Subscribe for N1000/month for downloading access and an ad-free site. Contact WhatsApp +2348140419490 if you can't pay / subscribe. SUBSCRIBE

24 yin

VIXEEN Complete Hausa Novel Document by VIXEEN


VIXEEN

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 114518



VIXEEN

Reading Time: 9 Hours

Added On: 07, Mar 2025

Author: Aisha Mohammad Sani (Xayyishatul Humaira) ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : NOBLE WRITERS ASSOCIATION

Author Phone : 08103080717

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 617.12 kb

File Type: txt

Views: 29+

Download: 61+

Last download: 13 hours ago

Description/Story: [11/20, 1:03 PM] Xayyeesherthul-humaerath🥀: *°°°VIXEEN°°°*

*NOBLE WRITERS ASSOCIATION✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
*https://www.facebook.com/106494781436168/*

_#5Stars/Zeeyter/Yel/Freeya/Vixen._

©️ *XAYYEESHERTHUL-HUMAERATH*

_Idan na ce kar ku bari a baku labari,tabbas ina nufin ka da ku bari ko da kalma guda ce na cikin wannan Novel din ya wuceku,wacce ta karanta kadai ke da amsar hakan😻_
★★★
Bismillahir-Rahmanir-Rahim

PAGE-1&2

Na mutu cikin rayuwa ba adadi.
Na tsani kaina.
Kuma ina jin tsanar kowa ma a duniya.
Ji nake rayuwata bata da wani amfani domin kuwa ko da tana da amfanin ma sai dai ga masu zalunta ba dai a gareni ba.
Cikata Shakara Goma a rayuwa ya rusa mun duk wani tunani da Farinciki, har ma da burina.
Babu abun da na sani illa rayuwar shaye-shaye.
Da kuma abun da ke kasance tsakanin Namiji da 'Ya Mace.
Ana zalunta a boye kuma bani da damar bayyanarwa.
Makaranta ta zame mun wajen zuwa in yi kuka ba dai karatu ba.
Kanin Mahaifiyata shi ne silar komai.
Ya maida ni babbar mace don dole domin Kusantata kawai yake aduk lokacin da yaso.
Da nai kokarin sanar da mahaifiyata sai ta nuna mun rashin amincewarta ga hakan, har ya kai ga ta sanar da shi kan cewa ya hukuntani.
Haka suka hadu suka mun duka, a karshe ya rada mun cewa in har na kuskure na kara gigin sanar da wani hakan ba ma ni kadai ba hatta iyayenawa zai iya hadawa ya kashemu.
Rayuwata ta kara mun zafi.
Amman Babu wanda ya damu da ya nake ina lafiya? Meke damuna!

Wanda har ya kai ga Kawayena na makaranta sun fara fahimta.
A karshe suka jani cikinsu tare da gabatar mun da shaye-shaye matsayin maganin kowacce Matsala.
Da hakan na fara har ya kai ga na zarce su a harkar.
Ya kai ga har satan na Kawuna nake a gida ina sha.
Karshe da ya fahimta da kanshi ya ke kara daurani hanyar sha har ma na zamewa Kawayena Dilar da ke saida masu cikin makaranta.
Yanzu shekarata goma sha Uku a duniya na fara ganin canji a yanayi jikina, bayyanar girma da tunbina ya yi,hakan ya tabbatar mun da cewa ciki gareni.
Mahaifiyata da Mahaifina sun jima da fahimta amman sun gagara tankawa saboda tsaro da son abun duniya.
Ya ake so in rayu?
Bayan kullum ina kara rayuwa tare da kara jin tsanar kaina ne?

KHADEEJA (Deejerh)
Australia

★★★
End of Three Months Conversation Zoom Meeting.
5Stars.

"Ma Sha Allah Welcome all, fatan kowa na lafiya?"
Khalil ya fada.

Farouk ne ya yi saurin Faɗin, "Alhmdu Lillah We are all fine."
Ya karasa maganar yana kallon Haiydar kafin ya ce, "Wai ina Gimbiya ne? Tunda an hanani cewa tawa."

Haiydar ya yi Murmushi kafin ya ce, "Kun kusa ai kai zan tambaya."
Dukansu suka yi dariya.
Zahra na fadin, "Madam na cen tana fama da babynta na san shiyasa baza ma ta sauraremu ba."

Duk maganar nan da suke Deejerh ce kawai bata yi magana ba,ga dukkan alamu ma hankalinta na wani wajen ta tafi duniyar tunani.

Farouk dauke da plate a hannu ya na cika baki ya ce, "Ina ga zamu iya fara yanzu ko? ."

Zahra tai dariya, "Eheen Food Master tunda ka rike abun tabawa ai dole hali dai ba zai canja ba.

Khalil ya ce, "Zaku fara ko, muyi muyi asan matsaya domin kusan lokacin barcina ya yi ba sauraren ku zan yi ba, fatan komai na tafiya daidai,ko akwai wani mai fuskantar wata matsala?"

Kowa ya amsa da ba komai fuska a sake cikin yanayin Farinciki, Khalil ya kalli Deejerh da har lokacin bata ce Komai ba,ga dukkan alamu ma hankalin ta baya wajen ya ce, "Deejerh meke faruwane? U look so silent like hankalinki ma kwantata baya tattare da mu lafiya kuwa?"

"Yanzu haka tunanin wani bazawarinta take, kasan Yara in suka fada Tarkon Luv basa yi da wasa." Farouk ya fada.

Dukansu saida suka yi dariya har Deejerhn.
Kafin ta ce, "umm Wallahi halin rayuwar da na ga al'umma ke ciki shine ya tada mun hankali, na kasa samun Nutsuwa sam, ko barci jiya banyi ba da na rufe idanu kawai mutane nake gani suna cikin yunwa da talauci."

Gyara zama dukaninsu suka yi.
Farouk ya ce, "Ba mu labarin mana."

Deejerh ta numfasa kafin ta ce, "Al'umma na cikin wani hali sosai na neman yadda zasu rayu su ingata rayuwar su da ta 'Ya'yansu, wasu yunwa na kashe su, wasu sun zama barayin dole, wasu matan sun zama mazinata don dai kawai abasu kudin da za su ci abinci, wasu kuwa sun koma shaye-shaye, ni banma san ya zan kwantanta lamarin ba amman mutane da dama da hankalin su talauci yasa sun zama marasa hankali Mussaman rayuwar iyaye mata, basu da jarin da zasuyi sana'a bare har ya kai ga su dogara da kansu abun ya matuƙar tada mun hankali Mussaman yadda naga ana amfani da kanunun yara ana lalata da su duk don karamin kudin da zasu sai abinci su sa a baki musamman yan Nigeria a yanzu."

Jikinsu ya yi sanyi duka sai da suka yi shiru na yan mintuna kafin Haiydar ya ce, "Duk da cewa wannan zaman bana aiwatar da Business Project bane amman inaga akwai bukatar mu ɓullo da wani sabon abu da zai iya taimakawa al'unma su samu jarin da zasu dogara da kai."

"Yes, nima hakan nake tunani gaskiya ko yane, ya dai zam an samu hanyar kawar da yunwar da zata iya kawowa al'umma tozarta." Khalil ya faɗa.

Zahra ta ce, "Mussaman Mata don sun fi shiga cikin uƙuba."

Farouk ya gyara zama kafin ya ce, "Akwai hanyoyi da dama na hanyoyin da za a samawa mutane aiki cikin sauki kun ga kamar Naija State suna noma sosai garin na da abubuwan ban sha'awa wanda cikin sauki za a iya nemawa mutane aikinyi,suna noma doya mai kyau, shinkafa da abubuwa da dama amman kuma hakan na kasancewa kowacce karshen shekara ne,sai ya kasance yanzu sun bullo da hanyar soiless farm lab , wacce wata hanya ce ta musamman da za a iya yin noma ba sai a lokacin damina ba, ba sai anyi amfani da kasa ba zallan ruwa kawai, wanda hakan wata hanya ce ta musamman kuma mai sauki da aka samowa manoma ko ince ga marasa aikinyi wanda cikin ma'aikatan kaso saba'in mata ne, talatin ne za a ce mazan, kuma an kawar da yunwa cikin al'umma ta wani bangaren yadda baza a taba samun rashin abinci ba, tunda kowanni lokaci ana noma, hakan ya matukar birgeni kuma ma karin karawan da ya kasance a kasata ne,kasar tawa ma jahata ta Mussaman kuma suna da fili a Mokwa wanda agun zamu iya yin Public private partnership da government muyi amfani da filin wajen Soiless farm lab mu dauki matasa aiki ko da daliban dake Agric Tech ne School dinsu na cen kuma a mokwa din ma ana iya samun Waken Suya da rake Sosai, sannan su ko yaushe ana iya samun Doya ba kamar su Benue da yake season ba, kai innace zan tsaya lissafo abubuwan Nigeria zaku sha mamaki fa."

Dariya Khalil ya yi,ya ce, "Umm wato zaka nuna mana bambamci kai dan Nigeria, koma yane dai hakan ya birgeni inaga ya kamata musa shi ciki a tsarin mu sannan ina ga ba iya Nigeria ake fama da talaucin nan ba zamu hada harda Niger sannan kuma mu bincika sauran ƙasashen ma In Sha Allah ."

Farouk ya ce, "eh ina tunanin hakan amman kafin nan ga wani abu mai sauki da ya kamata muyiwa mutane, na ga akwai wani abu da ke trending a media mutum zaiyi rigista da dala goma kawai kullum sai ya dunga Mining na tsawon shekara guda yana samun kudi a kalla kowanni wata za a iya samun 15k me zai hana muyiwa mutane rigista da dala goman kudin farko da duk wacce aka ma rigista zata cire sai ta biyamu kudinmu mu kuma zamu ci gaba da rabawa mutane kun ga cikin shekara guda in mutum na da tattale zai iya tara Kudin da zai kai masa jari ya fara kasuwanci ko cikin wata uku ne ma zuwa shida ba sai an cika shekara ba, daga nan in muka ga mutum kasuwancin shi ya haɓaka zamu iya tallafa masu ta hanyar kara masu jari."

Da sauri Deejerh ta ce, "Great idea my Friend, shiyasa nake ji da kai , kwakwalarka bata wasa ba ce."

Farouk ya ce, "eheen kin sanmu mu yan Nigeria ba irinku ba mu muna da hangen nesa."

Khalil ya katse da su, "ba sai kun fara ba, ina ganin kawai acire kudin ya kamata kuma kake ganin zai isa sai ku rarraba wa mutane da suka cancanta kuma kuka san zasu dawo da shi."

Da haka suka kammala meeting din suna gamawa wani Farinciki ya lullube Deejerh na jin cewa aranta ko ba kowai wasu da yawa zasu fita daga cikin matsala.
Kwanciya tayi tana kallon saman dakinta.

★★★Barci ne cikin idanunta sosai bata an kare ba kawai ji tayi ana
Domin cigaba da karantawa sai ku downloading.
Yadda ake downloading na littafin: ku tabbata kunyi register da shafinmu sanna kunyi login, idan bakuyi register a kasa zakuga maballai guda biyu daya an rubuta LOGIN dayan kuma an rubuta REGISTER sai ku taba su kuyi register, daga nan sai ku yi subscription koda na naira 1000 ne, domin sai kunyi subs dinann ne kadai zaku iya dauko littatafanmu.

Ya ya akeyin Subscription namu : Bayan kun yi Login ko register daga kasa zaku ga wani jan maballi (button) an rubuta SUBSCRIBE sai ku taba shi zai kaiku inda zaku zabi package wato tsarin subs na ku da mu. akwai na wata guda, watanni biyar da shekara guda. da zarar kun zaba zai kaiku inda zaku biya kudin, wanda daga nan sai ku cigaba da downloading kawai abunku

ABUN LURA : duk wani littafi da kuka gani a shafinnan kyauta ne, wannan tsari mun zo da shine don mu samu hanyar da zamu iya rike shafin muna managing na shi, izan ku kayi subs na mu tamkar DONATION ne ku ka yi mana, ku ka bamu kwarin guiwa don mu ciagaba da kawo muku sabbin littatafai, amma duk wanda ya ga bazai iya ba toh zai iya karanta littafin kyauta a cikin shafinnan namu batare da ya downloading ba, kawai ya yi kasa zai ga Koren maballi (button an rubuta) START READING sai ya taba zai kaishi inda zai karanta littafin.

Sannan duk wanda yaga kamn wannan process din zai bashi wahala kai tsaye zai iya min magana ta whatssApp +2348140419490, ya tura min kudin ni kuma zan dora mai subs din akan account na shi

NB: iya ta haka ne zaku iya karanta wannan littafi a shafinmu babu wata hanyar. DAN ALLAH KU DAINA MANA MAGANA AKAN MU TURA MUKU LITTAFI TA WHATSAPP, BAMA TURAWA HANYA GUDA MUKE TURA LITTATAFANMU SHINE WEBSITE NA MU https://taskarnovels.com.ng DUK MAI BUKATAR LITTAFINMU YA JE CAN YA KYAUTA NE, AMMA DOWNLOADING KUWA BA KYAUTA BANE SAI YAYI SUBSCRIPTION NA WEBSITE NAM
This is not the real Download Button


Read / Download VIXEEN

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

This is not the real Download Button
Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album