Join Our WhatsApp Group

KWARYA TA BI KWARYA Complete Hausa Novel Document by KWARYA TA BI KWARYA


KWARYA TA BI KWARYA

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 33998



KWARYA TA BI KWARYA

Reading Time: 2 Hours

Added On: 01, Dec 2023

Author: Binta Umar Abbale ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION

Author Phone : 08089965176,07084653262, 90899076_88137740_

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 191.05 kb

File Type: txt

Views: 965+

Download: 493+

Last download: 2 days ago

Description/Story: [1/13, 9:47 PM] 💜: *'KWARYA TABI 'KWARYA*
*NA*
_BINTA UMAR ABBALE🍒_ *bintaumarabbale@gmail.com*


*MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION📘🖊️*
_'Kungiyar Masu Nazari da Aiki da Ilimi_
_________________________
*Littafin na kudi ne....!*
_#300.....0542382124...Binta Umar gtbank...idan kati zaki turo #400 ne sai ki same ni ta wannan numbers..08089965176 _07084653262 Zanyi miki bayanin yanda zaki turo katin.......... Ga masu bukatar VIP Group 600 ne_
_Mutanan Nijar zaku tura dala dari ta wannan numbers katin airtal ko orange VIP jakka d'aya 90899076_88137740_



*SADAUKARWA NE*
*GA*
*HAJIYA SHAFA'ATU S YARI*
(Kainuwa dashan Allah✊🏻)
1&2
Lokacin dana shiga masarautar sai da nasha jinin jikina dan ganin yanda tarin bayin dake karkashin masarautar suka nutsu gabas yamma kudu Arewa dukkaninsu suna tsaye sunja layi mazansu da matansu da 'ya'yansu suna sanye da uniform wanda ke dauke da tambarin masarautar gaba da baya, kowanne kansa a sunkuye 'kwakkwaran motsi babu wanda yake iya yi.......Can wata rumfa na hango iyayen masarautar zaune kan kujeru na alfarma sun jeru su uku wanda yake tsakiyarsu shine nafi tunanin shine shugaban masarautar wato (Sarki Maimartaba) abinda yasa nake tunanin shine Sarkin sabida ganin yanda wasu mutane gudu biyu masu dauke da jajayen kaya suke tsaye a gefe da gefensa suna masa firfita da wani irin mafici mai baza gwanin birgewa........Shiru masarautar babu hayaniyar mutane busar algaita gami da sarewa ne kawai take tashi a gurin.
Cikin nutsuwa wasu lafiyayyun motaci guda guda su shigo cikin masarautar, Maimartaba ya fara yun'kurin miqewa tsaye fuskarsa dauke da wani qayattacan mirmushi, Ganin zai miqe yasa fadawan dake gurfane a gabansa suka miqe da sauri suna baza manya manyan rigunan jikinsu......Waziri Galadima Ciroma suma suka miqe tsaye sabida ganin maimartabar ya miqe, dan ganin iyayen masarautar sun miqe ya sanya dukkanin wa'inda suke zaune suma suka miqe tsaye domin girmamawa.......masu busar sarewar suka rud'e tare da sanja salo....gabadayansu suka nufi inda motocin nan sukayi parking suna ta aikin busa algaita gami da sarewa, Wani bafadane yayi saurin bude motar ya fito da sauri ya bud'e daya hannun ya matsa gefe guda tare da dun'kule hannunsa alamun jinjina ga wanda ke cikin motar "Barkan ka da dawowa masarautar gado Aliyu Haidar namijin zaki Sarki mai jiran gado fari kake mai farar aniya Ali baka fito ba sai da ka shirya hakika masarauta da duk wanda ke karkashinta yana murna da dawowarka lafiya." Wannan kirarin daga bakin bafadan yake fitowa....shuru gurin yayi na minti biyar kafin ya zuro qafarsa d'aya kafar dake dauke da takalmin sarautar na tsirawa ido cikin socond guda na gane cewar mamalakin kafar mugun d'an izzah! ne a qalla ya kai minti biyar da zuro kafa daya ya gagara fito da dayar ko me yake a cikin motar oho! gabadaya idanun kowa a gurin yake mutane da dama sun 'kagauta suyi tozali dashi mussaman na qasa wa'inda basu sanshi ba sai dai labarin sa, cikinsu har da Sumayya wacce ta kasance d'aya daga cikin 'ya'yan bayin masarautar itama idonta kur! a gurin tana jira ya fito daga motar ta ganshi tun kafin ya fito ta gazgata abinda jama'ar masarautar ke fada a kansa wato shi d'in mugun d'an izzah! ne mugun d'an d'agawa ne! mugun d'an gadara ne! Mugun muskili ne wanda babu wanda yake gane al'kibularsa sai mutum d'aya itace mamanshi amma hatta da mahaifinsa maimartaba baya gane inda ya dosa.

Cikin nutsuwa ya rankwafo ya fito daga cikin motar tare da zura bak'in gilashin dake hannunsa dan saboda gujewa had'a ido da jama'ar da sukayi masa caaa! da idanunsu ya tsani kallo a rayuwarsa shiyasa sam baya sakarwa mutane fuska mussaman mata dan ya fahimci kamar kallo a jininsu yake be sai ba ko shi suka raina suke k'ure shi da kallon 'kurrula.
Wasu matasan samari ne wa'inda sukayi sa'anni dashi naga sun fito daga d'aya motar su biyu suna sanye da kayan sarauta a jikinsu amma shi uban gayyar suit ne a jikinsa Shatima da Moddibo sune suka tilasta masa d'aura alkyabba a jikinsa saboda da ita sukaje airport din suka kuma sheda masa cewar maimartaba ne yace lallai su bashi yasa ya shigo da ita cikin masarautar.
Da sauri naga wasu bayi su hudu sun shimfid'a wani farin abu mai tsayi a dadai kafafunsa sai da abin ya dangane har inda iyayen masarautar suke Cikin nutsuwa yasa kafarsa akan abin ya fara tafiya.
Tafiya yake abokansa kuma 'yan uwansa na gefe da gefensa, yayin da masu busa algaitu suka cigaba da aikinsu tare da rufa musu baya....Lokacin masu camera man vedio camera suka fara aikinsu suma 'yan Jarida ba'a barsu a baya ba aikin daukar hotonsa kawai sukeyi shi kuma yana d'agawa jama'ar dake gefe da gefan sa hannu ammafa babu walwala ko ta kwabo a fuskarsa wanda ya kamata ace ya saki fuskarsa ya tar'bi dubbanin mutanan dake murnar dawowarsa gida ko a jikinsa daga karshe ma daya ga yana damun kansa sauke hannunsa yayi sai kawai ya sunkuyar da kansa ya cigaba da tafiya babu um! babu umum!! Sukuwa jama'ar masarautar sai kirari suke masa gami dayi masa fatan alkairi a rayuwarsa amma gogan bai d'ago kansa ba ballantana yasan sunayi.........."Wani irin takaici ne ya rufe ni naja tsaki tare da kauda kaina daga kallonsa tabbas na gazagata maganganun da jama'a sukeyi a kansa na rashin kirkinsa yanzu ina laifi ga wanda ke murna da zuwanka gami dayi maka addua idan da mutunci yaci ace ya d'ago kansa ya nuna jin dadinsa amma saboda tsabar izzah! ya gagara kallon inuwar inda mutanan ke tsaitsaye.
Silalewa nayi daga cikin iyayena na kama hanya domin tafiya can shashenmu na bayi, zuwa zanyi na huta dan bazan iya jurar tsayuwa ba rana sai duka na take gashi wanda akeyi dominsa baya gani, mahaifina kawai nake tausayawa dan ba wata cikakkiyar lafiya gareshi ba amma saboda tsabar bin dokar masarauta yasa ya lalla'ba ya fito ya tsaya a matsayinsa..............
*BINTA UMAR ABBALE*

*Kuyi sharing👏🏻*
[1/13, 9:47 PM] 💜: *'KWARYA TABI 'KWARYA*
*NA*
_BINTA UMAR ABBALE🍒_ *bintaumarabbale@gmail.com*


*MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION📘🖊️*
_'Kungiyar Masu Nazari da Aiki da Ilimi_
_________________________
*Littafin na kudi ne....!*
_#300.....0542382124...Binta Umar gtbank...idan kati zaki turo #400 ne sai ki same ni ta wannan numbers..08089965176 _07084653262 Zanyi miki bayanin yanda zaki turo katin.......... Ga masu bukatar VIP Group 600 ne_
_Mutanan Nijar zaku tura dala dari ta wannan numbers katin airtal ko orange VIP jakka d'aya 90899076_88137740_



*SADAUKARWA NE*
*GA*
*HAJIYA SHAFA'ATU S YARI*
(Kainuwa Dashan Allah✊🏻)
5&6
Bayan mun koma gurin tsayuwar mu mun nutsu sai maimartaba ya umarci yaron nasa daya fito ya nunawa jama'a farin cikinsa na dawowarsa masarauta lafiya....A lokacin idanun jamaa yayi caaa! a kansa kowa kokarinsa yayi tozali dashi, ni dai sunkuyar da kaina qasa nayi saboda jin yanda gabana yake faduwa haka kurrum naji bana bukatar kallonsa ba dan komai ba sai dan mugun halinsa na rashin ganin darajar mutane........Wani bafade ne yay gaggawar gyara masa abin magana ya saita masa daidai bakinsa, kamar wanda akayi wa dole yay gyara sai da yaja lokaci tukkuna cikin rashin walwala a fuskarsa da maganarsa yace."Alhamdullilah Allah kaine abin godiya. hakika nayi farin ciki mutuka daga dawo dani gida cikin koshin lafiya gami da tarin nasarori masu yawa." shiru yayi tare da sunkuyar da kansa qasa. Jin yayi shiru yasa nayi saurin dago kaina ina kallon gurin da yake, gani nayi kansa a sunkuye yana kallon 'kasan gurun tamkar me neman wani abu......Tsaki naja a cikin zuciyata nace"Wannan anyi d'an wulaqanci ya sani sarai jama'a shi suke sauraro amma ya fara magana yayi shiru, kaina na d'auke ina jin takaicin abinda yake......Gyaran murya ya kuma yi kafin ya cigaba da magana..."Sannan kuma nayi farin cikin samun iyayena da 'yan uwana da dukkanin wanda ke k'ark'ashin masarautar nan lafiya hakika naji dadi sosai da ganin yanda kuka fito 'ya'yanku da jikokin ku kuka nuna farin cikin ku dangane da dawowa ta gida Nagode sosai inayi muku fatan alkairi." yana k'are maganarsa ya janye bakinsa daga gurin abin maganar can kusa da Waziri ya koma ya tsaya har yanzu babu fara'a a fuskarsa.
Hayaniya da kace kace ne ya cika gurin, Wani bafade yayi tsawa tare da umartar kowa yay shuru kafin minti biyu gurin yayi tsit! Maimartaba ya miqe a nutse ya karasa gurin da abin magana yake, kafin ya fara magana sai da ya d'aga hannuwan sa sama alamar gaisuwa ga tarin jama'ar dake gurin.....Gurin ya sake rikicewa da hayaniya kowa sai fadin albarkacin bakinsa yake akan maimartaba. Da kyar aka samu sukayi shuru suka bar maimartabar yayi jawabi gami da miqa godiyarsa ga Allah ya kuma miqa godiyarsa ga tarin manyan mutanan da suka samu hallatar gurin suma bayin dake karkashin masarautarsa sai da ya miqa godiyarsa a gurinsu sannan ya koma ya zauna gurin zamansa, Baba Waziri yazo yay nasa jawabin Galadima da Ciroma suma sukayi nasu daidai gwargwado sannan maimartaba ya rufe taron da addua, ya miqe da niyyar shiga cikin gida fadawa ne suka kewaye shi suna ta gyara kintsi dai."!! Gurin ya karad'e da bushebushe gami da tashin muryoyin maro'ka da hayaniyar jama'a, sai da Sarki da muqarrabansa suka shiga gida tukkuna aka samu lafiya, jama'ar gurin suka watse kowa ya nufi 'bangaran da yake a cikin gidan.........Nida iyayena Cikin yanayi na ciwo muka shiga gurin mu, da sauri muka zaunar dashi, Tambaya ta ri'ke kafadarsa ni kuma hankali a tashe naje na d'ebo masa ruwa jiki na kyarma nazo na tallafo kansa ina kokarin bashi ruwan, bakinsa ya bud'e ina sa masa ruwan yana dawowa, lokaci guda zuciyoyinmu suka karye nida mahaifiyata hawaye muka fara, cikin karfin hali gami da kokarin janyo maganar yace."Ku daina kuka bashi ne abinda nake bukata ba."!
Zama nayi kusa dashi na rike hannunsa har yanzu hawaye bai da zubo min ba nace"Baba wai dan Allah me yake damunka kwana biyu ka'ki lafiya kullum cikin rashin kuzari da karfin jiki gashi kuma ka'ki ka bari a kira mai kula da lafiya yazo ya duba ka."
A hankali yace."Sumayya ba wani ciwo mai tsanani bane yake damuna zazza'bi ne mai zafi sai hajijiya gami da rashin kuzari to ni dik a tunani na ko shawara ce shiyasa na mayar da hankalina gurin shan maganinta amma yanzu ina ganin dole kije ki kira d'aya daga cikin masu kula da lafiya yazo ya dubani dan ni kadai nasan abinda nakeji a cikin jikina.
Tambaya hawaye ta share a sanyaye ta kalleni da fadin"Kiji can bangaran masu kula da lafiyar ki kirawo daya daga cikinsu yazo ya dubashi ni kaina jikina yay sanyi da wannan rashin lafiyar tasa a tsaitsaye fa ya kai sati hudu yanayi duk da yana shan maganin shawarar babu sauki kullum jikin rikicewa keyi."
Miqewa nayi da sauri nace "Bari naje can gurinsu na samesu." takalma na zura da saurin gaske na kama hanyar sashen masu kula da lafiyar gabad'aya bana cikin hayyacina ina tsananin kaunar mahaifina shiyasa rashin lafiyarsa ta d'aga min hankali mutuka.

"Sumayya." Sunana naji an kira da sauri na tsaya ina waigen bayana.

babu walwala a fuskarsa ya karaso inda nake tsaye kai tsaye yace."Ina Lawi yake ya bar aikinsa kamata yayi ace kafin mu fita gurin taro ya zubawa dokuna abinci yanda zai ishesu yanzu yanzu na shiga gurin na tarar da gabad'aya babu abinci a gabansu idan fa maimartaba ya samu labarin abinda yake zai fuskanci hukunci."

A marairace nace"Buba dan Allah kayi hakuri kada ka kai 'korafi wallahi babana bashi da lafiya tsayin sati hudu yake ciwo a tsaitsaye dukkanin abinda yake dauriya kawai yake dan Allah ka taimaka masa kana bawa dawakan abincin kafin yaji sauqi.

"Ke! saurara da wannan maganar.'' Nayi saurin kallonsa kwalla na kokarin zobomin, Ya cigaba da cewa''Kowa da kika gani akawai aikinsa a masarautar nan nawa aikin ma yafi nasa wahala tinda ni kwana nake a tsaye ina zirga zirga banga dalilin da zai sanya na d'auki nauyin wani na d'orawa kaina ba, ke aikin me kike da ba zaki d'auki nauyin mahaifinki ba kafin ya samu lafiya.

Hannu nasa na goge hawayen da suka zubo min nace" Shikkenan zanyi kokari ganin na dauki ragamar kula da dawakan kamar yanda babana yake yi amma ka san dai muna zaman karatu ranaku uku a sati ko kuma idan mun zauna tin safe sai yamma muke tashi.
D'aga kafad'a yay yace."Ke zaki tsarawa kanki yanda al'amura zasu tafi ni dai na fad'a miki ku kula da aikin ku kada maimartaba yaji wata magana.

Ajiyar zuciya na sauke mai zafi! nace"Shikkenan Buba nagode sosai insha Allahu zan iyakacin bakin kokarina." Gyda kansa yayi ya bar gurin, nima da sauri na wuce domin nufar inda nayi niyya.

Na jima a tsaye a bakin kofar d'akin nasu ina sallama kafin naji an amsa da fadin"Ko wacece ta shigo.'' Jim nayi ina tunanin shiga dan gabad'ayansu maza ne a ciki ina ganin kamar hakan bai dace ba.

Sallama na sakeyi, naji anyi min tsawa! da fad'in "Wai wacece take sallama ne ki shigo ki fadi uzirinki." Shahada nayi na tura kaina dakin....wasu na kwance kan katifunsu wasu kuma na zazzaune daga su sai gajerun wanduna.
Daga bakin kofa na tsaya nace"Dan Allah d'aya yazo ya duba babana Lawi bashi da lafiya."

Shuru sukayi min kowa ya cigaba da sabgarsa, raina ya 'baci! nace"Magana fa nakeyi muku kuna jina." 'Dantala ya zaburo min da hayaniya yace."Ke! babu wanda zai katse abinda yake a cikinmu yaje ya duba babanki idan kina so ayi miki abinda kike so ki shigo ciki muna bukatarki."

Cike da mamaki nake kallonsu nace"aikin ku ne fa mai zai sanya kuce sai nayi muku wani abu sannan zakuyi to ni ba 'yar iska bace idan kun saba latsa 'yan matan dake masarautar to ni ba' irinsu bace kuma wallahi idan bakuyi wasa ba yanzu zanje fadar sarki na sheda masa abinda kuke aikatawa..........A fusace! naga ya miqe yayo kaina zai mareni na kauce da sauri ina kare fuskata....wanda yake da sauqin halin cikinsu ne ya miqe tare da zira rigarsa ya kalleni da fadin" Shige muje na duba jikin mahaifin naki." Da sauri na fita daga dakin gabana sai faduwa yake......Tafiya nake zugwi zugwi ina mamakin al'amarin, kawai naji ana ta'ba min mazaunai! Da sauri na juyo ina kallonsa, murmushi yayi ya sosa kansa ido jawur yace."A gaskiya Sumayya Allah yayi miki baiwa mai mutukar daukar hankali, kina da duk abinda d'a namiji ke bukata a jikin mace kirjinki a cike yake dam-dam uwa uba mazaunai masu masifar rikimin lissafi wallahi tunda kika shiga dakinmu sha'awata ta tashi dan Allah ki bani damar mallakar wannan jikin naki wanda yake kokarin fitar dani hayyacina.

Kallonsa kawai nake wani 'katoton abu ya tokare min a ma'koshi nace"Yanzu Usman ashe kaima halinku d'aya dasu Dantala a zahiri...


Read / Download KWARYA TA BI KWARYA

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

1 Comments On KWARYA TA BI KWARYA
avatar
daiy

5 months ago

Reply

Good

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album