Join Our WhatsApp Group

HALIN RAYUWA Book 4 Complete Hausa Novel Document by HALIN RAYUWA Book 4


HALIN RAYUWA Book 4

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 46745



HALIN RAYUWA Book 4

Reading Time: 3 Hours

Added On: 24, Apr 2023

Author: Hafsat Sodangi ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : 07035586299

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 231.78 kb

File Type: txt

Views: 3193+

Download: 1315+

Last download: 4 hours ago

Description/Story: HALIN RAYUWA



4


HAFSAT G. SODANGI

Mr. Yunus Abdullahi Dabai

1

Hakkin Mallaka (m) Sodangi
Copyright O Sodangi

GODIYA
Godiyata har kullum ga Allah take, Masanin yau da
gobe, mai kowa mai komai, Gwani mai hikima wanda
yayi halitta tasa duka bibiyu, ya kuma halicci mutum da
Aljan don su bautata mishi,
Tsira da Aminci su tabbata ga cikamakin Anabawa
shugaban Manzanni, Annabin Karshe Muhammad
(SAW) da Alayensa da Sahabbansa da wadinda suka bi
ma tafarkinsa na gaskiya har zauwa ranar Altiyama,
amin.
Godiya mai yawa gare ku makaramta litattafaina, m
kusa da na nesa, Ubangiji ya saka da alheri ys kuma Rara karfafa zumuncin da ke tsakani, na gode.

SADAUKARWA
Sadaukarwar littafin ta lyayena ce, Ahaji Chindo
Muhammad Sodangi da Hajiya Fevime Musa Sodangi,
Ubangiji ya saka muku da alheri ya kums fara muku
lafiya amin.

TUKUICI
Tukuicin littafin naki ne:
KHADIJA CHINDO SODANGI (Mrs Nasiru ldris)
2

JINJINA
Jinjinar littafin taki ce Amarya ba kya laifi (Manc
Umar) Zuhuriyya lbrahim (Mrs LAwal Chindo Sodangi),
Ubangiji ya raya Umar da imani.

FATAN ALHERI GARE KU
Fatima Abdulkadir Kazaure
Hafsat Iliyasu Unguwar Rimi
Khadija Usman Nasarawa
Nafisatu Ibrahim Muhammad
Fatima Ahmad Shehu Kaduna
Maryam Muhammad Gusau, Zamfara
Umaima Abubakar Umar
Maijidda Uba Magaji
Na gode, Ubangiji ya saka da alheri, amin.

KUNA RAINA
Hajiya Maryam (Mami) Dan Hassarn
Hajiya Jamila Ibrahim Na Bature
Hajiya A 'isha Balarabe (Jazan)
Ubangiji ya bar zumunci amin.

3

LITTATTAFAN SODANGI:
1. Uwar miji
2. Naga ta kaina
3. Rabon kwado..
16. Wacece ni?
17.Wata fuskar..
18. Mijin ta ce
19. Garin banza...
20. Ga ni gare ka
21.Biyan Bukatar rai
22. Shamaki
23. Hattara
4. Cikar alkawari
5. Wayyo duniya
6. Yi wa wani..
7. Abu naka...
8. Mata ma su duniya
9, Nufin Allah
10. Kifin na ganinka...
11. Daga kin gaskiya...
12. Da kamar wuya...
13. Mai uwa...
14. Duk daya...
15. Mata da kicin dinsu
24. Kyautata
25. Ayi dai mu gani...
26. Tabbataccen al'amari
27. In kunne ya ji..
28. Halin Rayuwa
29. Mai Daki...

Littattafan ba sa nufin yi da wani ko habaici ga
kowa, sai dai an rubuta su ne don fadakarwa da
nishadantarwa, ana neman afirwa ga duk wanda yaga
wani abu yayi kamar abinda ya shafe shi, ba da shi ake
ba dace ne kawai.
4

HALIN RAYUWA4
A wannan lokacin ba zai yiwu in iya kwatanta halin
da nake ciki, ba na tsoro, abu guda daya dai da
zuciyata ta kasa yarda da shi, shi ne a in bar Rauhani
ya yi min abin da yake son yi min, da in har shi ya yi
min hakan sai na gwammace ma kawai gara duk abin
da zai faru da ni ya faru koda kuwa wani abu ne da ya
fi hauka muni.
Tsayarwa kaina wannan hukunci da zuciyata ta yi,
sai ya zama dalilin da na samu kuzarin takarkarcwa na
kurmawa Rauhani ihu da iyakacin karfina.
A bar ni bana son aikin, a bar ni kawai na ce a bar
ni. Abinda nake ta fadi kenan.
Iskar da ke kadawa a dakin ta tsaya nan take kuma
haske ya bayyana a dakin, sai ga Mallan a zaune a
wurin zamanshi, hularshi zaune daram a ken shi, nimaa
nayi maza na mike na zauna muka fuslkanci juna ni da
shi.
Maryam kin 6ata aikinki,kin yi duk abinda aka ce
miki kar kiyi, kin yi musu, kin yi gardama, kin yi
jayayya har da kokawa. Ya tafí yana fushi yanzu ya ya
kenan?
Ban iya buda bakina nayi magana ba, balle in iya
amsa mishi tambayar tashi, saboda har lokacin ina
cikin tsananin tsoro, jikina ma bai daina 6arin da yake
yi ba. Ban sani ba ko ya gane hakanne yasa shi kawo
shawarar cewa ya sake kiran Rauhanin ya ba shi
5

hakuri, ya yi aikin da ya zo yin don kar haukan da ya
yi alkawari ya same ni.
Nayi maza na ce mishi "Aa, a bar ni kawai." "A
bar ki hauka ta same ki? nayi shiru ban amsa ba, "Kin
gwammace kiyi hauka ko?" Na sake yin shiru, "To shi
kenan tunda abinda ki ka zaba kenan, dulk abinda ya
faru da ke dai ba za a sake kawo mana ke nan mu
karbe ki ba, tunda kina cikin bijirarrun mutane masu
taurin kai.
Sakamakon taurin kai kuma nadama ne. Ina kuma
yi miki albishir da hauka kafin fitarki cikin wannan
dajin." Yana fadin hakan naji an daka min wata irin
tsawa, wanda saboda tsananin tsoro na kasa fahimtar
daga in da tsawar ta fito Tashi ki ba mu wuri."
Abinda naji an fadi kenan da karfi.
Ina jin hakan nayi maza nayi waje, yankawa kawai
nayi da gudu ba tare da na tsaya neman takalmina ko
tunanin ta ina na fito ina kuma ya kamata in dosa?
Gudu kawai nake yi a cikin jejin nan, bana ko
waiwaye ban kuma san inda na dosa ba.
Gaba daya fatana da addu'ata bai wuce in isa
gaban mahaifina kafin haukar ta same ni ba. Ina gudun
ina kokarin jaddadawa kaina har yanzu dai da
hankalina, hauka bata fara samuna ba tukuna, tunda
duk abinda nake gani ina ganewa, ina kuma iya tuna
komai nawa sai in yi maza in ci gaba da karanta
addu'ar da damna nake ta karantawa Hasbunallahu
wani' imal wakil."
6

Ina cikin haka na hango wani mutum a gabanta,
tsoro ya kara kama ni, ina tunanin ko Mallam ne ya
turo shi ya zo ya mayar mishi da ni,
Nayi kamar in juya da baya saboda tsananin
tsoratar da nayi, sai kuma naga to ai in shi dinne ma
zan iya juyawar ya sake tare ni a inda na koma din,
don haka na dake zuciyata na ci gaba da taiyata har
naje kusa da shi zan wuce naga ashe manomi ne yake
aii a gonarshi, sai dai ban iya buda baki na tambaye
shi hanya ba, saboda kar ya gane ni din bakuwar jejin
ce.
Nayi tafiya rannan har na raina kaina, amma
zuciyata bata gaji ba, ko tsayawa in huta bana yi,
kokarina kawai in fita bakin hanya ne in ga gari in ga
ta inda na bulla don na riga nasan na kauce banya.
Ina cikin haka na sake hango wani mutum da sauri
na nufi wurinsli daga nesa kadan na tsaya na gaishe
shi nayi mishi tambaya kan hanyar da zan bi in shiga
gari
Barin abinda yake yi ya yi ya taya yana lallona,
ke kuwa ya ya aka yi ki ka kawo yanzu cikin dajin
nan? Ban iya ce mishi komai ba, don haka ya gaji ya
ce min Kina kusa da gari sai dai akwai tabkeken rafi a
tsakaninki da shi, in kin iya ruwa ze ki iya bin nan ki
fada raf ki tsallaka, in kuwa kin san ba ki iya ruwan
sosai ba, sai ki bi nari don rafin yana da zurfi, in an yi
ruwa ya kawo ba karamin ta'adi yake yi ba.
7

Na ce, Na gode. Har na fara tafiya ta nan din da ya
ce, sai naji ya daga murya ya ce min kiyi ta tafiya har
sai kin ga yar gada sai ki hauta ki tsallaka za ki ga
kauye a nan za ki samü abin hawa zuwa cikin gari."
Na sake cewa "To na gode.
Wannan hanyar da ya nuna min din ita nabi nayi.ta
tafiya har na kai inda ya ce zan ga gada, gadar ta
langa-langa ne, wanda mutancn wurin suka hadu suka
yi don su rinka samu suna tsallakawa zuwa inda
gonakinsu suke in ban da gudun ceton rai nake yi babu
abinda zai sa in iya hawanta.
Na isa kauyen, a lokacin da duhun dare ya riga ya
sauka ya mamaye ko ina, ga shi babu haske ko kadan,
don kuwa babu. wutar lantarki a kauyen, babu kuma
hasken farin wata saboda watan ya kusa karewa.
A haka na wuce kauyen nan nayi tafiya har inda na
samu wani mai mashin da ya yarda ya fidda i bakin
hanya a dalilin tsananin gajiyar da ya gani a tare da ni.
A kofar gida na samu Babana a tsugune yana tashe
da fitilar kwai, daga ganin ikuma nasan ya yi
wahala ya neme ni har ya gaji.
Ina isa gabanshi na fadi a kasa ina kuka tare da
fadin "Ka yafe min Baba." Ban wani tsaya bata lokaci
ba nayi maza na attaba mishi bayanin komai, tunda
nayi saa nazo gabanshi da hankalina, shi yasa nayi
maza na gaya mishi don ya sani saboda kar haukar ta
Same ni yayi tunanin zai yi ta wahalar neman min
magani tunda ba hauka ce da zata warke ba, ka
8

taimake ni Baba ka tsare ni wuri daya kar ka bar ni in
yi ta yawo a tube irin yanda nake ganin yan uwan
mahaukata suna barinsu suna yi."
"Ke Yahcuwuna. Ya kira sunan nawa cikin wani
irin yanayi na damuwa, "Ki daina yin haka bari fadin
irin wannan maganar, ya ya ki ke yi wa kanki
mummunan fata irin wannan? Nayi maza na ce,
"Baba mai Rauhani ne ya gaya min ai har kokawa da
Rauhanin ma nayi.
Ya mika hannu ya kama nawa "Zo mu shiga gidan,
na godewa Ubangiji da ya dawo min da ke lafiya."
Baba Lantana ta galla mishi harara ta ce, "Uhun, ai kai
kam ka shiga uku, yarinya ta tafi taje ta gama barikinta
ta dawo tana dingishin ta samu wadanda suka fi
karfinta, amma kana bari kana fadin wai ka gode
Ubangiji saboda ta maida kai sakarai."
Isyaku ya yi sallama daga tsakar gida ya tsaya yayi
tambaya, "Baba wai Anti Meron ta dawo?" Da sauri
Babana ya ce, "Eh, ta dawo." Ba tare da ya tsaya
tambayar in ji waye ba, ta sake fadin "Ka ji wani irin
rainin hankali ma Malam, sai ka ce ba tare suke ba, sai
ka ce ba shi ya kawota ya ajiye ya wuce gidanshi.."
tayi maza tayi kasake ta bar maganganun da take yi ta
koma sauraron bayanin da Baba yake yi min.
Ai ba za ki yi hauka ba, ai karya yayi miki ba
Rauhani ba ne, shi mutumin ne da kanshi yayi miki
wannan abin don ya samu ya tsoratar da ke, ki yarda
yayi lalata da ke. Ba mutumin kirki ba ne, Boka ne. Ko

9
Malamin tsubbu. Ba da Rauhani ki ka yi kokawa ba,
bai yi nasara ba ne a kanki saboda ke din mutuniyár
kirki ce, uwarki ma haka, Ramatu mutuniyar kirki ce
sannan bata da tsoro.
Baba Lantana taja mummunan tsaki "Wannan
Ramatu ai bata kyauia ba da bata jaka ku ka tafi tare
ba.". Tuni sai ta bar maganar da take yi ta ni da
Mubarak muka fita yawo, ta koma ta Rauhani da
hauka don tafi yi mata dadi.
"Hauka kam ai sai kin yi tunda Rauhani ya ce sai
kin yi, to shi yana karya ne ma da za'ka ce mata ba za
ta yi ba? Ba dai har nan dama Dijan take kai ba? Ai
kuwa dai kun tsokano tsuliyar Dodo."
Sallau yayi sallama ya shigo tare da fadin "Baba
ashe ta davo?" Ai ta dawo Sallau ya sake fita ya sayo
min shayi da biredi in banda yayi wannan dabarar
watakila da haka na kwana ni da Babana ba muyi
wannan tunanin ba, balle Baba Lantana.
Kwana muka yi Babana yana rike da allon
Karfenshi yana rubutu yana wankewa yana bani ina
sha, saboda na kasa ko da runtsawa ne in yi saboda
tsananin tsoron da nake ciki.
Washegari da sassafe sai ga Yakumbo Halima da
Yaya Dijah sun iso, ita kam Yakumbo taje wajen Yaya
Dijah ne wai ta ji taje na karbo sakon ko ban je ba naki
Zuwa? Yaya Dijah ta ce, "AI ma wunin jiya ba a ganni
ba ana ta nemana kan haka suka rankayo gida don Su

10

gani na dawo ko ban dawo ba? In ban dawo ba a nufi
gidan Malami."
Sai suka zo sulka same ni, Babana ya kwashe
bayani yayi musu, suka yi wa juna barka saboda ban
yarda na ambaci sunan Yakumbo Halima cikin
bayanin da nayi mishi ba, da ban san yanda suka
kwashe ba.
Bayan fitanshi ne Yakumbo ta rinka rantsuwa wai
tana so in yarda bata san haka yake.ba, don bai taba
nuna mata ba. Yaya Dijah ta ce mata "Haba Yakumbo,
bari wannan rantsuwa da ki ke yi, za ki kai ta in da za
a cuce ta ne da saninki."
Wai a wannan dan zuwan da suka yi sai da Baba
Lantana ta sossoka musu maganganun da Yakümbo ta
tanka mata suka yi fada kaca-kaca.
Ba karamin rashin lafiya nayi ba saboda wahala da
kuma ciwon da kafafuwana suke yi, tayi a dalilin
raunukan da suka samu ta hanyar taka kayoyin da ke
watse kan hanyoyin jeji da kananan itatuwa.
Duk da halin da nake ciki na kusan kullum sai
Babana yasa allura ya cire min wata kaya a kafa, ba
wannan ne abinda yafi damuna da tsaya min rai ba,
irin tabbatar min da Babana yayi cewar shi wannan
mutumin da muka je wurinshi ba kowa ba ne illa
Boka' saboda ni da kaina na ta6a kamanta wani hadisi
da ya ce, "Wanda duk yaje gun Boka ya kuma yarda
da abinda Boka ya gaya mishi, to ya kafurta da abinda
Manzon Rahama (S.A.W) yazo da shi, in kuwa yaje

11

wurin Boka bai yarda da abinda Boka ya gaya mishi
ba, to zai yi kwana arba'in yana Ibadar da ba za a
karba ba."
To wannene mai sauki a ciki? Sai na samu kaina
cikin wani irin yanayi ma tsananin rashin lafiya a
dalilin tsananin tsoro da tasin hankali, babu abinda
nake tsoro iris mutuwa a tsakanin wadannan ban samu
yar nutsuwar zuciyaia ba sai da Babana yayi min
bayani dalla-dalla, lokacin ne na dan samu natsuwar
zuciya ta na koma yin Istigifari da kyautata zato wurin
Ubangiji tare da kudurawa raina ba zan sake ba.
Ba zan sake zuwa wurin wani ba da sunan neman
taimako akan aurena ko a kan wani dalili na daban,
dama can ban taba ba, in ban da warinan lokacin to ba
zan sake ba gaba daya lamurrana dama ga Ubangiji
suke, ga. t shin kuma zan kara maida su, in kara
dogara in har da rabon zan yi aure an ubuta cikin
kaddarar rayuwata, to zan yi. Dor nayi Imani da
kaddatsare mai kyau da mara kyau.
Sanna rashin auren in har an kame kai ba zai
zamo munnaunan kaddara ba in har ba a rinka
watsewa ba, nan take nä shiga tunano manyan mata da
suka gama rayuwarsu ba tare da sun yi auren ba, ko
suka bar shi a shekarunsu naa kuruciya suka maida
hankulansu kawai wajen yin Ibadarsu, da auren da baa
san ka'idarshi ba, ba a tsare mutunci da
sharuddodinshi ba, ai gara barin shi yafi.
12

Nan take sai naji zuciyata tana kara raya min tsare
budurcina da yin komai wajen ganin budurcin nawa
yaci gaba da kasancewa a tare da ni, matukar ina cikin
hayyacina saboda in zamo daga cikin 'yanmata masu
mutunci da ke kaiwa mazajensu 'yanmatancinsu, ko
kuma suke gama rayuwarsu su koma ga Mahaliccinsu
da abinsu a tare da su.
Kan haka sai na kara kudurawa raina cewar zan
Kara kyautata sana'ata in kara riketa hannu bibbiyu
don ta zamo min abinda zan rike wajen ganin nayi ta
karatuna, ban zamo mai dora nauyina ga kowa ba.
Kusan satina biyu a gida ban fita ko'ina ba, ina
jinyar kafafuna a kwanakin nan duka babu wata rana
da gari ya waye har yamma tazo ba tare da Baba
Lantana ta jaddada min haukan da Rauhani ya ambata
min zai same ni ba, don kuwa in ita muna yi mata
rashin mutunci muna kwana lafiya, don kawai
Faddarar wahala ta kawo ta gidanmu, ta auri tsohon
ubanmu, to ai shi Rauhani ba zamu yi mishi iya shege
ya kyale mu ba, tunda ba tsoron ubanmu ya ke yi ba.
Ko kallonta bana yi, maganar tata kuma ba ta
damuna saboda a yanzu, na ragë damuwa da
al'amarinta, ban da haka kuma nafi yarda dá maganar
Babana a kan tata, don haka ina cikin kwanciyar
hankalina, ga kuma neman auren da nasan Yaya Dijah
tana yi wa Babana, wanda nasan ba da dadewa zai
tabbata, tunda na shaida abubuwa da dama da ta
gabatar.
13

eNa soma zuwa Makaranta, wai ashe dan wannan
neman nawa da Babana yayi a gidajen makwabta da ke
kusa ma wai abin magana ne, ya madidi ake tayi da ni
da shi ana fadin wai ai gashi nan ya ki aurar da ni yana
jira sai ya samu' dan mai kudi irin Mubarak.
To ga shi...


Read / Download HALIN RAYUWA Book 4

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album