Join Our WhatsApp Group

BAYI MA 'YA'YANE BOOK TWO Complete Hausa Novel Document by BAYI MA 'YA'YANE BOOK TWO


BAYI MA 'YA'YANE BOOK TWO

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 184919



BAYI MA 'YA'YANE BOOK TWO

Reading Time: 15 Hours

Added On: 10, Sep 2023

Author: Jameela Jameey ƴar mutan Kankia ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Manazarta Writers Association

Author Phone : +234 816 050 8316

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 1.03 mb

File Type: txt

Views: 588+

Download: 770+

Last download: 7 hours ago

Description/Story: BAYIMA 'YA'YANE BOOK TWO BY JAMEEY YAR MUTAN KANKIA


*BAYI MA 'YA'YA'NE*

~Touching Heart Story💔😭~


_BOOK TWO_

_By_
*Jameey Yar'mutan Kankia*


*MANAZARTA WRITERS ASSOC*
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
______________________


_Best of 2k21_


بسم الله الرحمن الر حيم



*Wannan Labarin Ƙirƙirarren labari ne kamar yanda kukaji tun a Book One,banyi shi dan cin zarafin wani ba, wanda yai dai dai da rayuwar shi aimin afuwa akasine🙏*



Episode 1&2

Previous on Bayima Ya'yane book one.


Jaruman Sarauniya Zulaiƙa suka gama shiri kowa ya hau saman dawakan su tace.

"Daga nan kufara bin hanyar Masarautar Raifasu bance ku ɓata lokacin kuba."

"Angama ranki shidade haka suka kama hanyar neman Yarima Malik......


Contious of Book two👇🏻


Koda suka fita Masarautar Daborah ba abinda suke shekawa sai gudu saman dawakan su kamar zasu bar ƙasar baki ɗayan ta, basu da buri da ya wuce su dakatar da Yarima MalikusSaif kamar yanda Sarauniya Zulaiƙa ta umurce su....


Itako Bahijja koda aka rufe mata idanu sai ihu takeyi amman a banza basu da niyar sakin ta ganin dagske suke zasu tafi da ita batasan sadda tasa hakoran taba ta gallama wanda ya riketa cizo ba shiri ya saketa da gudu ta runtuma ana kare, aiko suka rufe mata baya, cikin daji tayi batasan inda zata dosa ba duk tsoro yagama cika mata zuciya...

Suko bayin da Yarima Haishir ya turo dan duba masu masaukin da zasu zauna kafin ya shiga cikin Masarautar Raifasu cikin dare, haka suka dawo agajiye, da kallan tuhuma ya bisu ganin damuwa a fuskokin su, tambaya ya jefo masu yace.

"Lafiya naganku haka ya kuka samu Masarautar."? ɗaya daga cikin sune yai karfin hali yace. "Ranka shidade ba damar da zamuyi wani zagaye a cikin Masarautar nan saboda dagani akwai babban al'amari daya faru a cikin ta yanda mukaga bayin Masarautar da dogarawa kowa yana cikin alhini da jimama dagani akwai abinda suke nema mai mahimmanci atare dasu wannan dalilin yasa muka dawo sai komai ya lafa sannan musake komawa, tuba muke ranka shidade."


Wani ƙayataccen murmushi yayi wanda ba abinda ke cikin shi sai tsantsar zalinci da mugun ta ga mugun kuduri iri iri yana saƙawa sannan yace. "Badamuwa mujira zuwa anjiman ba abinda zamu fasa sai munba Sarki Baidulƙais mamaki.!"


Komawa sukayi wajen wani icce inda hadimai suka gyarama Yarima Haishir, ya zauna ba abinda yake tinanin sai yanda zai cimma Sarki Baidulƙais, ya rusa mashi duk wani farin ciki daya tanada na rayuwa....

➿➿➿➿➿➿➿➿

wajen su MalikusSaif sunyi tafiya mai nisan gaske har sun fara hangen garin Zanbi inda suka tunkari Masarautar Raifasu sai murmushi Yarima Malik keyi yana karajin karfi a jikin shi ba wanda idan shi keson gani sai Bahijja.

A wajen Sarkin Yaƙi kuwa suma sunyi nisan gaske, ba inda suka tsaya sai wata magamar hanya wadda ta kasu kashi ukku, duk da wadda suka fito ɗaya tayi gabas biyu kuma sunyi hannun haggo da dama, sai wadda suka fito tayi yamma, Sarkin yaƙi ne ya kalli wani Jarumin su Lurwan yace.
"Kunga munzo magamar hanya ta wace hanya kuke ganin yakama ta mubi dan mu isa da wuri."?

"Ranka shidade inaga mubi ta gabas din nan kodan samun nasara kasan dakatar da Yarima Malik ba karamin abu bane a wajen mu." cewar Lurwan da yagama maganar kanshi na kallan kasa, cikin gamsuwa Sarkin yaƙi yace. "Kwarai kuwa haka za'ayi dan haka mutafi watakil mu taddasu a hanya da alama tanan sukabi duba da yanda sahun dawakai, suka wuce ta wannan hanyar."da haka suka ci gaba daba dawakan su wuta.....


Itako Bahijja tayi gudu harta fara sikewa suma basu fasa binta ba, har suka fara hangen wani karamin kauye a gaban su, koda ta fara hangen gari bakaramin gudu ta karaba addu'a takeyi Allah yasa ta samu wajen ɓoyo dan daganin waɗan nan mutanen so suke su kasheta, tana cikin gudu taji ta banki mutun baya baya tayi zata faɗi taji an rikota da karfi sadda hankalin ta zai dawo taji an kifa mata mari a kunci, a gigice ta ɗago kai ta aza idanun ta kan wani murgujejen bakin mutun sannan ya shaƙe mata wuya da karfin tsiya haki tafara duk idanun ta sunyi waje kamar zata mutu, dai dai nan wa'anda suka biyota suka taddata zubewa sukayi ɗaya daga cikin su yace. "Gurfanai yakara girma ranka shidade kwace mana tayi da muka ɗauko ta harma cizona saida tayi kabamu ita nan mu farke ta kowa yasha daɗi dan daganin ta zatayi daɗi da yawa Oga."
sakin Bahijja yayi ranshi ɓace ya kifama shi mari cikin ɓacin rai yace. "Uwarka ce zatayi daɗi dan taɓewa har yarinya karama ta tsere maku dan kuna dakiƙai inda ta gudu fa?
ya kuke so mugaya mata shikenan aikin da tasaka mu ya tashi a banza a wofi kenan? kana maganar hutawa da yarinya ni ban fiko san hutun ba, ba ace mu taɓata ba kawai so ake mu kasheta!"

koda Bahijja taji ance so ake a kasheta ai take ido ya sake raina fata dan tsoro baki ɗaya ko haɗe yawu takasa gadan gadan sukayo kanta,ta zille ta sake kwasa a guje wannan karon cewa abita adawo da gawar ta, kota wane hali, Baiwar Allah Bahijja harji take ganin ta na neman ɗaukewa dai dai wata bishiya ta faɗi kasa ta bige kai batasan sadda ta suma ba, suko basuji basu gani so suke su kama Bahijja.

Shiko Yarima Haishir ji yayi yana bukatar zagayawa tashi yayi ya tafi wajen wani icce dake bayan su, ya duƙa kenan zaiyi fitsari yaji daf daf anyo kanshi juyawar da zaiyi sai yaga maza guda ukku sunyo kan wata yarinya dake kwance magashiyan kamar marar rai da sauri ya isa wajen yana kallan fuskar ta wani irin faɗuwar gaba yaji ya riske shi ganin Bahijja a sume duk jini ya wanke mata fuska, ɗauko ta yayi yaji ance.

"Kai ɗan saurayi ina zaka kaita miya haɗaka da ita."? Shiko bai fasa tafiya ba, binshi sukayi saidai ya kusa isa inda suka yadda zango wani kato ne ya shako wuyan Yarima Haishir yakai mashi wani wawan bugu a baki take bakin shi ya fashe da jini sannan suka fara dukan shi jin yanda sukai mashi taro yasa shi aje Bahijja wadda batasan inda kanta yake ba, nan suka fara artaba da Yarima Haishir, koda hadiman shi sukaji shiru hanya sukabi suka iske ana artaba da uban gidan su take suka afka akaci gaba da fafatawa, dai dai nan Ogan su shima ya iso ya iske ana dokuwa da yaran shi ga Bahijja kwance ba rai, shima kukan kura yayi ya afka, akaci gaba da artaba da yake ance Sarkin yawa yafi Sarki haka Yarima Haishir da mutanen shi sukai masu ligib yasa aka ɗaure su akatan icce sannan ya koma wajen Bahijja yafara sa mata ruwa bayan ƴan mintoci ta farfaɗo a hankali take binsu da kallo suna ido hudu da Yarima Haishir ta ingije shi zata gudu ya riko ta duk ta ruɗe zuwa yayi yasa aka fara gana masu azaba sannan yafara tambayar s, yace. "Miya haɗaku da Bahijja?" yanda sukaji ya kira sunan ta saida sukayi mamki shiru sukayi haka yasa akaita zanar su sannan Ogan su yace.

"Ance mu satota kuma mukasheta.!"
mamaki ya ishe zuciyar Yarima Haishir yace. "Waya saku miye hadin ku da Bahijja."?

Cikin sarkewar murya yace. "Gimbiya Yazira.!"


Koda kunnuwan Bahijja suka jiyo mata sunan gimbiya Yazira bakaramin mamaki tayi ba, cikin zuciyar ta ko cewa tayi. "Ohni Bahijja na shiga ukku n, ina ganin kaddara mina tsarema gimbiya Yazira da batasan taga ina numfashi mi nayi mata ta tsaneni har haka."? Tana cikin sakar zuci taji Yarima Haishir yace. "Duk akashe su baki ɗaya tunda basu da mutunci kafin su kashe Bahijja."

cikin sune ya ɗuri ruwa, suka fara ahi ita kanta Bahijjar bakaramin tsoro ya kamata ba, tana mamakin yanda kisan ɗan Adam ba komai bane a wajen mutanen nan, bata ida tunanin da takeyi ba taga kan wani ƙasa a ruɗe ta rushe da kuka mai tsuma zuciya saida yasa aka kashe guda biyu.


Sannan yace abar babban dan yakaima gimbiya Yazira labari Bahijja bata mutu ba, sannan yasa akai mashi dukan mutuwa ko ɗaga hannun shi bai iyawa sannan suka koma inda suka yadda zango, itadai Bahijja a ɗarare take duk takasa sakin jikin ta dasu duk da ta taɓa ganin Yarima Haishir, shi kanshi yaga yanda Bahijja takasa sakin jikin ta sai kallan ta yakeyi, itako taki bari su haɗa ido, hutawa sukayi, Yarima Haishir ne yace "kowa yahau doki mu koma gida."

tafiya tayi riba tunda mun samu abin da mukazo nema gashi yazo hannun mu cikin sauki batareda mun sha wahala ba." koda Bahijja taji abinda Yarima Haishir yace taji guiwowin ta sunkara sarewa ashe gudun gara tayi ta faɗa gidan zago shiko Haishir isowa yayi gaban Bahijja ya mika mata ruwa a wata silka yace ta wanke fuskar ta, ansa tayi a ɗarare ta wanke fuska, murmushi ya sakar mata sannan ya nuna mata wani doki yace ta hau su tafi, girgiza mashi kai tayi sannan tace. "Nagode da kuka kwatoni hannun waɗan nan mutanen dan haka zankoma Masarauta ta inda suka ɗaukoni dan inci gaba da hidima ga uban gidana."

Wani irin bakin ciki ne ya kama Yarima Haishir cikin sanyin murya da zai ribbace ta yace. "Da kunnenki kikaji sunce gimbiya Yazira tasa akasheki ke baki tsoron kisa ne."?

Murmushi Bahijja tayi wanda yafi kuka ciwo a cikin ranta tace, aitini aka kasheni aka rabani da iyaye na da Ya Malik dina da duk wani masoyana tuni na mutu dan ba irin azabar da Bahijja bata sani ba.

A zahiri ko cewa tayi. "Inma kasheni tayi bakomai akan hidima na mutu karka kamanta ni baiwa ce ko bakaga kayan dake jikina ba?" Shiko ya kafeta da mayun idanun sh,ko ƙeftawa baiyi ji yake kamar yagan ta jikin shi karfin hali yayi yace. "Bakiso in maidaki Masarautar ku wajen iyayen ki."
Da sauri Bahijja tace."Eh inaso dan Allah."
yanda yaji ta anbaci sunan ubangijin ta, sai yaji wani iri saidai duk daba addinin su ɗaya ba sai yasa takoma nashi addinin, a zahiri ko cewa yayi. "Yawwa ko kefa kibiyoni muje inkai ki Wajen Sarauniya Zulaiƙa kinasan zuwa Daborah."? Wani irin mummunan faɗuwar gaba taji ga baki ɗaya jikin ta yai sanyi tabbas duk inda tasan sunan Sarauniya Zulaiƙa tasan shi saidai ba shakka sunan Masarautar su kenan shiru tayi daka ganta kasan tana nazari, jin antaɓta yasa taja baya ta wurga mashi wani fitinannan kallo, sai ya tsinci kanshi tai mashi kwarjini sosai, murmushi yayi yace.

"Tunanin me kikeyi."?
Ajiyar zuciya ta sauke a hankali sannan tace.
"Shikenan ka tabbatar zaka taimakeni ka maidani wajen iyayena."? Da sauri ya ɗaga mata kai alamar eh, batasan sadda tasaki wani ƙayataccen murmushi ba mai karamata kyau da kwarjini, shiko sakin baki yai yana kallan ta, yanda yaga masifar kyawun ta yakara bayyana itako zuwa tayi wajen dokin da ya gwada mata wani bawa ya iso da sauri ya rike mata sirdi ta hau saijin dadi takeyi zata koma Masarautar su......


Haka suka kama hanya shiko saijin dadi yakeyi cikin sauki ya samu Bahijja zai kaita Masarautar su ya cika burin shi a kanta.
itako anata ɓangaren tanajin dadi ashe Yarima Haishir yasan Masarautar su tana godema Allah da ya kawo shi ya ceceta da haka suka cigaba da tafiya cikin daji hankalin ta kwance....

_Masarautar Raifasu_

A wajen Sarki Baidulƙais kuwa haka dogarawa suka gama zagaye kewayen Masarautar Raifasu basu ga Bahijja ba haka suka koma suka sanar dashi ba labarin Bahijj, bakaramin tashin hankali ya shiga ba, baisan sadda kwalla suka fara sintiri a saman fuskar shiba yanaji yana gani zai rasa abin hutawar shi, wadda ya dade yana mafarki tazama mamora a gareshi.

wani irin wawan duka yakaima iska yana fidda huci tashi yayi ya shige bedroom din shi ya rufo kofa da karfin gaske a zuciyar shi kuwa wani irin wutar shi'awar Bahijja ce ta dinga azazzalar shi jiyake kamar yai tsuntsu ko yasamu Bahijja ta dawo gareshi, magana yakeyi a zuci wanda baisan tana fita ba a zahiri yace.
"Na rantse da girman takobin kakana Sarki Gursu sainayi ajalin duk wanda nakama shi da Bahijja musamman idan zargin da nikeyi ya tabbata gaskia, tabbas saina ga bayan kowaye a cikin su."
faɗawa yayi saman gado kamar karamin yaro yafara kwalla....



Suko su Bahijja tafiya tai nisa itadai batasan inda ake dosa ba saidai tasan dagani Masarautar su tana da nisan gaske, wani wajene aka tsaya dancin abinci da hutawa, itako ruwa ta bukata tayi alwalla sai kallan ta Yarima Haishir yakeyi yaga ta kabbara sallah, wani bawan shine yayi kanta da takobi zai sareta, Yarima Haishir ya banka mashi wani matsiyacin kallo, baisan sadda ya komaba, itako haka tagama sallar ta ko ajikin ta dan basuyi ba sannan yasa aka kawo mata abinci, da takici saitaji wata irin yunwa tafara addabar ta batasan sadda tafara ciba, duk da batajin dadin komai a bakin nata....

_Masarautar Daborah_

Itako Sarauniya Zulaiƙa takai gauro takai mari tarasa yanda zatayi da ranta fatan ta Allah yasa MalikusSaif din ta,ba neman baiwa ya tafi inko har haka takasan ce tabbas ya zubda mata da girma da daraja ace ɗanta Yariman ta magajin ta ace ya ɓata lokacin shi kan neman baiwa.
da haka taji sallamar mijin ta ya shigo amsawa tayi, wanda ya kafeta da idanu yana nazarin ta tabbas yasan matar shi tana cikin damuwa wucewa yayi ya zauna kusa da ita.



Koda su MalikusSaif suka iso cikin garin, ba inda suka tunkara sai Masarautar Raifasu,
ba inda suka tsaya sai wata kofa ta baya, aje dawakan su sukayi Yarima Malik ne ya kalli Huzaifa yace......



_Ƴar Mutan Kankia ce❣️_


Share
Comment
And
Vote
❣️


*BAYI MA 'YA'YA'NE*

~Touching Heart Story💔😭~


_BOOK TWO_

_By_
*Jameey Yar'mutan Kankia*


*MANAZARTA WRITERS ASSOC*
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
______________________


_Best of 2k21_


بسم الله الرحمن الر حيم



*Wannan labarin ƙirƙirarren labari ne kamar yanda kukaji tun a Book One, banyi shi dan cin zarafin wani ba, wanda yai dai dai da rayuwar shi aimin afuwa akasine🙏*



Episode 3&4



"Bai kamata mu shiga wannan Masarautar a sirrince ba yakama mu shiga kai tsaye girman Masarautar mu da karfin ikon mu, ya girmi ace kamar mu munaima waɗan nan kaskantattun boye ba, dan haka mukoma ta babar kofar Masarautar sai mu shiga cikin ta dan ni nan ko airai ko a mutu da haka nazo dan in fanshi Bahijja.!"

kallan shi Huzaifa yayi yana girgiza kai cikin kulawa yace.
"Yarima kenan bai kamata ace mun shiga kanmu tsaye ba karfa kamanta makiyan mune basu...


Read / Download BAYI MA 'YA'YANE BOOK TWO

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album