gatacen"
cikin wani irin gurb'atacciyar turanci.


K'ara tura kanta tayi cikin cinyoyinta tareda k'ara rungume Qur'anan dake hannunta bisa k'irjinta mai barazanar rusowa.

Jitayi andafata tareda rungumata lokaci guda kuma sai kuka,ahankali take d'ago kanta saidai har yanzu idonta rufe yake,harta gama d'agokan bata bud'e idonba illa hawaye dake gangarowa bisa k'uncinta,wacce ta rungumata tace
" *YESMEEN*bud'e idonki nice."

Ahankali take bud'e idon har tawaresu kan fuskan k'anwar mahaifinta da sauri itama ta rungumeta tana kuka tana fad'in
" *UMMAH HABIBAH* sun kashesu,sunkashemana kowa,sunmaidamu marayu."

"kishiru akwai Allah,kitamusu addu'a"

"Taya zan daina kuka?"

"yaushe ruwan idona zaidana zuba bisa zaluncin da cin zalin da akamana?"

"har abada bazan dainaba,zan rayuwa inama duk wanda akama danginshi irin wannan cin zalin addu'ar Allah mana sakayya Allah yasa suyi k'ask'antacciyar rayuwa,sannan suyi mutuwar wulak'anci."

"naji kima me kitashi mutafi don yanzu unguwar ba kowa don ko jiya saida akasake kahomusu wani harin."

"kije kawai nizan zauna gara nima suzo su kasheni don ayanzu rayuwata batadawani amfani."

"bazan iya barinki ananba,yanzu duk danginmu mu uku kawai muka rage,kitashi muje yanzuma da taimakon sojojinnan nasamu nashigo garinnan."

Batakuma cewa komaiba tamik'e suka yi waje,wani harara take zubama sojojin don aganinta basuda wani amfani tunda har za'ayi wannan ta'asar basuyi yunk'urin hanawaba.


Fita sukayi daga konannen gidan suka nufi wajen motocinsu,kayanta data dawo dasu tahau d'iba suka sa cikin moton,kallon gidan kawai take tana k'ara rushewada kuka shikenan tagama rayuwarta agida?
Shikenan yanzu rayuwarta ya koma wani garin?

Meyasa basuyi jinkiri harsai ta dawo suhad'a da ita sukasheba?

Meyasa sukabarta araye?

Runtse idonta tayi yayindataji direban *UMMAH HABIBAH*
Ya tada motor, har sukabar garin jos bata bud'e idontaba,saida sojojin suka fiddasu garin kafin suka juya.




โœ๐Ÿป ~UMMYN YSRH~
[02/05, 6:02 a.m.] Zeee Bello: ๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž
๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž
๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž
๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž
๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž
๐Ÿ’ž
*YESMEEN*
๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž



*WRITEN BY:*
*UMMYN YSRH*



*ยฎPURE MOMENT OF LIFE WRITER'S*


*21~25*

Yau satinsu d'aya da dawowa,saidai sam batajin dad'in abin da ake ma Umman nata,yadda dangin mijinta da Uwargidan ta ke mata na gorin rashin haihuwa.


Shekarar ta goma da aure Allah bai bata haihuwa ba kullum cikin gori da bak'ak'en maganganu take sha,wajen mijinta kawai take samun sauk'i.

Wai da wanne za taji ne? yanzun da rashin dangin ta ko da matsalar kishiya da dangin miji na rashin haihuwa?.

Me yasa mutane suke manta cewar Allah shi ke bada haihuwa ba wayon ka ko dabarar ka ba?.

Wa za ta kai ma kukan ta a yanzu don ya sharemata hawayenta?

Y'ar uwarta da ta ke gadara da ita ko kad'an basu gaban ta a yanzu giyar kud'i na d'ibanta ta manta da su tayi watsi dasu ta samu sabin dangi, su d'in ba kowa bane a gare ta.

Zata ci gaba da kaima Allah kukan ta,shi zai mata maganin matsalolinta.


Haka rayuwars u ta kasance cikin gidan,duk da ba wani shahararren arziki ga mijin Ummah ba,yana da rufin asirin shi daidai gwargwado, yana kuma iya bakin k'ok'arin shi kan iyalan shi.


*YESMEEN* ta ware sosai sai dai ko da yaushe tunanin ta yana wajen y'an'uwan ta marayu,ko suna cikin wani hali?duk sanda zata wurga loman abinci bakin ta sai ta tuno dasu ko sun samu sunci?,idan sabon sutura zata sa sai tayi tunanin ko suma sun samu sun sa?


Da sauri ta shiga gida kamar zata tashi sama, ko sallama babu ta nufi falon gidan daidai zata wucesu taji ance.

"Toh jikan marasa kunya iyalan kalan dangi da chusa kai,kin shigomana gida ba sallama balle gaisuwa."

Juyowa tayi tana kallon mai maganar ji take duk sanda taga matar kamar ta dab'a mata wuk'a don tsanar DA ta ke mata.

Amsa tayi niyyar bata sai kuma ta fasa tace

"Sannun ku masu gida."

Wata daga gefe tace

"fad'i ki k'ara fad'i yarinya,gida namu ne sai dai mutum yazo yaci arzik'i ya k'ara gaba."

dariya tayi sannan tace
"Ruky kike kowa?
Kalleni tsaf kin san nafi k'arfin shigowa gidan nan inci arzik'i,ke kanki kinsani."

Umma Habiba ce ta fito daga kitchen tace

"ke Hanifa sa'i'on ki ne su da zaki rink'a musu magana haka?kul ko da wasa bana son hakan,wuce ciki k'awarki na d'aki."

Wucewa tayi tana watsa musu harara
Kishiyar Umma Hajiya Talatu tace

"ai dole ki korata tunda kin sa ta gama yi mana rashin kunya,haka dai zaki k'are akwashe_kwashen y'ay'an mutane da cika mana gida da manyan kashi."

Juyawa tayi ba tare da ta kuma tanka su ba. Zuciyarta sai k'una yake kamar ta Ciro shi waje ta huta don azabar zafin da ke mata.

Ihu yaran suka sa lokacin da ta juya suna ma Uwar tasu kirari da Sai Mama uwar masu gida.


D'aki Hanifa ta shiga tana kwalama Yesmeen Kira.

"Ke wallahi kin fiya Kira kamar makauniya,ki k'araso gani ciki guga nakeyi."

"Dallah ki tashi ki shirya anjima zamu unguwa."

"Unguwa kuma? Wacce iri,kuma ina?"

"Ohho! nidai ki tashi ki shirya zuwa k'arfe biyu zamu tafi."

"Idan nayi niyar zuwa ko ban yiba zaki sani dole kenan?"

"Malaman su aima dole kije Wallahi,bari ma ki gani b'ata lokacina nake gurin ki idan na had'aki da Ummah dole kije Baby."

Fita tayi tana mitar mutum kullum sunk'ume a gida kamar wani mummunan amarya.

"Me kikecewa?"

"Nace Allah barmu da wannan k'awa tawa y'ar ra'ayi da jan aji."

"zaki sani idan na rik'eki zaki gayan wace mummunar amaryar".

"Au! ashe kin jinine."

"A'ah kinsan na zama kurma."

K'arasa ficewa tayi tana dariya.

Kitchen ta nufa gunda Ummah keta k'okarin had'a abincin rana tace

"Ummah dama nazo tambayar ki ne don Allah Yesmeen ta shirya muje wajen hidimar bikin d'iyar k'awar Hajiyata."

"shine sai kin tambayeni? ai an zama d'aya."

"ai nace ta shirya muje wai ba za ta ba."

Tak'arasa maganar tamkar mai shirin kuka.

"tsokanarki take,jeki shirin ki zan mata magana."






โœ๐Ÿป *~UMMYN YSRH~*
[02/05, 6:02 a.m.] Zeee Bello: ๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž
๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž
๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž
๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž
๐Ÿ’ž

*YESMEEN*
๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž


*WRITEN BY:*
*UMMYN YSRH*



*ยฎPURE MOMENT OF LIFE WRITER'S*
*(P.M.L)*

_THIS PAGE IS 4 U MY CHUCHU๐Ÿ˜_

_ALLAH YABAR ZUMUMCI SO DA K'AUNAR JUNA_


*11~20*


Saida sukayi nisa da tafiya kafin ta bud'e idon da taji *Ummah Habibah* nacewa

"ohh! wato nan akazo aka zubara mutanenmu?"

Kallon wajen nayi asannan na gane wani gari muke, *TILDEN FULANI* mutanene birjik awajen mafiya yawansu matane da k'ananan yara sai maza y'an tsiraru,kowanne ka kalleshi kasan fitowan rashin shiri yayi.

Tsayawa moton tayi muka fita don duba y'an gudun hijiran ko Allah zaisa muga wasu daga cikin y'an'uwanmu.

Makarantar bokoce aka ba y'an'gudun hiriran da suka haura sama da mutane dubu uku,ajujuwa shine wajen kwanansu,rijiya guda d'aya tak shine wajen d'iban ruwa domin yin ibadansu da kuma girki ahakan wasu daga cikin y'an garin suna d'iban ruwan cikin gara kuna suna kaiwa gari domin samun taro sisi.

Kan sumintin da duk ya farfashe yayi rami shine makwansu,
Babu tabarma balle kuma katifa, ga buhun shinkafa uku da garin masara biyu da gwamnati ta aiko musu dashi don girkawa.

Jefe chan ga yara birjik sai kuka suke ba iyaye ba y'an'uwa,ankashe kowa nasu.

Shin wazai tallafi rayuwar wad'annan yaran?

Suwa zasu mayemusu gurbin iyayensu?

Wani irin rayuwa zasu fuskanta?

Wazai tallafi rayuwarsu ya basu ingantattaciyar kulawa?

Ahaka rayuwarsu zata k'are ko kuma zasu sami masu tallafamusu domin zama manyan gobene da ake ikirari?

Daga jefe nace mata babu mai iya baki amsar tambayarki,ki musu addu'ah kawai,Allah shine gatansu shine kuma jagoransu.
Allah ya rayasu bisa turba madaidaciya.


Juyawa tayi ta kuma ganin yadda yaran ke kuka da kiran iyayensu,juyawa tayi da gudu tana wani irin kuka mai tsuma zuciya,jitake kamar zuciyarta zai fito ya tarwatse.


Tunda ta shiga moton ta duk'ar da kanta k'asa ta runtse idanuwanta bata kuma bud'ewaba tanaji Umman nata suka shigo direba yaja ahankali tace

"Allah kawo muku sauyi cikin gaggawa."

"Allah kawo masu tallafawa rayuwarku"

"Allah bi mana hakkinmu,ya mana sakayya."

*AMEEEEEEN*

Ba wanda ya kuma magana har suka iso cikin garin Bauchi,unguwar Fedral low_cots suka nufa gidan Umman.


Suna isa ta wuce d'akin Ummah Habiba,ta ajiye kayanta bayan gida kawai ta wuce alokacin shida harda wani abu,gashi ko sallar azahar bataiba,tun d'azu neman gafarar ubangiji kawai takeyi na had'a sallolin da tayi,tana watsa ruwa ta d'auro alola ta sunkuya bada farali.





โœ๐Ÿป *~Ummeen yusrah~*
[02/05, 6:02 a.m.] Zeee Bello: ๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž
๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž
๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž
๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž
๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž
๐Ÿ’ž

*YESMEEN*
๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž



...


Read / Download YESMEEN

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album