Join Our WhatsApp Group

YARIMA ABDULMALEEK Complete Hausa Novel Document by YARIMA ABDULMALEEK


YARIMA ABDULMALEEK

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 33876



YARIMA ABDULMALEEK

Reading Time: 2 Hours

Added On: 02, Mar 2024

Author: Yusrah Musa Abubakar ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : ANNURI WRITER'S ASSOCIATION

Author Phone : 09055273614

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 179.84 kb

File Type: txt

Views: 565+

Download: 461+

Last download: 2 days ago

Description/Story: [11/25, 5:27 PM] Yusrah Musa Abubakar: *👑YARIMA ABDUL-MALIK 👑*






*💫ANNURI WRITER'S ASSOCIATION💫*






*Story & written*

*By*
*Yusrah Musa Abubakar*
*(Mrs Al'ameen Ahmed)*



*Dedicated to Zarah Musa Dan Adam*




*In the name of Allah the beneficent and the most merciful*





*Be good be helpful everybody will like 💗 u*



*Page 1*





Abuja fct babban birnin tarayya, misalin karfe shida na safe, hadari ne sosai ya taso garin ya bada kala mai kyau. Sakamakon rana bata fito ba, gashi ana kada iska mai ni'ima.


Wani kayattaccen layi ne, yasha kwalta mai kyau, sai walwali yake, gashi an kawata shi da fitilu masu d'aukar hankali. Tun daga farkon anguwar zaka san ba anguwar masu karamin karfi bace, yadda tsarin ta yake da tafka tafkan gidaje na alfarma.

Wani kyakkyawan gida ne, mai dogon gini ya gaji da kyau. Kuma ko ba'a fada maka ba kasan gidan sarauta ne, saboda yanayin zanukan jikin gidan da tambarin masarauta. Dai-dai wannan lokacin, wasu matane uku ne, ri'ke da wani mutum da kayan fadawa a jikin su. A yanayin rikon da sukai masa zasan laifi yai suka kamoshi.

A kofar tangame man get d'in gidan suka tsaya. Tare da 'kwan'kwasawa. Ganin haka yasa nace, bari na bisu, domin naga meke faruwa fadar. Irin tsaruwar gidan bata lokacine, tafiya ce mai tsawo sukai, sannan suka tsaya a wata iriyar kofa ta glass. Da alama wani suke jira. Sun kai minti goma a gurin, kafin suka hango shi tafe ta cikin glass d'in, da sauri suka bud'e kofar, cikin girmamawa suka duka masa.

Wai wai wai, masha Allah. Zan kad'i, wani kyakkyawan saurayi ne, fari tas dashi. Ya fito sanye da kayan army, wand'an da su kai matukar bala'in yin masa kyau. Umh da gani babu tambaya, wannan shine yarima Abdul-malik. Zare glass d'in idon shi yai, tare da zuba wa wanda aka kamo ido, tabd'i. Ni dai kauda fuska ta nai, dan wadannan razanannun idon na sa bazan iya kallonsu ba, wata firgitacciyar tsawa ya daka. Wanda ba mai laifin ba, hatta fadawan sai da suka tsorata. kowa yai zaman dabas a kasa, jiki na rawa,😂cikin fada ya fara magana" suraj na yarda dakai, shine zaka min haka? sai ka fada min uban waye ya baka poised, yace ka zuba min cikin abin sha, ko kuma ka karasa rayuwarka a gidan yari".


Kuka wanda aka kira da suraj keyi, amma ko kashe shi zaiyi bazai taba fada masa wanda ya bashi gubar ba. Ganin yadda jikinsa ke rawa, ya kasa mgn ya musu nuni da cewa, su tafi da shi su tambaye shi har sai ya basu amsa. Mikewa sukai, cikin girmamawa. suka tafi dashi, yana wani irin kuka. Dan yasan Allah ne ka d'ai yasan irin azabar da zai sha a gurinsu.

Gashin kansa yake shafawa cikin dunbin tunani to waye zai bada poised a bashi? waye keson ganin bayanshi? ganin ya kasa samun amsa yasa ya fito a part d'in, cikin wani irin taku ya nufi palon kakan sa, lokacin daya shiga dukkan ahlin gidan suna zaune a palon. Amma banda maman sa, dan bata wurin du'kawa yai, cikin girmamawa a gaban mai martaba. cikin tsananin so mai martaba ya riko hannun sa, yana murmushi. A duniya yana son Abdul-malik matuka a ransa. Kowa fuskarsa da walwala, banda Yahanasu da takejin duk duniya ba wanda take 'ki kamar sa. Wani irin firgitaccen kallo take binsa da. Ganin yadda mai martaba yake lailaya shi kamar jariri. Mai martaba ne ya fara magana "Muhammad ina fatan baka da wata matsala?" murmishi yai cikin jin dadin kular da mai martaba ke bashi yace "bana bukatan komai". kallonsa mai martaba yai "ka tabbata?" kai ya d'aga yana sakin wani kayattaccen murmishi. Ganin yadda yaha tai da fuskarta ita da mahmud kamar anyi musu mutuwa.

Abban mahmud shima dake kallon Yariman cikin kauna yace "idan akwai matsala ka fada min baba na, kasan ban san ganin ka cikin damuwa" tun kafin yai mgn yaha ta tare shi da fadin "haba mai sai kace wani yaro, sai tambayar sa kake, ai yana da hankali idan yana da matsalar zai fada. Idan adalci ne, ai ga mahmud meyasa shi baka tambaye shi ko yana da matsala ba?"

Murmishi abban mahmud yai yana kallonta, yace "ai in dai lamarin baba na ne, ni yafi gold a gurina. Ina ji dashi, ina ririta shi tamkar raina". Cikin bacin rai, yaha ke duban yarima kamar ana 'kara hura mata wutar 'kiyayyar sa a ranta. Kallon mahmud tai "tashi mu tafi" mi'kewa su kai, suka fita a dakin. Da kallo abba ya bisu yana mamakin wacce irin mace yake aure kamar yaha mara tunani haka Allah ya sau wa'ke. Duk ranar data kai shi bango zata sha mamakinsa.

Mi'kewa Yarima yai yana musu sallama ya fita, suna sa mai albarka. Part d'in maama d'in sa ya shiga, don kwata kwata idan bai ganta ba baya samun nutsuwa, yana shiga palon ya hangota kishingide, ganin sa da tai yasa ta mi'kewa zaune, tana tarar sa da murmushin kauna. Bako kunya yana zuwa ya kwanta a jikin ta. Hannu tasa a suman kansa tana shafawa, cikin murya mai sanayi tace "baby baka rabo da rigima har yanzun jinka kake yaro, kafa girma kosai ka fara ganin naka yaran zaka san ka girma?" mi'kewa zaune yai yana rike mata hannu a hankali yace "I love u my sweet momy fatan kin tashi lafiya? kuma ba wata matsala?" dariya tambayar ta bata tace "wato baby na fahimce ka, tambayar dasu mai martaba suke maka yau kuma ni ka kewa?" 'Kara rike hannunta yai cikin shagwaba yace "haba mama, kin san yadda nake jinki a raina ke d'aya ce tamkar da dubu. Dukkan wata soyayya da kulawata a gareki take ina matukar son ki my mah".
Murmushi tai cikin jin dad'i tace "na sani ba wanda kake so sama dani Allah yama albarka, sannan kuma kaci abinci? abinda baka so nace dagowa yai yana ganin ta kureshi da kallo yasa yace " eh zanci idan na koma" har lokacin kallonsa take tace "oh da gaske? toni ban yarda ba tashi muje ga abinci can kaci kada ulcer ta kama min kai".

Bata fuska yai irin baya so d'innan, mama tace "bazan barka ka tafi ba sai kaci ko kad'an ne," shiru yai yana karya wuya ya koma kalar tausayi dan ta barshi ya tafi. kiran sa akai a waya ya d'aga yana son kwacewa daga rikon datai masa amma taki sakin sa baiwace ta shigo da abincin ta ajiye sauke wayan yai yana kallon abincin ya dauke kai daukan spoon in tayi tana dibowa takai saitin bakinsa. Yai saurin rufe ido ganin idan ta biyeshi ba ci zaiyi ba ta aje spoon in tamai durar karfi da yaji.

Batun yaha kuwa suna komawa part d'ita ita da mahmud ta soma zagaya palor cikin taikaici, zama Mahmud yai cikin jan tsuka yace "wai dan Allah umma me yasa abba na yake min haka? kamar ba shine ya haifeni ba. Gaba d'aya ya tattare soyayyar sa, ya dorata akan Abdul-malik. kafin ya kira sunana sau d'aya, ya kira nasa sau goma. gaskiya na gaji". yaha ce ta juyo tare da cewa " af kwantar da hankalinka mahmud, na kusa daukar mataki kowama ya huta, amma kafin nan sai mun san yadda zamuyi mu shiga jikinsa. Kaga daga nan hakan mu yacimma ruwa, sai mu kashe shi ta ruwan sanyi, ba tare da an zarge muba. shine aure zanje gaban mai martaba nace ya kawo lokacin daya kamata ace ya aje iyali, idan har mai martaba ya yarda zan fadi yarinyar daya kamata ace ya aura"
Mahmud da hankalinsa yadan tashi yace "to wacce zaki zaba masa idan mai martaba ya amince?" zama tai tana kalln sa, tace "ina nufin hajara yar gidan yaya, kasan ta kusa zuwa". Mi'kewa mahmud yai" what umma hajara fa? aa da sake, abinda na dade ina mafarkin samu" yaha tace "kamarya? yace "haba amma ai kinsan nike son wannan yarinyar, gky ban amince a bashi ita ba".

Dafa shi yaha tai tace "karka damu mahmud zanyi maka bayani, ba kana son ganin bayan Abdul-malik ba? to ai dole sai ta wannan hanyar ce ka d'ai zamubi mu samu nasara, yanzu idan mukace zamu kasheshi ba wani dalili. Hakan zaiyi mana wuya, amma idan ya auri hajara zata she'ke mana shi, ba tare da munsha wahala ba. Kuma ba mai zargin mu, kaga zamu dawo mune da fada a gurin mai martaba idan ya zama babu shi. Kayi tunani ta wanna hanya ce ka d'ai zamu iya shafe shi, mu batar da tarihin sa har abada."
Cikin gamsuwa mahmud yace "kuma haka ne fa, kinga riba biyu zan samu, an kashe shi, kuma na auri wacce nake so" cikin jin dadi yaha tace "shiyasa nake yinka. Akwai fahimta, yanzu kaje ka tafi hospital kada lokaci ya kure ma, kuma ka sake tunani akan abin dana fad'a maka," tana kaiwa nan ta wuce shima mi'kewa yai ya fita.



***
Kano farawa, wata budurwace tafe a wannan anguwa ita ka d'ai, kyakkyawa ce ta ajin farko, kuma yanayin kayan dake jikinta bazai nuna maka cewa yar talakawa bace, sai dai ba haka abin yake ba muje zuwa mahaukaci yahau kura.

Wani gida ta bud'a ta shiga, amma iya yanayin sa zai nuna maka cewa gidan hayane, da wata tsohuwa suka hadu zata fita a gidan cikn tausayawa ta kalleta tana cewa "sannu kinji zainab, ki 'kara hakuri komai mai wucewa ne, ki daina sa tunani a ranki in Allah ya yarda wata rana zakiga ribar hakurin ki." Murmushin karfin hali zainab tai tana daga mata kai tace "ngd da kulawarki inna, sai kin dawo Allah ya tsare amin" inna tace tana ficewa. Ita kuma ta shiga gidan, bangare biyu na inna da nasu.
Da sallama ta shiga tanai wa matar dake zaune a gaban kuloli sannu da gida, ko cira kai batai ba balle ta sa ran zata bata amsa. Wuce wa tai ta shiga d'akin ta tana tunanin yaushe ne zata samu canjin rayuwa? rashin iyaye baiyi ba, gashi batasan kowa nata ba, balle ta koma wurin su. Mahaifanta sun rasu bata san danginta ba, sai hjy bilki kishiyar maman ta, wannan wacce irin rayuwa ce ta tsinci kanta a ciki? goge hawayen fuskar ta tai jin bilki na kwalla mata kira, cikin sauri ta fito tana cewa "gani umma".

Tsaki taja "wato zainab wuyanki ya fara 'kwari ko? sbd ke tinkiya ce kullum sai nayi da baki na akan fita da abinci shago saboda kin gado bakin halin uwarki, to wallahi wuya zaki sha a gurina" kuka zainab keyi dan idan akwai abin data tsana a duniya shine ka zagar mata mahaifa.
Bilki tace "inye hamshakiya danna zaki uwarki kike kuka? to ko tana raye zan zageta balle tana bayan kasa, ke dalla tashi ki fitamin da kayan sana'a ta, dan wallahi kikamin kwashe duka zaki mi'kewa tai ta f
ara diban kulolin tana fita dasu, tana shago taga Tanimu ya sauke hindu a mota dan girgiza kai tai cikin takaici, sai bayan la'asar ta koma cikin gida duk da abincin ya kare tun wuri, zaman ta a wajen yafi mata alkairi. Bata kud'in tai dai-dai Hindu ta shiga da bakar leda a hannunta, ta mi'kawa Bilki tana cewa "wanka zanyi in anjima Tanimu zai zo" kallon Zainab tai "ke jeki d'ebo mata ruwa za tai ba'ko, ba irin ki bace mai bakin jini, kuma ki dawo ki dafa mata wannan kazar"
'Kala zainab bata ce ba, ta d'au bokiti tana fita a gidan, bayan ta d'ebo tana shigo wa gidan a zaure suka hadu da Bashir, yana ganin ta cikin murna yace "masoyiya ta dama ke nazo nema, ya gida?" kallon sa tai, cikin takaici taja tsuka, zata wuce ya jawo hijab d'inta. bokitn ya fad'o ya fashe






WASH ALLAH GASKIYA KUNA KOKARI 😥
[11/25, 5:27 PM] Yusrah Musa Abubakar: 👑YARIMA ABDUL-MALIK 👑



💫 *ANNURI WRITER'S ASSOCIATION* 💫

By
YUSRAHMS ABUBAKAR


#YMA

Dedicated to Maman khaleel
Safiyya Aliyu

Ina matukar godiya da nuna kaunarki a gareni MY FEEDOH may Allah bless you and your household wannan page din naki ke daya har zuwa page 20 mallakar kine.

*If you go to the river dont swim 🏊 it can carry you away 🏃.

Page 2


Da gudu Bilki ta fito ganin abinda daya faru yasa tace kan ubancan amma Zainab anyi muguwar yarinya sbd bakin hali saida kika karasa min bokiti to wallahi baki isa ba saikin biyani mayya kawai mitsiyaciya ta karasa maganar tana janta ciki hakuri Zainab ke bata amma wani irin gigitaccen Mari ta sauke mata saida ta durkusa har kasa bisa kafafunta saboda azaba wanda hakan yai daidai da shigowar Inna da sauri ta karaso tana dago Zainab din dake kuka fuskarta tayi ja wani irin kallo taima Bilki mai nuna cewa wata rana zaki nadama tace amma wallah Bilki baki da da'a sau nawa zan fada miki ki daina dora hannunki akan yarinyar nan rashin iyaye fa ba hauka bane kinsan irin bala'in da kike kwasarma kanki kinsan hukuncin mai zaluntar maraya me yasa baki da tunani ko kadan ina tsorace miki ranar da zaki kuka da idanunki Zainab ba yarinyar da za'a wulakanta bace duk abinda ya sameki ki kuka da kanki na fada miki.

Kallon sama da kasa Bilki ke mata tunda ta fara magana sannan tace ahayye nanaye kaji mace da kwarton munafirci meye ruwanki a ciki amma ba laifinki bane da alama yunwa kike ji ga dusa can idan kin gama ci kije ki sha ruwa munafikar tsohuwa kawai tana kaiwa nan ta wuce ta koma ciki.

Da kallon suka bita inda sabo kuma Inna ta saba da wulakancin Bilki ba tun yauba hannun Zainab ta rike tace muje dakina Zainaba ki huta kinji ki ta hakuri komai mai wucewa ne Allah ya jikan Umar da Khadija ameen Zainab ta furta cikin damuwa amma ko babu komai tana samun sauki idan Inna ta wuni a gida.

Yau Yarima ke shirin zuwa kano gurin kakarsa zaune suke a palor mama ta kalleshi tace gaskiya babyna kana da kyau kamar balarabe "harka shirya kenan"? Da kai ya bata amsa taci gaba da cewa Allah ya kare min kai baby inaji a jikina kamar zuwanka gurin ammi alkairi ne tamkar zaka hadu da wani abu dazai saka farin ciki kuma ya zamo maka garkuwa a rayuwarka.

Ido ya zuba mata bayan ya gama jin jawabinta yai murmushi har dimple dinsa na lotsawa amma baiyi magana ba mikewa mama
tai tana kire hannunsa suka fita har mota tai masa rakiya kafin ta...


Read / Download YARIMA ABDULMALEEK

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album